← Book details Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 26

Sashe 13

Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ji tayi tamkar saukar aradu a kanta, kwal uba sunnana gatsal din nan ya kama dan uwarsa?

Ai kuwa tana dago da kai Saminu ya lura ashe ita ce a zaune da hijab dinta da ya jike da ruwa, ido ya zaro bazai manta dukan da ta yi masa ma wanda ko babansa bai taba yi masa irinsa ba duda dukansu da yake, ido ya kwalalo waje ya hade hannayensa waje guda

Ina ai gani ya yi hakan ba zata fishe shi ba, ganin irin yanda ta mike a zazafe ta nufo shi, daman a cike take da haushi tamkar ta fashe sai ga mai kan dauka ya tsokale ta,

Arcewa Saminu ya yi a guje yana ihun kiran sunnan mahaifiyarsa yana fadin" mama wujdane ce zata dake ni

Ai kuwa innna bata ankara ba sai giftawar Wujdane ta gani da gudu ta marawa yaron nan baya, da azuminta, da girmanta, da bakinta a kofa Lukman da abokinsa sun zo mata da kayan sallah

Kaka kara kaka wujdane nayi zaton kin nutsu ashe konto kika yi?😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲😲
[3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄

*15*

WRINTING BY *SAJIDA*

Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*

MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....

Yana zuwa masalaci jama.a sai harama ake ana mimika dabino ga gefe manyan jarkoki ne cike da su kunu ko tukudi masu sanyi wa.inda mutane ke kawowa sadaka, wasun kuwa daga can gefe suna ta kokarin gannin dan jaririn watan dake kokarin bacewa domin fitowar ranar ne

Nan da nan aka shiga musabaha ana godiya ga rabil izati, jama.a na neman yafiyar junnansu sannan ana ta buda baki

Shigewa ya yi cikin tarin mazan nan, ya zauna ana ta mimiko kunnu a kofuna

Karba ya yi yana hangen wasu tsofafi dake zaune gefensa, da alama dare duka yi har shan ruwa ya riske su,
Kansa ya juyo wajen MLan dake magana da Hamza, suna yar dariya da alama maganar mai dadi ce,

Haramar sallar da ladan yake maimaitawa a lasifika ya saka kowa mikewa masu kuskurar baki na yi, wa.inda a kuskuren suke har sun bi sahun sallah

Muryar Malan ne, wanda a ranar shi ya yi limanci yana jan sallar inda Alaidine yake ji gaba daya wata nutsuwa da tsoron Allah sun saukar masa, muryar malan ta saka shi nutsuwa fiye da tunanin mai karatu, haka ya samu kansa da zama bayan an gama sallar , almajirai sun bude karatu kamar kulun , wasun kuwa na zuwa kara daukan karatu qajen malan,

A hankali ya dauko alkur.ani shima, ya zauna har aka zo kansa ya je gaban malan, aka biya masa karatu wanda kwarai ya ji dadin hakan

Yana lure da malan sai da kowa ya watse kafin shima ya mike ya tafi bayan ya yiwa jama.a da dama salama, cike da fara.a ya fito ya kuwa dauki hanya yana doka sauri

Ajiyar zuciya Alaidine ya sauke, ga dukan alamu sun nuna mutumen kirki ne, aman zai kara nazartarsa, ya tabata idan har na gari ne matarsa ma haka toh zasu baiwa yaransu tarbiya, duda yanzu zamani ya zama na tir, domin kana tarbiyantar da yaron ne, a waje idan ya hadu da mugayen abokai suna warware maka tarbiyar yaro, shi dai abinda ya sani shine, bazai taba yarda irin rayuwar da yake ciki na rashi dacen macen aure ta kirki kanninsa ma ya fada a haka,

Shi dai adu.arsa shima ya samu mai dama damar kamar mayar anwar

Washe gari an tashi da sallah, inda cikin ikon Allah du jama.a sun ajiye azumi an tashi da sallah baki daya,

Zo ka ga yanda mutane ke shigo da fici,

Malan ya sha sabon farin yadinsa da Hamza ya dinka masa, ya dora sabuwar hularsa da takalminsa da Abdul Fatah ya kawo masa, sai sabon carbi da turare, fuskarsa na fitar da annuri

Yana fitowa ya tarar inna sai gyaran kayan miyarta take, da zabi biyu a gefe wa.inda ya saka aka kawo mata, sai aikinta take cikin nutsuwa, ta sha sabuwar atamparta ta saka kwali a idannuwanta, sai ta fito radam da ita sai sheki jikinta ke yi na mai da ta shafa vaseline dinsu sabo, ga turare da ta fesa yau ranar sallah kowa kwaliya yake

Cike da fara.a malan yake amsa gaisuwar yayansa, kyam kuwa yana karewa matarsa kallo wace ta fitp masa a yarinyarta, masha Allah shi kam ya godewa Allah da ya bashi innar yara a matsayin matarsa malakinsa

Haka samarin suka fice wajen idi , inda yan matan suka shiga taya inna aikin cikin gida da zabin nan da ake shirin tsantsara masu dafuwar cire kune🤣

Yau sallah kwana uku kenan, Jamail bai samu lekowa gidan malan sai a ranar nan domin hidomomin sallah gidansu a cike yake da yaya da jikoki ana ta shagali ana ta murnar sallah, harda Alawiya ma kanta ta zo bisa umarnin Alaidine wace take taku daidaiya tana yabawa khadija magana, itama tana ramawa

Shiru ya yi yana sauraron inna na yiwa Wujdane fada kan tace ba zata bi su yawon sallah ba shi da Aisha dake shiryawa da yayan ysyunsa da ya dauko yaran wajen Anwar da Boy, du sun sha shigarsu ta manyan kaya kamar ka sace su ka gudu

