← Book details Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 48

Sashe 9

Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sorry Barista, kada ku
auka na muku shishigi Please ku bita a hankali." Yana fadar haka ya wuce wurin motarshi ya shiga, wani irin fargaba yasa na rufe fuskana cikin shashekar kuka na gaya musu yadda aka yi har nasan takardan, "ban san cewa haka zai faru ba, ni dai na gaya mishi na san yadda Abba yake sign, sai ya ce min na gwada mishi, nayi mishi ya kuma je ya ga na Abba sak da irin wanda na mishi, bayan wasu lokuta sai ya kawo min takardu yadda yake azazzzalamin na saka mishi hannu wallahi ban tab'a sanin cewa irin wannan fraud zai aikata ba, don Allah nima ku yanke min hukuncin, wallahi " na fada ina wani irin kuka me cin rai.

Idanun Ya Ado yayi jajjur ya ce min.

" Me yasa Lubnah?

Kin san yawan ku
in da ake bin Abba kuwa?" Zuciyata ta ce ta tsinke na kalle shi a matu
ar razane, hawaye wannan na koran wannan ina girgiza kai na ce mishi." Ka rufa min asiri, wallahi ban sani ba, don Allah kada ka gaya min mutuwa zan yi." Na fada ina durkusawa a wurin, domin a rud'e nake don yadda zuciyata take tsinke kamar zata fado, zai sake magana Ya Tahir ya ce mishi.

"Ya isa haka yanzu ba lokacin magana ba ne, taya abubuwan da aka rasa zai dawo ake magana." "Koma cikin asibitin muna zuwa!" Inji Ya Ado, haka na mike a hankali har na koka can nesa da su Mama ina kallonsu idan har su Mama suka san nice nayi wannan aikin har abada ba zasu daina tsanata ba, zasu jima suna jin zafina, sai yanzu na fahimci me yasa Hafiz yake cewa ba zan tab'a tsere mishi, ashe wannan abin da ya aikata ne, dafe kaina nayi da hannu bibbiyu ina jin tsanar kaina da bakin cikin wannan halin nawa zama naji an yi a gefena, da sauri na kalle shi.

Mika min goran ruwa yayi yana kallon yadda nayi zuru-zuru, a hankali na d'aga goran na sha sannan na sauke ina me rufewa, kaina a kasa ina kallon goran.

"Gobe su Hindatu zasu tafi, na ce su tafi da ke!" Kallonshi nayi a hankali na dauke kaina, ina kallon kasa.

"Yanzu kayan sun riga da sun shiga cikin KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY, har an yi musu stamp ko?" Na tambaye shi, kura min idanu yayi kafin ya ce min.

"Eh!" "Nawa KUMO PROPERTIES take bin mu?" "Ba wani kudi me yawa take binku ba!" "Kamar ya?" "Eh kasancewar kayan gwanjo ne har na mai da musu kudinsu," kallonshi nayi cike da mamaki murmushi yayi ya ce min." Ba wani dayawa ba ne, kudin ruwan da yake ciki ne kawai yayi yawa, Alhamdulillahi an biya dukka." Shiru nayi ina ta wasa da yatsuna.

"Yanzu ya za'ayi kenan, a cikin gidajen da kumo ta rike ko za a sakawa asalin gidanmu kudi mu saya?" Murmushi yayi ya gyara zama ya ce min," idan kika ce a baku ma dukka dukiyar me sauki ne?" Ya ciro wayarshi da sauri na kwace wayar na ce mishi." A'a!

" " Yes idan har zaki yi dariya ba wani abu ba ne maza ci abinci." Akwai wani abu da na kasa ganewa akan shi, yadda ya saka Ni cin abinci.

Ya Ado da Tahir suka iso.

" Mr Turaki!!

" Hannu ya saka a bakinshi, suka yi shiru nima kallonshi nayi ya ce min." Ci abinci!

" A hankali nake ci ina kallonshi, na kasa dauke idanuna a kanshi, sannan na kasa daina cin abincin ba, a hankali na ajiye spoon din.

" Na koshi!" "Good!" Ya dauki sauran yana ci, yana fa
in.

"Ba kome yake bukatar ayi magana akan shi ba, je ki wurinsu Mama."
Tashi nayi na bar wurin ya ce musu, " zauna San." Ya nuna musu akan su zauna.

Sai da ya ci abinci ya goge hannunsa.

"Kun ga sakon kamfanin KUMO PROPERTIES NIGERIA AGENCY ko?" Gyada kai suka yi, " gobe muna da board meeting, Hindatu ta wuce da Luna Bauchi, gobe idan muka gama meeting din zan tura muku sako.

Ita kuma abinda ya sa na ce ta koma can, saboda wasu abubuwan zasu faru kai ma baka tsira.

" Daga haka ya mike, ya musu sallama.

Basu tab'a fuskantar crisis a kamfanin ba kamar wannan lokacin, idan har kana niman dan kasada, Turaki ya dauki wani irin kasada, abin da yake so dole sai anyi zama da duk masu hannun jari a kamfanin ayiwa Lubnah sassauci, xa a dawo mata da 75% na kayan Abba sannan zata yi aiki a kamfanin na tsawon shekaru babu albashi, shine yake son ayi vote a cire aikin nata, sannan yana bukatar goyan bayan kashi hamsin da biyar na masu hannun jarin, ta haka ne zai samu goyan baya, shi kanshi kudin da zai biya kamfanin domin a sake kayan ba karamin kudi ba ne, don ma Allah ya taimaka akwai dukiyar mahaifiyarsa na wurin kakanshi, wannan ya taimaka, ya bada kusan rabi da kwata shine 75 yadda za a dawo da kayan Abba cikin ruwan sanyi.

