← Book details Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 26

Sashe 21

Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tunani yake so yayi, so yake ya tsayar da tunaninsa, so yake ya gane a wani yannayi yake ciki so yake ya farka a mafarkin da yake , aman ina ba hali, zuru ya yi ya zubawa hoton boy ido dake mane da jikin bangon dakin, a yannayinsa kamar wanda yake son fitar da wani abin a jikin hoton , ya dauki lokaci mai tsayi wanda shi bai furta um bare um.um ba

Jamail ne zaune gaban tv yana kallo, duda a yau din nan ya tashi da wata faduwar gaba, aman yana dan jin karfin jikinsa kadan hakan ya saka shi mikewa ya watsa ruwa ya zo ya saka tv gaba yana kalo,

Direba ne ya tsayar da motarsa a harabar gidan Alaidine, Mom ta fito inda Aba ke tsaye yana jiran karasowarta ya fito daga cikin masalaci

Tana fitowa ta karaso fuskarta cike da tambaya,

Aba ya gyara tsayuwarsa, ya shiga shaida mata abinda ke faruwa,

Gim tayi tana sauke ajiyar zuciya, ta san da kwannan zancen Alaidine fir ya ki Jamail ya auri Wujdane dan yana shaida bata da tarbiya, sai gashi abin ya kasance a shi, wato dai Wujdane ta gidansu ce gwara ma su daina jayaya da hakan

Mom ta fara shiga Falon inda ta tarar Da Alawiya na zaune saman kujera tana shan fruits, ta sha kananuwan kayanta domin ana dan zafi zafi a garin, tana kalon series a tv

Mom ta yi salama ya kai sau hudu hakan ya saka ta shiga ,

Ido hudu suka yi da Alawiya dake zaune dangalgal ba wai dan bata ji salamar bane aa, cikin tsarinta kenan idan bata san da zuwanka ba ba wani tarba da zata iya yi maka

Gannin Mom bai saka ta irin zaburan nan ba, na gannin sirikinka a cikin gidanka, saima wani kara kalonta da tayi ta ce" au da Mom ce? Haba ni da naji salamar a raina nake fadin ko waye haka da wannan lokacin bayan lokacin hutu ne???

Mom ta danyi murmushi, ta ce" Alaidine fa? Yana gidan ne?

Alawiya ta dan daga kanta benensa, ta dawo da kan nata ta ce" toh ni dai na ga motarsa kuma na ji kamar budewar bangarensa, aman ban san ko yana nan ba, kin san baya son ana shiga lamarinsa idan har ba shi ne ya jawoka ba

Da mamaki Mom ta gyada kai ta koma ta yiwa Ba iso kawai , wanda yana shigowa Alawiya ta gaisheshi shima ba a wani mutunce ba , ya amsa yana kawar da kansa suka haura sama falon Alaidine

Ratsawa suke domin du dakunan da ya shige kawai a bude ya bar su, suna yi suna salama, har suka karasa dakin da yake zaune

Salama Mom ta yi ta maimaita, hakan ya saka shi dago da kansa yana amsawa fuskarsa na kan fuskar mahaifiyarsa

Kokarin mikewa yake yana fadin" Mom, ke ce??

Karasa shigowa suka yi gaba dayansu, Mom ta zauna daf da shi ta kamo hannunsa na dama da ta ji ya gauraye da zafi,

Aba ma waje ya samu ya zauna, inda gaba daya suka yi shiru ba wanda ya furta ci kanka

A hankali Alaidine ya dago da kansa ya sauke kallonsa kan Mahaifinsa, murya a shake ya ce" aman aba, bayan na sanar maka ga dalilina na kin ta shigo zuri.armu why Aba zaka aura min ita? Ita ce fa abinda Jamail yafi so a duniyarnan bayan ku, Aba ka ga irin yanda yake ba ci ba sha ba wani walwalar kirki dan kawai ta furta masa bata son sa ina da ya ji wannan labarin? Aba kuma bama wanu daban ba sai ni Aba? Ban wani takamaiman santa ba aman na ji bana sonta a cikin gidan kanina ko a abinda ya shafi yan uwana sai gashi Aba ka hada ni da ita? Abana la bani dama na yanke igiyoyin nan da ka daura min Abanna,

Elhaj Kadri bai katse shi ba, sai bayan ya gama, a gankali cikin muryar kontar da hankali ya ce" ni Alaidine danme yasa ka tsani yarinyar nan haka bayan kaima ka furta yanzu cewar bata yi maka komai ba?

Alaidine ya sauke ajiyar zuciya ya ce" Aba yarinyar nan munafuka ce, bata da nutsuwa, Aba ta wulakantar da kanta, sannan ai Allah ma yayi mana nuni da mu zabawa yayanmu iyaye na gari Aba

Aba yayi murmushi jin ta inda Alaidine ke son bilo masa, ya ce" ka san menene Alaidine, yarinyar nan ita ce ta biyu da na je da kaina nema maka aurenta har na dauro maka cikin ikon Allah, mahaifiyar Huzaifa ka saketa dan kawai ta jefe ka da kalmomi bayan kai namiji ne, kayi karatu mai zurfi kana cikin kara yi , a musulunci an fada mana cewa mace ana yi ana tankwasota ce, a nasarance an gwada hakan, aman cikin ikon Allah sai ka zamo wani mai auri saki wanda matan da ka aura ni ban taba kawowa raina cewar wai zaka yi hakan ba, to ka ga dai Wujdane amanata ce, ni kuwa zan gargadeka da babar murya, walahi Alaidine karya kake ka mayar da Wujdane karamar bazawara, idan na kawo maka ita gidanka karshen ki ka gutsutsura namanta, aman fa na hane ka, na haramta maka sakinta Alaidine, idan ka kyautata zamanka da ita ka so kanka da nutsuwarka idan ka muzanta kuma ka san hukuncinka

Mom ce ta dago da kanta gannin Aba maimakun ya lalaba Alaidine din aa, sai fada yake surfawa, yannayin tausayi ta yi da fuskarta ta ce" Aban Alaidine....

