← Book details Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 26

Sashe 23

Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yauma wannan datijawan da suka yi dare suka sha ruwa a masalaci ne suka kuma zuwa, sai dai wannan karin sun zo ne da alkhairi wa masalacin sun bayar da sadaka sannan sun zauna ana yin karatu da su,
Sosai yake satar kalonsu dalilin gannin dayan wanda ya fi tsufan ya matsa masa da kallo irin kallon nan na kure mutun

A hankali Alaidine ya mike ya fito ya ja gefen wata bishiya ya zauna yana kallon masu hucewa tamkar hankalinsa na kansu bayan tunaninsa kaf a wani wajen,

Bayan sati da daura auren su Alaidine , Jamail kam yana ta kokari koma nace alhamdulilahi yanzu sai abinda ba za.a rasa ba, domin sun shaku sosai shi da Aisha, yana jinta a kasan zuciyarsa, soyayar da yake ji tata irin ta a jinninsa take ne, sam baya son ko kuda ya rabi jikinta ko wani abin, yana girmama yanda take girmama shi, yana mutuntata kamar yanda ta ga tanaiwa mamansa, yana ji da su su duka yana girmama su Malan a kasan zuciyarsa domin su suka basu tarbiyar a yaba,

Aikace aikacen gidan nan sun dauke shi, basu da damuwa face na rashin mahaifansu wanda har zuwa wannan lokacin sun kasa sabawa a tsakaninsu suke jajantawa

Mom na iya kokarinta dan gannin ta dauke masu kew sannan sun saki jiki irin sosai din nan da ita, ba laifi ana samun ci gaba sai dan abinda ba za.a rasa ba a wajen Wujdane wanda shi kuwa miskilanci ne irin nata

Abinda ke birge Mom, yaren nada tsafta, ga tarbiya, suna girmamata suna kulawa da du wani abin da ya shafeta,
Mama suke kiranta da shi hakan ya saka take jinta a damuwarta sun debe wani wajen sosai sai abinda ba za.a rasa ba, sannan itama take lure da dukan lamarinsu

Alaidine kuwa rabonsa da gidan yau kwana na hudu kenan, yanzu haka boy ne ya tisa shi a gaba da kukan shi uncle dinsa domin Jamail zamansa ya zama kalilan a gidan

Yayi rarashin, yayi gadan aman Boy ya nace shifa uncle dinsa, cike da jin haushi yake kara buga number Jamail aman a kashe, haka anwar yana wajen aiki, ya rasa ya zai yi da shi kuma abin haushin Alawiya na kallonsa ko ci kanka bata ce da shi ba bale ayi tunanin rarashi daga wajenta

A hankali yake bala botiran rigarsa yana hangen yanda boy ke kuka hannunsa bibiyu a saman kansa, ajiyar zuciya ya saki ya fesa turare a jikinsa ya juyo da tissu ya gogewa boy fuskarsa sosai, ya dauko shi a hannunsa suka shiga mota suka kama hanyar gidan Aba

Yana karasowa bayan ya parka motarsa ya juyo yana kallon yanda Boy ya daina kukan yana dan wasansa, wato anyi masa abinda yake bukata?
Kansa ya dago yana dan duduba gidan, kamar ance ya daga kansa can wajen shukokin mangoro abarba da sauransu sai ganninsu yayi a zaune Jamail da Aisha a waje guda suna shan ice cream sai Wujdane a dan nesa da su tana ta jifan mangoro tana son ya fado ta sha

Ba wani hijabi a jikinta, doguwar riga ce ta saka irin gown din nan, ta dan yane kanta da dan kwalin rigar, rigar kalar fara ce kal dan kwalinta ma haka , sannan ta dan kama ta daga wajen mamarta sai ta baje kasa, kallonta yake kamar an kunna masa tv yana jin dadin yannayin sosai,

Boy ne ya tabo hannunsa ya kwabe fuska ya ce" dad Uncle☹

Ajiyar zuciya ya saki a hankali ya bude motar ya dauko shi ya nufi wajen Jamail da shi

Gaishe shi suke cike da girmamawa ya amsa fuska a dan sake har yana yiwa Aisha tsiyar cewa ta sake abinta
Sai ta danyi murmushi tana sada kanta kasa bata ce komai ba

Boy kuwa da gudunsa ya nufi wajen Wujdane gannin tana kokarin baso mangoro, yana zuwa ya gane ta ya ja ya tsaya yanai mata murmushi

Juyowa Wujdane ta yi ta zuba masa ido, haka kawai yaron tun ranar a gisansu ya shiga ranta irin yanda ya makale matan nan, a kulun tunanin ina yake take a kasan zuciyarta

Murmushi ta sakar masa sannan ta miko masa hannunta na dama ta ce" zo,

Kallonta yake bai motsa ba, sai ta dan girgiza kai ta miko dayan hannun nata da niyar tana son daukansa
Ai kuwa da gudunsa ya karaso yana bangale bakinsa ya ga dauka

Daukansa ta yi tana kakabe masa wandonsa da ya dan yi kura, bata bi ta kansu ba ta nufi falo dan so take ta yiwa boy wanka domin yaron da dati a jikinsa , dan kuwa mai yi masa wankan daman Jamail ne Alawiya ba wani damuwa ta yi da lamarinsa ba Alaidine kuwa baima san ta inda zai fara ba

