← Book details Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 48

Sashe 13

Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kul ki hada ni da wani ko kishiya zaki min dole sai bayan idanuna, wallahi sai na shayar dake mamaki!" Kura mishi idanun nayi kafin na ce mishi."Ni dai na gaji ka gaya min me kake so na biya ka abinda ka min oho dama ance muna zaman dadiro ko?

To gaya min inda zan zo na baka jikina idan zai wanke maka zuciya da asarar da
..." Tass naji ya kwashe ni da mari, wallhi sai da na nime jina da ganina na rasa.

Na kura mishi idanun cikin wani irin kaduwa da tsoro nayi baya.

"Ni zaki nunawa jikinki don ina bin ki?" Murmushi yayi ya ce min," kin yi kuskure amma zan bi yadda kike so amma ba ta wannan hanyar ba, ina da kudin da zan saye ki na gaya miki ni sayanki zan yi siyanki xan yi kuma ki saka idanun!

"
"So what?

Don ka saye ni ina ba kai ka halicce ni ba?

Kuma marina da kai yi ban yafe ba, don bani da karfin da zan rama, da kake cewa zaka saye ni ba iska na kuma ba zaka tab'a samun nasara a kaina ba, Iyayena ba kwadayayyu ba ne, idan don ku
inka da ka ke ganin ka saka yasa kake tunanin zaka saye ni kayi kuskure.

Da shiga cikin wannan Masifaffen zuriarku gara na koma gidan tsohon Mijina duk lalacewar masa tafi kashin shanu, ka je can ku kashe kanku mutane da basu da imani.

Idan don raina ne ba zan tab'a zama cikin azzalumai irinku ba, kai ma bibiyar rayuwraka ake." Cikin fushi ya bar gidan.

Na fashe da kuka a wurin wallahi ba zan ta
a shiga rayuwarshi ba, ba zan shiga ba gara ma da Allah yasa na koma gidan Ya Hafiz.

Cikin wani irin gudu yake bai kallon gabansa,a garin shan wata kwana ya daki babbar mota, tuni motar shi tayi wani irin tsalle, ta fada can yayi wani irin juyi motar tayi sai da ta fadi sau uku kafin ta dungura da kanta, haka yasa mutane suka taru a kan motar aka fara
arin ceto rayuwarshi...........
(Hegiya mai kan doya ta kahe shi)
[12/12/2025, 7:52
PM] Maman Walid: 11
Dakyar aka fitar da shi a motar aka wuce da shi asibiti, bayan na dauki wayarshi aka kira Auta, aka gaya mishi halin da ake ciki.

Ai kuwa hankalinshi ya tashi.

Ya gayawa Ubaid kafin wani lokaci sun isa asibitin.

Hankalin sun a tashe, duk wanda yake makusancin Turaki ya zo asibitin.

"Yaushe ya dawo da yayi hatsarin?" Babu wnada ya iya bawa Uncle Auta amsa domin hatsarin ya zo musu bazata, sai bayan awa biyu aka fito da shi, yana barci ba wani ciwo ya ji ba buguwa, anan suka wuni zubur har dare koda ya farka sallah yayi, anyi tambayar duniyar nan akan ya fadi dalilin hatsarin yayi shiru bai gaya musu ba, amma kuma buguwar da yayi a kanshi sai da dare yayi jini ya balle mishi ta hanci da kunne, sai a lokacin aka san ya ji babban rauni a kanshi, abin tausayi Daddah cewa take.

"Zaki tafi kamar Babanki ko?

Zaki tafi kamar Aisha da ya bar ni da kai, kada ki don Allah." Haka aka sauya mishi asibiti a daren zuwa babban asibitin Lagos ana isa suka shirya mishi aikin gaggawa domin idan jini ya ta
a kai zai iya samun matsala, basu fito ba sai karfe shida na safe, aka fito da shi kanshi ya kumbura.

Wurin karfe tara na safe, ina kwance tun jiya da ya tafi nake jin tashin hankali, ban kyauta ba sam ina jin haka a raina amma ina tsoron kiranshi kada ya gaya min magana ina tsoron kada ya ce na gama gaya mishi magana zan kira shi na ce mishi me?

Wayata ce tayi
ara na
auka a hankali na saka a kunnena.

Idanuna a lumshe.

"Lubnah baki da labarin abinda ya faru ne?" Jim nayi na san cewa zai bani labarin an kore ni ne don haka na ce mishi." Allah yasa haka shine mafi alkhairi, na gode da haduwa da kai, ka taimaka min sosai shima Ceo ba zan manta alkhairin da ya min ba, yanzu ya ake ciki yaushe samu yi maganar kudin da yake bin family kana tare da shi ne?" Cike da mamaki ya ke kara cewa.

"Da alamu baki san abinda ya faru ba kenan?

Mr Turaki yayi hatsari har an yi mishi aiki da safe nan!" Wani irin tsoro ne ya kama ni na dafe kirjina kamar zai dirko na ce mishi.

"Da yaushe?" Na samu bakina ya furta haka, "Da rana wurin karfe daya zuwa biyu!" Ji nayi kamar zuciyata zata faso fashewa da kuka nayi na ce mishi.

"Na shiga uku!" Na fada da karfi ina me kashe wayar domin nasan na ce ni ce sanadin shigar Mr Turaki wannan halin Family dinsa sai sun daure ni, Allah yasa Ya Ado yana gida na fita da gudu zuwa kasa na cigaba da kuka.

Allah sarki shi a tunaninsa ma ya zata an gaya min wani abu ne ya faru da Abba, ai kuwa ya riko hannuna da
arfi yana fa
in.

