← Book details Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 48

Sashe 38

Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Dama aure Ubaidullah zai yi?" "Eh kai ya jima yana son yayi aure shegiya tana hanawa na rasa gane me kika tsare mata take jin haushinki, yanxu zata ga rashin mutumci ganin idanunta ba ita yar iska ba!" Rike baki nayi ashe haka yake da rashin mutunci.

Ai kuwa ba washi gari Ubaid yazo yayi ta bani hakuri Allah sarki sai ya bani tausayi.

Idan baka samu mace ta gari ba rayuwarka tana cikin garari, wani ikon Allah ni da taso ganin nayi hauka.

Da na gayawa Dangina addu'a aka yi ta min Allah sarki saii ga Yadiko tazo ta kawo min maganin wanke mahaifa, da sauransu.

Satinta biyu ta koma, a lokacin har na gama hada lefen Ubaid ai yadda ta min kan kara haka zan mata na itacce.

Kuma na shiga gaba aka kai kayan auren, muna dawowa tayi ta hauka da ihu zata dake ni.

A raina na ce ko zaki mutu aure sai anyi shi......
[12/26/2025, 4:22
PM] Maman Walid: 30
Ihu da haukar da take yi, har cikin parlourn ina jinta, hankalina yana kan abinda nake ha
awa don na sha, "wallahi idan ina raye sai ga bayanki!" Ihu da hauka iri-iri tayi shi gashi an hanata shigowa gidan, a ranar dakyar ta koma gidanta, ina jin yadda yake ihu da tashin hankali.

Da yake mijina ya tafi wani meeting Abuja sai dare zai dawo haka na hada magani gyaran jiki, wurin karfe shida ya shigo a gajiye, karban jakan nayi kallonshi.

Yayi laushi na tab'a goshinsa ina fa
in.

"Anya yau lafiyarka lau kuwa?" Murmushi yayi ya wuce kitchen yana fa
in.

"I need water!" Na biyo bayanshi na bashi ya sha, sannan ya sauke ajiyar zuciya can kuwa ya fara wani irin tari.

"Me yake damunka?" Na rike hannunsa muka wuce cikin dakina, ina shafa bayansa.. sai da na taya shi wanka duk yayi laushi.

"Me ke damunka!" Masallaci ya tafi bayan ya dawo ya kwanta sai dai dama mishi kunu nayi ya sha, ina rike da hannunsa.

"Meke damunka?" "Bana jin dadi ne almost 3-days kenan." Sake tab'a wayarshi nayi na ji zafi rau.

"Baby you're burning!

Muje asibiti." Girgiza min kai yayi yana mai rike hannuna ya ce min.

"Please sir na da sweater!" Haka na wuce dakin na kawo mishi, ya saka nace mishi.

"Me kake so!" Girgixa min kai yayi yana fa
in.

"Bana jin yunwa." "Fisabiilillahi haka zaka zauna da ciwo?" "Hmm!" Ya ce min na rasa me yake min dad'i, duk ya rasa kuzarinsa, haka yayi ta zazza
i a kwanakin ya daina zuwa office sai da yayi sati s gida, wanda ya janyo aka kai shi asibitin da baya so.

Ruwa suka yi ta saka mishi, wani abin mamaki sai jikinshi ya rikice sosai.

Wanda ya saka ni cikin wani irin tashin hankali.

Wanda ya kai aka tura shi ICU, dole Mama ta zo.

A cikin kwanakin nayi wani irin rama domin bana cin abinci bana kwakwaran barci.

Tunda Mama ta zo take nazarin yadda yanayin mu alamata da danginsa idan ya wuce Daddah da Alhaji ELYakub sai Uncle Auta da Ubaid.

Kallona tayi ta ce min.

"Kina cikin abinci kuwa?" Murmushi nayi na ce mata.

"Ina ci!" Riko hannuna tayi ta ce min.

