← Book details Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 48

Sashe 19

Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" Juyawa nayi ina kallonshi, ya d'age min gira daya.

"Na miki kyau ne?" Murguda mishi baki nayi, tare da juya mishi kai.

"Ina tara duk wannan yanayin." Ya fada yana murmushi, tsoron da nake dannewa ne ya kara cika ni, kaina na kawar don bana son mu ha
a idanu yadda yake wasu abubuwan yasa ni na fara shakkar shi, anya ba wani abu yake bukata da ni ba.

Kamar yasan abinda nake tunawa ya ce min.

"Kina min kallon dan iska ko?" Da sauri na ce mishi.

"A'a!" Sai ya ce min.

"Ok ya kike kallona?" Gaba nayi ya ce min.

"Kila sake, kika shiga gaban wadancan mazan wallahi sai ma dauke ki cak!" Ya fada yana kallona, kamar nayi kuka haka na tsaya muka cigaba da tafiya.

"Allah yana gani ina da zafin kishi, kuma ina kishin duk wani abu da yake nawa, amma ba zan cigaba da ganin kina tafiya kamar doya ba, daga yau, idan da hali abayar nan a bashi a cikin gidan auren babban hijab da nikab is ok, ba takura miki zan yi ba amma ni ina da kishi, kuma ina son nayi koyi da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama.

Don ya ce duk mutumin da baya kishin iyalinsa ba zai ji kamshin gidan aljannah ba." Yana kai aya na kame kaina na tsaya a gefenshi.

Muka cigaba da tafiya wani shagon yan Indonesiya muka nufa yayi ta saya min manyan hijab da masu ha
e da riga, wanda babu shape, kallonshi nake ina mamakin yadda yake jidar kayan.

Wani ikon Allah, bai bar ni na dauki ko daya ba, shi ya riko kayan muka je wani shago wurin cin abinci, ya saya min abinda zai saya min sannan ya kawo muka wuce.

" Fuskarki tana da tsada, ni ban da Uncle Auta ya so ai ko dinner ba zan yi ba, iya walima ce ta maza.

Domin bana son shigar nan da kowa zai ta kallon surarki, bayan biki kuma na ce na kaso mutane ana saka hijab." Abin mamaki ya bani yadda yake magana kamar bashi ba.

"Baki ce kome ba!" Share shi nayi na cigaba da tafiya." "Idan har zamanmu ya samu albarka da Yara, tow ni dai kada ki so yara dayawa domin zan iya kishi akansu." Sai lokacin na kalle shi kafin na ce mishi.

" Ranar Hafiz ya gaya maka ai ba dan iya haihuwa ba domin ina da matsala, sai dai idan zaka kara aure." Na fada ina cigaba da tafiya naki na kara magana.

"Ni kuwa ina ji a jikina rabona ne ya dawo dake gare ni." Ban kula shi ba, na cigaba da tafiya.

Shima ganin yadda na dauke kaina akan shi yasa shi share ni.

Abin namu kamar masu aljanun, kowa yana iya share dan uwansa ba wai don baya son ala
ar ba ne a'a kawai wani yare ne da nasan iya zuciya ke bada labarin ga juna.

Kallona yayi, aka yi dace nima shi nake kallo, murmushin gefen baki yayi ya ce min.

"Kina gulma ko?" "Me yasa baki son magana bayan kin mai da ni kanari?" Ban ce kome ba, idan ka tuna rayuwata da Ya Hafiz yadda xan ta mishi hira da surutu amma shi baya ma ta ni, aikin gabanshi yake idan ya gaji ya ce na ishe shi da magana.

Shafa bakina nayi, a hankali tuna yadda wani lokaci da jimawa ya marin bakina wai na cika surutu.

"Wani abu ne?" Girgiza kai nayi, "Lubnah yaushe zaki bani labarin aurenki na baya?" Kallonshi nayi, "kana son sanin past dina ne?" Gyada kai yayi, shiru nayi ina kallonshi, kafin na ce mishi.

"Idan na gaya maka kai ma zaka daura naka azabarka ne a kai?" Murmushi yayi ya ce min.

"I'm not that type!" Cigaba nayi da tafiya, idan na gaya mishi labarina ba mamaki shima ya shirya nashi wulakanci ko kuma ya hango tumemmen abinda na aikata na shiririta ya juya min baya.

Domin ni duk abinda zai dakatar da wannan auren ina tsoronshi.

"Zan baka labari amma ba yanzu ba!"
"Ki barshi sai ranar da aka kawo min ke?" Kallonshi nayi wata zuciya ta ce min. *Daga nan ya dankara miki saki ko?*
Lagos
Hafiz ne gaban Manyan Yaran Alhaji ELYakub Kumo,
Mudansir, Khaulatu, Sameerah, Abbas da Zeenatu.

Sai Yaransu.

Yana shan ruwa ya kalle su da kyau kafin ya ce musu.

"Ni Lubnah nake so bani da wata ala
a da ta wuce ita.

Idan har muka iya tafiya a boat daya, za a dace idan kuma kuka ce ba zaku ban goyan baya ba, da sauki amma a farmake ni ba zai mana dad'i ba.

Yaron nan dai naku ne, ni kuma Matar da zai aura ce tawa."
Shiru suka yi suna kallonshi yadda yake kallon tsarin gidan.

Dariya yayi irin wanda ya san kanshi.

"Gayen nan yasan kanshi, baya wasa da ibada ko wani abu da ya shafi ibada, mutum ne da duk bala'inka haka zaka barshi, ba dai tsafi ko sihiri.

Allah ya bashi sa'a, amma auren Lubnah shine kuskuren da zai yi, domin ba zan iya kallon tayi gaba ina tsohon mijinta ba."
Shiru suka yi a hankali ya zauna yana kallonsu daya bayan
aya.

