← Book details Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 31

Sashe 2

Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Makaranta na da tsada sosai amma duk bayan shekara biyar suna bawa 36 state na Nigeria scholarship dai dai this time Zakiyya is the luckiest a plateau state.

Hawaye ne ya kara zubo min yanzu shikenan na rasa wannan daman sadeeq ne yace no no daina kuka zamu samu yayah sai kije ki zauna a gidanmu ki dinga zuwa tare da kannena.

Wani sanyi ne ya ratsani duk da bani da tabbacin yayah zai bari, illai kuwa yaya yace sam bai san wannan zancen ba yace taje ta shiga makaranta irin nasu na ya'yan talakawa.

Ba yanda basu yi da yayah ba amma sam yaki sadeeq baiwa kowa sallama ba ya dau mota sai kano.

Bai isa kano ba sai da akayi isha kasancewan bai taso da wuri wajen abban shi ya fara shiga aiko yayi sa'a yana tare da daddy kaninshi.

Bayan sun gaisa daddy ya kalleshi cike da mamaki yace babana me ya kawoka gida a wannan lokacin?

Ya sunkuyar da kai tare da sosa keya da mukullin.motan shi yace wallahi daddy wata yar matsala ce ta taso.

Abba yace tohhhh matsala dai bata wuce ta kudi me yasa baka yi waya an turo maka ba

Kara sunkuyar da kai yayi yace abba ba matsalan kudi bane ina wannan abokin nawa da nace muku yana taimaka min sosai daddy ai kai ka ganshi.

Dadyn ya gyada kai yace eh haka ne wani abu ne ya sameshi

Yace ah ah dama......... Ya kwashe komi ya gaya musu.

Abba yace toh yanzu kai me kake nufi so kake mu daukota mu kawota gidan mu kai ka tabbatar da halinsu ne.

Daddyn ne yace Alh tabbas naga yaron kuma na yaba da halinshi duk da ba a shaidan dan mutum amma the boy look innocent.

Abba yace toh shikenan tunda kace haka gobe tunda Saturday sai ka bishi ka lallabi mahaifinsu.

Yace toh shikenan Allah ya kaimu,suka amsa amin sadeeq ya runsuna yayi godiya kafin ya shiga cikin gida kowa sai murnan ganinshi yake ba kaman BB(big bro) dinshi da shima ya dawo weekend sai fadi yake lil bro naji dadin ganinka it has being quite long da na ganka hope kana karatu.

Shagwabe fuska yayi tare da rungume dan uwanshi yace i miss u too BB.

Dan patting dinshi yayi yace kar ka damu zan nemi transfer zuwa rukuba barrack na jos sai ka dawo wajena kawai da zama ya fadi haka yana jan hannunshi zuwa side din su.

Dariya sadeeq yayi yace ahhhhhh yayah sai dai ka dinga zuwa kana duba ni dan tsakanin rukuba barrak da main camp akwai shegen nisa.

Yace ok we will see about that muje mu samu mu huta nima dazun nan na iso.

******* ******* ********

Washegari ko daddy da sadeeq suka dau hanyan jos sammako suka yi saboda haka kafin azahar sun isa hwol.

Sun ko yi sa'an samun yayah a gida abin mamaki kuma ashe daddy shine mutumin da yayah ya taimaka ya bawa kyautan kayan lambu.

Gaisuwa suka yi sosai na mutunci kafin daddy ya fada mishi abin da ya kawoshi

Murmushi yayah yace alh banki ta naka ba amma ita zakiyyan wata irin yarinya ce me kawa zucin gida ba lallai ta yarda da zaman can ba.

Daddy yace ai malam annabi yace a nemi ilimi ko da a birnin sin ne kuma can kanon akwai yarana da yaran dan uwana sa'o'inta kuma suma duk Jss one zasu shiga....... Da kyar da sidin goshi suka shawo kan yayah ya yarda amma sai ana sauran sati a koma makarantan yayah da sadeeq zasu kawota.

Daddy sai godiya yake yi kaman shi aka yiwa abu, har abin ya bawa yayah mamaki har ya dinga jinjina irin karamcin bayin Allahn nan.

Kayan lambu ya shiga gona ya hadowa daddy sosai har da su timatir daddy yayi ta godiya har ya tafi akan sai sun kawo zakiyyan.

TAFIYAN DA YA ZAME MIN MAFARIN MATSALOLINA.

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 3.

Yau ce ranan tafiyarmu duk murnan da nake yi da dokin zanje makarantar da nake so,sai na tsinci kaina da rashin son barin mahaifata.

Kuka nake yi sosai haka inna da salma kaman wacce aka ce bazan dawo ba in na tafi.

Dada dai kam baza ka iya gane yanayin da take ciki ba haka na barosu.

Ni,yayah da yah sadeeq da ya auwal ne muka yi tafiyan.

Tunda uwata ta haifeni ban taba zuwa wani gari ba banda cikin jos sai ko bauchi wajen babban yayarsu dada hajja da take aure a can.

Tafiyar tayi min nisa da rashin dadi saboda rashin kyan hanyan saminakan nan.

A galabaice nake lokacin da muka isa garin kano,sosai garin ya min kyau ya kayartar dani.

Manyan idanuwana na fito dasu sosai ina ta kalle kallena zuciyata sai tsinkewa take yanzu a wannan garin zan yi rayuwa?

Ban kuma tsinkewa da al amarin ba sai da muka zo wani tabkeken gida bani kadai ba hatta yayah da yah auwal sun kadu da ganin girman gidan da haduwarsa.

