← Book details Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 26

Sashe 10

Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cike da bacin rai ta ce" eh man, dan me ba zan dake shi ba? Shi dan *Shege* ?

Tamkar an dauke wuta haka abin nan ya dirar masa, wanda ya yi sanadiyar kara nutsawarsa a rayuwar duhu,
Hannu ya daga ya wanka mata lafiyayen marin da ta kai kasa bakinta ya fashe take gefen kuncinta ya sundume

Hannunsa na rawa ya nunata ya ce" *na sake ki saki biyu* idan kin samu miji zaki iya aure domin baki da idata

A lokacin mahaifinta ya bayana a fallon yanda ya mayar da ita tamkar ganga, yayi alkawari ba dai a gidansa ba

Cike da tashin hankali ta nufi gidan su Alaidine din ta fadawa mahaifiyarsa da kanta komai,

Duda ta ji haushi hakan, aman sai ta ga idan ta kiri khadija ta yi butulci , domin itama da aka kore ta mijinta ya rungumeta, hakan ya saka ta bata daki take zaune tamkar gidansu

A haka aka yiwa Anwar aure da matarsa Bahija, yarinya mai daraja mai daraja mutane,

Tun daga wannan lokacin sai Alaidine ya dawo sabo, yakan zubawa mace kudi domin ya gama fasara su a kudinsa suke so, ya aura idan kun jima ku yi wata biyu ya salame ki domin yakan gwada mace cikin hikima, idan bata tangarde wajen rikon xilon dansa ba, toh zata nemi fitina wajen gididige sannin waye shi hakan yake sakawa ya bale igiyar ya dauki wata

Yaro da shi auri saki ya mayar da shi tamkar a jininsa, abin nan na ciwa mahaifansa tuwo a kwarya, dan gujewa ya afka zina yake saka mahaifinsa nemamasa auren da anje an kwan biyu a gundule shi, domin zuciyarsa ta fi karfinsa ba zai yiwa wara banza uzuri ba

Wannan kennan,

Ci gaban labari

Haka ya fito da katon jirginsa na wasa ya mikawa Jamail ya ce" plz ka je da shi kawai, ya kwana wajenka aman karka yarda ka je da shi gida ( dan kar Khadija ta hadu da shi )

Daukansa ya yi yana ta yi masa dabara inda boy ya karkata hankalinsa gannin za.a fita yawo

Jamail na fita bai zame ko.ina ba sai gidan inna, dan ya je ya ci dambun da take domin ba karamin tafiya da imaninsa ya yi ba

Yana shigowa ya tarar da mutuniyar tasa tana yanyanka albasa, Aisha kuwa tana daka yaji,
Bayan ya gaisar da innar ya samu waje ya zauna Boy na lilike masa dan rashin sabo

Inna ta fito da kuli a leda baka tana fadin" yau ga miji yau ga miji, tana kokarin yiwa boy wasa aman ya lafe ya ki yarda ta dauke shi haka ma Aisha

Wannan ledar ta mikawa Jamail ta ce" yarona haka zamu fara da kai? Kul ka kiyayi fara hakan da ni sai na ji ba dadi

Cike da gannin girman tsohuwar yake kallonta, ya yi murmushi ya ce" inna, yaya ne ya fitar sadakar da yake bayarwa, shine na karbo maki naki, inna kennan idan Abdul fatah ya kawo ba zaki karba ba???

Wata kunya ce ta kamata, haka yake mata wannan wayon sai ya nuna kenan dan shi ne ya yi mata abu ba zata karba ba,

Mikewa ta yi dan zuba dambun tana adu.ar allah ya sa ya gama da duniya lafiya da shi da mahaifansa

Ihu boy ya saka wanda ya saka Wujdane saki wukar da take dan yanyanka albasa tana kallonsa

Fitsari yake ji sai ihu yake kuma ba zasu taba shi ba

Cike da jin haushi Jamail ya ce" zan fa wanwanka maka mari Boy meye hakan? Ka nutsu a cire maka wandon ka yi mana

Aa shi ya dage sai ihu yake shi jacuzzi jacuzzi,

Tsaki Wujdane ta ja ta mike ta nufo shi, cikin yaren turanci ta miko masa hannu tana fadin" zo nan boy dina na kai ka ka yi fitsarin na baka chocolate

Ai yana jin hakan ya dare gannunta yana sauke ajiyar zuciya ta yi bayi da shi

Gaba dayansu da ido suka bita na mamaki, duda sun san dan ya daina ihun nan ne ya daina damunta da ihu ya saka ta lalaba shi, domin itama ba wani onuwa daya take sha da yara ba, basa shiri da yara hakan ya matukar basu mamaki,

Jamail ya juyo wajen inna ya ce""::

........☹
[3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄

*11*

WRINTING BY *SAJIDA*

Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*

MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....

Jamail ya juyo wajen inna da mamaki fal a shinfide a fuskarsa ya ce" inna, daman kanwata tana shiri da yara?

