← Book details Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 48

Sashe 20

Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya Allah ka kai mu ranar da zan ga auren Bature!*
Da yake haka wasu suke kiranshi a cikin family
insu, wai Bature duk da bai da kalar fatar Mahaifiyarshi, amma kuma yana da yanayi da turawa.

Musamman i
wayar idanunsa.

Ranar da muka gama Umara, Mama take gaya ai zan bi Mr Turaki da Jasminah, dubai akwai hoton da za'a yi a can, Aunty Hindatu da Aunty Innah suna can, ya biya musu kudin tafiya da kome da kome.

"Mama sai!" "Allah ya shirya ki!" Ta fada sannan ta cigaba da hada kayan tafiyarta gida, haka kuwa aka yi Mama ta bar Saudiya, koda Mama bata nan, na kame kaina kada ya ga babu Mama ya sauya halinsa, sai dai wani ikon Allah, bai ta
a kallona ya ce yana son wani abu ba, har wani nuna mishi rashin yarda nake idan ya zo kusa da ni, amma wani murmushi yake, mun ya ce min.

"Ni fa bana da ra'ayi ne akan zina, da ina da shi wallahi ban san iya adadin matan da suke kawo min kansu ba, don haka ki daina min kallon Kasungurmin dan iska.

Ko a kasar nan idan ina son mace har dakina zata biyo ni.".

Hararanshi nayi.

Domin na lura ba ruwansa da kunya.

Kwanan Mama biyu da barin kasar muka wuce Dubai, su Aunty Hindatu suka zo daukata da Ubaid da Matarshi, wacce na ga yanzu ta sake kamar ba ita tayi ta haukar zubar da mutuncinta ba.

Sai da na wuni na huta kafin muka je inda Ubaid ya kai min dinki kayan pre-wedding din.

Sai da na huta domin mai hoton daga kasar China aka dauko shi, ranar dai hoto kala goma goma muka yi da kaya
aya, muna gamawa aka ce kanwar Mamanshi ta iso daga Germany da wani cocktail gown, wanda aka zuba mishi wasu pearl masu bala'in kyau da daraja, yadda ta rungume ni tana fa
in.

" Lunah ko?" Gyada kai nayi, tana murmushi ta ce mishi.

"Kayi sa'ar mace gata da kunya!" "Ni kuma mara kunya kawai ki ce Bilyl baka da kunya sai na sani, Lunah zaki sammin kunyarki?" Shi dai bai da ta ido, haka ta wuce dakin da ya kama mata, washi gari muna karyawa muka wuce wurin gyaran jiki da gashi.

Ina jin wata baturiya tana tambayar ko ina son wig ne?

Nace a'a ina da gashi na dai-dai gwargwado ina zan kara da gashin doki, haka muka gama wurin karfe biyar sai da muka yi sallah sannan aka min kwalliya muka fito, yau kan da Laffaya shi kuma jamfa fari tass laffayar fari ds ratsin golden, maganar gaskiya mun yi kyau a yadda ake hoton kamar mutumin yasan kan aikinsa, a rana na hudu muka saka wannan cocktail gown shi kuma suit ya saka baki, a wannan ranar ne muka yi hoton da har ya tab'a jikina wato hannunsa a kan kuguna, sai kallonshi nake a sace.

"Ai da mutane ni ba shaidani ba ne." Ya fada yana murmushi, ni kuwa sai kunyar su Aunty Hindatu nake ina ta astagafarallah, har aka gama na yau yana sake ni na sauke ajiyar zuciya kamar wanda ya cakume ni.

Sai satar kallonshi nake.

Bayan mun koma masauki yake bawa Ubaid labari sai dariya suke lokacin da muka fito cin abinci ya muka hada idanu, d'aga min gira yayi na daukr kai.

Sako ta turo min da cewa. *Kin yi kyau* kallonshi nayi, ban san lokacin da na sake murmushi ba, na tura mishi da cewa.
_Hmmm_
Sai da ya d'ago kai ya kalle ni, sannan ya cigaba da abinda yake.

Bauchi
A Bauchi kuwa ba karamin shiri Mama take ba, duk da bangaren Maza sun gaya mata basu bukatar kome akwai kome a gidan, amma Mama ta ce a'a ita fa ajiye kwarya a gurbinta....
[12/15/2025, 10:14
PM] Maman Walid: 16
Kaya irin wanda ba a zata ba, shi ta saya domin kudin da ta bada aka mata sayayya a kano aka kawo, kwana biyu da dawowarta Ya Ado ya zo da wasu key guda biyu, ya ajiye mata yana fa
in.

"Mijinta ya sayi gida anan Bauchi yace kayan da kika mata a zuba anan gidanta na Gombe akwai kaya yanzu haka jiya aka saka wasu an kawo su daga kasar waje.

Nan kuma an barshi idan sun zo ganin gida zasu sauka anan ko ita idan tana bukatar haka." Shiru Mama tayi domin abin Turaki ya fara bata tsoro, kada fara gulmar sun samu me kudi sai tatsarshi suke, bata son tashin hankali da surutun mutane.

"Baki ce kome ba?" Girgiza kai tayi kafin ta ce mishi."Ni lamarin Bilal ya fara bani tsoro, kada Yaron nan ya wulakanta min Yarinya, kada ya kashe kudi ya fanshe da tozarci." Girgiza kai Ya Ado yayi yana fa
in.

"Ban ga yayi kama da haka ba, mutum irinsa kwanciyar hankali yake bukata ba tashin hankali ba." Gyad'a tayi amma lot of thinks suna zuwa a ranta, tana tsoron kada ta sake jiki a dawo ana musu dariya." Tashi tayi ta nufi dakin Yadiko ta gaya mata abinda yake faruwa, kusan sai lissafinsu ya zo
aya, hankalinsu ya tashi.

