Sashe 16
Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Shi kuma irin nashi borin kenan, a kyale shi yayi yadda yake so ai matarsa ce idan ya gama fushi da kishin zai sauko a saka ranar da ya dace." "Baffa me kake nufi?" "Eh abinda nake nufi kenan;" ya tashi ya bar parlourn.
Karfe tara na dare Taj ya shigo gidan, yana parlourn abinda Uncle Auta da Nurse tana wanke ciwon, kallon Taj yayi ya dauke kai kamar bai ganshi.
"Good evening Sir?" Banza yayiwa Taj Uncle Auta ya amsa mishi, tsayawa yayi a can gefe nurse din ta gama ya sauke rigarshi ya kishingida yana jin zafi da shigar maganin.
"Sir!" Bai iya karasawa ba saboda yadda ya bu
e ido akanshi.
Zubewa a kasa Taj yayi ya dawo gabansa.
"Kayi hakuri wallahi kuskure ne, wallahi ban san cewa ita din taka ce ba." " Wai mai ya faru ne?" Murmushi yayi ya ce mishi."Tashi ka tafi!" Ya cigaba da kallon tv, Uncle Auta ya kara mishi tambayar me ya faru, amma yayi shiru can ya kara cewa." Wai kai meye matsalarka ne da kowa kake son samun matsala ne?"
are ayaba yayi ya gutsara yana kallon tv, " naji irin rashin kunyar da kayiwa su Khaulatu."
" Taya zan yi kunya arba'in da wani abu idan na ji kunya kai zaka bani auren Dadah karama?
Kai ko kai ka min rashin mutunci zan rama daidai gwargwado, kowa ya ji yadda ake ji." Daga haka ya cigaba
da cinye abin da ta kawo mishi.
"Tow shi Taj fa?" "Kama shi nayi yana rike hannun Matar Turaki!" Daga haka na cigaba da abinda yake sai kuma Uncle Auta yayi shiru wato maganar gaskiya shine zai matu
ar wahala zaka samu sune suka mishi laifi, shi kuma kamar mace wurin gasa bakar magana.
"Dazun mun yi magana akan lamarin, ina ga kamar su a bangarensu akwai babban challenge da dole ta bangarenka ne za a samu masalaha.
"Shiru yayi kafin ya ce mishi.
"Gaskiya bana ganin akwai wata mafita, zan duba in sha Allah."
***
A few weeks later na ji gara na koma Bauchi na gaji da lagos, har saka wayata nake a gaba ko zai kira ni, amma mutumin nan na rasa inda ya saka ni, abin da nayi nasan nayi kuskure amma taya zai manta da ni bayan nasan cewa mutumin nan yana kokari tow ya zanyi da danginsa?
Sune.
Daukar wayar nayi ina kallon sunansa wato Masifaffen da na saka sunanshi.
Wani bude kofar dakina aka yi da wani karfi ban san lokacin da na danna kiran ba.
Wayar na cillar tare da kallon kofar dakin.
"Kika ce zaki koma Bauchi?" Bakina yana rawa na ce mishi.
"Eh Ya." "Aikin fa?" "Yace kada ka kara zuwa!" "Ke wacce irin mutum ce bai shegen taurin kai?" "Ya Ado ba fa!" "Amma kece kika ce zaki ajiye aikin?
Ya Ado ya kake so nayi?
Baki
aya an hade min kai a office din kamar wacce nayi wata zunubi, wacce take kula ni itama ta daina kula ni.
Ya Ado ina son aikina ina son na, amma kullum turo min sakon barazana ake akanshi.
Na rasa yadda zan hatta wurin aikin ina ganin yadda ake bina idan ban ajiye aikin ba ya zan yi?
Ni kaina bana son nayi haka don za'a ce saboda abinda ya mana zan yi butulci amma ka fahimci wani abu bana son saboda ni ya samu matsala da kowa zan koma Bauchi."
"Hafiz ya can yana jiranki amma kin sani ko?
Kuma Baban Jama'are yana bibiyar Abba akan ki koma gidan Hafiz, ki sani ba zan shawarar gidan Hafiz ba, amma ki bude baki ki cewa CEO ya turo domin shine irin mijin da kike bukata.
" " A ce na aure shi saboda abin duniyarsa ka fahimta mana!
Allah yanzu" " wannan yarinyar Allah ya san dalilin da yayo ki a yanzu baki shiga cikin arnan farko ba, wurin taurin kai.
Da ba karamin wahala za'a sha dake ba, shi Mr Bilal din ya ce ba zai iya kare ki ba ne?" Tura baki nayi na ce mishi." Ya ce maka yana sona ne?
Ina korata yake a jikinshi gara na koma Bauchi na huta!
Ko ban koma gidan Hafiz ba aure zan yi." Na manta da wani zancen wayar ya Ado ya zuba min idanu ya ce min." Yanzu kina nufin zaki koma gidan Hafiz kenan?".
" Ya Ado mugun da ka sani." Tass naji saukar hannunsa a fuskana, ban san yadda akayi ya tawo gabana jikinshi yana rawa ya ce min.
" Har fata kike ki koma wancan kazamin rayuwar?
Burinki shine ki wulakanta Mama da ta gama kunce zaninta a kasuwa ko mr Turaki bai ce yana sonki ba, wallahi kin ji na rantse da Allah na bashi ke, idan kin so ki shiga bariki aure babu fashi domin ba ma zaki koma Bauchi satin nan zan daura auren na ga uban da ya isa dakatar da ni, bari ki ji sadaka zan bashi ke.
