← Book details Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 48

Sashe 21

Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Karfe daya na rana suka iso lokacin gidan ya cika a gidan nan Aunty Zakiyah da Aunty Munah basu nan, amma har Raliyah daga Jos sun zo yan kaduna ma sun zo, suna sallah dangin Mr Turaki suka iso wurin karfe biyu da minti talatin.

Tun daga bakin kwananmu aka rasa inda za a ajiye motar yan kawo kaya, abinda nake gani a blogs yau shine a kaina, yadda aka yi ta fitar da kayan ana shiga da shi kai rakiyan kawo kayan har da yan sanda da civil defense, aka kawo kayan aurena.

Wato ba iya jijjiga table nayi ba karya table din nayi, domin har daga makotan unguwarmu shigowa ake zuwa ganin kayan.

Ni kan tunda na shige uwar dakin Mama ban fito ba, a babban parlourn baki aka karbe su, koda yake ba abinda xan cewa Yayuna sun fitar da ni kunya ba zan iya cewa kome ba, a cikin wa
anda suka kawo kayan har da wata baturiya anan suke cewa kanwar Mamanshi ce ita ce autarsu wato Miss Herlim, bayan an karbi Kayan an kuma bude anyi addu'a, sannan aka yi addu'a, kafin suka ce.

"Tow mu dai zamu wuce ba kwana zamu yi ba!" Ita Miss Herlim ce ta bukaci ganina, Aunty Hindatu ta ce mata tazo, ina zaune a dakin aka shigo da ita, ko bata gabatar fa kanta ba nasan Yar uwar Mamansa ce.

Tana shigowa ta rungume ni, tare da kama hannuna ya saka min wani abun hannu.

"Inji Mamanmu, tace a sakawa Labubu wannan." Shafawa nayi ina kallonshi murmushi na ce mata.

"Na gode!" Murmushi tayi ta ce min.

"Mafarkin Son zai tabbata, don Allah ki mishi adalci yana sonki so na hakika, mutumin kirki ne bai ta
a niman matan banza ba, na kirkin ma baya bi, bai ta
a shan giya ko wiwi ba, balle kuma taba.

Mutumin kirki ne sosai.

Zai kula da ne, ki rike mana shi amana maraya ne bai da Uwa bai da Uba sai kakanni.

" Sai yanzu na tuna mun yi fada ashe bar muka bar Dubai a tare muka sauka a lagos, mu kuma sai muka sake bin wani jirgin zuwa Jos, bana son tuna abinda ya fada mu, domin raina bacci yake.

Koda yake ba laifinsa ba ne na me hoton ne, da kuma nima, Kodayake ai ba wani abu bane, awurin daukar hoton ne ya min tashin
a'a, na kusan gaya mishi magana, amma ya dauko duk laifin ya daura min domin kuwa bai yarda yayi kuskure ba, har sai da Auntynshi ta shiga lamarin, nasan ya hanani saka turare mai karfi amma Aunty Innah ta saka nu sawa.

Shine ya nime yayi min rashin mutunci.

Har yau mutumin nan ya ki kirana ya bani hakuri bayan yasan shi ne da laifi, murmushi nayi nace mata.

" In sha Allah!" Haka ta fita duk wani abinda muka yi sai da aka hada musu tas suka tafi, bayan tafiyarsu Yadiko ta ja kofar ta rufe.

Domin kuwa bata ji a ranta a bude parlourn ba, haka kowa ya gama son gani sai bayan tafiyarsu aka bude tare da zuba idanun akan kayan aka gama gani aka rufe parlourn, bayan isha aka tattara kayan sai gidan Ya Umar aka kai can, karshe aka bar gidan da kamshin yan gayu, wurin karfe tara Ya kira Mama suka sha hira yayi ta godiya.

Tare da farin ciki an karbi danginsa da mutunci an karrama su..

Ni dai ban san yadda suka kare ba, domin barci ya kwashe ni sai wurin karfe biyu na dare na farka nayi alwala na gabatar da nafilla, ban kwanta ba sai karfe hudu saura na kwanta.

Washi gari mota Ya Tahir ya kawo aka mai da yan jama're, suna barin gidan nima Aunty Raliyah ta kai ki saloon, muka je aka gyara min kaina, ana wanke min kai kalman Jalilah ya dawo min inda take cewa.

"Na ga sai wani murna kuke kasa dai a zurma dayawa domin dai kaf duniya babu me iya miki kirkin da Hafiz ya Miki!" Ta fada tana murmushi, nima na ce mata..

"duk wnada ya goyi kare yasan yadda zai da bakinsa, Malama ina miki farin ciki, zaki auri abinda kika jima kina jira." Daga haka ba barta a nan.

Murmushi nayi kawai ganin Ya Hafiz take, haka aka wanke kaina da kafana aka gyara min farce na.

A ranar da muka dawo gida.

Mama ta bani ruwan zam-zam take gaya min cewa.

Yadiko ta biya aka hada min daga can Belaye, aka kawo min.

Shi dai bai ce musu kome ba, ya ce a cigaba da shiri aure za ayi shi kuma akwai haske d duhu amma hasken tafi yawa, Tunda ta fadi haka suke sadaka kome badawa suke sadaka, kamar zasu zauce saboda kawai Allah ya bada zaman lafiya, haka yasa kowa ka gani a hidimar da aka fara hankalinsa kwance.

