← Book details Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 48

Sashe 28

Alakar Zuci Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ina zan ji kunya tunda gidan mijina ne!" Na fada ina murmushi, tabbas yayi kewar abincinta, amma kuma fushin da yake da ita har yau ba daina jin zafi ba.

Sai da ya ci ya koshi sannan na bashi ruwa ya sha kafin ya mike.

"Yawwa Goodluck;" na ce mishi sannan ya wuce abin dariya a fusace yayi tafiyarsa.

Haka na gyara table din na kai kome kitchen, sannan na wuce dakina.

Ina waya da Mama muka gaisa sosai har da Yadiko.

Kafin muka yi sallama.. ina zaune wani idea ya fado min wata rigarshi na dauka na saka, yau ko da karfi sai mun shirya wallahi na gaji.

Ni ko labarin Hafiz ban kara ji ba, ina zaune ina karanta wasikar jaki ya shigo ya shirya zai fita ya ce min." Bani key zan je KUMO FAMILY MANSION!"
"Sai gobe yau lokacina Better go to your room, babu inda zaka na gaya maka." Daga haka na cigaba da wasa da kafana.

Sake baki yayi yana kallon yadda take mishi tsirfa kala-kala.

Abin ya bashi mamaki.

Haka ya koma dakinsa can naji ana buga min kofar gida kofar na je na tsaya ya zuba min idanu ganin Hijab har kasa na ce.

"Waye?" "Uncle Auta ne " aka bani amsa.

"Ai sannu me kake bukata?" "Wurin Turaki na zo!" "Ayya sai dai gobe amma yau turaki nawa ne ni
aya." "Ki yi hakuri ki bani aronsa." "Ina ka je kawai da ya tafi har tsawon sati uku ka tambaye ni ya gama amarci ko bai gama ba, amma haka na zuba mishi idanun don haka sai ya biya kwanakin da yayi baya tare da ni wuce wurin Maman Daddah kafin na kira ta na gaya mata kun fara niman sabin yan mata!" "Tow haka abin ya koma!" Ya juya yana fa
in haka juyawa nayi na kalle shi yana rike da hularshi.

Cike da mamaki yake bina da kallo.

"Kayi lokacinka yanzu nawa ne!" Na wuce dakina.

Fitowa yayi da sauri daga ban daki, jin yadda aka shiga sallah, ya sa shi kara nufar kofa a zafaffe domin yana tsoron kada ta kara sashi rasa sallah Asr kamar yadda ya rasa ta Dhur, sai dai kash kicibs suka yi da ita cikin hargitsetsan yanayi da yake kara karayar mishi da wasu kwarin gwiwa da yake da shi, kin kallonta yayi domin haka na iya Dragging dinsa into wani part da bai shiryawa ba, cikin makirin muryanta da rabonsa da ya ji muryan kusan sati uku kenan, ta ce mishi.

"Malammmmmmmmm!" Jin wani abu yayi ya tsaya a tsakiyar kansa ban da ita da tasan tasirin da muryanta yake da shi, da ba zata tab'a kiranshi da wannan yanayin ba, hade rai yayi ya cigaba da tafiya don baya son ya kara kallonta ba tare da ya nufi masallaci ba, ada idan aka ce mishi mata dangin shaidan ne baya tab'a amincewa, dawowarta gida yau a karo na biyu ya amince ita din tafi kowa sanin hanyar da zata kashe shi, kafin ya gama tunani ta kara cewa.

"Malammmmmmmm yunwa nake ji!" Raka'a na biyu da aka kai ya saka shi dafe goshinsa tare da watsa mata harara, ai kuwa ta shiga buga kafarta.

"Shi kenan kamar yadda ta min dazun ta kara yanzu dole nayi sallah a gida " ya rasa yadda zai yi da ita tare suka ci abinci amma yanzu tana kara mishi wani abu wai yunwa take ji.

Zuba mata idanun yayi ya juya zai tafi, na bi bayansa har dakin ya shimfida abin sallah, nima na fito naje nayi alwala na dawo dakin na samu ya fara bin bayanshi nayi muka yi sallah tare.

"Yunwa nake ji!" Na fada a hankali ina matsawa kusa da shi.

"Malammmmmmm!" Juyowa yayi ya rufe min bakina.

"Naji!"
Tashi nayi a hankali zan fita daga cikin dakin ya ce min.

Na yarda so halitta ce, ya ratsa zuciyata, amma ba zan jure abinda ya faru ba , ki min bayani Lulu... ina sauraronki ya aka yi Hafiz ya zo gidan nan?"
Murmushi nayi tare da zuwa na zauna a gabanshi, hannuna na kai gaban rigarshi na shiga balle bottom din.

Bai hana ni ba sai ma kallona yake.

"You like it?" Gyada kai nayi a hankali ya cire rigar tarin kwanji da tsokoki suka bayana.

Daga nan labarin ya sauya, wasu abubuwan dai sirrin Turaki ne da ni, domin na fahimci wata rayuwar daban take da lissafin mai karatu, shi bako ne a bangaren, yayinda ni yar gari na kasancewa wacce take rayuwa a wani bangare na garin, kamar yadda ake cewa mata suna suka tara haka ma mazan suna suka tara, a daren nan namiji gwarzon mijina, y goge min hadda baki
aya ya bude kaina ya zuba min nashi iya nashi shi dayansa.

Ya daura ni a lissafinsa wanda iya ni ka
ai ya daurawa, akwai rana mai matu
ar daraja irin wannan ranar?

Akwai wata rayuwa mai dadi irin wannan rayuwar?

Mutumin nan ya wanke min duk wani abinda nake ji ko nake gani.

