← Book details Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 31

Sashe 30

Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cigaba akayi da shagalin biki k'ara sakin jiki nayi aka cigaba da harkoki da ni daman haka Allah ke abin shi da yanzu na d'aga hankalina nayiwa mijina tijara ko danginshi da yanzu na ji kunya.

Anzo tafiya da fareeda nace zan bi sam yah rid ya hana nayi ta kuka amma sai ya fita ma ya barni gaba d'aya ma.

Nima ko na tubure salma ba zata bisu ba dan naga take takenta in ta samu ta tafi ba dawo zata yi ba.

Haka aka gama biki aka kai ko wace amarya gidanta fareeda k'auyan mu aka kaita inda zata yi sati kafin su wuce lagos

Sauran kuma duk nan cikin kano suke zaune muna tare.
***** ***** *******
Cikina ya shiga wata bakwai wanda yayi dai dai da watan salma biyu a kano kasancewan tana hutun GSCE ne.

Yau saura kwana biyu ta tafi sai shirye shirye muke,yanzu ma muna zaune muna shirya kayan da tela ya kawo wanda na bayar a d'inka mata.

Kallonta nayi nace" yanzu salma maimakon kiyi zaman ko anan sai yah rid ya sama miki makarantan cikin anguwan nan ko wace muka gama amma kin ki ko?"

Tab'e baki tayi tace "nifa na gaya miki ba zan iya zaman kano ba gwara min kusa da dadana ke baki zauna a gida ba nima ba zauna a gida ba munta barin dadan kenan? Kuma ma ni ko sha'awan zama garin nan baya bani yanzu ma ji nake kaman in janyo ranan tafiyar"

Harara na balla mata nace kin dad'e baki jawo ba,da ki jawo da karki jawo ranan yana zuwa in kin ga dama ki fi ruwa gudu."

Dariya ta kyalkyale da dan ta san na riga da na k'ulu ne.

Doorbell muka ji hakan yasa duk muka mik'e dan ganin waye.

Yah sadeeq ne had'e rai salma tayi ta gaishe shi kafin ta wuce kitchen abinta.

Zama nayi ina gaisheshi yace " zakiyya irin wannan kumatu da kika ajiye sai ina haka?"

Dai dai lokacin da salma ke ajiye mishi ruwa nace "ai da ban kai matarka kumatu ba"

Dariya yayi kafin ya ban amsa yaga salma na shirin shigewa da sauri yace salamatu zo.

Dawowa tayi ta zauna ido yake so su had'a amma sam tak'i ni dai ina zaune ina kallon ikon Allah.

Ajiyar zuciya ya sauke yace " jiya BB ke gaya min zata tafi jibi wai"

Nace "eh wallahi bata gaya maka ba kenan?"

"Hmm bata gaya min ba ni sam ban san me nayiwa salma kwana biyu ba take wani shashare ni"

Juyowa nayi na kalleta nace ke kuma ta hannun daman yah sadiq me ya had'a ku?"

D'aga kafad'u tayi tace "ni nace ya min wani abu ne ba fa komi"

Da sauri yace " toh ki bari sai wani sati ni in mai dake da kaina kinga yanzu abuja na nufa"

"Ah ah zanje in fara shirin school ka bari kawai driver ya maidani"

To kawai yace amma da ka gani ba haka ya so ba bandir d'in 200 naira ya ajiye mata wai tayi tsaraba sannan ya mana sallama ya tafi.

Kallonta nayi nace "salma akwai wani abu tsakanin ki da yah sadiq ne?"

A firgice ta d'ago tace ah ah me kika gani?"

"Ba komi kawai dai naga yanda yake ji dake ne tun da"

Yamutsa fuska tayi tace "kema ai kin san haka yake shi dai k'ok'arin shi ya ga ya samarwa mutum farin cikinshi duba da yanda kema ya dinga k'ok'akarin sama miki naki farin cikin.tun daga samun makarantar ki har izuwa hana ayi miki kishiya"

Ajiyan zuciya na sauke nace haka ne naji dad'i da ya kasance babu wani abu a tsakaninku kar ya zama na shiga tsakanin farin cikin ku in kuma yace zai had'aku banwa fadeela adalci ba ta guji zama kishiyata ni in had'ata kishi da k'anwata?"

Tab'e baki tayi wanda na lura haka ya zaman mata jiki kwana biyu tace" toh kima kwantar da hankalinki ba wannan batun,ni d'in ma gaba d'aya guda nawa nake da kike wannan maganan?"

Shiru nayi ina kallonta dan ban isa in d'orar da wani abu akan halayen salma ba tunda ba wani rayuwa muka yi ba duk da take y'ar shekaru sha biyar tana da wayo sosai.

**** ******* *****

Na riga na shiga watan haihuwa na cikin yayi k'ato kaman mai d'auke da y'an biyu.

Wata ranan juma@ muna kwance da yah rid bayan ya dawo sallah muna hira.

Shiru nayi da maganan da nake yi ganin ciwon da nake ji tun safe ya tsananta.

Ankara yayi da halin da nake ciki ba shiri ya kinkimeni sai hospital.

Banyi wani dogon nak'uda ba amma kam naji azaba ba,dan kasa kuka nayi wani ciwon yafi gaban kuka sai ido da nake zarewa ina had'a zufa.

D'ana namiji na santalo me kama da ubanshi sak sai haskena da ya d'auko.

Murna a wajen familyn nan ba a magana yah rid tisa ni yayi a gaba yana kallona tare da babynshi ko k'iftawa bayayi.

