← Book details Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 48

Sashe 15

Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ya Ado ka ba Mama hakuri tayi hakuri, wallahi ba zan kara ba." "Ya isa haka in sha Allah babu abinda zai faru."
Fushi Yayuna mata suka dauka, kusan na rasa inda xan saka raina.

Karshe Taj na kira na tambaye shi ko Oga yana gani ya ce min eh yana nan." Don Allah ka zo ka kai ni na gaishe shi."
Shiru yayi kafin ya ce min.

" Ok zan zo yanzu!" Wata Turkish gown ma saka, sai mayafi da na lallube jikina da nayi da shi, na fita tare da yiwa Yaran sallama na fita bayan na turawa Ya Ado sakon zan fita.

Taj ya zo ya dauke ni na ce mishi.

" Na gode amma ka taimaka min mu saya mishi fruit!

" Tunda na shiga ya ce min." Amma wani ya taba gaya miki kina da kyau?

Gaskiya kin ha
u.

" Ha
e rai nayi ban kuma magana ba, har muka isa inda na saya mishi fruit, muka nufi gidanshi.

Sai magana yake min amma naki amsa mishi.

Har muka isa gidan, yana tsayar da motar na saka kai xan fita rike hannuna.

" Meye haka ina miki magana kin share ni?" Juyawa nayi na kalle shi, kafin na kalli hannuna.

Yadda na mishi wta irin kallo sai da ya ji tsoron sake ni yana cewa." Sorry na jima ina son na gaya miki gaskiya ina sonki!" Murmushi nayi mishi sannan na ce mishi.

"You too late, domin ni da CEO muna son juna!" Da wani irin sauri ya cire hannunsa a kan nawa yana fa
in.

"Don Allah kada ki bari ya san da wannan zancen wallahi zai iya korana." "Ni ba haka nake ba, amma ka kula sosai kowacce kwarya da abokin burminta." Daga haka na fita a motar, haka na fito dauke da abinda na sayo mishi na nufi cikin gidan.

Da sallama yana tsaye jikin window, yana juyowa muka yi ido hudu da shi.

Sunkuyar da kai nayi ina wasa da jakan hannuna.

Takowa yayi ya wuce ni zuwa upstairs, wani irin abu na ji, ina tsaye sa ga
Airah tana saukowa a hankali.

Wani irin rufewa idanuna yayi na sunkuyar da kai ina ambaton Allah.

Bayan ta fito ta wuce kitchen.

Bai sau ko ba ita kuma bata ce min na zauna ba.

Haka na cigaba da tsayuwa har zuwa wani lokaci.

Ya sauko daga sama sanye da wasu kananan kaya a jikinsa.

Idanuna yana kanshi.

Na ce mishi.

"Ya jikinka?" Kamar bai ji ni ba, ya wuce na ajiye mishi kayan a sama inda yake na ce mishi.." nazo na kara baka hakuri ne!" Sosa kunnensa yayi yana latsa wayarshi, da na cigaba da magana tashi yayi ya riko hannuna ya janyo ni ya kai ni bakin kofar ya ce min..

"kada ki kara zuwa inda nake!" Ya bude min kofar, zuba mishi idanun nayi na ce mishi.

"Ba zaka kyale ni haka, ka gaya min ba bukata na ne a rayuwarka ne?

Idan ka fada min haka wallahi zan tafi na rantse da Allah zan tafi, ba zan kara zuwa gare ka ba amma idan ka ci-gaba da tureni zan cigaba da zuwa har sai ka gaya min abinda yake ranka."
"Zan rufe gidana kin ga yarinyar da zan aura tayi shiru kada ta ji babu dad'i." Haka ya saka na fito, na tsaya a kofar shiga gidan, ina tsaye har danginsa suka zo, babu wnada ya ce min ke uwaki.

Ko sun yi maganar ne sai ga Uncle Auta, ya shigo bai shiga ba ya ce min.

"Zo muje!" Girgiza kai nayi na ce mishi.

"A'a ba zan tafi ba sai ya gaya min me yasa yake ture ni."yayi juyin duniyar nan amma naki binsa Sai da ya shiga sai gashi ya fito.

Amsar key yayi ya wuce ni, na tashi na bi bayanshi.

Tunda na shiga motar yake waya da harshen Russian, bai fada wayar ba har muka isa gidan, dab zamu shiga kwanar ya mai da wayar video call.

Wata har dattijuwar baturiya ce ta ce min.

" Labobu;" kallonshi nayi fuskarshi a ha
e, gaishe ta nayi da harshen turanci ta amsa mun jima muna magana tana min tambayoyi ina amsa mata, kafin ta juya cikin taushin murya take rarrashinsa, ban san me take ce mishi ba, naga ya sake mata murmushi.

Nima sai na tsinci kaina da murmushi.

Bayan sun gama ya karasa da ni gida.

Sai da na zo fita ya ce min.

"Ki daina zubar min da mutunci, idan zaki yi haukarki ya tsaya ina nan, kada ki kara zuwa kada ki kara kusantar inda nake idan ba haka ba, zan miki wulakancin da kare ba zai ci ba, wai ke an ta
a yin wa mutum dole ne?

Bakida zuciya ne?

Kada na kara ganinki a gidana.

Idan na kara ganinki nasan me kike nufi da haka!" Ya fara min wani irin kallo irin na yan iska, da sauri na kare kirjina tare da yin baya, ban san lokacin da hawaye ya zubo min.