Yar iska mara kunya!" Cin mutuncina Ya Ado yayi min, kiranshi yayi a waya ya ce ya shirya nan da sati biyu.
Ai kuwa na fashe da kuka har da ihu, na kira Mama ko zata goya min baya amma ta ci mutuncina tare da cewa, idan da na san wutar da ake hurawa a Bauchi da ba zan fara kiranta ba, tayi ta sakawa Ya Ado albarka.
Ai ban san lokacin da na fara rashin lafiyar karya ba, Ya Ado ya ce ko mutuwa nayi sai an daura auren naje gidan shi ayi min jana'iza.
Kwana biyu da faruwan lamarin ba sai ga Uncle Auta da sadaki ba, shi kuma Ya Ado yace a kai Bauchi, lokacin da suka isa Bauchi Ya Umar da Ya Tahir suka amsa, tare da Alhaji Sa'idu.
Domin har da baki daga Gombe babban hidima aka yi, lokacin da labarin ya isa Jama'are an kawo sadakina, sai hankalin kowa ya tashi.
Immediately sai ga Ya Hafiz a lagos, duk da Ya Ado ya hana shi shiga gidan amma yadda ya haukace sai da naji kamar nayi mishi wani kuskure mai girma domin kuka yake wiwi yana rokon ko za a kashe shi ne ya yarda fatanshi ya mutu ina tare da shi, akwai wani abu da na kasa rabuwa da shi a tsakanina da Ya Hafiz shine tausayi, ina tausayinsa wanda na fahimci cewa har yau zuciyata tana tunawa da shi, sai dai da ba tuna da tarin laifuffukanshi a tare da ni, sai na ga bai cancanci nayi wasa da rayuwata ba, amma kuma shi Mr T zai zauna da ni bana haihuwa ne?
A rana na biyu da yake zuwa gidan na fita, wanda sai da nayi danasanin fitar da nayi.
Domin kuwa lokacin da na fita na same shi yana tsaye ya zuba min idanun Ya Hafiz da na sani
an gayu ne na fitar hankali amma wannan na gabana kamar wanda aka kamo shi daga cirani, gashi ya yamutse kamar wanda aka biyo bashin masifa, kallonshi nayi na tuna yadda yake min dariya a baya.
"Me kake bukata?" "Ki yi hakuri!" Shiru nayi ina kallon kasa ashe akwai ranar da Ya Hafiz zai bani hakuri?
Ashe akwai ranar da zai zo ya ce min nayi hakuri?
Na zata shi mutum ne me ra'ayin kansa ba a saka shi ba ya ji kuma baya gani.
"Amma kasan na amshi sadakin wani ko?" Tsayuwar motar Mr Turaki a gaba damu ya kashe ya fito, ya tsaya yana kallonmu.
"Ya Hafiz kayi hakuri ka rabu da mu, ban san me ciwon kai ba sai da na ha
u da shi, ban san yadda zuciya take ji ba sai da na same shi a rayuwata, nasan kuruciya tasa na amshi soyayyarka amma shi zaman jirana yayi har wannan lokacin, ina jin wani abu a kanshi."
"Karya kike yi, wallahi karya ce bakya sonshi kudinsa kike so don ya biya muku bashi." Ya cigaba da zage -zage.
"Wuce ki shiga cikin gidan." A hankali na juya ina kallonshi, hawayen dake ta danne shi ya sauko da gudu, na saka bayan hannu na goge.
"
A wancan ranar da ya tsaya a gabana, rawan kai da rashin sanin ciwon kai yasa naki kulawa da tarin Alkhairinsa, amma a yau da yake gabana sai nake ganin kamar banbanci sabon rayuwar da yake bibiyata da shi ba, nayi laifi amma haka ba yana nufin daga ganin Sarkin fawa sai miya tayi zaki ba ne, wancan da ya tsaya min a wancan rayuwar kama yake da gardi irin almajirai da aka
auki nauyinsu.
Madadin yau wanda yake gabana, CEO ne guda mai cike da kammala da nutsuwa, ba kamar wancan na baya mai yawan murmushi da fara a ba.
A yadda nake kallonshi tsaf zan buga kirji nace shi din masoyina ne amma kalaman Ya Hafiz da ya fada ya saka ni jin wani irin abu ya tsaya min.
" Kana ta murna ka kai sadaki shi sadaki ba aure ba ne, kuma idan har a Bauchi za a daura auren in sha Allah ta haramta maka.
Domin kuwa ni ne mijinta a duniya ni ne a lahira!" " Ya Hafiz wannan rayuwata ce, me yasa sai ka lalata min rayuwata ?
Me na maka kake son saka ni a damuwa?
Na zata duk tarin alkhairin iyayena da suka maka sai ka tozatani?" Murmushi yayi alamar ya samu nasara ya a kaina sai ya juya kan Mr Turaki ya ce mishi.
"Ka sani baya haihuwa, domin!" "Waye ya gaya maka kowa yake bukatar Haihuwar?
Ni ita nake so, ba wani abu ba, idan don wani abu nake bukata baka isa ka aure ta a farko ba, ka.
Ji na gaya maka kul!"
"Wallahi baka isa ba!
Lulu ki dawo gare ni hatta Arzikin Abba yana tare da aurenmu tunda muka rabu masifa suke ta faruwa baki gane ba ne?
" Cikin wani irin baki ciki.
Na juya zan fita suka fara fada kamar zasu kashe kansu.
Kasa magana nayi ina kallon maza biyu a gabana, na rasa yadda zan yi da rayuwata.
Ban gama nazarin abinda zan fa musu ba, sautin muryan Ya Hafiz ya daki dodon kunnena.