Ranan suna nace sunan yah sadiq nake so asa dariya kawai yah rid yayi yace saboda ya hana a miki kishiya ko nace "ba wannan ba kad'ai amma yana d'aya daga ciki"

Yaro yaci Abubakar sadiq taron suna yayi goshi dan manya motoci biyu daga hwol ga su fareeda mutanen lagos salma ce kawai bata zo ba wai makaranta.

Y'an uwana sun so tafiya dani mamah ta hana tace abarni wajenta tunda nima na kusan komawa makaranta haka kuwa akayi wajen mama na zauna nayi wanka na.

SAWWAMA QAWWAMA😘
[10/15, 6:51 PM] Hafsat Abbas: 💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 48.

Zauran biebie this page is for una, u gals dey try una dey encourage person make una keep it up

Abubakar bai cika shekara ba na samu wani cikin murna a wajen yah rid ba a magana yace dama yanda ya dad'e bai yi auran nan ba dole y'ay'ansa suyi rushing din zuwa duniya.

Amaren mu duk sun haihu banda fadeela da tayi b'ari.

Fareeda 'yan biyu ta haifa dukka mata intisar da ibtihal Yusra kuma ta haifi me sunan dady ana ce mishi waleed sai halima kuma ta haifo me sunan abba ana mishi inkiya da abulkhair.

Abubakar na da shekara daya da wata bakwai na haifi umar farooq,shima umar bai cika shekara ba na samu wani cikn.

Kuka na saka bayan naga test din da nayi ba zai yuwu ba haihuwa yasa ni a gaba ya hana min karatu cikin kwanciyar hankali in bana da ciki toh ina da goyo bari inje in sami yah rid gaskiya.

Zaune yake yana aiki a laptop kasancewar promotion dinshi ya kusa karkashin jagoranci *GENARAL* *ALIYU* *MUHD* *RUMOH* wanda yake abokinshi kuma me gidanshi inda shi genaral din ke k'ok'arin ganin brigadia general Ridwan ya samu promotion zuwa major general.

D'auke laptop d'in nayi daga gabanshi na had'e rai, kallona yake da mamaki kafin yace " precious ya akayi ne?"

Hawaye ne ya fara zubo min shar shar tuni hankalinshi ya tashi ya kamo ni yana son jin matsalata.

Cike da shagwab'a nace"hayatee gaskiya ni wallahi kana hana min karatu" sai na kuma fashewa da kuka

K'walo ido yayi yana kallona yace "precious ya za ayi in hana miki karatu bayan kin san nafi kowa son kiyi karatun nan duk da takura min da karatun yake yi."

Volume din kukana na k'ara nace " eh mana ba gashi ba kullum sai ka dinga min ciki tun ban yaye yaro ba sai a ganni da wani cikin gashi yanzu ma an kuma."

Dariya ce ta kama shi duk da tsananin farin cikin da yake yi dan ya gane wani cikin ne dani bai hana shi tsokanata ba yace "toh laifina ne ni kadai? It takes two people ayi cikin nan ke d'in ce kullum buqatan ban ruwa kike da na dawo kike mak'ale ni ba dole kiyi ciki ba."

Haushi ne ya kamani ganin inda ya dosa juyawa nayi na fara tafiya ina cewa " toh wallahi ko a zubar da wannan ko kuna daga shi na gama haihuwa in ma zan k'ara haihuwar sai na gama makaranta."

A zuciyeya m'ike ya damk'oni juyo dani yayi ina fuskantarshi idanunshi sun yi ja saboda tsabagen b'acin rai nuna ni yayi da hannu kafin da kyar ya samu ya furta

"Wallahil azim kika yi min sanadin gudan jinina ko kika nemi yin tsarin iyali akan wani banzan karatunki sai na mugun sab'a miki kuma in datse d'an iskan karatun in ga yanda zaki yi"

Ya wurgar dani lokaci d'aya kuma ya taroni tunawa da yayi ina d'auke da ciki fita yayi a gidan gaba d'aya.

Ni kam wani tsoro ne ya kamani ganin ya koma min tsab yah rid d'in da na sani da lalubawa nayi na zauna ina dafe da kirjina,hawaye ma ya kafe a idanuna dan tun bayan shiryawan mu wannan shine karo na farko da yah rid yayi fushi dani haka har yake ja min layi.

Ranan bai shigo gidan ba sai da ya tabbata nayi bacci da ya fita sallahn asuba kuwa bai dawo ba har na tafi makaranta.

Fushi ya tsira sosai sai da na kwana uku ban sa shi a idona ba yammacin ranan ina zaune ya shigo ya wuceni ko kallo ban ishe shi ba.

Tashi nayi na bi bayanshi wani milk kalan yadi naga ya fito dashi mamaki ne ya kamani ko ina zashi da yamman nan.

Fitowanshi daga wankan ya katse min tunani na nufe da shagwaba na karb'i towel din hannunshi ina goge mishi ruwan jikinshi.

Zaunar dashi nayi na d'ane jikinshi na sak'ala hannaye na a wuyanshi cike da shagwab'a na fara magana" haayatee kasan wannan horon ya min tsauri pls kayi hak'uri ko mafarkin k'ara b'ata maka rai ba zan k'ara ba ka yafeni kaji mijina.

Ban bashi daman magana ba na had'e bakinmu ina mishi wani salon da na san ba zai iya resisting ba.

Ai kam tarkona ya kama dan dama na san 'yan kayana shi yasa yak'i yarda mu had'u ya san yanzu zan dawo dashi kan layi.

Ban barshi ranan ya taking lead ba ni na riding abina wanda hakan ya k'ara rikitar dashi.
Chapter 30 · 0% Book details