← Book details Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 17 OF 48

Sashe 17

Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke ce silar farin cikin iyayenmu, ki dawo aurenmu domin kaf duniya babu namijin da ya isa ya zauna dake, don ni nafi dacewa da ke.

Luluna ki sani babu wani namijin da zai so ki sama da yadda na so ki!"
Sautin murmushin CEO na ji yana mai kallon agogon hannunsa ya ce min.

"Think wisely, ba zan raba ki da Ex
inki ba.

Amma ki sani ten years ba ten months ba ne, ba kuma ten weeks, ba ten days ba ne ba kuma ten hours ba ne.

Ba kuma ten minutes ba ne, na ajiye kome dominki duk lokacin da kika shirya ina nan ina dakonki."
Sai na shiga rud'ani CEO ko Ya Hafiz waye zan komawa...........
[12/14/2025, 9:16
PM] Maman Walid: 14
Ji nayi kaina yana wani irin juyawa, da karfi na ce musu.

" Ya isa nace ya isa haka.

Ka je ka amshi sadakinka kai kuma na kara ganinka sai na kashe kaina sai ka auri gawata." Na juya cikin gidan da sauri don na gaji da maganarsu.

Muryan Hafiz ya kara tsayar da ni.

"Idan baki dawo gare ni ba.

Wallahi haka zaki kare rayuwraki babu namijin da ya isa kallonki!"
"Ai kai ba Allah ba ne muna nan zaka ga tayi aure, don abu kazan kazanka ubanka!" Inji Ya Ado da ya fito.

" Kuma wannan da yake gabanka shi ne Mijinta.

Aure kake cewa ba zata yi ba?

Kai ne zaka hana auren, kambu tow Bismillah macuci azzalumi mara imani.

Ina ga sai an shiga tsakaninka da Lubnah tunda abinda kake nufi kenan katon dakiki jahili."
Tas Ya Ado ya wanke Hafiz sannan ya bawa Mr Turaki hakuri.

Tun daga nan na kara shiga damuwa, lokaci zuwa lokaci ina ganin sakon kudi da kati da kuma data, tow me zanyi da shi?

Ni ire-iren wa
annan abin basu wani burge ni.

Amma haka na share na cigaba da harkan gabana, Ya Hafiz ma bai daina kirana ba tare da barazana, har na rasa yadda zan yi da raina, a gefe kuwa Mr Turaki ya zuba min idanun bai kara bin ta kaina ba, sai dai abinda na fahimta shi irin mutanen nan ne masu iya dafa mutum da ruwan sanyi ba fa
a ba zagi amma wallahi gara yayi min hargowa irin na Hafiz amma ina ko da wasa bai
ara bin ta kaina ba, har ranar da na bar lagos, sai da na isa gida na huta na ji yana ta waya da Mama da Yadiko, zuwa yanzu na fahimci yadda Turaki ya samu fada a gidanmu, yadda ka san su kwanta ya bi ta kansu, Mama kuwa tasa ni tayi a gaba tana min gyaran jiki da jike jike take min, tare da dauke min huta.

Ban san inda ta hadu da wata yar maradi, matar nan har gida take zuwa ta min gyaran jiki.

Ko waje bana fita saboda gyara da kulawa.

Sai abin Yadiko nake jin an saka auren wata guda, tab'e baki nayi kamar wacce ta ga kashi na ce mata.

"Kuna ta wani damuwa bayan shi ba sona yake ba!" Na fada ina tura baki, rike baki Yadiko tayi ya ce min.

"Inji waye?

Waye ya gaya miki baya sonki?

Ko kafin ki zo sai da ya zo kwanansa daya ya koma ko garinsu bai je ba, a tsohon dakin Sani ya sauka.

Mijin da kika samu ba karamin mutumin kirki ba ne, har wurin danginmu sai da ya zaga ya gaishe su.

Ke ki godewa Allah." Tura baki nayi na ce mata.

"Ba wani sona yake ba kawai ganin haka kike kawai." "Soyayyar ta daki hancin kaniyarki, baya sonki kuma haka za ayi auren idan kin shiga ko sha piya-piya ki mutu ja'ira kawai." Inji Mama tana mai sake labulen, tana mita akan Yadiko take biya min nake iskanci kala kala.

A daren Hafiz yazo gidan yayi ta kuka yanzu zai cika baki zuwa anjima zai koma yayi ta bada hakuri.

Zuwansa na uku kenan, babu wnada yake kula shi.

Ganin haka Yadiko ta fito ta ce mishi." Amma kasan haramun ne nima a cikin nima?" " Yadiko ina son Matata, aka raba ni da ita." " Uwarka ta rabaka da ita!

Ita ta kawo khulu'i amma bata kai kotu ba, uwarka da yan uwanka suka kai kotu, don mune marasa zuciya sai mu dauke ta mu dawo maka da ita, sakarai kenan ai Lubabatu ta wuce lisafinka abinda baka zata ba ne ya same ka, tunda baka so ta samu miji irin wanda take tare da shi, sai ga shi bata cutar da kai ba, ta samu mijin kere sa'a shine bari ka lallabo kazo da wata fitinar da zata janyo a dakatar da auren ko?"
"Ai kuwa ko Hasiya da ifritai take yawo bata isa ba wallahi, lokacin da ka rabu da ita ai cewa kayi mata a gari kamar jamfa a jos, ina zaka kai kayan wanki, da Allah ya tashi sakayya sai gashi ita da kake mata kallon ba zata samu mijin da bai kai ba, sai gashi Allah ya bata wanda baka isa ka tsaya a gefensa ka ce ka tab'a auren Lubnah ba, kai ko a lahira ka ga Lubnah ka ce kasanta sai Allah yayi mana hisabi, fita kafin na watsa maka ruwan zafi dan iska mara mutunci idan na.