" Ina son na kunna mata masifa ne daga ranar aurensu zuwa ranar da zan mallaketa.

Wannan aikin ba zai samu ba, dole sai da goyan bayanku, kafin nazo nan sai da na san kome a kanku, kowa da inda yake tsaye da kuma abinda yake nima.

Ni kuma ita yarinyar nake so, idan har zaku bani damar haka tow ai zamu tafi a jirgi guda." Mikewa yayi zai bar parlourn ya kalle su, murmushi yayi ya ajiye musu wani takarda ya ce musu.

" Ga shi nan number wayata ce.

" Daga haka ya juya ya bar parlourn, yana fita suka dauke ajiyar zuciya lokaci guda, kowa sai kallon dan uwansa yake domin baki
aya sun kasa nutsuwa da shi, da ace yau a cikinsu yake da sauki amma bako ne taya zasu yarda su bashi amana idan tazo ta ci amanarsu fa?

Duk da sun ga farauta a cikin idanunsa da kalamansa da alamu ba kudi ko wani abu ya kawo shi.

Kuma baya bayan kudi.

" Ni dai na yarda da shi!

" Inji Khaulatu mahaifiyar Badr, domin ita Allah ya gani duk hanyar da za a raba lamarin nan tana cikinsa.

"Nima ina tare da shi!" Inji Hajiya Sameerah mahaifiyar Batul.

"Nima ina tare da shi!" Inji Hajiya Zeenatu, "ban gane kuna bayanshi ba?

Kuna nufin idan aka fasa auren Bilal da Lubnah zaku aura mishi Yaranku ne?" Shiru suka yi ya sake murmushi ya ce musu.

"Ku nutsu dai amma maganar a fasa aure ba zai taso ba!"
Tun daga nan suka shi shiru, amma kowacce da yadda take hada gwaraman da zai fitar da ita.

Haka suka watse babu tsayayyen ra'ayi a tsakaninsu domin kowa yana ji da son rai a cikin lamarin idan aka lalata auren da yarshi zaa yi.

After like three suka nemi Hafiz don s cikin kwanaki uku nan Alhaji Mudansir yayi kokarin ganin shawo kan Mahaifinsu, amma yace aure ba fashi duk abinda Hafiz ya gaya masa ya gayawa Alhaji ELYakub amma tace eh ya sani don ya kara tabbatar mishi har takardun asibitin Lubnah ya fitar mishi da su, ya ce.

"Ka gani sun gama nasu na turawa musu da na Turaki,saura ranar muke jira tunda daga amaryan har Angon basu kasar sun tafi Umara."
Wani abu ya tsaya mishi a rai haka yasa shi ya kullaci lamarin a ransa, ya kuma zauna da Hafiz baki
aya ya ce mishi.

"Ban san me zaka yi ba, amma ka taimaka mana a lalata lamarin nan!" Murmushi yayi yana fa
in.

"Wannan aikin nawa ne fa taimakawan mata, ni nasan Lubnah ba kuma san rauninta, ku kuma sai ku nimo raunin naku." Haka yasa duk suka yi shiru, murmushi yayi sannan ya ce musu.

"Harkalla ta fada amma ku sani duk abinda zaku mata ku jira ni na baku shawara yadda kome zai tafi."
Tun da ya fadi haka ya mike abinsa, ya bar su da nazarin yadda kome zai zo musu.

Alhaji Mudansir ya ce musu..

"kasancewar Badr da ita aka fara ku sauran Yan mata ku goya mata baya, idan ta samu Turaki kamar mu ne, muka same shi, idan har ciki tayi da shi to ku sani namu ne, babu amfanin rigima duk abinda zaku yi ku tuna Shari'a mace daya zata bashi damar aura a cikinku, sai kuma ita Lubnah take!

" Yadda yake magana tare da tsara kome, ya kuma gaya musu shi zai dauki duk wani abu idan ya faru.

Tabbas sharrin da tuggun da suke daukarwa kansu Babba ce kuma ba karamar da zaa ce zata lalace nan kusa ba, Babban al'amari da zai tab'a zuciyar kowa suke dauka.

Don haka ya basu shawara da su kwantar da hankalinsu a hada kome a nutse a yi kome yadda ya dace.

Bangaren Alhaji ELYakub Kumo, wata yar kanwarsa da take England tana aure ita ya turawa duk wani abinda ake bukata na.

Kayan aure ya ce yana so kafin daurin auren, domin ango da amarya zasu tafi Dubai yin hoton pre-wedding picture.

Lokacin da labarin lefen da za a hada Hajiya Safinah zata hada, abin ya zo musu bazata, sun shirya zalunci gashi wai pre-wedding picture din ma a Dubai za ayi wannan abin ya tsaya a ran Hajiya Khaulatu, domin kuwa tayi amfani da wannan damar tayi ta sake wasu kananan magana da habaici a status dinta domin Hajiya Safinah ta gani, ita kuwa irin mutanen masu bala'in niman na kansu ne daga can take hada kayan aure ta tur
o nan Nigeria, ai kuwa kannenta suna gani, suka shiga bawa Hajiya Khaulatu amsa, musamman da suka san kome.

Wata cikinsu mai suna Hajiya Kulsum ta daura hoton Ango da Amarya a gaban Harami, ta rubuta. *Zabinsa ce, bai duba me take da shi me iyayenta suke da shi ba kawai soyayyar yarinta ne tun tana yar mitsitsiya yake jiran wannan ranar, na ga na dating Ina jiran Pre-wedding da kuma After wedding a Ka'aba.
Chapter 19 · 0% Book details