← Book details Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 26

Sashe 24

Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Idannuwansa ya kawar da sauri daga bangarensu mamaki kamar ya kashe shi ya fada motarsa ya ja ya fice a gidan

Yauma kamar wasu lokutan , parka motarsa ya yi dan nesa da gidan ELHAJ MUHAMADU DA KUMA ELHAJ ABDALLAH, wato kakaninsa shi fa ba zai ce ga kamaninsu ba aman yana iya shaida yayan gidajen, shi Elhaj Muhamadu shine mai yaya da dan dama shi kuwa Elhaj Abdallah dansa daya wanda ya yiwa aure matar ta haifi yaro daya, aman a yau sai yake gannin ana ta shigi da fici a yannayon tashin hankali

Motarsa irin mai glass din nan ce mai duhu, ba zaka iya gannin na ciki ba sai dai shi ya ganka hakan ya bashi damar mayar da hankalinsa yana gannin datijai na shiga cikin sauri wasu na fitowa wasun su na kara shiga cikin gidan Elhaj Abdallah

Haka kawai yake jin wannan ba lafiya ba dan haka sai ya kara zama yana kallo,
Ganni ya yi an fitar da babar makara irin ta manya, an nufi cikin gidan da ita

Gabansa ne ya yanke ya fadi, ya bude motar kamar zai fito ya dan dakata yana kallon wajen kofar gidan Elhaj Abdallah, jin an bude kofar

Datijon nan da ya gani sau biyu a masalaci ne, wannan wanda ya kafe shi da ido yana kallonsa ya fito daga gidan ya maida kallonsa kofar gidan Elhaj Abdallah,

Wata mata ce ta fito da bakin hijabinta har kasa, du yanda ta kai ga tsufa sai da gabansa ya fadi dan hango tsantsar kama da mahaifiyarsa Hajiya Marwa, tsai yayi da ransa yana kallonta ta dan dakata daidai wannan datijon ta kamo hannunsa ta yi masa magana wada ya saka shi sauke ajiyar zuciya ya shafa kansa sannan ya yi gaba ta bi bayansa har gidan Elhaj Abdallah

Mayar da hankalinsa ya yi, yana nan zaune aka shinfida tabarma lakadediya

Ba.a jima sosai ba aka fito da gawar a cikin makara,

Shi dai ba zai ce ga wanda ke cikin makarar nan ba, domin ba sannin tsohon gidan ko tsohuwar gidan ya yi ba,

Saurin fitowa yayi, gannin ana kokarin salatar gawar, da saurinsa ya dauki butar ya bi layin masu azamar yin alwallah dan gabatar da sallar gawar

Da Alaidine aka salaci gawar nan, aka dauketa yana kalo wani baban saurayi ne a gaba wajen rikon gawar

Bai tambayi kowa ba, ya shiga motarsa har ya dauki mutane aka nufi makwontai, har zuwa lokacin bai san wanda ya rasun ba

A makontan ne ya ji ana ya Abdallah, ya Abdallah, ya Abdallah, hakan ya tabatar masa cewar namiji ne ya rasu

Cikin ramin ya ga wani datijo fari da wannan saurayin suka saka gawar a cikin ramin suka gyara mata konciyarta hakan ya nuna masa cewar sune mafi kusanci da gawar

Fitowa suka yi a hankali aka yiwa wannan bawa sutura, jama.a suka fara watsewa ana ta yiwa mamata adu.a

Da dayadaya du aka watse aka bar sai yan tsirarku da suma suka dan bazu wajen sauran kaburan

Mutun uku ne a zaune daidai da kabarin nan, wannan tsoho wato Elhaj Muhammad sai yaron nan da dayan tsohon

A hankali Elhaj Muhamadu ya dora hannunsa a kafadar Elhah Abdallah ya ce" ka yi hakuri, ka tashi mu tafi a yi ta masa adu.a Allah ya bashi ikon amsa tambayoyin kabari, Allah ya bashi haske da ni.imar dake cikinta, shi da ya rigaye mu bai yi sauki ba, mu da muke jira bamu yi jinkiri ba,

Saurayin nan ne ya fada kan Elhaj Muhammad ya saki kuka ya ce" yanzu shikennan Abanna ya rasu? Shikenan bani da kowa? Sai su kaka da umana? Shi kennan na rasa jigon rayuwana?

A hankali ya shafa bayansa ya ce" ba.a yiwa mamata kuka haka, a cikin makontai muke ba.a son yin yawan magana a makontai idan har ba adu.a ba, aman ka sani *ABDUL KADRE* Allahn da ya amshe shi ya fi mu son sa, sannan bai barka kai daya ba, kana da wani uban mai sunnanka!

Da sauri Elhaj Abdallah ya dago da kansa ya sauke idannuwansa a kan Elhaj Muhammad, bai iya furta komai ba ya mike ya nufi fita a makontan inda suka biyo bayansa

Alaidine dake zaune gefe ya dukufa a kusan wani kabarin yanaiwa mamata adu.a sannan hankalinsa na kan magangannun su elhaj , a nan ya fahimci cewar Kanin mahaifinsa ne ya rasu, wanda su biyu kawai iyayensu suka malaka a duniya, sannan wannan tsohon shine mahaifin mahaifinsa yaron nan kuwa dan mahaifinsa, a takaice dai rasuwar nan ta shafe su, mutuwar nan su aka yiwa

