← Book details Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 31

Sashe 11

Bani Nayi Kaina Ba Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

By Sawwama A.

Page 18.

Fuuuuuu yayi waje ina jin motsinshi na fashe da kuka ina rike da boobs dina dan na san wani jarfan ya zo min.

Turus ya tsaya yace ke lafiyarki? Yarfe hannuna na fara in tallabe da boobs dina da dayan. Hannun

Ina shesheka nace yah ba kai bane ka danne min.

Juyawa yayi da sauri ya koma dakin dariyane ya cika min ciki da gudu nima nayi dakina ina tikan dariya.

Shi kam yana shiga dakin kanshi ya dinga bugawa da jikin wardrobe yace lallai yarinyan nan tatacciya banda fitsara wato sai ta tuna mishi ya tura fuskarsa a tsakankanin boobs dinta kwafa yayi ya koma ya fada kan gadonshi ya kwanta.

Ni kam dariya naci na gode Allah sannan na tashi na je tattara gidan table na kalla na tuna yah bai yi break ba wani dariyan ne ya kufce min naje na gyara kitchen na koma dakina zuciyata fes na dau wayata na hau watsapp na kutsa groups din da aka sani.

Abin mamaki ya bani ganin yanda yanzu ba kunya mata basa barin kansu ya kulle ko da yanda naga ko labarI za a rubutawa sai an sa harka.

Lallai a wannan lokacin duk macen da ta gagara gyara gidanta ita taso dan akwai alternative da yawa da zaka samu solution.

Sai azahar na tashi nayi sallah na canza kayana zuwa wondo 3 kwata da ya rike min hips kyam.

Sannan na dau karamar half vest na saka na sake gashina na nufi kitchen dan daura girki.

Da sauri nayi na wadancan kartin sannan nayi namu murmushine kwance a fuskata ina tunanin ya zamu karke yanzu kuma.

Ina cikin setting table ne ya shigo daga masallaci dariyane ya kubce min ganin yanda ya wani hade rai.

Harara ya galla min yace ke dan ubanki waye sa'anki ubanwa kikewa dariya juyawa nayi da sauri dan wani dariyan ke son kubce min.

Shi kam wani yawu ya hadiya da bai shirya hadiyewa ba ganin hips dinta cikin wannan 3 kwatan kut lallai yarinyan nan munafuka ce kullum zaka ganta sum sum a cikin hijab kaman mutuniyar arziiki Ashe itama shedan din kanta ne.

Juyowa nayi ganin ya shagala da kallona yasa na kara juya mishi su ina cigaba da abin da nake yi.

Dan juyowa nayi na dan kankantar da ido nace yah lunch is ready.

Da kyar ya tattaro kuzarinsa ina kallo Adams apple dinshi na up and down ya karaso table din ya zauna yana zabga min harara.

Dan durkusowa nayzan serving dinshi cikin sarkewan murya yace malama matsa min zan sa da kaina dan matsawa nayi ina toshe bakina dan na san boobs dina da suke tsokale mishi idone ya sa yace in bari in ko haka ne da sannu zan raba kaina da aikin bautan da yakw sani.

Komawa nayi zan wuce palo in ya gama inzo inyi nawa lunch din

Ke! Aljana zonan sum sum na karaso zan durkusa yace zauna.

Na dan dofana duwawuna yace ke dan ubanki shekararki nawa?.

Nace 17 da wata tara... Ban gama rufe baki ba yace la ila ha illallah shine kika iya wannan karuwancin uban wa yace ki dinga sa kananan kaya agidan nan?

Shiru nayi ina tunanin karyan da zan gilla mishi dan tabbas in banyi da gaske ba sai ya rushe min plan.

Ke ba dake nake ba kika kafeni da shegun mayun idonki.

Hannuna na cusa cikin karkashin gashina na tsinci muryana nacewa mamah ce tace in dai ina gida kayan da zan dinga sawa kenen da nace mata ba zan iya ba tace toh in bansa ba bata yafe min ba na karasa fadin haka ina zazzare ido dan ni kaina nayi mamakin ta inda karyan ya fito.

Kure ni yayi da ido yana tunanin anya kuwa ba karya nake ba sai dai ai kowa ya mata shedar arziki kuma sarai ya san mama zata rina kwafa yayi ya fara cin abincinsa.

Ni kuma na cigaba da zama zuciyata na lugude dan dagowa yayi ya hararen yace uban me kike kallona sai na kware wai ke baki san kaifin wadan nan idanuwan naki bane me kaman ball ko da yake dole yayi kaifi tunda ke mayya ce.

Kuyi hakuri da sawwama qawwamanku😘

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 19.

UP UP AUNTY ZUWAIRAT MAHASSADANKI FADAWANKI ALLAH YA KARA DAUKAKA KI AMEEN

Tsam na mike na shige dakina ina tabe baki sai da na tabbatar ya gama naje nayi nawa break din na kara kimtsa gidan.

Wayata na dauka dan yanzu na samu aikin yi ina ta bin chart din da akayi bani nan.

Haka muka dinga yi da yah Rid kai daga baya ma sai muka fara wasan boye baya bari mu hadu.

Yau kwanan mu hudu bamu hadu ba ni kuma wallahi na gaji da shirgawa wadancan kartin girki sai kace wace tayi auran gidan yawa.

Na kudurta niyyan yau zama zanyi ba zan kai musu ba zan jira sai ya fito in dau mataki murmushi ne ya subuce min tuno abinda na shirya.