"Lafiya meye?" "Na kashe shi?!" Na furta tare da rike bakina da karfi, na fashe da wani irin kuka.

Na zube a kasa na cigaba da cewa.

"Na kashe shi Ya Ado ni ce nayi mishi magana, ni ce na gaya mishi magana, ni ce nayi sanadin hatsatinsa.

Wallahi bani da yadda na iya ne, na gaji ne family dinsa ba zasu iya dakatar da shi ba, amma ni sun san dole na nisanta kaina da shi, idan suka san ni ce zasu zo kaina!" Murmushi yayi ya ce min.

"Kina sonshi ko?" Cak na ji kukan ya tsaya na kalle shi, "me yasa ka min wannan tambayar?" "Ok shi kenan gara ya mutu kowa ya huta!" Rufe bakina nayi na shiga girgiza mishi kai.

"Eh kai meye amfanin saninki da yayi a rayuwarshi tunda bakya sonshi?" Anan yayi ta zazzaga min magana da fada wanda ya sa naji kaina kamar zai fashe na ce mishi da karfi.

"Waye ya ce maka bana sonshi?" Sai kuma nayi shiru, na kifa kaina a tsakanin cinyoyina, na cigaba da kuka.

"Kina sonshi?" Gyada mishi kai nayi ina kuka.

"Da gaske kina sonshi ba wahala zaki bashi ba ne?" Cikin shashekar kuka na ce mishi." Ina tsoron kada ya min rayuwar Ya Hafiz ne amma wallahi ina sonshi don Allah Ya Ado kada ya mutu!" " Shi kenan daina kuka in sha Allah ba zai mutu ba!"
Haka yayi ta rarrashina don nayi shiru ya kira Uncle Auta, ya tambaye shi ya gaya mishi.

" Ok zamu zo asibitin ni da Lubnah." Yana gama wayar ya ce min.

" Je ki shirya amma ki sani kasa ki sake ki yi wani magana idan muka je." Gyada kai nayi haka na haura sama, na shirya sannan na sauko, muka tafi asibitin hankalina a mugun tashe, a lokacin da muka isa iya mazan familyn ne a bakin kofar sai kakanshi.

Wani irin kuka ne ya zo min, haka na isa na gaishe su kafin na isa bakin kofar da kana iya hango shi kwance.

Komawa daya daga cikin kujeran wajen nayi na zauna tare da fashewa da kuka, Kakanshi kallona yake yana murmushi ya ga yadda na daura hannu na kaina ina kuka, Ya Ado ya ce min.

"Tashi ki koma gida, tunda bakya jin magana!" Hadiye kukan nayi hawaye na zuba, "kina tsoron kada ya mutu ko?" Kallon kakanshi nayi da yayi maganar.

"Me yasa kika zo bayan kin ce bakya sonshi?" Wani irin bugawa zuciyata tayi, "sun miki barazanar zasu miki wani abu ne ko?" Hawaye ne ya shiga zuba min.

"Lubabatu Bilal yana sonki tun baki zama mutum ba, yana sonki tun da ranar da ya daura idanun akanki, Bilal kowa shakkarsa yake amma ke din kece rauninsa.

Yana iya yiwa kowa tawaye har da ni kaina amma ke ya kasa sarrafa kanshi akanki, gani yake idan ya fito ta kowani fuska ya ce yana bukatarki zaku iya zarginsa da cewa ba don Allah yake sonki ba, Lubabatu Bilal ba kashin yadawa bane, yana da kudin da zai aure ki da karfin tsiya amma yana son ya ji da bakinki kina bukatar shi a rayuwarsa.

Idan wani ya kara kiranki ya miki barazana akan Bilal ki gaya min kotu ce zata raba mu, amma ke idan kika cutar da Bilal Allah ne ka
ai zai mana hisabi, yana sonki yana kaunarki, yana tausayinki yana jin ciwon halin da kike ciki, yasan idan ya takura dayawa zaki fama ciwonki yasa yake nan a tare da ke, baki yi mamaki yadda kome naki yake tsaye a cikinsa ba, ga Bilal nan a karo na biyu idan ya mutu mun yi asara amma samun namijin da zai tsaya miki a matsayin namiji kuma bango ni dai nasan me na haifa, mahaifinsa kuma yasan me ya bar min, Ubansa a tsaye yake akan kome haka shima yake, shi din zagi ne a waje amma gabanki kamar dan tsako ne, ki yiwa zuciyarki adalci tana bu
atarshi amma tsoronki zai kai ki ya baro.

Ki yiwa kanki adalci yana bukatarki, mu kuma muna bukatarshi." Yadda dattijon yake min magana da adalci yasa zuciyata ta bude hankalina ya koma baki
aya kanshi.

A hankali na mike zuwa kofar dakin, ina kallonshi yadda yake barci a wahale ni ce ma jefa shi cikin wannan yanayin?

Ni ce na saka shi a wannan halin?

Yanzu nice na saka shi a wannan halin?

Ni ce sanadi kenan.Durkusawa nayi kasa ma fashe da kuka, na rasa me yake mun dad'i.." kai ta gida kada itama ta samu wani ciwon?" Haka Ya Ado ya d'aga ni, ya kai ni mota sannan ya koma ban san me ya faru ba, sai dai na ga kyakkyawa farin ciki a tare da shi.

Ai kuwa zazza
i ya rufe ni.

Yadda nake kukan ya matukar d'aga mishi hankali, har muka isa nasiha yake min, sai da Aunty Zakiyah ta bani magani na samu kaina, zuwa dare kome ya dawo min.
Chapter 13 · 0% Book details