Hannu Aba ya daga mata ya dawo da hankalinsa wajenta, ya ce" na gaji da zubawa yaron nan ido yana auri sakin nan, yau da ace yana da kane mata aka yi masu haka yaya zai ji? Baya tunanin haihuwar mace a nan gaba? Ke kar na kaiki nesa Momynsu baya dora abin a kanki yayi tunanin idan hakan ya same ki yaya zai ji?

Da sauri ya dago da kansa , daman idannuwansa sun gama rinewa, shi ya tsani ana jan magana guda, aman shine Abansa zai saka momynsa? Shi du duniya ai ba wanda ya kai momynsa zama mutumin kirki, sannan ira kadai ce macen da ya sani ba munafuka ba,

Mikewa Elhaj Kadri ya yi ya fice, wanda bai tsaya ko.ina ba sai bangaren da Jamail yake, zuciyarsa cike da tausayin yayan nasa, aman idan bai fitowa Alaidine ta bayan gida ba ya aika ya saki Wujdane a yau yau din nan domin bata ce masa komai,

A hankali Mom ke kontar masa da hankali, wanda yana sauraronta a kasan zuciyarsa yana ayana yanda zai koyawa yatinyar nan hankali, Mom ta ce" idan ma kana zarginta koda idannuwanka sun nuna maka da ba mai zama dam bace, ka yi hakuri ka rungumeta sanadiyarka sai ka ga ta shiryu son, yau da ace mahaifinka yayi watsi da ni, da yanzu bansan inda kake ba, mai yiwuwa a watsar da mu gaba dayan mu a raraba mu,
Ta karashe zancen tana kallon kasa tana gannin tamkar yanzu ne abin ke sake faruwa da ita

Tausayin mahaifiyarsa ne ya tsarga masa zuciya, a hankali ya dora kansa saman cinyarta ya ce" Mom, ke kadara ce, karki hada kanki da wannan banzar

, tana shafa sumar kansa tace" kowa ma kadarar ce ke afku masa kafin daga bisani idan yaci gaba to wannan kuma yana neman izgili, sannan yau kowa da ka ganni yana son ya zama dan mutunci, yana son ya rayu a cikin mutunci, karka yi gagawar yanke hukunci dine,, ka bi mahaifinka a hankali ka ga dai yanda ya dauki zafi da kai, dan haka ka faranta masa kar ku fito rana fa,

Shi dai sauraronta yake, sannan abinda ya sani ne bai isa ya rabu da yarinyar yanzu yanzu ba, a hankali idan hankalin mahaifinsa ya konta zai nemi ya raba auren nan, shi fa ba zai iya zama da yarinyar da kanninsa ke so tamkar hauka ba, shi yama zai iya wannan cin amanar, ga yarinyar fitsarariya ai idan ta samu hakan birgeta ma zai yi

Sosai Jamail ke kuka rungume a jikin mahaifinsa, wanda ya gama jin abinda ya faru, harma Aisha na zaune a matsayin matarsa Wujdane kuwa matsayin matar yayansa, ya sani ne shikenan Wujdane ta kubuce masa, domin da wani ne aka aura mata shi sai yayi jiranta, aman sai ya fado kan yayansa kuma a yanda abansa ya fada yayan nasa ya tsaneta tamkar ransa, ya san wanene Alaidine, idan ya tsani abu ya fiya zurfafawa a lamarin hakan ya saka shi jin tsoro matuka a kasan zuciyarsa, koma wa zai auri Wujdane dinsa baya so ta wahala, duda Alaidine ya kasance wanda ya raine shi, ya bashi tarbiya, ya kaunace shi, ya bashi dukan bukatu na nan gidan duniya, mutumin da ya sha salwantar da farin cikinsa wa su, ya san ba wani rabo kuma tsakaninsa da Wujdane, ya hakura da Wujdane, aman zai roki alfarmar kar a wulakanta masa da wujdane, hakan ne ya saka shi fashewa da kuka ya rungume mahaifinsa,

Sosai yayi kukansa har ya gode Allah, kafin yake tsagaitawa yana share hawayensa, a hankali ya ce" Abana, Allah ya sa hakan shi yafi zama alkhairi, Allah ya saka maku da alkhairi ya kara lafiya, Allah ya biya duniya da kiyama

Wani irin abu ne ya saukowa Aban wanda ya matukar kashe masa jiki, Jamail, jamail, ba dai hakuri ba, jamail ba dai daukan girma ba, haka Aba yayi ta lalaba shi, ya samu ya dan ware kafin yake iza keyarsa ya kimtsa suka fice tare masalaci

Bayan salar magariba, sosai ake ta rabon abincu na sadaka da godiyar allah, Aba ne ya zubawa Alaidine ido gannin bashida niyar tayar da motoci a je daukan amaren bayan gidan cike yake da jama.a, wanda alaidine din na can yana fama da Alawiya wace sai a lokacin ta ji mijinta yayi aure ta tare shi da koke koken sam bata san zancen ba, yayi zuru yana kallonta........
[3/27, 10:00 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄

*22*

WRINTING BY *SAJIDA*

Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*

MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*
Chapter 21 · 0% Book details