"Kamar kina da ciki ko?" Da sauri na kalleta babu kowa a wurin, na ce mata.

"Ciki Mama?" Gyada min kai tayi, nayi kasa da kaina.

Tun last week ya dace period din ya dawo amma har yanzu shiru, sai ciwon gefen ciki da yawan kasala.

Na zata ko don rashin lafiyarshi ce.

Rufe bakina nayi da hannuna daya na kalleta.

"Innalillahi wainnalihir rajoun!

Mama!" Hannu ta saka min a bakina.

"Mijinki ma kamar hannu aka saka mishi, bani da tabbas amma ki shirya mu koma gida!" "Mama!" "Ba zan barki anan ba, domin shima a nan din farautar rayuwarshi ake idan har shi ba a kyale shi ba, kema ai baki tsira ba.

Waye kika yarda da shi a cikin danginsa!" "Tarik!" Na furta kai hatta Uncle Auta da Ubaid ban yarda da su ba,.

Kiran Tarik nayi a waya..

"My boy ina son ganinka don Allah!" "Ina nan tafe gobe in sha Allah!" "Muje gidan Adamu!" Bata gayawa kowa dalilin tafiyarmu ba, haka muka isa gida, dai naji kamar nayi kuka, idan na tuna yadda na barshi.

Kusan kwana nayi da zazza
i, washi gari Tarik ya iso ban san me Mama tayi ba amma da safe ruwan zam-zam ta mika min muka fita, Tarik ya zo ya dauke ni.

Lokacin da muka isa Asibitin Uncle Auta da Ubaid muka samu sai Kakanshi.." Jiya ina kika tafi?" "Naga kamar tana bukatar hutu shine na tafi da ita ku yi hakuri."
" Ba kome Hajiya, dama mun damu ne." Inji Kakanshi.

Wucewa nayi dakin da jakar zam-zam, na shiga na same shi a yadda na barshi.

Ruwan addu'ar nayi Bismillah na shiga shafa mishi, shigowa Uncle Auta yayi ya ga ina shafa mishi ya zo ya taya ni.

Har muka gama ya ce min.

"Addu'a ko?" Gyada kai nayi, murmushi yayi ya ce min.

"Mun yi da Baffa zaki koma gida zamu tafi da shi Russia!" "Zan bi ku!" Girgiza kai yayi na ce mishi.

"Ni nafi dacewa na zauna a gefenshi." Na fada ina mai fashewa da kuka, fita yayi ya bar ni a dakin, dA sauri na juya gare shi, na riko hannunshi na kai kan cikina.

" Please wake up ka ji feel your baby a marana, please ka tashi we need you." Na fada ina kuka.

Na rasa yadda zan yi haka na fito na same kakanshi na ce mishi." Don Allah ka bar ni nan tafi da shi, don Allah ku bar ni, na biku.

Mama ki ce su bar ni kin ji Mama ki roka min shi don Allah." Kallon su Mama tayi a nutse, ta ce musu.

"Ku barta ta bi Mijinta!" A yadda suka tsara babu ni, amma da yake Allah ya mata baiwar iya sarrafa kanta sai gashi sun amince.

"Shi kenan ta shirya!" Haka Tarik da Mama suka kawo ni gida na shirya tsaf, sannan na hada kayana na kashe kome na gidan abincin da yake frij na kai cikin gidan Uncle Auta, sannan na rufe gidan, muka wuce asibitin.

A daren muka wuce Russia, lokacin da muka isa can Russia har da Uncle Auta.

Yadda aka Karbe mu yafi kome dad'i, nima damuwa da rashin hutu yasa ina sauka a jirgin na yanki jiki na suma.

Haka aka wuce da mu asibitin.

Sai da nayi kwana biyu ina barci na farka, koda na farka Aunty Herlim na gani a gefena.

"Lunah sannu kin farka?" Gyada kai nayi ina murmushin karfin hali.

