← Book details Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 31

Sashe 10

Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ya ta sambatunshi shi kadai yana shiryawa, manyan kaya ya saka light blue shada anyi mata karamin dinki ya dauko navy blue din hula ya kafa tare da sa navy blue din takalmi ya daura agogon fata shima navy blue sosai yayi kyau ya haska abinshi.

Yana fitowa ya sameni a zaune a palo ina jiranshi dan ko sukunin yin breakfast ban samu ba saboda doki.

Kura min ido yayi a zuciyarshi yake fadin wai wannan wata irin aljanar yarinya ne wai bata san tana da kyau bane zata wani sha wannan adon.

Sanye take da jan gown yar dubai me fararen stones a jere a gaban rigar da hannun rigar sai ta rollong farin veil ta saka farin heel ga jakarta fara.

Kun san jan abu da daukan ido balle an hadashi da fari kuma a jikin farar mace ai ba a magana ga fuskarta ta sha light make up.

Ajiyan zuciya ya sauke ya nufi table ya zauna da sauri na karasa na serving mishi abinci na hada mishi tea.

Na koma palo na zauna yana daga dining area yana cin abinci idonshi na kaina.

Tsakuran abincin yake duk dadinshi amma zuciyarsa daci take mishi dan ya san duk inda suka gifta sai an kuma kallonta.

Tsaki ya dan ja zuciyarshi na mishi zafi shi yasa fa shi baya son mace mai kyau dan Allah ya gani yana da tsananin kishi.

Wani tsakin ya kuma ja a ranshi yace toh ai ita wannan ba sonta nake ba balle inyi kishinta kawai ona kishin aurane dake kanta ne.

Ke jeki kiyi shigar da kika saba baki da aure ma hijab kike sakawa balle yanzu da aurena dan kin rainani ko kin tashi ko yaya.

Ina zumbure zumbure na mike nayi hanyan danki
Kut ni kike turawa baki da sauri na girgiza kai.

Kwafa yayi yace kar ki wuce wallahi kika bata min lokaci tafiya zanyi abuna.

Da sauri na shige naje na saka riga da skirt din atamfa na daura hijab dai dai guiwa a kai.

Da na fito kallona yayi ya kau da kai yace shegiya ko ya tayi sai tayi kyau.

Dan zaro idona nayi dan naji abin da yace sai ma ya ban dariya.

Ko da muka je bakin mota tsayuwa nayi dan ban san ina zan shiga ba ko bayan da ya saba sani in shiga zan shiga ko yaya oho.

Ganin ya shige yayi shiru ni yake jira ya sa na bude bayan motar da sauri na shige kar in sha rankwashi da safen nN

Kutuman uba waye driver dinki kara zaro ido nayi ina mamakin halin yah Rid din nan da sauri na fito na shiga gaba.

Kamshin motan ya sani lumshe ido a haka muka fita daga gidan idona a lumshe dan kallona yayi yaga idona a lumshe.

Wani haushin kanshi yaji shegiyar yarinya komai tayi kyau yake mata kwafan da yayi ne ya sani bude ido.

Mun hau titi sosai tuki yake cikin kwarewa da burgewa sosai ya tafi da hankalina dan ya min kyau sosai bai cika sa native ba.

Na shagala da kallonshi ina jin komai zan yi dan in juyo da hankalinahi kaina zanyi dan ina jinshi har cikin jinina.

Sosai na shagala da kallonshi shi kuma yana can yana kallon yan waje da suke kalle mishi mata.

Haushi yaji da bai dau mota mai duhun glass ba ai ya san maganin yan iska mai kallon matan mutane in dai zasu fita soja zai jasu su zauna a baya yaga ta inda zasu kalleta😂

SAWWAMA QAWWAMA😘

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 17.

Haka muka isa yana ta wani cin magani ni dai Allah Allah nake yayi parking.

Ko kashe motan bai yi ba na fice na shiga gida da gudu kai kawai ya girgiza yace Allah ya shirya.

Ina shiga duk yan gidan na zaune a palo har da yah sadiq ma shima ya zo.

Oyoyo amarya cewan momy su yusra suka taso suka rungumeni nan na zube ina gaishesu.

Yah sadiq yace zakiyya zakin dada zaki zakin yayah me yah rid yake baki kika yi bulbul haka.

Duk akayi dariya ni kuma na sunkuyar da kai ina murmushi.

Yah rid ya karaso ciki nan yah sadiq ya tashi ya rungumeshi yana fadin oyoyo my BB i miss u.

Shima rungumeshi yayi yana dariya yace lil bro yaushe ka shigo haka?

Yace wallahi tun jiya BB yanzu nake tambayan zakiyya me kake bata ne haka tayi buleliya.

Kunnanshi ya kama yace lil bro baka da kunya matata ce buleliya kake kiranta da sunan ta gatsau( Ridwan dan basaja🤣).

Dariya duk aka yi a palon ban da mu uku da muka san basaja ne kawai.

Kama kunnuwanshi yah sadiq yayi yace afuwan BB aunty zakiyya afuwan ya juyo gareni rufe idanuwana nayi da tafukkan hannuna na boye a bayan Halima.

Haka muka zauna ana ta hira har aka kira azahar duk muka watse.

Muna shiga daki yusra ta ja dogon tsaki tace yah rid makiri ne ji yanda yake wani nunawa kaman ya damu dake.

Tabe baki nayi na shiga toilet abuna na dauro alawla.