Ganka kamar na ga mutuwata haka nake ji.

Yanzu ka kawo kara ta auri wanda ya fika saboda bakin ciki sa mugunta.

"
Kusan abinda Mama ta fada gaskiya ne, yanzu Ya Hafiz ya dawo ne don yaga xan auri wnada ya fishi, da ace baya ne ko a jikinshi tunda yasan wanda zan aura bai kai shi ba, amma a cikin lokaci kalilan yaji labarin wnada zan aure haka yasa yake jin kyashi da hassada, yana niman hanyar da zai bata kome kowa ya rasa.

Wannan abin ya d'aga mishi hankali.

Shi yasa yake ta wannan koke -koken Mama kuwa ta rantse ya sake zuwa sai ta mishi babu dad'i, ya kullaci auren nan a ransa kuma duk inda ya zane, zai lalata auren nan sai yayi.

Hafiz
Tunda ya bar gidan yake kiran Hajiya amma bai same ta ba, ya kirata yafi sau uku.

Amma bai same haka ya koma gefen titi ya kira Nana, ta dauka.

" Ina Hajiya?" " Bata nan" ta bashi amsa, " Nana ya zanyi?

Ba zan iya barin Lubnah ta auri wancan mutumin ba, idan ta aure shi wallahi ko na fada na ta
a aurenta karyata ni za ayi.

Na gayawa mara mutunci cewa har hauka tayi ya ce shi ma mahaukaci ne zasu zauna cikin kauna da soyayyar mahaukata.

Nana kamar xan mutu don Allah ki gaya min yadda zan yi?" Ya tambaye , har da kuka kamar yaro.

Shiru tayi ta ce mishi.

"Ni dai ina kyale su, ka kyale musu rayuwarsu, rayuwata ma ta ishe ni ina cikin tashin hankali ba zan iya tsayawa ka kara cutar da Lubnah ba, domin duk sharrin da Hajiya ta tura mata gashi nan akan nawa Yaran, mijina ya sako ni a gaba ni ba sakakkiya ba ni ba mai aure ba, sannan kai kanka kana cikin arzikin Lubnah ne tunda har yau babu wnada ya ce ka bashi key
in motar da ake tukawa ashe kuwa dole ka barsu su rayu cikin kaunar juna, idan kuwa ka dage sai ka raba su, wallahi karshe rabon da yake tsakaninsu ya kashe ka."
Sai yau yake wani irin danasanin hana Lubnah haihuwa yasan yadda Uwa take akan Yaranta, ba zata tab'a hakura da Yaranta, ta auri wani namiji ba, yau gashi yana ji yana gani wani zai dauke mishi Lubnah, yau da yana da Yara da ita wallahi ko da iya Yaran zai saka dole ta dawo, kuma ya daura daga inda yatsaya.

Amma bai san wani abu yasa ya ki hada jini da ita ba, a yanzu idan kalle ta sai yaji kamar bai ta
a mu'amala da wata mace bayan ita ba, sai ga ita
aya ce zata iya daukar laluranshi, ita
aya ce zata so shi zata iya hakuri da shi, wani shegen kishi ne ya kama shi ya kira Hajiya sai lokacin ta dauka tana fa
in.

"Lafiya dai?" "Hajiya so nake a nakasa min mijin da Lubnah zata aure tun kwanaki nake gaya miki a yi abinda zai hana auren, kamar yadda aka binne zancen bashin nan amma kin ki yin kome!" Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta ce mishi.

"Hmmmm Yaron nan da zai auri Lubnah Kakaninsa akanshi suke, suna tsaye akanshi yadda baka zata ba, ita kanta Lubnah Uwarta tana tsaye a kanta babu yadda za ayi wani abu na sihiri ko tsafi ya same su, domin suna cikin kariyar Allah.

Sannan idan aka matsa mutum zai iya fuskantar gagarumin lamarin wanda mutuwa ce.." shiru yayi duk da wannan bala'in tsoronshi da mutuwa a fili take, duk abinda za'a kawo mutuwa a cikinshi yana gudu.

" Hajiya a nakasa shi ya koma ba namiji ba!" Ya fada yana kallon titi.

"Baka gane bane?

Ba fa abinda za a iya mishi domin Yaron jikinshi a tsare yake itama Lubabatu babu wani abunda zai iya zama a jiknta, da kamar da ne zaka iya amfani da yadda za a zuba mata abincin da zata ci, in sha Allah za a dace amma a yanzu ko me ka bata ba zata tab'a karba ba." "Hajiya a hada a kayan gudunmawar da zaku basu, na hakura amma wallahi sai ta fito saboda matsala.

"
" Ka shirya mutuwa?" Ta fada mishi cikin kosawa da maganarshi, " sannan ka sani irin wannan aikin ba karamin kudi yake ciki ba, idan ka shirya sai ka turo ku
in aiki da na yanka, amma ka sani ba zanje na amso kayan aikin ba, kai zaka ne can ka amai kayanka ni nawa na shiga tsakani ne!

" Bai ji ya fasa abinda yayi niyya ba, dan kudin da ya samu a wurin wani abokinsa ya tura mata akan kafin ya iso Jama'aren sai ta je ya amso.

Haka ya cigaba da tafiya yana ta sake sake.

Yadda idan aka yi aikin Lubnah zata kasance da shi domin auren maza biyu zata yi, yasan abinda ya shirya mata.
Chapter 17 · 0% Book details