Mutumin nan ya dasa min so da kaunarshi tare da bu
atarshi a kodayaushe.

Sai bayan kome ya lafa ya kara rungume, yana shafa bayana kamar za a kwace mishi ni!

"Thank you Lunah!" Kwantar da kaina nayi a kirjinsa, ina jin wani irin yanayi yana ratsa tsakaninmu.

Mun fi awa a makale da juna, kafin ya tashi ya ha
a mana ruwan wanka, kin shiga mu yi nayi amma haka ya tilasta min na shiga muka yi wankar muka fito.

Kunyarshi kuma sai ya cika ni, riga da wandonsa ya dauko min na saka, ya gyara gadon ina kallonshi.

Bayan ya gama ya janyo ni jikinshi muka kara kwanciya, kanshi ya daura a kirjina, na rungume shi.

Furfura kanshi na kai hannuna ina tsige su ya ce min..

"Kin ga furfura ko? lokacin da na ganki ina talatin da wani abu, yau gani ina bawa arba'in baya, tunda kika amince kika aure ni, zan gaya miki, ina da lafiyar da zan jiyar dake farin ciki a ranan da muka kasance! kawai ki kaunace ni ki bar jin kunyana domin ni bani da kunyar!" Tabbas bai da kunya, amma sai na tsinci kaina da kasa magana na cigaba da wasa da gashin kanshi.

Ina murmushi da jin wani farin ciki a raina ya ce min.

"Ki ce min wani abu? ina jiran kalmanki ko da ta a'a ce." Murmushi nayi ya d'ago kai yana kallona, wani irin tartsatsin kauna nake hangowa a cikin idanunsa.

He like me, sama da yadda nake tsammani.

Chakulkuli ya fara min nayi ta kaucewa, daga karshe yayi nasarar daukata ya daura ni akan kafarshi yana fa
in.

"Shi yaren soyayya ba ruwansa da yare ko kabila, ba ruwanshi da jinsi mace ko namiji, shi wata halitta ce da take wanzuwa cikin zukatan masoya imma mutane imma wasu halittun na daban, ya kike fahimci haka?

Ni na fahimci haka ne lokacin da na hadu da ke."
Akwai wani irin dad'i da nutswa idan ka ji namiji yana fitar da abinda yake ransa.

"Ina sonka Malam, sai dai ina tsoron kada ka juya min baya, ina tsoron kada ina murnan na rabu da Hafiz!" Rufe min baki yayi yana girgixa min kai.

"Allah ya min tsari na zama kamar Hafiz Allah ya rufa min asiri na zama irin Hafiz, Ubangiji ya hanani ranar da zan zama kamar Hafiz.

Kai Allah ya nuna min mutuwata sama da ranar da zan ga na zalunci matar da nake aure ba." Kifa kaina nayi a goshinsa na ce mishi.

"Na gode!".

" Me yasa kike godiya!

" " Ai kai mutumin kirki ne kuma me cika alkawari ne, shi yasa nake maka godiya domin zaka cika alkawarin da ka
auka.

"
Haka kawai na zauna ayi min sakiyar da ba ruwa, mijina yana sona nima ina son mijina, akan me zan bar wani ya shiga tsakaninmu, a ranar duk a gida yayi salollin, wurin karfe tara aka buga gidan ya kalle ni, murmushi nayi na nufi kitchen na dauko key na mika mishi.

Ya je ya bude Kofar.

" Ka fito daga prison kenan?".

Murmushi yayi sannan ya amshi ledar kafin ya kara magana ya banko kofar, Uncle Auta ya ce mishi." Ni ka wulakanta?".

" Sorry Uncle!" Wato mu fa sai yau muke cin kazar amarci, muka ci muka yi nak, sannan muka baje a parlourn muna hira da kallon wani film.

Daren ranar dai dayawa zasu so jin labarin amma kuma, ai lamarin Babba ne fa.

Domin ni kaina sai da naji kamar na gudu mutumin nan wayo ne da shi, amma kuma duk abinda zai yi tausayi yake ba ni domin ya jima bai yi auren ba, ni kuma sai na mishi uziri, sai da muka kwashe sati daya cib sannan ya fara zuwa office shima din dakyar na lallaba shi, har da cewa Uncle Auta da Ubaid zasu mishi dariya ya ce musu sai ya rama min kwanakin da baya nan, riko shi nayi nace mishi.

" Wato bazani kayi kana gaya musu sai yanzu muke amarci!

" " Ai ke kika gaya musu!

" Zare idanun nayi na ce mishi." When?" " Kin manta kenan.

" Yana tuna mun ranar na ji kunya ta kama ni da gudu zan fita ya riko hannuna.

" Ban da gudu don Allah!" Kaina na daura a kirjinsa ina murmushi.

"Kin yi kyau kullum kara kyau kike min!" Ya fada min wata katuwa magana a kunnena, kunya ta sa na kifa kaina ina fa
in.

"Yaushe zaka fara jin kunya?" "Hala ranar da tsufa ya cimma ni!" Girgiza kai nayi na raka shi har wajen sannan ya shiga mota ta bar gidan nima na dawo parlourn, tunda na dawo na shiga aikina, karfe uku saura na wuce lokacin na kusan gama hada sobo, da yake yace zai zo da baki tuwan shinkafa miyar Egusi nayi, ina ta aiki na ji an buga gidan na zata shi ne ina zuwa na bude Matar Uncle Auta da Ubaid sai wasu mata biyu da yan mata uku.

Murmushi nayi na ce musu.." Barkanku da zuwa ku shigo!" Na wuce kitchen na kawo musu ruwa.

Na juya zan tafi na ji daya tana fa
in.
Chapter 28 · 0% Book details