← Book details Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 31

Sashe 28

Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba kaman zakiyya da take cikin zarin da na sani na hana mijinta hakkinsa kuka take tuk'kuru gudun kar ta janyo hankalin mutane kanta yasa ta mikewa ta shiga part din yah rid tana rusan kukan nadama.

A dai dai wannan lokacin yah rid din ya shigo bangare dan yana da tabbacin 'yammatan na wajen walima kuma akwai abinda zai d'auka a bangaren.

Sai dai me? Precious dinshi ke rizgan kuka ita k'adai tsayawa yayi yana kallonta dan bata san ya shigo ba ya san ba komi ke damunta ba illa kishi da yana da yanda zaiyi ya k'auracewa auran nan da yayi amma ina bakin alkalami ya bushe fadeela ta yi nasaran wargaza mishi farin cikin sa.

A hankali ya k'arasa shiga dakin ya rungumota ta baya yana fad'in "precious ki yafe min bani da wani wayo ko dabaran k'auracewa auran nan fadeela tayi nasara akaina."

Da sauri na juyo na rufe bakinshi da tafin hannuna nace "haba mijina ya kake irin maganan nan bazan tab'a goya maka baya kak'i bin maganan abba in nayi haka na zama butulu tunda nima haka aka had'a ni da kai ba tare da kana so ba kuma ka aure saboda biyayyarka a garesu dan me kuma yanzu dan abin ya zagayo kan fadeela in mata bak'in ciki alhalin annabi yace" _imanin d'ayanku baya cika face ya soma d'an uwanshi abinda ya sowa kanshi__eh na san da zafi akwai kishi but i have to fight dan in samu in k'arfafa maka guiwa kayiwa abba biyayya, amma sai me sai na kasance na k'aurace maka ina horar da kai da abinda baka da laifi ko d'aya akai. Mijina ka yafe min na maka alqawarin zan so fadeela in k'aunaceta zan gujewa duk wata fitina da zai wanzu a tsakaninmi kaima ka min alqawarin riketa a matsayin mata kar ka bari shed'an la'annane yayi nasara akanka wannan karon kar ka bari kuyi irin zaman da muka yi daga farkon auranmu"kuka ne yaci karfina na fad'a jikinshi ina wani irin kuka mai cin rai.

Tsam ya rungumeta ya kasa magana sai ja da idonshi yayi kaman wanda aka yiwa turare barkono ina ma zai samu ya zubar da hawayen nan shima da yaji dad'i ya jawa fadeela Allaj ya isa yafi shurin masaki.

Fadeela ce ta juya a guje tana wani irin kuka dan tun da zakiyya ta fara magana tana tsaye tana jinsu saboda itama gudowa tayi daga wajen waliman saboda tsoro da fargaba da ya cikata.

Sai kuma tazo ta tarar da su a haka wani irin nadama ne ya shigeta mai ta aikata haka? Saboda zunzurutun _hassada_ya Allah kasa mufi karfin zuqatan mu.

Da yah sadiq suka ci karo rik'ota yayi yana tambayanta lafiya?

Fadawa tayi jikinshi tana kuka wanda saida tsigar jikinshi ya tashi jin lallausan nonuwanta da suka mannu da kirjinshi.

Cikin kuka take furta" kaicona yah sadiq kaico da irin halina na son zuciya na biye zuciyata na cutar da baiwar Allahn da bata tab'a nufina da wani mugun abu ba, bata tab'a min ko da kallon banza bane."

"Tir da rayuwata yah sadiq tunda har zanyi k'ok'arin shiga tsakanin farin cikin masoya biyu yah sadiq ka taimakeni ka samowa rayuwata mafita ina tunanin nayi nadama a k'uraren lokaci ban isa in tunkari su abba da batun fasa auran yah rid ba dan ko kad'an yah sadiq bana sha'awar auran yah rid bana sha'awar shiga tsakanin zakiyya da farin cikinta yah sadiq ina so in samarwa zakiyya farin ciki kaman yanda take kokarin samar mi yah sadiq ya zanyi?"

Rabata yayi da jikinshi yana tunanin ya taimaka mata ya taimaki zakiyya da BB d'inshi ne ko ya? Toh shi kuma nashi burin ya kai ina kuma? Rintse ido yayi yana tunanjn mafita.(masu karatu ku bawa sadiq mafita)

SAWWAMA QAWWAMA😘

[10/15, 6:51 PM] Hafsat Abbas: 💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 45.

*
Laugh wan kill me🤣kuna ban dariya kowa burinshi kar ayi wa zakiyya kishiya,kun manta kishiyar nan fadar Allah ne,in ba ayiwa wasu ba dole a ma wasu. To kusha kuruminku wannan page din naku ne masu tsoron kishiya na sadaukar da shafin nan dungurun gum gareku luv u all** 😘😘

**** ***** ****
Shirye shirye ake sosai ji nake zuciyata kaman zai buga sauk'innta d'aya gani ga y'ar uwa rabin jiki duk da k'ank'antar shekarunta ita take k'ara kwantar min da hankali ba dan haka ba k'ila da juriyata ta gaza.

Kaman yanda yah rid yace ana saura sati ya iso lokacin muna zaune a palo ni da salma ina oiling mata dogon gashinta yah sadiq ya shigo na dade ban ganshi ba sai naga ya k'ara min wani girma da kyau kamannin shi da yah rid ya k'ara fitowa.

Cikin farin ciki dan kaman yah auwal haka na d'auke shi komi na zama yau yah sadiq shine sila shine sanadin zuwana kano.

"Yah sadiq idonka kenan rabona da kai tun bikin mu" shiru nayi ganin hankalinahi baya kaina asalima yana can yana kashewa salma ido.

