← Book details Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 26

Sashe 12

Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da ido suka bita gaba dayansu, inda Lukman ya saki wani lalausan murmushi da ya bayanar da hakoransa waje, a fili ya furta Alhamdulilah, yanzu adu.arsa daya Allah ya sa mahaifin baban nasa ya yarda da wannan magana domin ya nace kan sai ya aura masa yar uwarsa Zuhra wace sam baya jinta a layin matan da yake sha.awar rayuwar aure da su

Haka suka karaso suka tarar da inna na ta tatar koko Wujdane na gefe tana gyara dambun shinkafar da zasu yi, ta zagine ta ce ita zata yi komai bayan Jamail ya nemi alfarmar a yi masa ya kaiwa yayansa dan yana da son dambu

Jefi jefi takan saci kallonsu da Aisha dake famar gyaran lemo na shan ruwa, a daidai wannan lokacin Abdul Fatah ya karaso cike da gajiya shi kan idan yana azumi akoy son jiki

Shima nan ya tile wajen su Aishar ana ta labari da Jamail wanda sosai a gidan ba wanda bai yi sabo da shi ba, tsananin yana son wannan zuri.a

Inna ce ta dan dago da kanta, ta yi ta yi ta hani kanta yi masa magana aman ta kasa, dan zama ta yi kafin ruwa ya tafasa tana kallonsa, a hankali ta ce" Jamail, ka yi hakuri, aman na kasa jurewa, shin Jamail wannan kayan abinci da ka kawo mai kennan?

Dago da kansa ya yi da sauri, daman ya san a rina shi ya sa yaki yarda ya zauna daga shi sai ita a gidan, wannan kayan kuwa yayansa ne ya bude yana talafawa talakawa shima yaje masa da bukatar a deba masa ya kawo gidan malan dake bada karatu a masalacinsa, hakan ya saka aka cika mota da su shinkafar gwomnati, hatsi, gero, macaroni, cuscus, kai harda su man kuli a babar jarka da su magi, kafin ya karaso sai da ya biya wajen malan ya fada masa da kuma fadin sakon yayan nasu na kar kowa ya tafi gida da wuri dan yana can baban shagonsa na abinci ana ta fitar da sadakar kafin ya karaso anguwar nasa, duda ba shine ke rabawar ba, domin a cikin masalacin mutane dadaya ne suka san shine mai taimakon nan, da yawa ba zasu shaida shi ba a boye yake

Kafin ya yi magana inna ta ci gaba da fadin" ina jin tsoron hakan Jamail, tunda aka haifeni har zuwa yau da furfurana a kai ban taba tara kayan abinci irin haka ba, Jamail ba wai ban yarda da kai bane ko wani abin, iyayenka basa tuhumarka da dawainiya da kake da gidan nan yau da kulun? Shin baka gannin ya yi yawa ne duda ka fadan cewa kai kana yi ne idan ka ga yin hakan ya dace, ka daukeni tamkar mahaifiyarka ne, malan mahaifinka, kana son talafawa mu, aman Jamail ya dace ka sasauta, ka ga da ba dan Wujdane na gidan nan yau ba da tuni layin nan sun cikani da kai kawo dan tsegumin mai ke faruwa a gidan nan, Jamail bana son abinda zai zo ya jagula kyakyawan zumuncin nan dan Allah

Jamail ya yi murmushi, a hankali ya juya wajen Abdul fatah ya ce" ni yaya a kasuwar sabon gari ma kana dan taba kasuwanci a can ko???

Abdul Fatah ya ce" sosai ma, ai nan din yafi kwari kasuwancin domin a da soso nake kaiwa yanzu tsaron shago nake na siyar da irin turarukan nan na mata na shafawa

Jamail ya gyada kai ya ce" Masha Allah , Allah ya taimaka, aman yaya ka san wani da ake cewa Elhaj ALAIDINE MAI KAYA?

Abdul fatah ya ce" tap, ai wanda bai sanshi ba toh ka tabatar bako ne, domin tun daga kan hausawa da inyamurai dadaya ne basa bin reshen kasuwancinsa, suma dan basu samu ba, aman du yawancin haraka sai ka bi ta gefensa idan kana son ka ga komai ya je maka da sauki ga biyan bukata

Jamail ya ce" madallah, kuma ba tonan asiri ba, dan Allah yaya Abdul fatah, yana da tausayin na kasa da shi?

Abdul fatah ya ce" a kishin kishin din da ake yadawa wai ba wanda Allah ya cida haduwa da shi ba, aa, koda sako yake na bayar da zaka ko sadaka Allah ya sa ya biyo layin ka warke, yauma fa ana can store dinsa karka so ka ga layin jama.ar, ai sabko zan yi dan na samu gaba gaba, ba wani bambanci ko almajiri ko baba ko yaro ana sadaka ne da zuciya daya, aman ba wanda ya gansa ance yana ciki, mutane da yawa layin da suka yi dan su gansa ne da idannuwansu domin alkhairinsa ya jima da tardo su aman ka ga bawan Allahn nan ko mai yasa baya son a gansa

Sosai Abdul fatah ya dage yana bada labarin Alaidine, sai da ya koro da surutu ya dakata ya ce" aman kai ya aka yi ka tambayeni sunnansa? Ko ka sanshi ne??