Tuni yayah ya fara dana sanin amincewa da zuwan wannan gidan gashi shi yanzu ba zai iya janyewa ba coz he is man of his word.

Yah auwal ma cike yake da mamaki duk da ya san su ya sadeeq masu kudi kama da yanda shi kwata kwata bashi da matsala irin ta dalibai tunda shi har motan hawa yake da ita kirar civic 2 door amma bai taba tunanin suna da kudi haka ba.

Sauka sosai aka musu a gidan guest room aka kaisu,suka cika cikinsu da abinci kala kala da aka tanadar musu.

Bayan sun kammala sunyi sallah daddy da abba suka shigo aka sake sabon gaisuwa kafin yayah ya damka musu amanata suma suka karba.

Yaya cewa yayi baza su kwana ba a yau zasu tafi ba yanda abba bai yi da shi ba cike da ladabi (kasancewar duk zasu girmeshi) yayi musu bayanin yana da harkokin da zai je ya duba ga dalibanshi bai ce musu zai kwana ba.

Haka suka fito musu da tsarabar da muka kawo musu na kayan gona da su daddawa kuka kubewa da sauransu.

Su yah sadeeq ma sunce ba zasu kwana ba dan suna da test ranan monday gwara suje suyi karatu.

Haka suka tafi suka barni ina sharan hawaye shiga dani cikin gidan suka yi tare da kirawo matan gidan.

Alh abdullahi shine asalin sunan abba yana da matan aure 2 haj Hauwa itace matarsa ta farko tayi haihuwa 3 basa dadewa suke rasuwa a na hudun ne Allah ya tsayar mata inda ta haifi danta namiji RIDWAN a lokacin safwan(daddy) shima yayi aure inda ya auri sadiqa ta haifa mishi Ibrahim tsakanin Ridwan da Ibrahim wata bakwai ne Ridwan ya girmi ibrahim.

Bayan Ridwan haj hawwa sai ta kuma haifan rabi bata dade da haihuwan rabi ba alh abdullahi ya dada aura ya auri haj maimuna shekarn rabi biyu haj maimuna ta haifi sadeeq sai mustapha sannan sannan ta haifi shafa shekarun shafa uku ta rasu.

Ita kuma haj hauwa tun bayan haihuwan rabi bata kuma haihuwa ba sai suka zo suka samu ciki a lokaci daya da ita da haj maimuna da haj sadiqa matan daddy itama lokacin ta haifi yara biyu bayan ibrahim Aisha da kasim.

Haj sadiqa ce ta fara haihuwa inda ta haifi yan biyu fareeda da fadila, satinsu biyu haj hauwa ta haifi yusra kwanan yusra talatin da hudu haj maimuna ta haifi halima wanda sune sa'o'ina.

Dakinsu yusra aka saukeni kowa sai yabon irin kyau na yake yi kowacce tana so in kwana a gadonta.

Mama ma(haj hauwa) sai nan nan take dani haka momy kowa burinshi ya faranta min dan in sake a gidan.

Washegari mama tasa muka shirya muka je gidan haj mahaifiyarsu abba ta ganni daga nan muka wuce gidan daddy

Su fareeda sai murna suke da zuwan mu da zamu tafi ma dagewa suka yi sai da suka biyomu.

Sosai na sake da yan gidan bani da matsalan komi har abba yasa yah mustapha ya cike min form din islamiya.

Ba aji daya aka sani da su yusra ba kasancewar na musu nisa su suna aji daya ni biyu.

An koma school daddy yaje ya daidaita min komi muka fara zuwa dukkanmu har su yah mustapha driver ke kaimu.

Haka rayuwa taci gaba da garawa bana zuwa gida hutu sai in anyi hutun 3rd term saboda islamiya yah sadeeq da yah auwal su kan zo weekend wani sa'in in anyi hutu kuma kullum muna tare da yah sadeeq yana bani labarin yan gida.

Mun shiga Jss 3 lokacin shekarun mu 13 alamomin girma sun fara bayyana a jikin mu su fareeda sai rawan kai ya karu an fara zama yammata.

Muna zaune a dakinmu har dasu fadila muna shirya irin ankon da zamu yi tunda bikin yah ibrahim ya kusa ko ince suna shiryawa danni da ido nake bin su.

Fadeela ce tace wallahi kar mu yarda muyi anko da kowa gamu nan har biyar muyi ankon mu daban kawai mu fito a kannen ango abinmu.

Shewa suka yi dukka yusra tace daddy zamu je mu sama ya bamu kudi muje mu dirji swiss less a gidan aunty rabee kasancewar ita kasuwanci take daga dubai zuwa india.

Halima tace kin kawo idea ai ba karamin casu zamu sha ba wannan bikin dan ma wannan a takuran na nan dawowa.

Sai kuma duk jikinsu yayi sanyi suka hada rai yusra tace ni wallahi dama a ta turashi kasashen wajen ya daina zaman nigeria kwata kwata.

Fadeela tace hmmm yah RIDWAN ko masifa carab halima tace ko jaraba ba ni duk shekara ukun nan da yayi baya gida ko kadan ban yi missing dinshi ba.

Yusra tace missing dinshi ai sai yah sadeeq dan shi dama in kinga rahamarsa toh ya sadeeq na wajen ko yah ibrahim, ya ibrahim din ma ai dan bai mishi da wasa ne shi shegen son girmanshi ne yayi yawa.

Fareeda tace toh ba dai yaga shine babba dukka ba shi yasa yake mana mulki.

Su aunty Aisha dai sun huta da suka yi aure abinsu Allah nima ina gama secondry aure zanyi.
Chapter 2 · 0% Book details