← Book details Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 26

Sashe 18

Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wujdane ta dafe kanta da ya dauki sara mata, ta kuma dago da kanta ta ce" yanzu fisabililahi ka rasa wace zaka ce kana so sai ni? Shekara uku kacal fa ka bani a nan gidan duniya, ni kuwa ba bakin uwa ba ba na uba ba zan auri yaro? Ai ni ba zan soma soyaya bama da yaro domin ko lukman hakan ya saka na yi watsi da shi, Look Jamail, ka ga dai ina gannin girman ka, dan haka dan Girman Allah karka soma irin wannan abin ba zai fishemu gaba dayanmu ba, danme zaka yi kokarin kawo min irin wannan wulakancin daidai wannan lokacin? Shin ganni ka yi bani da mai tayawa ko? Jamail idan na yi soyayay da kai ka fadan mai na gane mai? Jamail ni idan ba shekara arba.in da biyar namiji ya yi ba, bana jin zai iya zama da ni a matsayin mata domin sai an samu mutumin da ya fara manlakar hankalin kansa kafin yake gane zama da ni a rayuwa,
Please buden kofa na tafi,

Kallonta yake, cike da mamakinta, yanzu shi take gannin ba zai iya rayuwa da ita ba,? A irin hakurinsa , zai iya ciyar da ita ya yi mata sutura ya biya mata dukan bukatunta na gidan duniya, shin a mai ta dauke shi? Tana nufin ya yi mata kankanta ko me? Aman ai NAMIJI BAYA KADAN , dan me zata fara fasara shi ta haka,

Hannunta ta mika inda ta ga ya dana ya kile motar ta dannan ta bude ta fice abinta ta nufi wajen Mairo da ta tarbota an sha kayan sallah

Kokarin bude motar Aisha take, dan ta fice itama, sai jin muryar Jamail ta yi yana fadin" Aisha ta ina na kasa? Shin menene makusata? Aisha ki taimake ni dan girman Allah ki fada min menene aibuna?

A hankali ta dago da kanta dan bashi amsa, sai dai mai a lokacin da suka yi ido hudu da Aisha wani iri yanda gabansa ya yanke ya fadi har sai da ya katse tunaninsa na sakonni,
A hankali ya bude idannuwansa da ya dan lumshe ya sauke su a fuskarta,

Murmushi Aisha ta sakar masa ta ce" yaya Jamail baka da wani makusa, kawai sai a hankali aunty zata fahimci inda maganarka ta nufa ka ji? Kar ka sakawa kanka damuwa domin Aunty ta jima da irin wannan ra.ayi nata na cewar sai dai ta auri mutun mai shekaru shi ne zai iya rayuwar zaman aure da ita, ka yi hakuri insha Allah zanyi kokarin gannin na karkato maka da hankalinta ka ji?

Cike da sanyin murya ta yi maganarta wanda ya kashe masa jiki, sam bai san dalili ba, a haka yana kallo Aisha ta bude motar ta fito inda ta hango babur din Lukman ya faka yana faman shawo kan Wujdane kan ta yi hakuri ta saurare shi

Ba Wujdane ta dawo gida ba sai da ta saurari Lukman harma suka shirya kan fadan da suka yi , daga nan ma ta bi bayan mairo suka shiga yawonsu a cikin anguwar wace ba ita ta dawo gida ba sai can da dare sosai

Malan ne zaune, a yau km Wujdane ta tabo masa ransa, bayan ya fada masu gaba dayansu su hadu bayan sallar magariba su yi adu.a wace sukan yi du bayan azumi, sannan a ci abinda ya samu, wannan karin harda dan akuya ya sayo da tarin kayan miya wanda sai su kadai ne suka yi adu.ar shekarar sannan suka shiga shirye shiryen yankansu suna ta shagalinsu banda Wujdane dake anguwa yawon fitinar fada

Salama ta yi , wanda sai a lokacin gabanta ya yanke ya mugun faduwa, dalilin hango tarin karan dake ci ya haske tsakar gidan nasu, ga kuma gefe kai da kafafuwa na akuya a aje ga Aisha sai aiki take ita da inna gefe kuwa Hamza ne rike da wayarsa yar nokia yana amsa kira

Kallon da inna ta yi mata ya sage mata gwuiwar nufar su, hakan ya saka ta nufi dakin mahaifinta dan ta bashi hakuri

A hankali ta dakata ta yi salama daga kofa

Kafin Malan ya amsa mata salamarta ta ji dau an fauketa da wani gigitacen mari,

Kafin ta ankara ya shiga balata da kafarsa ransa a matukar bace

Da sauri malan ya fito daga dakinsa ya karaso wajen Abdul fatah dake jibgar Wujdane tamkar an aiko shi su inna kuwa ko su dago kansu sai aisha ce ta mike tsaye jikinta na bari tana kallon yayan nata na dukan yayarta

Malan na karasowa ya ce" aa, aa, Abdul Fatah me haka? Baka da hankali ne? Ka daina kafin na wanka maka mari fa?

