← Book details Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 31

Sashe 26

Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi tayi a cikin barcin shima murmushin yayi ya sunkuyo a sumbaci bakinta kafin ya furta i love you dearly my flying squirrel.

Hannu yasa ya daga rigarta ya dora hannusa a flat tommy dinta kaman bata da komi lokaci daya ya tuna da fadeela yar lukuta ko makaho ba zai comparing matarsa da wannan kundumar yarinyan ba🤣

Sumbatar cibiyarta yayi ya mike dan ganin lokaci na tafiya.

Yana fitowa daga bedroom din mama na shigowa dan kallonta yayi yace mamah ni zan wuce anjima mustapha ya mayar da ita gida.

Tace bara ta kwana ba girgiza kai ya dan yi yace tana da makaranta gobe ko da shike ba da safe take da lectures ba ta kwana kawai sai goben ni bari in wuce lokaci na kurewa.

Toh Allah ya kiyayye ya tsare sai nan da sati biyun kenan?

Yace sai in Allah ya kaimu ni na wuce.

Toh Allah ya tsare yayi albarka ya bada abinda aka je nema.

Amin ya furta kafin ya fita mustapha ya kai shi airport.

Ban farka ba sai da ana kiran sallar magrib da ciwon kai na farka alawla nayi na gabatar da la'asar da magrib.

Mama ce ta shigo dauke da tray da sauri na tashi na karba tace kin dai samu kin yi sallah gyada kai nayi nace eh ina wasa da yatsuna.

Hannun ta kamo tace diyata ki kwantar da hankalinki kinji kinga condition din da kike duk da dama ni na san baza ki ban kunya ba.

Gyada kai nayi nace inshaa Allahu mama zan kiyayye ba zan dinga daga hankalina ba.

Yauwa yar albarka Allah ya miki Albarka ridwan din ya wuce ai kina bacci kici abinci kije wajen yan uwanki kuyi hira.

Toh nace mata kawai ina mamakin yah rid wato tafiya yayi bai min sallama ba.

Wayata na dauka bayan mama ta fita na danna number dinshi.

Bugu daya biyu yayi ya picking amma sai yayi shiru.

Danna zuciyata nayi na saki murmushi mai sauti nace ba dai fushi mijina keyi dani ba? Dan Allah ya rufa min asiri ya daina fushi dani kar Allah ya kamani.

Ajiyan zuciya ya saki lokaci da ya furta zakiiiiiyyyyyaaaaa i really miss you.

A hankali nima nace i miss you more my hub dan Allah ka yafe min bazan kara ba.

No no no baby ni zaki yafewa ke akayiwa laifi ai ni bana fushi dake.

Cikin shagwaba nace kayi mana bayan ka tafi ko sallama har ma da wani ce min zakiyya ba precious ba.

Dariyan jin dadi yayi ganin zakiyyarsa ta saki ranta.

Hiran soyayyan mu muka sha yana kara kwantar min da hankali nima ina kara mishi kwarin guiwar yiwa abba biyayya ko ba komai daddy ya wuci a kyamaci yarsa.

Shi dai sai dai yace anya zan iya precious.

Zaka iya in Allah ya yarda you are doing it for daddy not her.

Haka dai muka yi sallama yana ta wani turturjewa.

Sallahn isha nayi na tafi dakinmu na da su yusra na zaune ko wacce da waya a makale.

Lokaci daya duk suka yi sallama da samarin nasu suka zubo min ido cike da tausayawa.

Hararansu nayi nace meye haka kallon kuma na meye.

Halima ce ta rikoni ta zaunar dani tace zakiyya kwata kwata bamu san me zamu ce miki duk bamu da masaniya kan abinda fadeela ke shiryawa.

Murmushi nayi me ciwo nace toh meye kuma na damuwa ba dai ya rid bane gata ga shi ai.

Ba tare da na shirya ba na fashe da kuka tare da rufe fuskata da tafukan hannuna.

Kuka nayi me isata suna lallashina fuskata cike da hawaye nace me nayiwa fadila haka duk mazan duniyan nan ta rasa wamda zata so sai mijina.

Yusra a lokacin da nake murnan na samo kan yah rid a lokacin ne tayi sha'awar tarwatsa farin cikina? Duk akan me? Wannan kyaun da nake dashi fa BANI NAYI KAINA BA fa Allah ne yayi ni haka da zata dau kahon zuka ta kafa min.

Rungumeni suka yi suna tayani hawayen yusra tace saukin abin daya yah ba son auran yake ba bata sani ba kanta take shirin muzgunawa dan tabbas yah rid sai yaci mata uwa.

Girgiza kai nayi nace kun manta ne nima da haka muka fara kun manta yah rid ya kini ya nuna min tsana ne daga baya yazo ya soni???

Toh haka itama zai so ta watakila ma fiye da yanda yake sona tunda ita yar uwarshi ce na karasa maganan gwanin tausayi.

Tsaki halima taja tace ki daina irin maganan kema din yar uwarmu ce ai yanda fadeela take takaman ita kanwarshi ce kema haka kike kanwarshi tunda iyayyenmu basu bambanta mu.

Kai kawai na gyada na zame na kwanta dan ni kadai na san yanda nake ji.

Washegari na shirya muka tafi gidana na dauka abubuwan makaranta na muka wuce.

Bayan na fito daga lectures ina zaune karkashin wata bishiya ina cin popcorn sai ga fadeela da wasu kawaye da ta samu a nan makaranta.

Tsayuwa suka yi a kaina tare da kwashewa da dariya daya daga cikjnsu tace fadeela kishiyar taki fa ba laifi.