Ranar Juma'a Goggo Alti tazo, ta ce ta bar Goggo Uwani da Talatuwa a can, musamman ita da zata yi auren yarta, amma wani ikon bayan isha sai fa Goggo Uwani, kamar an wurgota daga daka, abinda ya bawa kowa mamaki an daura auren Hafiz da Jalilah.

Ranar Juma'a daren saukar kur'ani aka yi, ba ayi kome ba.

Washi gari kafin daurin aure aka yi walima wanda karfe goma aka yi shi, ana gamawa sha daya saura muka aka kara shirya ni.

Tun daren jiya aka kawo mai lalle da asuba ta zana min yayi kyau ya zauna das a hannuna.

Da yake a masallacin gwallaga ake daurin auren, dubannin al'umma suka shaida daurin aurena.

Bilal Haris ElYakub kumo
Lubabatu Usman Umar Jama'are, akan sadakin sisin gwal, guda ashirin da biyar.

Lakadan ba ajalam ba.

Idan ka ganshi a wurin kowa sai ya san an daura aurensa domin yayi wani irin zuru-zuru.

Bayan an gama aka dauki hoto da manyan baki sannan aka wuce gidansu amarya.

Ina sanye da wata farar doguwar riga wacce aka kawo daga wurin kakanshi a can Rasha, sai mayafin da na rufe kaina da shi aka fara guda alamar angwayen sun shigo sai da suka gaida aka yi addu'a, sannan aka kira ni parlourn baki, koda na isa gabanshi na je, wani irin rungume ni yayi kirjina yana buga tara-tara, ya ce min.

"Finally Mrs Bilal Haris Turaki.....
(Allah ya gani page biyu na so baku amma ciwon do da gefen kaina zuwa goshina ciwo yake min sosai kuyi hakuri zuwa gobe don Allah)
[12/16/2025, 1:37
PM] Maman Walid: 17
Yadda ya rungume ni naji haka a jikina, sai yanzu nake jin kamar ina safe place, he became mine, kara rungume shi nayi hawaye na zuba min tabbas mutumin nan yayi hakuri ya jira har Allah ya bashi, duk wanda ka gaya ya jima yana nima to kada ka ga dare daya ya samu kace ta wata hanya ya samo hakuri da juriya.

Dakyar aka janye shi sai gu
a ake mana, kafin aka fitar da shi.

Parlourn Mama suka shiga ya zube akan gwiwarshi, da sauran yan uwansa ta ce mishi.

" Bilal ga Lubabatu nan na baka, Bilal idan ka gaji da Lubabatu kada ka wulakanta min ita ka kira Ado ko Tahir ka ce su zo su
auki Kanwarsu, Bilal kada ka tozarta min Yarinya idan tayi maka laifi ka kawo min ita ni nan nasan abinda zan mata, Bilal don Allah idan ba zaka zauna da ita kada ka kore ta, ka.

Kira a zo a dauketa.

Ku shaida na roke shi da kada ya wulakanta min Yarinya don Allah kada ka wulakanta min ita wallahi tana maka ba dai-dai ba, ka gaya, zan zo har gidan na iso kota.

Ka yi hakuri ka duba rayuwarta na baya ka rike min ita da adalci.

Zata maka biyayya ba zaka tab'a hanawa tayi ba, kayi hakuri don Allah."
"In sha Allah Hajiya babu abinda zai faru, idan yayiwa Lubnah wani kawunansa ni zan fara sare mishi kai." Inji Uncle Auta, Ubaid ya ce mata.

"Hajiya in sha Allah haka ba zai tab'a faruwa, Hajiya ya iya zaman jiranta duk ya tsufa ya zama Kasungurmin tuzuru kafin baiwar Allah ta amince mishi ai kin san baba tsoho zai rike yar Matarshi da amana!" Ai kuwa aka yi ta dariya sannan aka yi addu'a.

Suka nufi dakin Abba, kasancewar yana jin nauyin Turaki da irin abinda ya mishi, mika mishi hannu yayi Turaki ya ri
e ya cewa Ya Ado.

" Kira min Auta!" Ya Ado ya zo, abokan wasa sun saka ni a gaba wai a bamu fili kawai tunda sun ga mijin ya gagara boye zallamarsa a fili nima har da wani cusa kaina kai Jama'a, wata abokiyar wasana yar kawuna kenan take min wannan tsiyar.." Hindatu fito da ita Abba yana kiranta?" Ya fada a gaggauce, baki
aya muka kalli juna, wani irin tsoro da tashin hankali muka shiga dukkanmu haka muka fito musamman yan uwana.

Haka muka fito aka shigar dani har gaban Abba tsoro ya gama cika ni.

" Bilal Turaki ga Lubabatu nan na baka ita, Bilal Turaki kada ka saka min Y'a kuka, idan ba zaka iya ba ka dawo min da ita don Allah, don Allah kada ka cutar da ita, ta sha fama da rayywarta na baya idan har bata maka ba, ka kira ni na tura Yarana su daukota.
Chapter 21 · 0% Book details