Na ce mishi.

"Hakuri nake baka, ni ba yar iska ba ce amma tunda kallon da kake min in sha Allah ba zan kara zuwa ba, idan na kara zuwa ko na kulaka suna na ba Lubabatu ba ce!" Na fita daga motar na barshi a wurin ina kuka domin na fahimci wani irin kallo yake min.

Jan motarshi yana fa
in "Good gurl kada ki kara zuwa ni kika sayawa mutunci.

Da gudun tsiya ya bar unguwar ko tunawa da ya yi hatsari baya yi.

Lokacin da ya isa gidan damuwarsa biyu ya tirke Taj domin ya ga abinda yayi mata daga window yana daga cikin dalilan da yasa ya mata haka, na biyu abinda ta kawo mishi.

Lokacin da ya isa kai tsaye inda ta ajiye mishi leda bag din ya nufa, yadda ya je ya ga babu shi babu dalilinsa ya kwalawa Airah kira tare da tambayarta.

Da sauri ta ce mishi.." yanzu Badr ta wurga a wancan gwandon sharan.

" Wani irin zare idanu yayi kafin ya ce mata.

" Ko Ubanta da Uwarta basu isa na ajiye abu su sauya min wuri ba, ke ubanki ne ya ce ki sauya mishi zama daga inda yake?

" Da sauri ta nufi inda ta jefa ta ciro tana fa
in." Kayi hakuri hamma." Kamar zata yi kuka ya ce mata.

"Oya je ki wanke ki kawo min, abin Lubnah ko a kashi aka saka zan wanke na ci!" Mahaifiyar Badr ta ce masa.

"Allah yasa na asiri ake baka ba." "Ni nake bata kudin da zata kaiwa bokonta domin wallahi ya iya aiki.

Domin ta mallake ni."
"Allah yasa ba wani abu take wankewa take baka ba ." "Ai yanzu nake son gaya miki ko shi ta bani nake sha, ba matsalar babban matsalata shine yadda ba ayi mana aure nayi da kaina naji abinda masu mata suke ji, idan suna.....
(Dan iska
[12/13/2025, 7:26
PM] Maman Walid: 13
Watsa mishi ruwa Ubaid yayi domin kaf a duniya babu kunya cikin lamarinsa, ya kauce ruwan ya watsu a gefenshi.

"Kai wani irin mutum ne da bai san ido ba?" Ubaid ya tambaye shi, "ido?

Sun aka ace maka sun san idon ne?

Matar da nake so zasu gayawa Magana sai nayi shiru saboda ina son su so ta?

Kai ji idan suka ce basu sonta ni ina sonta.

Zan iya rayuwa da iya ita ba tare da nayi nadama ba, zan kuma iya datse alaka da kowa domin ita, gaya min wani abu nake bukata?

Yau suna tare da ni ne domin abinda nake da shi ita kuma tana guduna ne saboda su.

Idan da yau babu su babu abinda nake da shi tabbas rayuwata sai tafi haka citta."
"Me yasa kake karawa matsalar nan fetur ne?" "Saboda na gaya maka su din basu gaba, idan babu su iya Mujitafa gare ni su basu da abinda zasu ba ni, idan aka ce iya kai ne babu abinda zai saka na kalle su.

Su gode ma da nake kula su oya su bar min gida!"
"Amma kasan dole matarka ta shiga cikinsu?" Ya fada yana kallon shi ya kara da cewa.

" Dole Matarka tasan su din naka ne?

" "I fuck su nawa ne, kai dalla su fita min ina da kake magana anan basu ne suka turawa Matarka hotonka da Lunah ba?

Ko an gaya maka basu ne suka tura min hotonka da Lunah ba, kai ma kana manta da bala'in mutanen nan su fita kafin na kira Dattijo ya min waje da su." Jin haka yasa baki
aya suka mike tare da barin parlourn musamman yadda ya kara da cewa." Damuwarku na auri Yaranku idan suka samu ciki da ni na zama next victim to ba da ni ba!

Da naci guba a hannunku gara na mutu a tsaye.

Sai kace an ta
a soyayya ko auren dole kun bi kun dame ni.

"
Suna fita Ubaid ya mishi magana ya d'aga mishi hannu yayi ya ce mishi." Tsaf kafi kowa sanin waye ni Please je ka wurin matarka kada ka dame ni!

" Shima ya samu nashi kason, ba musu ya bar gidan, ya kara wanke fruit din da kanshi sannan ya zauna ya fara ci kusan abinda ya ci kenan, fitowar Airah da take jin kome ya watsa mata harara ya ce mata." Ki tattara abinda kika dafa ki je na gode." A rud'e ta ce mishi." Sir me na aikata?

" Wani ha
e rai yayi sosai ya ce mata.

" Taya xan yi bakuwa tazo gidan nan amma ki ganta ki basar da ita kin san how she meant to me?

Da zaki ganta ki share ta don ni na share ta?

Daga yau kada ki kara zuwa gidan nan, wannan shine zuwanki na karshe sannan ji gayawa mutanen da suka turo ki ita din rayuwata ce.

" Yadda ya mata tas ya kore ta, abin ya bata mamaki domin kuwa yanzu ta fahimci dalilin da yasa yake bala'in ashe basu shiri Yes tasan basu shiri amma kuma meye na jin haushin kowa?

Labarin nan har kunnen Alhaji ELYakub, murmushi yayi yana fa
in.
Chapter 15 · 0% Book details