Hade rai tayi tace eh kam ba laifi amma kyaun nata bai kare ta da komi ba tunda gashi ina kokarin shiga gidan mijinta.

Kwashewa suka yi da dariya dayar tace kai amma an yi kyaun asara ashe dai akwai inda kyau baya amfani.

Mikewa nayi zan wucesu fadeela ta rikoni tace ina kike shorin zuwa zakiyya ai ban gama ba ki shirya karbata a gidan mijinki nan da kwanaki kadan.

Kuma kisa a ranki ni da yah rid auran mu mutu ka raba ne babu rabuwa domin rabuwar mu na dai dai dai da rabuwar zumuncin mu kefa?

Kuna iya rabuwa a ko da yaushe tunda ba uwar da kika hada dashi.

Hannunta na kabe daga jikina nace da alama zuwan da muke yi islamiya raka mu kawai kike yi tunda kika iya mantawa musulmi dan uwan musulmi ne toh in baki sani ba yau ki sani yah rid dan uwana ne kuma mijina.

And da kike maganan zaki shiga gidan mijina toh bismillah gaki ga gidan zuciyar mijina ne sau dai hange daga nesa ke ko hangen ma baza kiyi ba dan yafi karfin ganin ki balle ki shiga.

Hannu ta daga zata mareni runtse idona nayi ina jiran inji saukan mari sai dai shiru.

Bude ido nayi naga an rike hannunta gam..........

SAWWAMA QAWWAMA😘

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 44.

Dago ido nayi dan inga wanda ya rike mata hannu Halima ce rik'e da hannun fadeela.

Cike da bacin rai Halima tace "da alama wad'annan kucakan k'awayen naki sun koya miki shaye shaye"

"Dan kam in ba shaye shaye ta fara ba, ba yanda za'ayi tayi gangancin kai hannu jikin wacce take so precious to yah rid"

Cewar yusra.
"Wallahi kinji kunya fadeela an fadi ba nauyi baki da girma sai na jiki banda rashin girma meye naki na sako wad'annan sokayen a cikin hurumin gidan mu?"

Yusra tace" to ma me zakiyyan tayi mata banda neman magana ? Ita da zaki aure mata miji bata tsokane ki ba sai ke gwana mai d'an uwa"

Cike da rashin gaskiya fadeela ta fara borin kunya " to karya nayi ba d'an uwana bane? Karya ne ita din ba bare bace a cikin mu?"

Cikin daga murya Halima tace " karya kike zakiyya ta wuce bare a wajenmu ko da bata auran yah rid ,ita y'ar uwarmu ce balle tana auran shi har da rabo. To wallahi ki kiyayi kanki in kina son zaman lafiyanki da yah rid gwara kin nutsu kin girmama mishi precious"

Cikin k'araji tace wallahi abinda ba zai yuwu ba kenan wacece wata zakiyya ku take y'ar uwa a gareku bani ba banzaye marasa aikin yi marasa kishin d'an uwa.

Ta ja hannun k'awayenta suka tafi.

Tsaki yusra taja tace " Allah ya sawwake ya shirya"
"Ameen" muka amsa a tare.
Hakuri suka ban nace "hakurin name fadeela y'ar uwata ce ba komai ke damunta ba illa kishi so muyi mata uzuri"

Halima tace "kishi? Wani irin kishi ke da ita wa ya kamata ya nuna kishinshi a zahiri"

Yusra tace " toh ita hankali gareta ko zakiyyan ai baki ga ta biye mata ba" kwafa tayi tace tab wallahi da ta mari zakiyya yau a yau din nan ba gobe ba zan kira yah rid in gaya mishi"

"Da ko taci ubanta karshe ma ya tubure watakila yaki auran dan Allah zakiyya ki daga mishi hankali yaki auran nan ni yau da fadeela son Allah da annabi take yiwa yah rid kuma kuna shiri baza mu kyamaci auran ba tunda itama y'ar uwarmu ce amma ita ba Allah a ranta fitina ce kawai take son tayarwa." Cewan halima.

Ajiyan zuciya na sauke nace "ni kuma bazan kulata ba,ba zan kuma dagawa mijina hankali ba tazo ta zauna Allah ya bamu zaman lafiya ai kowa ya iya allonsa."

"Haka ne Allah ya mana zabi gaba daya ameen".

***** ****** ****

Bayan na koma gida shiru har dare banga fareeda ta dawo ba waya na d'auka na kirata dan jin me ya hanata dawowa tunda na san ta san yah rid ya tafi ko duk shirye shiryen ne.

A lokacin tana zaune da labtop gabanta tana duba lectures d'inta dan ta nan take karatun kafin ta tare a lagos din.

Fadeela kuma na kwance tana chart,wayar fareeda yayi ringing.

Sai da gabanta ya fad'i dan har ga Allah tana tsananin jin kunyar zakiyya wai ace y'ar uwarta ce ta sako ta gaba.

D'aukan wayar tayi had'e da sallama bayan mun gaisa ne nace"ke kuma lafiya ban ganki ba har anyi magrib?"

Inda inda ta fara can sai tace "bari in sa a kawoni" ta katse kiran ba tare da ta jira ansanta ba.

Mtswww wani dogon tsaki fadeela taja kannan ta d'aura da fadin "shegiyar yarinya mara zuciya meye nata na kiranki kuma kije mata gida?"

"Ina ruwanki cewar fareeda ko ke ta kira kuma ma wa ya sako ki a maganan mu ke da ita waye mara zuciya kina neman kai kanki inda ba'a sonki zaki wulak'anta."
Chapter 26 · 0% Book details