← Book details Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 26

Sashe 11

Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ido ya bita, yana kara godewa Allah, matarsa, uwar yayansa, abin alfaharinsa, mai gane matsalarsa mai kula da fara.arsa, ita irin zumudin nan na ta ga kudi ma bata da shi, yana kara godewa Allah da du irin murdaden halayen Wujdane kudi baya gabanta, haka ya mike ya kara daura Alwallah ya shige dakinsa dan gabatar da salolinsa ya kuma kara godewa Allah da wannan budi da ya yi masa

Da sasafe kamar kulun, Wujdane ta fito daga wanka ta yi turus dalilin inna da ta ganni a dakin nasu zaune, dukawa ta yi har kasa ta kuma gaishe ta da kwana, innar na amsawa

Mikewa ta yi tana son saka kaya inna na binta da ido,

Dan murmushi inna ta yi a can kasan ranta take fadin kunyar karya irin ta wujdane, ita ba za.a ga tsiraicinta ba, gannin ta kasa saka wandon ya saka innar juyar da kanta tana kallon kofa

Aishama dariya take kasa kasa tana kokarin murza man kuli dake cikin wata yar farar roba a jikinta domin shine mansu idan man ya kare

Yan dari biyar biyar biyu ne a hannun innar, ta juyo ta mikawa Aisha sannan ta mikawa wujdane

Tsai suka yi suna kallonta, da alamun neman karin bayani

Zama ta yi ta ce" a jiya cikin ikon Allah sosai Allah ya yi budi a gidan nan, shine yau mahaifinku du irin kiye masa da nayi kan ba za.a baku hakan ba ya tirje min kan ai samu aka yi, shi ya sa ya bada wannan kudin ya ce na baku ku adanna idan bukatar sayen wani abin ya taso maku sai ku saya, ko dan saboda makaranta ma

Murmushi Aisha take ta saki, tana godewa Allah a fili ta ce" masha Allah, masha Allah, Allah mun gode maka, Allah ya kara budi , ya kara arziki mai anfanni

Amsawa inna take ta juyo wajen Wujdane, ta ga ta ajiye dari biyar din a nan kusan innar sannan tana kokarin saka hijabinta, inna ta ga yanda kitsonta ya tsufa sosai haka, to aman dan me bata dauki kudin ba ko ta raina ne? Inna ta ce" toh ke sarauniya, ya zaki jefar min da kudin a nan ne? Ko kin raina ne?

Juyowa Wujdane ta yi da sauri tana kallon inna wai ta raina, ta dan girgiza kanta bata ce komai ba

Takaici ya cika inna , yau miskilancin na banza harda ita za.a yiwa, ai kuwa ta shiga fada inda take shiga ba ta nan take fita ba, Aisha du ranta ya bace gannin inna na yiwa yar uwarta fada da safiyar nan, ita kuwa ta sada kanta ta yi zuru tana sauraron fadan innar na rashin dalili a wajenta, bayan inna ta gama tana harararta ta dan dago, ta sanyaya muryarta ta dauko kudin ta mikawa innar ta ce" innata, ba wai rainawa na yi na, koda baba ya dage kan sai an bamu sai ki rike a wajen ki, cikin ikon Allah koda wata rana abinci ya dauke da ajiya ai za.a yi anfani da shi, mu ba kudin mota muke biya ba dan zuwa makaranta, ko a makaranta Aisha ke sayo min abincina, kenan inna na wajen Aishar ya ishe mu har ya yi yawa, insha Allah idan ta sayo manta na shafawa vaseline dari da hamsin sauran sai ta ajiye mana a wajenta tana sayo abincin a makaranta kinga sai ki huta da bamu kwana biyu ko??

Tana gama fadar haka ta sakawa inna kudin ta mike ta fice da ledarta ta mauludu da aka yi a anguwar aka raraba ita ce jakarsu ta makarantar ta saka litafinta da biro

Da ido inna ta bisu bayan fitar su, shar ta ji dumin hawaye a gefen idannuwanta, a hankali ta goge ta daga hannayenta sama ta shiga karanto adu.o.i wa yayanta baki daya

Malan kam yau fara.arsa ta ki ta yanke, bayan ya biya kudin makarantar Wujdane ya zarce masalaci dan akoy karatun safe da zai bayar,

Bayan ya gama ya yiwa mutane salama ya fito , ya shiga doka sauri dan zuwa kasuwa domin a lokacin har karfe biyu na rana ya yi,

Oda ya ji ana yi kamar da shi ake hakan ya saka ya dan waiga

Anwar ne da wani saurayi a cewar malan shima mai cikar kamala a gefen Anwar din sai dai wannan tamkar ya fi shi girma da isa, bakin gilas a fuskarsa da waya yana dan dadanawa

Malan barka da warhaka, za.a je gida ko na ga sai sauri ake, cewar Anwar yana gaisar da malan din cikin mutuntawa

Malan ya amsa yana mai dan sakin fara.a ,

Alaidine ya dago da kansa, sai ya samu kansa da cire glass din idannuwansa, a hankali shima ya furta" barka da rana Malan, ka shigo mu saukeka man na ga ana rana

Murmushi Malan ya saki ya ce" aa ba komai yaro, ai kasuwa ma zan je ba gida na yi ba

Anwar ya matsawa malan kan ya shiga ko kasuwar ce su sauke shi domin suma can suka nufa, hakan ya saka malan shiga motar tasu da ya karewa kallo sannan ya bada nutsuwarsa wa bakin titi yana kallon yanda motar ke gudu aman tamkar bata motsawa dan irin motocin nan ne da idan ba wani baban gargada aka shiga ba ba zaka san an shiga ba