"Ya Jikin shi?" Na tambaye ta ina kallon dakin, murmushi tayi ta ce min.

"Yana dakinsa." Gyada kai nayi na rufe idanuna.

"Kwanaki biyu kina barci!" Kallonta nayi na ce mata.

"Kwana biyu?" Gyad'a kai tayi tana murmushi.

"Amma babu inda yake ciwo na kira likita?" Gyada mata kai nayi, danna abu tayi sai ga nurse sun zo, tare da likita a bayansu, bayan an gama duba ni suka min tambayoyi, na basu amsa.

"Ki huta zaa yi miki scan nan da dare!" Bayan sun fita na shiga wanka, na fito nayi sallah.

Sannan na wuce dakinsa.

Lokacin da na shiga naga sun daura mishi karfuna, zama nayi na dafe kaina.

Ina kallon yadda ya koma lokaci guda, wani irin kuka nake ina kiran sunan Allah, tunawa nayi da kayan da nazo da shi, na kalli Aunty na ce mata.

"Ina goran ruwan da yake jakata." "Yana gida zan saka a kawo miki!" "Ina so yanzu nan!" Haka ta bar Asibitin, bayan minti ashirin sai gata, dauka nayi na shafa miishi a jikinsa da ko ina.

Da dare na je aka yi min scan sannan anan aka gano cikin sati biyar da kwanaki shida, hawaye ne ya zubo min, na koma dakin ina kallonshi yana barci.

A bisa ka'ida ba za a zauna da shi ba, amma saboda yadda suka ga koma suka bar ni, sallah biyar sai na saka shi a cikin addu'a.

Idan dare yayi kuwa sai gari ya fara haske nake komawa gefensa na kwanta ina kuka har nayi barci.

Ban sare ba, ban tab'a give up ba.

Addu'a na saka Allah a gaba.

Ruwan zam-zam din na karewa na gayawa Auntynsa suka nimo min har da ganye magariya, anan ne na ga ikon Allah, na kuma.

Yarda akwai sihiri a tare da shi, tunda ya kwanta baya motsi numfashi ma da taimakon inji yake yi, amma ina fara ayatul shifa, ya fara motsi.

Tunda na fara sai nima na fara jin wani irin abu yana yawo a kaina, idan na kwanta barci zan ga kamar aka bina da gudu.

Sau biyu na ga haka, sai na kira Mama ina kuka na gaya mata.

"Bar kuka haka, ki tuna akwai wanda yake bukatar kulawarki bayan Turaki, ki tuna da abin cikin ki ko ba don kanki ba, in sha Allah zan taya ki daga nan." "In sha Allah Mama!" Na fada ina kuka, tayi min nasiha sosai sannan ta kara min addu'a sosai.

Haka na kara kai mi, amma kuma idan na tuna akwai Allah sai na ji bana tsoro.

Haka na cigaba da na shi, Turaki bai da Uwa bai da Uba, nice abu biyu zuwa uku.

Jasminah tana Kano, bata san me yake faruwa ba.

Nan kuwa dangin Uwarsa ba musulmai ba ne.

Haka na tsaya ba dare ba rana, ina addu'a.

Aunty Hindatu ta kira ni ta min jajje take gaya min anyi saukar Alqur'ani da yanka, Abba yasa an tara almajirai, sai na fashe da kuka.

Sannan an raba namar sadaka gida gida, abinci kuwa har kofar fada aka kai aka rabawa almaji
rai.

Sannan anan ware tsangaya uku akai abinci da ruwan sanyi aka raba.

Nayi kuka kamar raina zai fita, sati daya aka dauka aka addu'a, sati na zagayowa ya fara farkawa, wani bin idan ta bude idanunsa har da tashi da karfi kamar zai tashi sama, sai anyi mishi allurai yake komawa barci, na kira Mama na gaya mata, ta ce min.
Chapter 38 · 0% Book details