Cikin wasa "yace k'awas kin shigo kano ta dabo kin zaune abin ki"

Dan hararanshi tayi tace "kaji da shi dai ga adda zaki na maka magana kana nan kana neman magana"

Ajiye kwalin da ya shigo da shi yayi ya fara sosa kai yace "ah ah zaki! Zaki! Zakin yaya! Zakin dada! Kina nan abinki"

"Da ina zata je?" Cewan yah rid da ya shigo yanzun.

Da sauri salma ta rufe kanta tare da tashi ta karb'i kwalin jakan hannunshi.

Ni kam kallonshi nake da mamaki kwata kwata bai gaya min zai zo wato gashi ango ko k'wafa nayi cikin raina.

Sunkuyowa ya danyi ya rungumeni a jikinshi tare da manna min peck da sauri salma ta wuce ganin rashin kunyan mijin yayarta.

Yah sadiq kam cewa yayi "ahhhh BB ko kunyan lil bro babu? Kema har dake zakin nan."

Dungurinshi yayi yana murmushi yace" lil bro kuma ga sa ido kuma ka daina cewa matata zaki yayarka ce fa."

Dariya yayi ya hade hannayenshi waje d'aya🙏🏽tare da furta "sorry matar bb"

Murmushi nayi na mik'e na shiga ciki dan lokacin wani suya zuciyata keyi tsananin d'oki har ya dawo ko ce mishi akayi baza a bashi matar ba in ya dawo oho.

Ruwan wanka na hade mishi fitowata daga toilet d'in kenan ya shigo da sauri ya k'araso ya rugumeni yana fadin "how i missed youw wifey"

D'an zame jikina nayi nace "ga ruwa can ka samu kaje ka watsa sai ka ci abinci."

K'ara janyo ni yayi yana shinshina jikina tare da baza min kisses tuni ya fara kashe min jiki.

Zubewa muka yi a gado ya cigaba da hargitsa min lissafi "baby your boobs are getting larger" ya fada a lokacin da yake daura bakinshi a kai.

Numfashina ne naji yana d'aukewa yah rid ya san salon illata zuciyan mutum da gangan jikin mutum yanzu haka zai zo yana yiwa fadeela?"

Wani k'arfi ne ya zo min bam san lokacin da na hank'ad'a shi ba na tashi zaune ina rufe kirjina da hannuwana.

Kallona yayi da rinannun idanunsa da suka kankance saboda jaraba yace "precious ya haka kin san fa nayi kewarki?"

Rigata na d'auka ina mayarwa nace "ka san dai mun bar yah sadiq shi k'adai"

"And so? In mun bar sadiq fa sai bazan keb'e da matata ba? pls come on" ya fadi hakan yana kokarin kuma janyo ni.

Kaucewa nayi na nufi k'ofa nace sai ka fito.

Sake baki yayi kawai ya bita da kallo menene haka kuma precious bata tab'a k'inshi ba "ya Allah help me out" ya furta a fili tare da mik'ewa ya nufi bathroom.

***** ******* *****

Wasa wasa zakiyya taki ba wa yah rid hadin kai tana mishi komi amma tak'i ya kusanceta in ya nemi matsa mata ta saka kuka si kuma lallabata yake yi baya son b'ata mata.

B'angarena na danne zuciyata ina walawala duk wani events nayi k'ok'arin halarta kaman ba ni za ayiwa kishiya ba.

Fadeela ma ta shiga hankalinta ko kad'an bata takaleni ba.

Gobe ne ya kasance d'aurin aure yau za'ayi walima a gidan abba saboda haka dukkanmu muna gidan.

Gaba daya b'angaren yah rid muke har amaren ana yin sallan la'asar aka fara taro.

Amare duk sunyi kyau cikin fararen abaye sun rolling kansu da golden gyale yayin da ni kuma aunty rabi ta sani saka golden color gown na rolling farin gyale sauran mutane kuma ko wacce ta saka royal blue din gown da yellow gyale ,sosai wajen ya k'ayatar.

Malam juwairiyya *Nasiba* k'awar yusra ta musu hanyanta.

Sosai tayi wa'azi ta kuma nishad'antar kasancewan duk wanda ya santa macece mai barkwanci.

Sosai malama zuwaira tayi magana akan hakokin aure da irin fushin ubangiji kan mace mai k'auracewa mijinta.

Tayi magana kan ha'inci, da yanda hassada ke cinye kyawawan aiki, tayi magana ta fadakar sosai wanda sai da jikin kowa yayi sanyi.

Duk da yanda malama zuwairan tayi k'ok'arin sako barkwanci hakan bai hana zuciyoyin mutane cika da tsoro ba.

Ba kaman zakiyya da take cikin zarin da na sani na hana mijinta hakkinsa kuka take tuk'kuru gudun kar ta janyo hankalin mutane kanta yasa ta mikewa ta shiga part din yah rid tana rusan kukan nadama.

A dai dai wannan lokacin yah rid din ya shigo bangare dan yana da tabbacin 'yammatan na wajen walima kuma akwai abinda zai d'auka a bangaren.

Sai dai me? Precious dinshi ke rizgan kuka ita k'adai tsayawa yayi yana kallonta dan bata san ya shigo ba ya san ba komi ke damunta ba illa kishi da yana da yanda zaiyi ya k'auracewa auran nan da yayi amma ina bakin alkalami ya bushe fadeela ta yi nasaran wargaza mishi farin cikin sa.

A hankali ya k'arasa shiga dakin ya rungumota ta baya yana fad'in "precious ki yafe min bani da wani wayo ko dabaran k'auracewa auran nan fadeela tayi nasara akaina."
Chapter 28 · 0% Book details