← Book details Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 26

Sashe 25

Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hakan ya saka ta saki ranta ta shiga aikinta da kazar kazar dan su yi su kamala, suna yi suna tambayar Lami irin abubuwan da Mom din ke yi ( iyaye mata, mu kula, kana da shi ko baka da shi idan baka koyawa yaron naka ya wahala ba, idan baka koya masa abubuwan ba, ba lale ne ya je gidan hutu ba, kuma yau ko gidan hutun ya je zai so ace shima yana shiga kicin dinsa yana sarafawa mijinsa kalolin girkin da zasu kara shakuwa a tsakaninsu ba wai kawai mai aiki ya girko ya kawo masa ba, idan yaron naka ya horu da wahalar tun a gida, aikace aikacen ku, wankinsa, du inda zai je ba zai sha wahala ba, sannan kai kanka sai dai a bika da adu.a, Allah ya sa mu dace)

Dankalin nan suka soya, bayan sun yiwa zabin nan suyar sama sama inda suka yi wani taushi, sai vinaigrette, sannan suka hada jus na kwakwa da madara pink suka markade kwakwar suka tace ta tas sannan suka hadeta da madarar nan sai kankara da dan siga da suka hada domin Mom bata hada jus da irin kayan kanshin nan ,

Lami ta jera masu saman katon plat suka kama suka fito

Direct wajen table din suka kai suka ajiye wanda su Mom suka bi su da kallo, a can kassan zuciyar Mom tana jin wani irin farin ciki marar misaltuwa, tana ta faman yi masu adu.a sannan tana so ta dandanna girkin su

Kiransu ta yi ta fada masu cikin sif akoy kaya su kimtsa su sauko a karya

Sama suka hau , wannan karin fakin Wujdane suka fice a tare

Wujdane ta fara yin wanka, kafin take fitowa Aisha ta ciro masu atampa da hijabai, irin hijaban nan masu hannu da tsakiya a hannun sannan da dan tsayinsu domin sun dan zarta gwuiwa, ta dorawa wujdane kalar ruwan anta a saman atamfarta ita kuwa ta dora fari, duka yanda zasu hau atampopin ne

Nan da nan suka shirya abinsu, sai bayan ta dage ta sakawa Wujdane kwali wada idannuwan suka cika da hawaye na kwalin domin ba wani sabawa ta yi da sakawan ba

Sai da ta jima kana take bude idannuwanta ta sauke su a fuskar Aisha

Mirmushi Aisha ta saki tana kallonta, a can kasan zuciyarta kuwa tana taslima ga wannan tsarin Halita na yayarta

Girar Wujdane a tsare take, bata taba asketa ko wani daidaita ta ba, ba baka sidik bace maroon ce sannan ta daidaita tsaf a zagayayiyar fuskarta
Idannuwanta tsarinsu sai dai ace masha Allah, idan ta saka kwali kuwa har wani kyalkyalin kwalin suke su kara haskawa, sai lebenta kuwa ainayinsa pink color ne, ga motsi kadan takan dan laso shi hakan yake sakawa koda yaushe a danyace yake koda bata saka man lebe ko jan baki ba, gashin idannuwanta kuwa gazar gazar haka suke da tsayi da shanyewa, a hankali suke saukowa suna dan magana kasa kasa kasa

Har sun hau table din, Mom tana zuba masu abincin

Khadija ma an tasota daga bacinta, tana zaune kanta daure da dan kwalin shadar dake jikinta, wace ta kwana da ita abinta,

Aba kawai ne da Mom ransu fes, idan ka duba yannayin Alaidine du kamar ya fasa ihu ya bar wajen yake ji, Jamail kuwa du zuciyarsa a karaye na irin yanda Aba ya yi ta yi masu nasiha, Khadija kuwa daman da kyar ta samu bacin, tana jin haushin bayan gata a gidan Aba ya je ya aurowa Alaidine wata matar, ai kuwa ta dauki aniyar sai ta koyawa Wujdane hankali sannan zata jata a jiki ta fada mata sirrin Alaidine din dan idan fada ya hada su itama ta kiraye shi da shegen ko ya saketa ta huta,

A hankali suka zauna, a kujerun da ba kowa wato tsakiya suka saka khadija dake zaune, sai ya kasance Wujdane tafi kusanci da Jamail dake kusan Mom, sai Aisha ta zauna kusa da Alaidine dake kusan Aba, aman kuma suna facing din junna wato kowane na iya kallon dan uwansa sak idan hakan ta kama

Abincin aka fara ci, inda kake jin karar cokula na kara a cikin plat, Khadija kam yayi mata dadi a baki, Alaidine ya ki ya kai bakinsa dan kyankyami sai da suka hada ido da Mom ta yi masa nuni da idannuwanta kan ya ci, hakan ya saka shi cin a tunaninsa ba zai ji yanda yake so ba

Sai dai ga mamakinsa wani taushi, kanshin kayan kanshin nan da dan gishirigishirin ya saka shi lumshe ido, a boye ya saki ajiyar zuciya ya dan gyara yana fakaitan idannuwan mutane yana dan tsakura

Sosai jamail Jamail yake cin abincinsa dan ya san girkinsu daman, a hankali ya dago da idannuwansa cikin sa.a kuwa suka sarke da na Aisha wace ta dago dan zuba ruwa