Bayan mun iddar da sallah ne yusra taje debo mana abinci da ta dawo tace inje mama na kirana.

Na tashi naje zaunar dani tayi tace zakiyya kin san dai ban daukeki a matsayi suruka ba asalima tun da aka kawo ki gidan nan nake jinki kaman yar da na tsuguna na haifa.

Na dan gyada kai tace good abin da nake so dake shine kiyi kokari ki dinga sanar dani duk wani damuwanki.

Ki fada min ya yanayin zamanku da Ridwan yake ina fatan bai cutar dake??

Ni duk wannan kulawar da yake nuna miki a gaban mu ban gamsu dashi ba ki gaya miki baya miki wani abu dai.

Kasa nayi da kaina ina tunanin in gayawa mamah tsiyar da yake tsula min ne ko kuwa.

Kai fada mata bashi da amfani hakan na iya kara janyo min tsana a wajenshi.

Gwara in dau makaman yaki da kaina ba wai in dinga hadashi da uwarshi ina bar mata yakina ta min ba....

Zakiyya ina sauraronki ta dawo dani daga tunanin da nake.

Nace ah ah mama ba komi wallahi ba abinda yake min yana kokarin kyautata min.

Mamah ta sauke ajiyan zuciya taji dadin abinda zakiyya ta fada mata ta tabbatar zakiyya matar rufin asiri ce dan yusra ta gaya mata duk abin da yayi a gabansu.

Ta sauke ajiyan zuciya a ranta tace Ridwan bai san an mishi gata ba.

Ta tashi tace ina zuwa dawowa tayi da wani jaka ta zauna tace tashi ki dauko cup da wani jug a cikin fridge.

Na mike na dauko jug din a fridge dinta na kawo cup din.

Ta zuba min markadadan kankana da yasha dabino da kwakwa da madara a ciki na sha.

Tace ki shanye wannan kafin ki tafi kuma kema ki dinga yiwa kanki kullum har shima ki dinga hada mishi nace toh.

Jakan hannunta ta bude ta dauko katon goran swan ta zuba min zuma ne shima me kyau shima da alama da akwai kwakwa da dabino a ciki shima ta zuba min cup na shanye haka ta dinga bani hadehade ina sha.

Daga karashw ta tashi ta dauko min wani hadaden pepper soup da yaji hadin magani amma an tace baza kace da ruwan magani ma aka dafa ba tace in cinye.

Ina cikin ci su yusra su ka shiga kutumelesi lallai yarinyan nan wasa tare ci bambam ta kai hannu zata dauka mama ta buge hannun.

Halima tace wallahi mama wannan son kai ne kin kunshe yarki a daki kina bata kayan dadi mu an ware mu.

Tace eh in kunji haushi kuyi aure haka sukallo naci na rage mama ta ajiye min sauran tace da la'asar na karasa haka aka yi kuwa.

Da dare ma wani hadin naman ta bani na ci na kora da ruwan kankanana.

Sai tara muka bar gidan muna shiga gida kowa dakinsa yayi.

Da safe da na tashi akwatin english wears dina na sauko na bude hadaddun english wears din da aka cika min na bi da kallo.

Haka na dinga dagawa ina kallo daya bayan daya ni kunya ma suka dinga bani.

Daga karshe dai na dauko wata purple gown dogo har kasa amma bashi da ko hannu vest.

Na saka boobs dina ne naga ya wani dago saboda karfen dake jikin breast curve din gashi rigan silk ne ya bi jikina.

Kama kaina nayi a tsakiyan kaina in a pony tail style light make up nayi na saka slippers.

Na wuce office dina wato kitchen simple breakfast na hada mishi likewise men dinshi.

Ni kuma na dama oats na zauna a palo ina sha sai gashi ya fito sanye da 3 kwata da bakar body hug shi dai irin suturunshi kenan

Kamshin gidan da na girkinta ne ya bugi hancinshi dining ya nufa ya ja kujeran dining din.

Motsin kujeran ne yasa na san ya fito da sauri na taso na nufa shi daskarewa yayi a wajen lokacin da ya hango fadadden hips dinta ke juyawa?

What the hell ya furta a kasan makoshinsa karasowa nayi na tsuguna a gefen kujeransa nace ina kwana yah.

Idonshi na kan boobs dinta da suka taso adams apple dinshi sai up and down yake😜

Kara maimaitawa yayi gyara muryansa yayi yace lfy murya a cushe

Mikewa nayi na fara serving dinshi shidai ya kafe idannunshi akan boobs dina dan kifowa nayi kaman zan fadi sai ga fuskarshi a tsakiya kirjina hannuna a bisa kafadunsa.

Shi kanshi baisan lokacin da ya rike kugunta ba ya kara tura kanshi a cikin kirjinta yana inhaling kamshinta.

Ganin yana shirin fito min da boobs waje yasa nace wayyo yah zafi da sauri ya sakeni yana mai tsanan kanshi.

Tunkudeni yayi da sauri ya nufi dakinshi kanshi ya rike da hannu biyu ya illahi me na aikata ? Yarinyan nan zata rainani na rabi jikinta.

Shegiya jarababbiya wallahi sai na ci ubanta wato ita zata seducing dina ko yayi kwafa.

Junior ya kalla yanda yayi attention ranshi ya kara baci ji yake kaman ya kama ya karya kasa kasa yace kai dai baka da zuciya yana hararan junior 😜😝

💖BANI NAYI KAINA BA💖
Chapter 10 · 0% Book details