Anwar ke dan jan Malan da zance inda Alaidine ya yi shiru yana mamakin surutun Anwar

Ni Malan ina Yar rikici ne take??? Cewar Anwar

Malan ya dago da kansa ya saki murmushi jin an ambaci Wujdane ya ce" ai fa ana nan, sun tafi makaranta da yar uwarta, Wujdane rigima ba, aman an dan kwana biyu ba.a yi ba mai yiyuwa adu.a ta ci karfinta

Anwar ya yi ta dariya abinsa,
Haka suka karaso suna dan labari da Anwar aman Alaidine yayi kif, tun gaisar da Malan din da ya yi bai kara komai ba

Daidai babar kofar suka sauke Malan inda suka juya dan karasawa shagonsa na atamfofi

Malan ya yi masu sayaya daidai gwargwado harda su macaroni ta zamani, da fulawa da shinkafa da su magi mai gishiri , sosai ya yi masu tsince tsince sannan ya karasa shagon masu sayar da kaya
Nan ya sayawa inna atamfa da hijabi biyu, ya sayawa su Wujdane hijabai suma da atamfar kala biyu ,shine harda abaya yar dubu da dari biyun nan da yan takalma plate masu kyau da turare da mai na shafawa, rigi rigi almajiri ke binsa da kaya har ya zo fita ya ga yan abubuwan hannu, ya dakata ya sayowa Wujdane da Aisha sannan ya sayi sabulu sinki guda,
Malan dai ya yi sayaya ya kashe kudi bai fi dubu shida a aljihunsa ba ya nemi adaidaita ya yi shata har gidansa

Zaune suke Inna na tsefe mata dokar kanta da ta tsufa sosai har sai ta laluba take jin tufkar kitson tana yi tana mitar gaskiya Wujdane sai kin canza hali, ke daki yi tsaftar ko ina aman bakya so a taba maki kai??

Idannuwanta a rintse, jin taba kan nan nata take tamkar inna na yankan naman jikinta

Malan ne ya shigo da ledoji Aisha ta tashi ta tarbo shi, ya koma dan dauko sauran kayan

Yana daukowa Motar Jamail na tsayawa daga dan nesa da gidan kadan

(Talauci ba zai hana yin walwala a cikin gida ba idan har an gina rayuwar gidan a kan tubali mai kyau)
[3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄

*13*

WRINTING BY *SAJIDA*

Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*

MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....

Mom dake sama ta lumshe idannuwanta ta shiga yiwa yaronta adu.ar shiriya bayan komai da ya faru a idannuwanta duda bata ji takamaiman mai ya bata amsa ba ta san dai ba maganar dadi bace, tana adu.ar Allah ya sa wannan auren ya kasance ya shiga ransa, ya sota tamkar ransa, sannan ya shinfida shakuwa a tsakaninsu, tana adu.ar ta samu sarakuwar da zata zamo tamkar yarta, matar Anwar akoy mutunci da mutunta su, damuwar nesa ga yara sai ya kasance weekend kawai suke samun yi
Gaisuwarsa ta katse mata tunanin da take ta bada hankalinta kacokam kansa

Wujdane, Wujdane, ki saurareni mana, haba Wujdane ya dace a ce na samu karbuwa a wajenki daidai wannan lokacin, ki tuna fa a kala na kwashe wata biyu na bin bayanki, haba Wujdane dan adam daraja gare shi, ki saurare ni

Juyowa Wujdane ta yi, tana dan dubansa ta cikin nikab dinta, a can kasar zuciyarta tana aiyana" ya salam, yanzu Baba da ya fitar da maganar wani ta tsayar da miji wai ya yake so ta yi ne? Ko dai Lukman din nan kawai zata fadawa idan har yana son nata kawai ta aureshi ta huta da wannan rayuwar,

Ki ban amsa mana Wujdane, cewar Lukman yana kalar tausayi

Kanta ta dan dafe hango su Jamail sai a lokacin suka shigo kwanar shi da Aisha, ta juyo wajensa ta ce" ka ga dai azumi ne, ba.a sha ruwa ba ya zaka tare ni da azumina kanai min wasu maganganun soyaya? Na fada maka ni ban santa ba, ni ban iya ba, sannan ai ba ni na takuraka kan sai ka bi ni dole ba ko???

Tausasa muryarsa ya yi , ya ce" kwarai na san da azumi a bakin mu , aman maganar da nake miki na neman aure ne, kinga dai da dare ba samun ganninki zan yi ba, ki taimaka ki lamunce min na turo iyayena bayan sallah insha Allah da sannu zaki so ni Wujdane

Ido ta dan zaro gabanta na faduwa, daidai su Aisha sun karaso inda Aisharma ke gaishe shi cikin mutuntawa, Inna ta aikesu Jamail ya dage sai ya yi rakiya,

Dan jerawa ta yi da Aisha inda Lukman ya biyota da kalo da kalar tausayi,

Ko mai ya tausasa mata zuciya, ta juyo a hankali daidai da Lukman, murya a can ciki ta ce" Allah, ya dayaba, ya sa nufin da ka bayana alkhairi ne, ya nuna lokaci

Tana gama fadar haka ta daga kafarta sosai inda ta wuce su ta fada gida,
Chapter 11 · 0% Book details