Yadiko ta kira Baban wansu da yake wani gari a misau wato belaye ta gaya mishi halin da ake ciki, ya ce su bashi kwanaki uku kafin nan zai musu magana.

Amma yanzu su bada sadakar Pure water, bata gayawa Mama ba, ta saka sayo mata ruwa jaka goma aka kai masallaci da wani Islamiyya a nan dutsen tanshi, aka yi ta addu'a kuwa.

Zuwa yamma ta gayawa Almajirinsu akan ya turo musu Yara akwai abincin sadaka.

A yammacin Ya Ado ya bada kudi ayi cefane aka sayo har da nama, aka tashi aiki ba ji ba gani.

Store Yadiko ta shiga ta fito da ledar takeaway ta fito da shi tana fa
in.

"Wannan na hidimar biki ne, amma gashi zan yi amfani da shi, Ya Allah ka shiga lamarin nan!" Ta fada tana ajiyewa Abba da ya zama sai mishi kome ya turo keken da yake zaune a kai ya fito ya ce musu..

"Saboda naki Lubnah shine na zaku aurar da ita baku gaya min ba?" Shiru suka yi kafin Mama ta katse shirun da cewa.

"Tunda aka zo tambayar aurenta nake binka na gaya maka amma me kace min?

Cewa kayi kada na
ara saka ka cikin abinda bai shafe ka ba.

Yanzu kuma saboda kafi kowa adalci zaka ce munki saka ka cikin hidimarta." Murmushi tayi irin wanda kana gani zaka fahimci yadda take jin zafin abin a ranta.

"Amma ina da hakki akanta?

Idan aka cigaba da yin haka waye zai dauke ta da daraja.

Duk wannan rawan kafar da kuke yi ku sani bare ne ba dan uwanta ba." Ya fada ranshi yana jin zafin abin, basu kula shi na can ya ce musu."idan har albarkata ce zata rike auren Lubnah ba zan saka mata ba." Murmushi Mama tayi ta ce mishi.

"Tabbas rayuwar auren Lubabatu yana bukatar albarkanka amma ka sani ko ka saka ko kada ka saka aure babu fashi, kuma ka rike albarkanka ai naji Talatu da Uwani zasu bashi Jalilah da wannan nake son ka sani kamar yadda Lubnah tayi gaba har abada Hafiz da Jalilah ba zasu tab'a tarda da ita ba.

" Daga haka ta wuce dakinta ba zata kara miishi magana, haka.

Yayi ta fada har yana fa
in saboda abin duniya suka likewa turaki!

Yadiko ta ce mishi." Eh kai tunda ya fitar da kai kunyar kallon mutane da bashin da Tsinannen Yaron can ya ciyo maka, dole ka samu bakin magana ko kunya baka ji ba.

Ka zauna kana dabbawa kanka wuka.

" Tayi tsaki ta cigaba abinda take yi.

A can Jamaare fa haushin Yayun Lubnah sun tsaya kai da fata ba zata koma gidan Hafiz ba, shine suka yi zuciya tare Da bawa Hafiz auren Jalilah, wannan shine mafarkin Jalila ta sami Hafiz kuma burinta ne gashi nan ya cika zata samu Hafiz yadda take so, sai dai Hafiz shi baya ta ita domin kuwa zuciyarsa baki
aya tana can ga son zuciya.

Hatta hada auren bai san anyi ba domin ya je kulla nashi makircin.

Kwanaki goma sha biyu muka dawo daga Dubai a matu
ar gajiye da tarin tsaraba.

Wanda muna isowa aka yi ta tura kayanmu wurin
inki, har gida matar ta zo tayi ta amsa tana, duk da ya cewa su Aunty Hindatu akwai kayan biki daga Russia za a kawo don kome booking yayi daga can, mun dawo da kwanaki uku.

Wanda yayi dai-dai da bikin saura kwanaki,
Da safe Aunty Hindatu suka zo gidan ina zaune a daki ina karyawa suka shigo, kallonsu nayi na ce musu..

"Lafiya kamar an koro ku?" "Gobe zasu kawo kaya!" Wani zabura nayi tare da nufar daki suka biyo ni da yake Mama tana dakin Abba, daga nan ina jin yadda suke sa'in'sa da alamu maganar auren ne, sai da ta fito muka fahimci, ai akan auren ne domin kuwa ta ce ya bada abinda za ayi hidimar bikin ya ce shi ba zai bada ba, ya rigada ya tura Jama'are shi yanzu ya tura daurin auren Jama'are, shine take fada wai ayi bikin a can, ita kuwa ta ce ba yarda ba shine fa abun ya kai ga sa'in'sa.

Shi ya ce idan ba a Jama'are ba sai dai a fasa auren ita kuma tayi tsalle ta tuma ta ce babu wnada ya isa ya mata wannan rashin adalcin.

Karshe sai ga gidan ya cika da Yayuna dakyar aka lallaba Mama ta amince, amma kuma da Ya Umar ya zauna da Abban ya gaya mishi abinda yake faruwa domin har gidan Ango sun buga katinsu gobe za a kawo kayan aure, sai jikinsa yayi sanyi dama daga can aka zuga shi da yake bai da lissafi ya zauna a kai.

Dakyar aka kashe maganar a daura auren Hafiz a can, Lubnah za ayi bata a gwallaga, sannan shi Hafiz ranar juma'a ne yayinda lubnah ranar asabar ne.

Wani ikon Allah a masu zuwa amsar kayan har da Jalilah tazo ganin kayan auren, da yake gulma da munafunci ya kawo su.
Chapter 20 · 0% Book details