Sun yi kallon cikin ido na wajen sacond biyar kafin ya sakar mata murmushi mai kayatarwa wanda ya sakata jin kunya ta yi saurin mayar da kanta wajen abincinta ta kasa dauko ruwan sannan ta kasa ci gaba da cin abincin

Kamar hadin baki suka miko hannayensu dan daukan baban flask din jus din , ita ta san jus ne a ciki, shi kuwa a zuwan ruwa yayi masa, hannunsa ne ya doru saman nata,wani irin dago da kai yayi jin hannu tamkar na jariri, caraf suka hade idannuwansu,

Idonta ta rintse jin hannun namiji a saman hannunta, ta yi gagawar budewa, shi kuwa shagalta ce yayi da kallon idannuwanta, yanzu kuma sai suka bashi sha.awa mainakun haushi, aman abinka da miskili sai ya watsa mata hararar da ya saba

Bakinta ta yatsina ta dan karkace shi ta murguda masa shi kana ta janye hannunta tama fasa daukan jus din,

Mamaki taru ka kashe Alaidine mana, tambaya yake yiwa kansa" wai dam fitsarariya ce har haka? Daga hararanta sai ta murguda min baki??

Tashin Aba ne ya katse masa tunaninsa, inda Mom ta mike ta mara masa baya suka haura gefensa

Kokarin mikewa yake, wanda kafin yayi wani yunkurin har Khadija ta gifta shi ta shige kicin

Gannin du ana tashi ya saka su harhada kayan da aka ci abincin, sai Wujdane ta fara tafiya dan kaiwa kicin

Hadewa suka yi da Khadija ta fito a kicin din, Khadija ta yi mata kallon kaskantaciya, sannan ta dan saki buda a hankali ta rage muryarta ta ce" farin ya kaishi wannan karon kennan, zaki gane baki da wayo idan ya shige ki tamkar gonar talaka sannan ya rataba maki saki uku, ni din nan dai ni ce a yi a gama ina kallonku, domin nice kadai na iya daukan cikinsa na haifa masa Boy, du wata ta bayana karya ce ko yar gidan wanene balarana na ji a labari cewar ba.a tara aka tayar da kai ba

Tana gama fada ta fice bagazan bagazan ta tafiyarta dakinta

Zuru Wujdanw ta yi tana antayowa kanta tambayoyi, wannan ita ce matar tasa ko mai? To aman ya akayi bata ga wata shakuwa ta matar da har suka samu yaro da shi ba tsakaninsu? Ko tana matarsa danme zata fafada mata magangannu haka mararsa dadi? Ko an gaya mata son mijin nata ake ne? Daman sakin nawa yayi tun yanzu da bani da kamarsa a masoyana

Kwafa ta yi ta shige kicin din tana ayanna bafa zata dauki iskancin matarsa ba, du a tunaninta Khadijan matar Alaidine din ce

Tana dawowa ta tarar sai Jamail kadai , Aisha tana kicin din bata fito ba,

A hankali ta karaso wajensa tana murmushi ta ja ta tsaya ta ce" yayana, ina neman alfarma

Dago da kansa ya yi ya sakar mata murmushin shima, ya ce" Au, yau kuma? An amince na girman ne ko mai? Oh aunty wujdane manya

Kawar da kanta ta yo tana dan turo bakinta ta ce" dan Girman allah kar ka wakanta min Aisha, Jamail Aisha yarinya ce, bata da wani tunani in ba na kuka ba, kuma karka manta itama sai da ta jo hukuncin da aka zartar a kanta, karka wulakanta min ita na roke ka

Sai da ta gama, Jamail ya ce" na san Aishana yarinya ce, duda da farko ba ita na so ba aman ina mai tabatar maki zan kula da dukan lamuranta, karki wani damu kin ji?

Murmushi ta saki, wanda har sai da hakoranta suka bayana, Aisha da ta lafe ta rabe tana sauke ajiyar zuciya domin komai a kunnanta ya fito, sai Alaidine dake sama ya tsura masu ido, shi dai bai san mai suke cewa ba, aman a yannayinsu sai kawai yake hango tsantsar nishadi a tatare da su, gabansa ne ya fadi ya shiga tambayar kansa, ko dai yarinyar nan ta bata masa kani shi ya sa ya haukace shi yana sonta, Aba ya tashi ya aura masa kanwarta kar dai su dora daga inda suka tsaya ( ku ji fa😳😳)

Ficewa yayi a gidan ba tare da ya yiwa kowa magana ba ya nufi gidansa

Zaune Alawiya take, ta sha ado da doguwar rigarta ta atampa, Alawiya fa ba baya ba wajen kyau, sannan fara ce tas itama, gashi dai ne bata da shi, shima dan ta wakanta shi ya kakarye yama dadage, bata samu yin girki ba ta tashi da fitinar ina ya je, dan du a tunaninta bama a gidan ya kwana ba

Tana sakar zucinta sai gashi ya shigo , ransa a kololuwar bace, Alawiya kuwa ta mike ta tarbe shi da sabon salon iskanncinta

Kallonta ya tsaya yi tana furta masa kiri kiri cewar" daman auren da ya kara ita ta san dan sex ne, aman ko kunya baya ji ya tafi gidansu ya dane mace sannan ya dawo mata gida ya wanke dauda? Domin ba alamar ya wanke daudar da ya kwaso a jimin wata karuwar,........

Dago da idannuwansa da suka yo jajajir yayi, ya sauke su a kan Alawiya dake masifa ita an taba ta,
Chapter 25 · 0% Book details