Mikewa Wujdane ta yi ta fito ranta a bace ta fada wanka, ko maganar ma yau bai samu ba domin sai take ganin ai laifinsa ne shi ya jaza aka takurata wani yawon sallah

Fitows ta yi ta shige dakinsu, tana sauraron yanda yaren suka cika gidan da surutu

Mai ta shafa, ta dauko bakar abayar da Malan ya kawo masu ta walwale tana niyar sakawa

A hankali Aisha ta rike hannunta ta ce" Aunty, ki yi hakuri dan Allah na dan gyara maki fuskar ki, kin ji auntyna dan Allah ba dan ni ba

Yatsina fuska ta yi ta zauna , Aisha taa dan samu ta dan gyara mata fuskar duda kwali ne kawai sai girarta da ta caje mata ta daidaitata, fir ta ki a saka mata jan baki a pink din lebenta sai dan lips aka dan goga mata,

Abayar ta saka bayan ta daura zani daga ciki don karta like mata a jiki,

Gashin kanta take faman sai ta dunkule waje guda dan ta daure aman idan ta gwada nada mayafin abayar sai gashin ya cunkushe,

Tsaki ta ja da ta saki gashin ta nanada ta ga ya yi dan cicif a jikin nata tana ayana wannan ai sallon iskanci ne

Kallonta kawai Aisha take, sam kalar Wujdane ba ta bahaushiya bace, ba ta yan africa bace, tamkar wata balaraba haka ta fito ga kalar adon jikin abayar duwatsu ne blue da fari sai suka haskaka idannuwanta masu kwayar ido blue

Dan takalminta plat ta saka, suna yiwa inna salama wace ta yi masu gargadi sosai , ta kara kawa Wujdane kune banda fada,

Haka suka fito inda Jamail ya kasa daina kallonta, a kasan zuciyarsa yana ayana daman haka take ? A hankali ya lumshe idannuwansa bayan ya bude mata gaba ta shiga da Boy a hannunta ta zauna a kasan zuciyarsa ya furta" ya Allah, idan har inna da rabon auren wannan baiwa taka , Allah ka kadara min shi kafin nayi kaura gareka

Haka ya zagaya ya shige ya ja motar ya fara nufar gidansu domin can zai fara kaisu kafin su karasa park

Yana zuwa mamaki ya kashe shi irin yanda gidan yayo tsit, tamkar ba mutane bayan a fitarsa ma ya barsu a barbaje suna ta shalakwalinsu harda yayan kawayen Mom dinsu

Juyawa ya yi sai ya hango motar yayansa, wace ranar idi ya fara takata, a fili ya furta" yawa ga dalili dodonsu na gidan

Su dai ba wanda ya fahimci maganarsa, sannan Aisha da Wujdane sun kasa fita a motar, mamaki, tsoro, da komai ya zubun masu, tambaya suke yiwa kansu, wai daman Jamail nan nw gidansu? A irin gidan nan yake rayuwa aman yake zuwa ya zubar da kansa ya dangwali abincin tukunyarsu ya sha labarinsa ba abinda ya dame shi?

Ku fito mana, muryar Jamail yana kallonsu, yaran ma haka suna kallonsu

A hankali ta sako fara kal din kafarta wace bata yi mata kunshi ba, hakama Aisha ta zuro tata da ta sha kunshi masha Allah

Suna fitowa Wujdane ta ja ta yi tsaye da Boy a hannunta taki bin bayansu tana kallon kasa Boy kuwa na ta yi mata magana yana murnar yau ya zo wajen kakaninsa

Daga saman gidan yake tsaye, ya dage labulen kofarsa yana kallon balbalin gidan Alawiya a gefe tana shan jus tana kada ido tanai mai bayani adadin kudin da take bukata dan kaiwa yan gidansu barka da sallah,

A kan idannuwansa suka fito,
Kwarai ya ware idannuwansa yana kallon su, har du suka shige banda yarinya daya da ta tsaya da Boy a hannunta,

Mamaki yake, su waye wa.innan kuma? A ina boy ya sansu boy da kin yarda shine harda yarda da baki haka?

Bai gama tunaninsa ba ya ga Jamail ya dawo ya harde hannunsa daya a kirjinsa yana ta zuba murmushi da alama lalaba ta yake

Gabansa ne ya yanke ya fadi , wani haushin yarinyar ya darsu a zuciyarsa , a fili ya furta" rashin tarbiya ne ko kwadayi ne zai kai budurwa gidan su saurayinta kafin ma a yi masu baiko????????

Alawiya dake zaune ta dago tana kallonsa dan sai ta ji kar ya yo magana, a fili ta furta magana ce????

Kafin ya bata amsa ya juya ya fito dan tabatarwa zarginsa, idan kuwa hakane sai ya sabawa Jamail, daman ba yar gidan mutunci ya je ya dauko ba? Mai yake son mayar da kansa da su kansu ne??????????????????????

Toh fa
[3/27, 9:59 AM] ‪+234 803 957 7698‬: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄

*14*

WRINTING BY *SAJIDA*

Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,

*SAJIDARKU CE*

MARUBUCIYAR:

*YAR MAHAUKACIYA*

*DUK KARYAR KADA*

*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*

*NEMAN NA KAINA*

................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....

Wani irin fitowa ta yi da gudu, burinta ta damki yaron nan ta jijiga masa jiki ya gane bashi da wayo ko ta samu sa.ida a cikin zuciyarta
Chapter 13 · 0% Book details