Du irin yanda Wujdane ta kai ga taba ran mahaifinta abu na farko ne da ya fi tsana a taba lafiyarta

Cike da bacin rai Abdul Fatah ya nuno Wujdane da yatsarsa ransa a bace ya ce" Aba, shin yaushe yarinyar nan zata yi hankali ta samu nutsuwar zuciyarta ne? A yau wajen samari ana labari har ta kai an daina jin nauyin nawa a gabana ake cakalkalarsu ita da wancen jakar kawar tata, shin a mai kika dauki rayuwarki na ya mace ke wujdane,,? Ko maza a wannan lokacin suna kofar gidajensu aman ku yanzu kuka fito daga gidan mai alaro wai kun daki amaryarsa? Shin Aba yaushe zaka bari yarinyar nan a koya mata hankali?

Sai fada yake yana huci inda Wujdane ke zaune dangagar a kasa tayi zaman yan bori, kuri da idannuwanta sai kallon yan gidan nasu take, ta jibgu dan jibguwa aman ba ko digon kwallah a idannuwanta sai cicije lebe take

A hankali.Malan ya ce" duka ba shi ne magani ba, daga hannu da kake a kanta yana iya jawo maka raininta a lokacin da kake bukatar ta girmamaka, ni kaina a yau Wujdane ta taban zuciyata, bani da wani uzuri da zan yi mata a gabannan sai maganata ta karshe shine ta fitar da mijin aurenta nan da sati biyu kacal, idan ba haka ba ni zan yi mata miji,

Malan na gama fadar haka ya shige dakinsa ya zauna yana hangen Wujdane wanda yake kokowa da zuciyarsa kan kar ya fito ya lalasheta,

Itama kifar dakin nasa ta tsurawa ido, zuciyarta na halbawa, irin halbawar nan mai sauri sauri, da sauri ta juyo da idannuwanta ga innarsu, aman inna bata kallonta daga karshe ma innar daki ta shige, yayi sauran daga ita sai yayunta da kanwarta wanda cikinsu idan ka cire Abdul fatah kowane ji yake kamar ya rugo ya rungumeta ko zata daina jin zafin dukan da aka yi mata, Hamza kuwa cike yake da jin haushin dukan da abdul fatah ya yi mata duda ya hana shi daga hannu samanta aman shine zai yi ta kwalo da ita a haka din nan baya gannin yanda jikin wujdane yake tamkar na jariri zai kama dukanta haka

Wujdane ji tayi wani abu na bun fuskarta, a hankali ta kai hannunta daidai gurbin idannuwan nata ta lalubo

Da sauri ta kai idannuwanta tana kalo, eh da gaske hawaye ne, hawaye ne take , hawaye ne a fuskarya, ai bata san lokacin da ta mike tsaye ba ta.......

Readers, i.k so sorry, hidindimu ne suka yi min yawa, insha allah da na samu sasauci page zasu ninniku sannan a kan lokaci, daga sajidarku
[3/27, 10:00 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄

*20*

WRINTING BY *SAJIDA*

Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*

MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....

Aba ya ce" Malan Laminu ina nemawa dana *Alaidine* auren yar wajenka *Wujdane*

A tare suka dago da Malan da Alaidine, wani irn faduwa da gabansa ya yi har sai da ya dafe kirjinsa, ya dago da dara daran idannuwansa daga wayarsa da yake duba ball da aka yi Barça da Reel, a wani haukace ya juyo wajen abansa wanda ya yi masa kallo daya ya dauke kansa ya mayar wajen Malan Laminu wato Malan, da malan ishak

Kamar da wasa Alaidine na zaune dangalgal a gabansa da kudin aljihunsa mahaifinsa ya daura masa aure da yarinyar da a ranar da ya ganta tsanarta ta darsu a ruhinsa, a yanda ya fahimci rayuwarta bata da kamun kai har tana furtawa namiji ya yi mata kadan kennan ta san mazan ne, yarinyar da shi bama zai nuna kamaninta ba, yarinyar da kanninsa Jamail ke so kamar ya mutu, yarinyar da yayi yanda yayi dan karta shigo zuri.arsu a matsayinta na wada sam bai yarda da lamarinta ba, yarinyar da a duniya idan da akoy abinda zai nuna da kyama toh tabas itace domin kawai haka ta darsa masa rayuwarsa a zuciyarsa sai gashi

An daura auren *Elhaj ALAIDINE abdul kadri, DA WUJDANE Laminu bisa sadaki naira dubu hamsin lakadan* , da *JAMAIL ABDUL KADRI DA NANA AISHATU LAMINU A BISA SADAKI NAIRA HAMSIN LAKADAN*,

Nan fa ya ci gaba da yadawa ya zo kan soron gidan Malan ya rangada wannan labari

Aisha ta zabura ta mike tsaye jikinta na wani irin bari, kallonta ta maido wajen innarsu da itama ta yi zuru cike da mamakin sunnan Alaidine da aka kira da sunnan mijin Wujdane, tambayar kanta take shin waye Alaidine kuma? Ko dai malan sadakar Wujdane ya bayar?

Wujdane ce ta fado jikin inna, ta kankameta sosai domin wani irin sanyi sanyi ne yake ziyartarta, da wata irin faduwar gaba, kanta yayi mata wani irin nauyi, haka ma zuciyarta, bakinta yayi wani daci ta rasa gane kanta, a hankali ta dago da idannuwanta da kwayar cikinsu ke ta wulgawa tamkar zasu fado, zufa na keto mata ta zube idannuwanta cikin na mahaifiyar wace itama sak irin idon Wujdane din ne , murya a shake ta ce" innata, Lukman dina bai zo ba ko innata? Innata wanene *Alaidine* kuma????????
Chapter 18 · 0% Book details