Sashe 17
Bani Da Zabi Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idannuwansa ya sauke kan Wujdane cike da tarin tausayinta, sai a yau yake tuhumar kansa shin gazawa ne yayi da halayar wujdane har ya yanke hukuncin yi mata aure da gagawa haka har gashi ana nema a wulakanta ta ko me? Shin bai dauki rayuwar wujdane a matsayin kadarar da Allah ya dora masu ba be ya lamunce yanda take ne har yaa saka gagawa a lamarinta bayan ya kwana da sannin gagawa aikin shedan ce? Ina tunaninsa ya je har ya bari fushinsa yayi rinjaye a yarsa mafi soyuwa a cikin zuciyarsa?
A hankali ya karaso daidai lokacin da inna ta shigo, itama ta sha shigarta ta alfarma ta zauna tana kallon yannayin mijin nata murya a raunane ta ce" Malan, ni lafiya kuwa ake kananun magangannun ne?
Dago da kansa daga kallon yayansa da suka zubo masa idannuwa ya yi, ya hadiye wani yawu mai wuyar fita , a hankali ya ce" innar yara, yaron nan ne shiru na wajen Wujdane, ko lafiya?
Gabansu ne ya fadi gaba dayansu, Wujdane ta jimke hannun Aisha wace jikinta ya dauki dumi ta kontar da kanta saman bayan Aishar tana wani nishi ciki ciki na bacin rai
Malan ya ce" abinda nake so da ku shi ne ku gaba dayanku shine kar ku yarda ku tayar da hankalinku kam komai, ku yi tawakali da dukan abinda zai samu bawa mai kyau ko mara kyau kadararsa ce daga ubangiji, ki zauna da su bara na je kawai
Mikewa Malan ya yi ya fice, zuciyarsa a matukar karye ya fita wajen jama.ar dake zaune abin har ya zama na magana sai dauka ake danma wa.inda suka zo da Alaidine basu tarki yin wani cece ku ce bisan lamarin ba suna dai mamakin danme idan dayan bai zo ba ba za.a daura da daya ba?
Zama Malan ya yi, inda a hankali ya dan duko da kansa wajen Aba, da kuma Malan ishak ya ce" ina gannin Elhaj kawai a daura Na Jamail din, domin wa.innan basu da niyar zuwa, da alama ko sun fasa ne
Kafin Aba ya yi magana sai ga karan wani tsohon babur furrrrrrrrrrrr ya tunkaro anguwar, direct wajen jama.ar ya karaso, sai dai abin mamaki Lukman ne a saman Babur din nan
Suturar jikinsa yau kam ba tsari, Lukman mai son wanka yau kam ba wannan daukan wanka
Bai damu da irin yanda aka zuba masa ido ba, haka ya sauko ya ratso har gaban malan kafin yake zubewa nan kasa
Du girma irin na Lukman ya saki kuka mai cin zuciya yana bin jama.ar dake wajen da ido
Kallonsa Malan yake bai iya hana shi kuka ba, saima dan langwabar da kai da yayi
Abdul Fatah ji yake kamar ya kama da wuta a zaunen nan da yake, yana son yin magana aman Hamza ya tsare shi da ido
Hamza ne ya mike ya karaso wajen da Lukman yake ya kama shi ya mikar da shi, suna kallon juna ya ce" Lukman, lafiya? Mai yake faruwa haka ne?
Lukman ya sada kansa, yafi son su kasance daga shi sai Malan sai wujdane dan sirinta abinda ke faruwa, hakan ya bukata sai dai ina , malan ji yake daga inda yake ba zai iya motsawa ba
Aba ya dago da kansa ya mike a hankali ya ja hannun lukman, domin a duniya komai yana bukatar sirri, koma menene, sannan a yau rana ce ta zulumi.cike da zuciyar Malan, gannin Hamza ba zai dauki wannan ragamar ba, Malan kuwa zuciyarsa bukunta ya matar masa da jiki ya saka Aba mikewa inda ruuu aka bi su da ido harda Alaidine da ya cika da mamakin shi kuwa Aba ina ruwansa, daman ya za.a yi ya gama mora a waje sannan ya aura? Yayi yaya da ita? Shi ai ba mahaukaci bane, da gani a yanda ya gama shagalinsa da ita yanzu zai zo masu da wani bayani, shi dai komai za.ayi ba zai yarda Aba ya canza abinda yayi niya ba, wato ya aurawa Jamail Wujdane haka kawai a bata masu zuri.a? Haka kawai? Ai yau za.a yita ne a wajen nan
Lukman na kebancewa da Aba ya shiga koro masa bayani kamar haka" yau kwana biyu da mahaifina ya dauran aure da yar uwata, bisa sharadin sai an auran ita za.a barni na auri Wujddane, du ban fadawa su Malan ba domin ona son Wujdane bana son abinda zai rabani da ita, tun jiya nake gannin abubuwan da basu dace ba, inda mahaifiyata ta bukaci na jawo kudin sadakin Wujdane din su adana,
Kawai ina zaune nake jiyo magangannunsu suna labarin ai lefe ma da na tara na wujdane aka ce min an kawo ashe ba ita aka kawowa ba gidan su yarinyar da aka aura min suka kai, karshe ma kudin sadakin na Wujdane da na bayar ajiya mahaifiyata ta sayo keken dinki da kayan dinki wai zata shiga koyon dinki da na auro mata yar iska
Hakan ya bakantan rai na ritsasu cike da bacin rai na saki yarinyar saki daya,