Shi kam a bangaren ridwan wani hali yarinyan ke sashi shi ya san he is a lust but he always take control over his feelings sai dai yanzu abin na neman gagaranshi akan yarinyan nan.

Gata shegiya kullum yariyan is adding salt to his wound kara daga mishi hankali take wani sa'in in junior yayi attention ji yake kaman ya kurma ihu ya sha maganin har ya gaji.

Shi yasa ma ya kauracewa ganinta dan tabbas yana ganinta junior ke attention shi kunya ma yake ji ko tana ganin alamun junior.

Ko yanzun da ya kaurace mata ba wai yana samun sukuni bane wani sa'in gwara ma ya gantan ko ba ko mai zai samu relief sai dai yana ganinta sai dai in bai kadaice ba surarta tyi ta mishi gizo kenan.

Yunwa ce ta adaddabe shi ya kalli time tsaki ya dan ja bari in yi sauri in je tunda na san yanzu 13 ta riga ta shiga dakinta.

Sai dai me turus yayi lokacin da ya hangota a hakimce sai da gaban shi ya fadi.

Tasowa nayyi na dan durkusa a gabanshi ina kwana yah.

Ya illahi wannan shedaniyar yarinyan yau duk da ta saka dinki amma anci mutuncin material din boobs dinta kaman zasu faso waje.

Makut ya hadiye yawu yace lafiya kafin ya juya ya janyo kujera ya zauna.

Tun ranan da ya cusa kanshi a kirjina ya yaye min sa mishi abinci.

Kitchen na nufa na dauko katuwar flask din sojojinshi nayi hanyan waje.

Abinci ya dauka zai kai baki bai san lokacin da yace ke ke ke dan ubanki ina zaki je haka.

Na juyo a dan razane nace yah abinci zan kai musu tunda kace kar su shigo cikin gidanka.

Wani muzurai yake yana hura hanci yace toh shine zaki je a haka tsaya ma tukun kullum haka kike kai musu?

Cikin rawar jiki nace eh yah a wannan flask din nake kai musu sai in dawo in dau su plate.

You know damn well am not talking about the goddamn food ya fadi hakan cikin tsawa tare da buga table da hannunshi tuni ya'yan cikina suka kada ganin yanda ya rikide tashi daya idonshi yayi ja jijiyoyin kanshi da na hannunshi sun tashi haka kike fita ki kaiwa wasu katti abinci?

Wai yaushe kika fitsare ko dama sa hijabin na munafurci ne munafuka kullum ko a gida da hijab nake ganinki zamanin da baki da aure ma kenan sai yanzu dan rainin wayo.

Kinji na rantse na kara ganinki kin fita da irin wannan shigan sai na lahira ya fiki jin dadi sai na kona fuskar da kike takama da ita in sabule fatar da kike ji da shi.

(Ko ya zaiyi da boobs din da hips oho🤔)

Kuma ki ajiye food flask din nan ke in kara ganin ma kin dafawa wani shege abinci a gidan nan ki ga get out of my sight my friend.

Da gudu nayi hanyan dakina ina haki zuciyata fal da farin cikin samun sa'a lallai mama tayi gaskiyan cewan zan juya yah Rid a sannu.

Shi kam duk uwar yunwan da yake ji haka ya kasa cin komi flask dinsu ya sunkuta yayi waje ya kai musu ya kuma basu kudi su je su saya duk abinda suke buqata na girki su dingayi da kansu ya kuma gargadesu da in yaga idon wani kan matarsa sai ya kwakuleshi.

Key ya zara ya bar gidan yana fita ibrahim ya kirashi akan yazo ya sameshi a danladi na sidi dan Allah akwai case.

Can ya nufa gidan wani abokin ibrahim din abinda ya ji shi ya kuma daga mishi hankali.

Matar abokin ibrahim ke cin amanarsa da drivern da shi ya dauko mata shine suke son rid din ya sa a koya mishi hankali.

Sai yamma ya dawo ranshi a jagule ranan sigari ya busata ba adadi tun safe ba abinda ke cikinshi sai hayaki.

Yana shiga gidan dakinta ya nufa.

Lokacin wanka na fito ina sa bra ya kwankwasa ya shigo halin da yake ciki yasa ko sha'awa bata bashi ba.

Gobe zan wuce bana buqatan in kara ganin kin fita har sai na dawo zan tafi da drivers dinki kafin in san yanda zanyi.

Toshe hancina nayi ina gyada kai saboda yanda ya cika min daki da warin taba.

Murmushi yayi ganin halin da nake ciki yazo ya tsaya a gabana ya daga tabar da hannunsa yace baki son warinta? Wowwwww.

Ya mat wani zuka ya busa a fuskata tuni na fara tari zuciyata na tashi juyawa nayi da sauri ya damko hannuna yayi wani murmushin mugunta yace hmmmm da show is about to begin ya sake ni ya fita.

Kashe AC nayi na bude windows dina na fesa ai freshner na kunna burner na sa turaren wuta sai a lokacin na ajiye numfashi

SAWWAMA QAWWAMA😘

💖BANI NAYI KAINA BA💖

By Sawwama A.

Page 20.

This page is dedicated to all my fans, luv u very plenty.

******* ******* ******-

Washegari ban ma san tafiyanshi ba dan sammako yayi sai tashi nayi babu shi.

Na koma normal life dina sai kewarshi da nake yi in na zauna ina tuno dramern mu in ta dariya kaman mahaukaciya.
Chapter 11 · 0% Book details