Biye yake da bayansu a hankali, idannuwansa kyam a kanta, shi yakan manta cewar ya tsayar da kalonsa a saman kanta, yakan manta cewar ya shagalta da damuwa da yannayinta , har dan murmushi ya saki jin labarinsu da Boy, yana son mai kula dansa abinda ya sa yafi shakuwa da Jamail kennan irin yanda ya shaku da Boy sannan ya sakar masa aljihunsa har shima ya malaki na kansa yake wadaga da aljihunsa, yana girmama girman du wanda ya damu da rayuwar yaronsa

A hankali ta tura kofar gilas din dakin ta shiga, hankalinta a wajen Boy dake jan jelar gashinta

Kan uba, ke sauke min yaro sauke min yaro, ko kunya bakya ji? Mai ya hada ki da yarona?
Khadija ce ke hargowa tana nufo wajen Wujdane dake rike da Boy, abin mamaki shima yaron sai ya riketa gam yana dan cusa kansa a kirjinta

Ja ta yi ta tsaya tana kallon Khadija, a kasan zuciyarta tana mamakin wannan irin tsana haka, kuma a hankali take fahimtar ba wani abu tsakaninta da Alaidine din kuma ita dinma ta lura ta ganni ba wani abin tsakaninsu da shi ba wani kula juna suke ba aman ita sai kishin hauka take zubawa ta hanata sakat, ita kuwa kawar da kai take bata son kula ta dan tana tsoron abinda zai iya faruwa tana matukar jin kunyar Mom

Kokarin sauko Boy take, ya ririke rigarta ya saki kuka yana fadin " no no bana so bana so sauka ni................

Dan tsai ta yi da shi a hankali ta ce" ka ga mamanka na son daukanka my Boy, ka je mamanka ta yi maka wankan ka ji?

Boy yaki cika ta sannan yaki yarda ya saukan,

Ba sai kin sauke shi ba, ki tafi da shi kawai

Murya ta daki kunnenta, a hankali ta mike da Boy ta dan juyo dan gannin waye ya yi maganar,? A tare gabansu ya yanke ya fadi bata tankasa ba ta nufi dakinta da boy

Ya zaka yi man haka aban Huzaifa? Ni da yarona har ka fifita wata a kaina a wajensa sannan a gabansa? Ya kake so ya dauki lamarina ne ? Ni fa na haife shi!

So what? Dan kin haife shi a da baki nuna masa kulawa ba sai yanzu? Idan ke kika haife shi zaki haife shi ke kadai ne? Ko kin san kashin sa da fitsarinsa? Bana son yawan haye maki kina kokarin tura ni rami, *MATATA CE* wannan, tana da damar daukan yarona ta kula da shi

Idannuwa ta kankance ta ce" matarka fa ka ce? Matarka fa? Yaushe ma ka aminta da matar taka? Ai a sanina bata amsa kiran matarka ba domin bata ma san kalarka ba a zahiri, auren hadin?

Kema ai auren hadi ne ko kin manta? Ya katseta, tsam ta yi ta juya zuwa dakinta

Zama ya yi a wajen , shi bai haura saman ba shi bai tafi ba,

Can yake jiyo dariyar Boy har kyakyatawa yake, tsam yayi yana hangen saman a kasan zuciyarsa yake tambayar abinda ke faruwa?
A hankali ya mike ya nufi saman, du takunsa daya sai zuciyarsa ta buga masa wannan lamari na rage masa karfin jikinsa, yana saka shi a damuwa ainun

A hankali ya tura dakin ya shiga, bayanta kawai ake iya gani, ta cire mayafin na kanta ya kasance gashinta a baje a gadon bayanta, cakulkuli take yiwa boy wanda har daga kafafuwa yake yana ihun dariya

Tsam yayi da ransa, wani irin nishadi ya tsinci kansa a ciki, kallonsu yake inda ya ja a hankali ya rufo kofar dan kar su gansa sai dai me yana juyowa suka yi ido hudu da Mom.........😳
[3/27, 10:00 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄

*26*

WRINTING BY *SAJIDA*

Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*

MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....

Ido ta tsurama yannayinsa, kamar kallon tuhumar nan haka take jifansa da shi wanda ya saka du ya wani kawar da kai, can ta basar ta ce" sai nake jin kamar dariyar mai gidan?

Juyowa ya yi ya ce" eh shi ne yake dariyar nan

Mom ta yi murmushi ta ce" eh lale, wa ke yi masa wasa ne???
Du da gangan take tambayoyin nan, dan kawai ta dabirtar da shi ta kuwa yi sa.a ya daburcen,

Kai ya sosa ya ce" am em ..... ina jin bakuwar nan ne🤷🏼‍♀

Mom ta kale shi da kyau ta ce" bakuwa? Muka yi? Ko su Aisha suka samu ziyara ne???

Wannan karon tsayar da kallonsa yayi a kan Mom din yana nazarinta, kirkiri ya lura Mom din na kokarin sai ta kure shi ne, a hankali ya sauke ajiyar zuciya gannin Mom fa amsarsa take jira, a hankali kamar ba zai yi magana ba ya ce" aa fa, wannan dai wada aka aura min......
Yana fada ya juya da saurinsa dan ya bar mata wajen ,

Mom ta saki murmushi ta dan daga murya dan ya jita ta ce" ai Wujdane da Aishana ba baki bane, sai dai su sauki baki , gidansu ne harma sun fi mutun yanci!

Murmushin ya yi shima yama fice a falon kwata kwata wanda wani abu ya mugun bashi mamaki, wato Jamail ne ya dora Aisha saman cinyarsa a hankali ya cafke lebenta sai kissing yake,
Chapter 23 · 0% Book details