Wannan ya tunzura zuciyar mahaifana suka yi rantsuwa da idan dai na zabi auren Wujdane ba ni ba su duniya da kiyama
Hakan ya tayar min da hankali, ya fitini tunanina, ya fitar da ni a nutsuwata, ba inda ban je ba dan a zo a baiwa su mahaifana hakuri aman abin ya ci tura shine tun jiya zuwa yau na zama tamkar mahaukaci yawo kawai nake, ni yanzu ga sadakina na samo a aura min ita kawai mu yi tafiyarmu shikenan
Sauraronsa Aba yake cike da tausayi, sai kawai yake gannin kamar rayuwarsa ke maimaituwa a nan,
Kamo kafadunsa ya yi ya ce" karka yarda, koda wasa karka kuskura ka ki bin abinda suka fada, tunda har kai kadarar taka ta fito a haka, ka rungumeta kawai Lukman, ka sani a duniya babu kuskuren da zaka tafka sama da take maganarsu, Wujdane dai mace ce wada take gaban iyayenta, ysu ba zata kaunaci namiji ya tsameta ya kaita a rayuwar wahala ta gaban abada, shin baka tunanin abinda zaka cewa Allah? Da ace mahaifinka ya aminta ni zan dauki nauyin aura maka Wujdane, aman ina hakinsu dake kanka? Aljanarka tana karkafin digadigensu, basu kore ka ba, zabinka ne bai yi masu ba, ka nutsu ka farka giyar soyaya ke dibanka, babu innuwar da ta kai ta iyayenka lumshi da dadi ko a nan duniya bale a kiyama, lale auren wace ake so yana da dadi aman kuma zaman lafiya da iyayen mu ya fi dadi dadi, Lukman idan ka samu nutsuwa ga numberna ka nemi gidanna mu tatauna, ni ina baka shawara ne wai ba a matsayin dan na girme maka ba aa, sai a matsayin wanda ya san me hakan ke nufi, dan haka idan muka zauna zan baka tarihin rayuwana
Wani irin sanyi jikin lukman ya yi, ya dubi Aba kimar Aba kadai zata haneka karyata lafuzansa hakan ya saka shi fadin" Malan fa? Kenan na bashi kunya? Wujdane fa? A me zata dauke ni na cuce ta ? Elhaj ka san hausa yanzu abinnan sai ya yi ta bin Wujdane har ka ga ta rasa miji a sanadina?
Aba ya yi murmushi ya dafa kafadar Lukman ya ce" *ALLAH ZAI HANA*
Yana gama fadar haka da hanzarinsa ya dawo ya bukaci a nutsu za.a daura aure
Hannunsa ya mikwa Alaidine ya miko masa kudin sadakin Jamail
Aba ya juyo ya raba kudin hannunsa gida biyu wato dubu hamsin hamsin, ya mikawa malan isyaku ya irga ya ce dubu hamsin, ya sake miko dayan ya irga ya ce" wato dubu dari kudin sadakin....
ABA ne ya katse shi da fadin " *AA, DUBU HAMSIN BIYU, WATO KUDIN SADAKIN YARINYA BIYU, YA JUYA WAJEN MALAN YA CE" MALAN INA NEMAWA YARONA........*
🌚
[3/27, 10:00 AM] +234 803 957 7698: 🦄🦄 *BANI DA ZABI*🦄🦄
*17*
WRINTING BY *SAJIDA*
Da sunnan Allah mai rahama mai jin kai,
*SAJIDARKU CE*
MARUBUCIYAR:
*YAR MAHAUKACIYA*
*DUK KARYAR KADA*
*DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA*
*NEMAN NA KAINA*
................... *BANI DA ZABI* INSHA ALLAH....
Kallo suke yi masa na rashin fahimtar inda zancensa ya nufa,
Zuciyarsa yake dana, tunda ya fara ai sai ya gama, a hankali ya dan matsa hularsa baya wanda ya baiwa sauran gashin gaban goshinsa damar fitowa,
Ajiyar zuciya ya sauke yana kallon Wujdane a hankali ya furta" dole na kirayi hakan da yaki, yaki ne na zuciyar mutun guda, ina son shiga yakin da na san zan jigata aman kila wa kala zan cima burina,,
Aisha kam daidai wannan lokacin zuciyarta tamkar ta balo ta bar kirjinta, kallonsa take cike da faduwar gaba inda wujdane bata ma san inda maganarsa ta nufa ba
Kai ta dan dafe ta ce" wai yau abinda ka tashi da shi kennan Jamail? Ka bude mana mota mu fita ka ga an fara lekowa daga bango da kofa ana lekomu na san an fara cicira mu ne, ni shi ya sa bana son matse maka guri, yanzu a anguwa za.a dauka wani abin ne har a zo anai maka tambayar rainin hankali,
*Wujdane i love you*
Katsewar mitar Wujdane kennan, wanda yayi daidai da wani irin bugawa da zuciyar Aisha ta yi, haka zuciyar Jamail ta shiga luguden duka ba kakautawa
Shatata Wujdane ta yi tana kallon Jamail, ita bata ma san me kunuwanta suka ji takamaimai ba, hakan ya saka ta sakin wani malalacin murmushi tana kallonsa ta ce" ban ji mai ka fada ba?
Jamail ya sauke ajiyar zuciya ya dan waiga gefen Aisha ko zata taimake shi, aman ina kanta a sade a kasa wanda ba zaka fahimci halin da take ciki ba,
Juyowa ya yi yayi kundubala da tsoron dake dukan zuciyarsa ya ce" cewa na yi ina son ki Wujdane ko laifi ne??
Wujdane ta dan kada idannuwanta irin tambaya da idannun nan, tana kallonsa kafin ta furta" mai kake nufi da maganar nan naka ne?
Jamail ya tsareta da ido, wanda itama cikin idannuwan nasa take kallo, ya ce" shin hausar ce baki fahimta ba Wujdane ko menene???