Jamail ya saki murmushi, ya juyo wajen inna da Aisha da suke kallonsu sun rataba masu hankalinsu dan gane inda wannan labari ya nufa, Wujdane kuwa na daka tsidahu a zuciyarta tana aiyana mai kuwa zai hana shi banda girman kai irin na masu kudi,

Jamail ya ce" inna, kinga masalacin da malan ke bayar da karatun nan toh nasa ne, a wajensa na karbo kayayakin nan, ina fada masa a kawo na gidan Malan yace na je gidansa na fitar wai danma matarsa mugun hali ne da ita bata son kyauta wa wasu da ba yan gidansu ba, domin yan gidansu sun cika gidan tana ta fitarwa aman idan wani ya zo sai ka ga ranta ya baci, bata son ana rabar mata miji, ni na san da shine ya fitar ko yana tsaye aka fitar da bansan bama ya zamu kare da ku inna,

Inna ta dafe kuncinta ta ce" toh ikon Allah, shi kuwa wannan bawan Allah haka yake da sannin romon sadaka? Allah ubangiji ya jibanci lamuransa, ya bashi ladan sadakar da yake ta kasance masa haske a gobe kiyama, aman a anguwarku yake ko???

Jamail ya ce" shine mahaifin boy

Su duka sun cika da mamaki har wujdane dake daka sai da ta dan dago ta dan kale su, ta mayar da kanta sai ta tsinci kanta da cewa ai gwara da bai zama aku ba irinka(🤦🏻‍♀🤣)

Haka sukai ta labari tsakaninsu, wanda Inna ta yi gum da mitar kayan nan sun yi yawa ta bi su da adu.a,
Abdul fatah da ya ji dambun nan shi za.a kaiwa sai ya lalubo dubunsa guda ya fice, bai dawo ba sai da sayaya niki niki ta su kifi da albasa yanda za.a yi yar jijibar miyar ci da dambun Aisha kuwa cike da murna ta karba ta shiga gyarawa

Konci tashi ba wuya, azumi har ya zo karshe wanda ake saka ran wayewar gari da sallah za.a tashi,

Idan ka shigo layin su Wujdane abin sai ya baka mamaki, duda karamar sallah ce aman cikin ikon Allah ko.ina ka wulga yara ne da yan mata da samari kowane na faman gyara kansa kunshi wa.inda basu samu yi a shekaran jiya da jiya ba

Aisha ce zaune ta gama hada sibkarta, tana bin Wujdane da kalo, ta san ita zata yi mata kunshin aman sai dan kai kawo take tana kara share gidan da baida dati ko kadan, su Mairo ma sun yi aiken dan girman Allah ta taimaka wannan salar ta dan yi masu komai kadan dinsa , fakat ta furta ba zata yi ba

Aisha ta kali ledar ta kuma dagowa ta shagwabe fuska ta ce" yanzu aunty ba za.a yi min ba kunshin nima Aishar ki?

Dan harare ta jefeta da shi, inna dake dakin malan tana ta faman gyara masa domin ana saka ran a ranar zai dawo daga masalaci da yayi kwana goma sha biyar , ta ce" ai fa sai ki zauna jiran ta yi maki, ba sai da na fada maki ba ki nemi mai kunshi mai neman na kanta wace ba zata wulakantaki ba tayi maki abinki tunda ke kin amince mace ce ke kina son gyara ki barta da shirmenta aman ke kin nace sai nata dan ta iya take yiwa mutane yanga, ita ta zauna a yi mata kitson ma ya gagara ta kunce dokar kuma ta daure gashin duda ba inda zaku ai ana samun baki, sai ka kimtsa kaima ka ji dadi irin na kowa, aman kiri kiri ta hade fuska ba damar yin wani abin na jin dadi

Kai wujdane ta dafe, ita dai ta rasa mai ya sa innarta komai ta yi sai ta ga rashin dacewar hakan
Bata shirya yiwa Aisha kunshi a lokacin ba aman dan ta rufe bakin innar ta zauna ta shiga zana mata

Aisha murna fal cikin ranta, a zahirin kuwa sai doka murmushi take, domin kunshin ya zanu, nima masha Allah na furta domin idan ba miskilancin Wujdane ba ta iya kunshi ashe har haka, tamkar wata amarya Aishar ta koma anyi mata kananuwan kitsonta ga yalwar gashi sosai, fuskarta ta jayu da kyau, ga kuma kunshi,

Inna na gamawa ta dora ruwan zafi a murhu, wanda yana yin zafin ta juye ta silka shi da ruwa ta zuba yodo a rabin, a sauran kuwa ta juye a buta, fir ta yiwa wujdane jan ido ta zo ta darje mata kan, wanda har wani zafi fatar kan nata ta fara, aman wata iska mai dadi na shiga kofa kofa na gashin nata, sosai ta ji dadin yanayin nata har innar ta gama daga nan wajen tun kafin ya bushe ta shafa mata mai mai maski maski ta hade shi ta daure mata shi a tsakiya sosai ta ja shi yanda fuskar zata dan fito, sannan ta tufke shi ta laulaye mata shi sosai

Zo ka ga wuwurga idannuwa wajen wujdane, kan nata ya dauki ciwo a lokacin wai anyi mata kitso, har wani lumshe shanyayun idannuwan magenta take tana cije lebenta dalilin hayaniyar anguwar

Wani yaro ne Saminu ya shigo a guje tun daga kofa ya kwala salama, yana shigowa ya ja ya tsaya,
Saminu ba dai firirita ba, akoy shi da taurin kai ,

Yana kale kalen gidan ya ce" wai aka ce ana magana da Wujdane
Chapter 12 · 0% Book details