Amma koda yayi haka bai zama dole ya iya haka ba, domin sai da goyan bayan abokan kasuwancinsu.

"
Don haka ya koma ya samu Jasminah da Uncle Auta da Ubaid wanda shima ya shigo cikin tafiyar, domin yasan kaf duniya babu abinda zaka yi yanzu ya burge Turaki kamar ya goya mishi baya akan Lubnah, da ya zauna yayi nazari sai ya ga babu riba, don haka ya zauna yana zaune aka fara tattaunawa, a daren suka yi ta tura sako da kiran masu hannun jari da rokon alfarma sannan suka gaya musu akwai sako su duba, kafin dangin mahaifinsa su san abin da yake faruwa mutane hudu din nan sun gama kome basu bar gidan ba sai karfe biyu na dare, kwanciya yayi a parlourn.

Maganar gaskiya zuciyarshi ta gaji a yanzu fa ya dace ace ya ajiye iyalinsa na kansa ne...........
(Ku yi hakuri yau nayi baki ne)
[12/10/2025, 11:24
AM] Maman Walid: 8
"Hmmmm!" Ya furta a hankali, ai yanzu kome ya lalace, domin bai isa ya ce zai tun kari.

Maganar aurenta babu shi tunda yanzu yasan duk abinda zai yi cewa za ayi don yana da alaka da abinda ya faru ne.

Washi gari har da makara tun yana Sallah asuba da ya dawo madadin ya motsa jiki sai ya kara kwanciya, har sai da aka yi ta buga mishi kofar parlourn ya farka ya shirya a gurguje, a lokacin da suka isa kamfanin dayawa masu hannun jari a kamfanin sun iso shi yake da kashi sittin da biyar amma yana bukatar goyan bayansu a kowani hali, Tarik ya gani tsaye yana murmushi, ya ji dadin ganin Tarik domin shima zai bada nashi gudunmawarsa, amma kuma ta wani gefe yana bala'in shakkar kada Tarik ya kuma shige mata, gaskiya yayi farin ciki amma kuma gefe guda yana bakin cikin da zuwan Tarik domin yanzu zai dagula mata lissafin da yake
arin daura mata, haka yayi ta bin manyan baki yana musu godiya domin bai kawo zawo bashi hadin kai har haka ba, ai kuwa daga nan suka wuce asalin conference hall din da suka shirya don baki.

Haka kuwa suka hadu baki
aya, babban adduarsa ya ga Uncle Auta da Kakanshi, kuwa wurin minti goma da fara faron suka shigo da yan uwan Babansa, ajiyar zuciya suka sauke aka fara meeting din, cikin ikon Allah da girmamawa, ake gabatar da kowacce bayani da kuma dalilin taron, har aka zo wurin da ya kawo maganar Lubnah, shiru hall yayi da yake ba shi yake bayani ba, Taj ne.

Ya cigaba da cewa.

"Idan har da muna son yin gaban kanmu ne da ba zamu tara ku a nan ba zamu yi gaban kanmu amma manufar ita ce mu samu ha
in kan kowa yadda zamu fitar da sakamakon kome, sannan yarinyar bata bukatar tayi aiki a kamfanin mun dauki duk wani abun da ya dace, wannan Madadin kamfani muna niman abokan hulda su bamu damar basu 75% na abinda aka karba daga gare su, zamu biya kudin sauran kuma zamu rike izuwa reshenmu da yake garin Gombe!"
Shiru aka yi Alhaji Mudansir ya ce.

"Gaskiya ban amince ba, idan har sai lallai anyi haka tow sai dai a kada kuria idan ka fimu tow shine zamu amince idan kuma baka fi mu ba, zaka hakura da tsarin jin kai ga dan kamfani sannan zata cigaba da aikinta, ai
addara ce kuma tana kan kowa." Bai san me Alhaji Mudansir ya taka ba, amma kuma sai yayi zuciyarshi ta karaya, kuma abinda ya fada din sai mutane suka bashi goyan bayan haka, dakin taron ne ya samu halartar Hajiya Sameerah da Hajiya Khaulatu, sai Khamis da Badr, Mimi da sauran yan gidan kumo da suke garin lagos, suna tare da Alhaji Mudansir, a hankali ya sauke ajiyar zuciya yana kallon yadda suka taru kuma duk sun zauna, baki
aya sai ya karaya.

Chairman na kamfanin wanda ya kasance Alhaji ELYakub Kumo, yana kallon yadda Turakin yake faffutukar tsayawa kanshi, ba tare da ya nuna musu karaya akan idanunsa ba, ya kuma kalli bangaren iyalinsa wanda yasan sun zo ne domin saukar da Turaki daga matsayinsa."yadda za ayi shine duk wanda yake tare da Mr Bilal Haris kumo Turaki, zai d'aga wannan White paper din, wnada baya tare da da shi ba zai ya d'aga ba, zamu kirga da mutanen da suka d'aga ne." Duk aka amince, sannan ya cigaba da kai taka takardun gaban jama'a, bayan ya gama sai ga wasu bakin turawa suna zuwa Uncle Auta ya tafi ya gaisa da su, sannan suka samu wuri suka zauna wannan yasa murnan Alhaji Mudansir da Abbas ya koma ciki domin basu tab'a zatan haka zai faru, taron ya tara mutane, kuma aka sake jawabin abinda ya wuce.
Chapter 9 · 0% Book details