Inna ta yi dariya ta ce" kanwar taka a abin mamakinta baya karewa

Suna tsaka da maganar inna ta zuba masa dambun a plat dan madaidaici ta fito da Boy ta gyara masa wandonsa ta dawo ta zauna tana kallon kofa wani abu na fizgarta kan ta ficewarta

Wani yaro ne ya yi salama da naira goma a hannunsa, yana dan rakubewa ya ce" inna wai ana salama da MaMa,

Inna ta dago da kanta tana kallon yaron ta ce" wa ke salama da ita? Yama fa ya yi bana son fitar nan

Yaron yana dan bari da hannayensa ya ce" wai ya ce ace lukman ne

Firgigit ta dago da kanta daga kallon kasan da take a tare da Jamail, shima bai shirya ba ya dago cike da mamaki da karyata kunnayensa, Lukman? Waye lukman? Daman Wujdane na zance da saurayi???

Tunaninsa ne ya katse daidai lokacin da Inna ke fadin" to ai tana jin ka

Harara ta watsa masa ta ce" ka je ka ce ta yi baci

Tun kafin ta rufe bakinta yaron ya juya a guje yana maimaita maganar da zai fadi din dan kar ya manta

Tsam Jamail ya tsame hannunsa daga cikin abincin ya mike ya darwaye ya yi hanyar kofa

Da harara Wujdane ta bi shi ta ja tsaki ita kadai tana fadin natace

Yana fita ya tarar da Lukman na faman buga babur dinsa

Salama ya yi masa ya mika masa hannu suka yi musabaha

Lukman kallon Jamail yake, a yannayin girman jikinsa ba zaja bashi shekara 20 ba sai dai sama, ga cika ido

Murmushi Lukman ya saki ya juya a hankali a can kasan ransa yana ayana du da soyaya ba ruwanta da kyau mulki ko arziki ba, zab gwada nawa sa.ar ( toh fa )

Zaune yake cikin falonsa ya dafe kumatunsa da hannu bibiyu yana sauraron mahaifiyarsa hajiya Marwa, cike da hikima ta ci gaba" Haba Alaidine, ka ringa sasautawa zuciyarka, yanzu tsakani da Allah mahaifiyar boy na zaune ita ta ki ta sake suren wani, kai kuwa ka yi rantsuwar ka gama zaman aure da ita, du bama wannan yanzu dan tana gidan shikennan ba za kana leko mu ba? Ni yaya kake so nayi ne?

Cike da kaunar mahaifiyarsa wace bata taba nuna kyamarsa ba ya ce" Mom, idan ta yi aure ta bar gidan zan koma zuwa, mom

To kai ya maganar auren naka ne? Ta katse masa hanzari, ta ci gaba da fadin" ko na zaba maka ne???

Dago da kansa ya yi wannan karin, yana kallonta ya ce" Mom aa, bana so ki zaba min na dawo na kuma saka ki kunya, zan yi auren kwananan insha Allah

Kallonsa take tana jin ciwon irin rayuwar nan nasa, arziki dai na gidan duniya Allah ya malaka masa, wanda yana cikin mutanen da ake maganarsu a kasar, aman ka kasa zama cikeken mutun ta fannin ajiye iyali????

Ajiyar zuciya ta sauke ta shiga kiran layin mijinta dan jin a goben zai taso kuwa daga abujar wajen meeting?

Malan na shigowa d fara.a fiye da da cikin gidan,

Bayan sun gagaishe shi inna ta dauko kudin nan da ko kirgawa bata yi ba ta ajiye da niyar malan ya zo ta danka masa,

Kafin ta yi masa bayani ya karkace ya ciro kudi a aljihunsa yana ta aikin murmushi ya miko mata

Ido ta fitar waje bata karba ba ta ce" Malan wannan fa??

Fuskarsa wadace da murmushi ya ce" Masalacin da nake bayar da karatu, wato wanda yayan Jamail ya gina, a yau aka shigo aka nemi malaman dake bayar da karatu da masu kula aka bamu dubu ashirin ashirin, sannan a lokacin elhazen kamar hadin baki suka shiga bamu kyaututuka, kinga dai cikin ikon Allah yau a masalaci kinga abinda Allah ya bamu baki daya malaman na bada shawarar a hade kawai a raba domin akoy wa.inda yau basu samu halarta ba, su din ma ba masu karfin bane, sai aka bi shawarar nawa aka hade aka kasa kinga na tashi da wajen dubu arba.in da shida

Kallonsa kawai take a can kadan zuciyarta cike da tausayin mijin nasu da kuma godiya ga Allah, ta san dai ko ba komai a yau ya kara samu domin ma.aiki,

Murmushi ta yi ta mika masa na hannunta ta yi masa bayanin yanda suka yi da Jamail

Adu.a kawai yake yiwa bayin Allahn nan yana ta godewa Qllah kafin ya sake kallonta cike da fara.a ya ce" kin ga sai na kai kudin makarantar Wujdane, dubu bakwai ne da dari hudu da Malan din ya lisafa abinda ya dace sai na cike, sannan ku samu ku yi sabin dinki ku sayi su mai su dan turare sannan a sayo abinci ko???

Cike da murmushi take kallonsa tana amsa masa, da insha Allah, sannan ta gyara zamanta a dukan abinda ya zana bai sako kansa ba, domin cikin ikon Allah samarin gidan suna iya kokarinsu wajen yi masa sutura da su kansu, danma karatu na dauke hankin Abdul Fatah,

Mika masa gaba daya kudin ta yi, ta ce" malan du abinda Aka zana Allah ya idasa nufi,

Tana gama fada ta mike fan gabatar masa da shinfidarsa
Chapter 10 · 0% Book details