Cikin mutuwar jiki ya dawo kusan kabarin nan ya zauna, adu.a yayi ta zubawa kamar ba gobe, bayan ya gama ya dora hannunsa ya ce" Aba, baka sanni ba, ni dan dan uwanka ne, ina mai yi maka adu.ar samun nutsuwa a cikin kabarinka, Allah ya karbi bakuncinka ya sa mu ma mu cika da imani

Yana gama adu.ar nan ya mike a hankali ya fito, zuciyarsa du a mace, yana duba irin tarin kaburburan dake konce yana aiyanawa a ransa cewar " *KULU NAFSIN ZA.IKATUL MA.AUT* ba wanda ya isa ya tsira fa, mutuwar nan sai an yi ta dole (😭)

Tuki yake zuciyarsa tamkar ta bale, yana tafe yana tuna yannayin da Elhaj Abdallah ya nuna da aka tsankwalo sunnan abansa

A haka har ya karaso gidansu, yana sauka ya nufi falo

Abansa ya tarar a zaune a falon, yayi zugum yana kallon tv,
Karasowa yayi ya gaishe shi ya nemi waje ya zauna ya rasa ta inda zai fara

Mom ce ta fito daga kicin ta taho da jus a hannunta , tana karasowa ta mikawa Aba tana kallon Alaidine ta ce" ka dawo?

Amsa mata ya yi yana kallon Abansa,
Hankalinta ta maida wajen aba ta ce" Aba yara idan zuciyar taka bata daina bugawar ba ai gwara a tafi asibiti ko? Dan na ga tun jiya kake jin yannayin nan

A hankali ya muzkuta yana kallonta ya ce" Momyn yara, ai faduwar gaba ne kawai ba komai insha Allah

Gaba daya jikinsa ya gama mutuwa, tausayin mahaifinsa ne ya tsarga zuciyarsa, bai san ta inda zai fada masa rasuwar kanninsa kanninsa uwa daya uba daya, wanda may be ya jima rabonsa da shi, mai yiwuwa ya jima bai saka shi a ido ba, aman yaya zai yi? Mutuwar nan dai an yi ta, sannan shi dolensa ne , kuma musulmi ne du abinda zai faru zai yi hakuri ne

Muzkutawa ya yi ya ce" ABA,

A tare suka dago suna kalonsa wanda ya kara kayar masa da zuciya, daurewa ya yi ya ce".......
[3/27, 10:01 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄

*24*

WRINTING BY *SAJIDA*

Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*

MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....

Happy happy birthday to you, happy birthday to you, happy birthday to you *YAYA HAYAT* happy birthday to you@ *Allah ya sa wannan shekara ta zamo daya daga cikin shekaru da zasu zo maka da cikar lafiya, su kara maka daraja, su kawo arziki mai anfani, hsppy bufday*

Mom ta yi kiran Lami,

Lami ta fito tana gyara hijabinta dan tunda ta kyala ido ta ga Alaidine a gidan da safen nan ta shiga kimtsa kanta tun kafin ya fita bayanta

Tana zuwa ta raba tana amsawa

Mom ta yi dan murmushi ta ce" ki fitar min da zabi a cikin frij ki saka min su s ruwa yanzu zan fito na hada breakfast , yau na yi rana

Amsawa Lami ta yi ta juya insa Wujdane ta kama hannun Aisha ta mikar da ita dan su bi Lami

Mom ta cel" aa, yar gidan Mom ina zaku tafi ne? Ku fa je ku huta kar ku kwashi gajiya da yawa kun ji?

Wujdane ta dan juyo, ita kam da alama zafa a saka ta yawan magana ne s gidan nan, s hankali ta ce" zamu hada kayan karin ne *Mama*

Mom ta yi murmushi, ta lura aikace aikacen nan sabonsu ne, dan haka sai kawai ta barsu suka tafi kicin, aka bar su Alaidine da su Mom , nsn Aba ya dora daga inda ya tsaya a jawabinsa mai shige da gargadi, sannan ya basu umarnin su tsaya su karya kafin su tafi

Raba aikinsu suka yi, Wujdane kam bata iya wani dogon rarashi ba aman idannuwanta kyam a kan du wani motsi na Aisha,

Aisha ke feraye dankalin turawa ita kuwa Wujdane na gyaran naman da take kokarin dora shi silale

Sosai ta kara wanke naman, duda daman ba wani dati ne da shi ba, ta kawo tukunyarta ta zuzuba shi, ta kawo su kayan yajinta , su gishirinta kadan ta zuzuba sannan ta dan zuba ruwa kadan bayan ta saka albasarta

Lami ce ta kunna mata gaz wanda har sai da ta tsorata yanda wutarsa ke da zafi, ta dora ta rufe tukunyar ta zauna tana daka atarugun da zata hada vinaigrette da shi tana kallon yannayin Aishanta, yanzu da zuciyarta da dadi da tuni ta cika mata kune da labari

A hankali ta matso kusa da ita ta kama mata yankan dankalin turawan,
Kanta a kasa bata wani dago ba ta ce" *kar ki kwalafa da gannin daidai fa a wajen da namiji, sannan ki cire damuwa a ranki insha Allahu Jamail zai so ki kin ji?*

Dago da kanta ta yi tana klon yayar tata, sai ta sakar mata murmushi, sai a lokacin ta farga da irin yanda ta tayar da hankalinta bayan ta san a yanda aka yi auren nan, tausayin Wujdane ne ya ratsa mata zuciya, ita sam bata wani nuna damuwarta ba bayan ta sani sarai itama bata wani jin dadin hakan dake faruwa da ita
Chapter 24 · 0% Book details