← Book details Al'farma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 44

Sashe 38

Al'farma Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read

""""""""""Washegari bayan nayi salla nakuma komawa nakwanta,karfe 9 Mommy tatadani ta umurceni danaje nakuma gasa jikina kodanaje bathroom din bayan nagasa jikina sainazarce dayin wanka kafin nafito" zuwa yanzukam sosai nadaina jin zafin harnakan mance dawani abu yafaru,simple makeup nayi harnadau kayana danazodashi jiya ajikina zankuma maidashi sai Mommy tace ay ga kayan dazakisanan abayanki,nawaigo danganin kayanda take nunamin din,watah garnanniyar atamface dinkin riga da sket kallo daya zakayiwa atamfar kasan bakarama bace,nadauka nasaka sanna naje gaban mirro nafesa turaren Mommy nadaura dankwali saina koma nazauna.jim kadan Mommy tashigo daukeda kayan breakfast tadireshi saman table,tace gyara maza kici yanzu nace toh saitafita.nagyara zamata nafaracin lafiyayyiyar break dinda Mommy tashirya da hannunta,dasallamarsa yaturo kopa,na amsa sallamar batareda nadagoba kamshinsa yaharwaye dakin asannu nalumshe idanuna tareda shakar daddadan kamshinsa,bansan isowarsaba sai jin sa nayi yazauna dafdani asannu nabude idanuna cikin kasa da murya nace inakwana,yasakala hannunsa tabayana yadada masodani jikinsa sosai,An'tashi lfy?yakwanan kadaici da sanyi?shiru nayi bance dashi komaiba,yasunkuyo da fuskarsa yaleko fuskata saiyadan shafi gefen fuskata da alama kinsha sanyi yau dakinbi mijinki jiya dayabaki dumi maigamsarwa,naturo baki gaba araina nace saikace kullum dashi mukekwana indai wanna duminne banaso.saiyagyara zamansa yasanya hannu mukacigaba dayin break din tare,koda muka gama saina kwashi kayakin nakaisu kitchen kodana dawo dakin saina taddashi tsaye rikeda mayafina ahannu yanaganina saiyayi saurin masowa inda nake yasanyamin gyalen akaina saiyariko hannuna yanafadin taho mutafi lokaci zaikuri"binsa dakallon tanbaya nayi kannace wani abu Mommy dayanzu shigowarta tarigani fadin ina kuma zaka kaita bayan kasan balafiya garetaba,yace Mommy wani rashin lfy kuma kokinmance 11:30pm zamubar kasan,kiduba kiga yanzu 11:19pm,zatakuma magana saiyayi saurin sakin hannuna yakariko na nata yace Mommy da itazamutafi dole saboda wanna time din bazan samu damar kuma zuwa Nigeria dawuriba Mommy to taya zanyi natafi nabarta,dan ALLAH Mommy kada kihana intafi da ita pls,bakaramin dadi Mommy tajiba aranta dankuwa tasan RUMAINA tasamu babban muhalli acikin zuciyar dan nata bazatamance lokacinda Nazeerat take kuka akan zatabishi shikuma yaki harsaida itada kanta tatirsasashi kafin yatafi da ita saigashi yau shiyakeson tafiya da RUMAINA har yana magiya,saitayi hamdala ga Ubangiji daganin dannata yasami farinciki ga matar nasa,saitadan batarai sanna tace,kada katafimin da diyata kaje karika wahalarmin da ita kokuma karikayimata mugunta har idan nasami labari tofa dakaina zanji nadauki yata,dasauri yace ALLAH Mommy nayarda saiya sanya hannunsa a aljuhu yazaro waya ,yace wanna wayar natane dazunna nasaimata shi kinga tawanna hanyar zaki rikajin komai daga gareta,cikin jin dadin kalamansa saita jawo ni tahadamu gabadaya tarungume tanafadin ALLAH yayimuku albarka yadauwamar da farinciki arayuwarku, ameen muka amsa dashi,nan tariko hannumu mukafito waje har parking lot takaimu ,kaman anyi usur wa yangidan sukarika fitowa sunaimana fatan alkhairi nida Ummee da Basma rungume junarmu mukayi saikuma mukafashe dakuka dakyar Mommy tajanyeni tashigardani cikin motar sanna ta umurci driver yaja mutafi"nan motocin sojoji sukarufamana baya da jiniyarsu,muna fita daga gidan saiyajanyoni jikinsa yarungume yana bubbuga bayana,lamo nayi ajikinsa sai sauke ajiyar zuciya nake,batareda bata lokaciba muka isa airport munasauka anakiran sunanmu,driver yadau akwatinmu ya isaga ma ay katan jirgin,jama'a saitururruwar zuwa suke sunata gaisuwar da kirarin bangirma,sunafadin ALLAH yakare NAKOWA yatsaremaka hanyarka,shiko sai daga musu hannu yake yanabinsu da murmushi,yana rikeda hannuna muka haura matattakalar jirgin.saiware ido nake waiyau nice acikin jirgi mamakina bai karuba harsaida mukashiga cikin jirgin,nan nashigayiwa Ubangijin hatittu tasbihi lallai ALLAH maigirmane kuma mai daukaka maiyin abundayaso gabawansa,lallai wanna rahamar daga ubangijinane,sit dindayake tacan baya mukazauna ni inata gefen window shikuma yanagefena, koda ma ay'katan suka fara sanarwa akan adaura belt's jirgi zaitashi nidai ido nakurawa sarautar ALLAH dan bansan ta inada zanfaraba,saibin mutanecikim jirgin nakeda ido ganin kowa natakorin daura belt's insa araina nace yau akeyinta,ban inda tunaniba sainaji hannuna ajikina yana sakalamin belt' in,nasauke numfashi ahankali,yana gama dauramin shima yadaura nashi,batareda batalokaciba jirginmu yadaga.......
4:00pm na Nigeria wanda yayi daidai da 2:00pm abirnin Switzerland ,jirgin yasauka ababban filin saukar jirgi dakecikin birnin Switzerland.
Bayan minti 15 dasaukar jirgin asannu jama'arciki sukafara sauka,muma mukarufamusu baya"ya'ilahi yalillahi fatubarakallah masha ALLAH"abunda nafurta kenan lokacinda nasinci kaina acikin birnin Switzerland, fadar tsaruwansama batalokacine, dagacan wasu mutane masu sanye dakakin sojoji nakasar Nigeria dakuma na nan kasar Switzerland din sukafito daga cikin wasu motoci wanda akalla yawan mutanen sunkai 30 cikin sauri sauri gudu gudu sukanufomu gamanyan bindigogi ahannunsu sunkuma daddaga bakin bindigar kamar masushiga filin daga.cikin firgici da kidima narike hannunsa da karfi jikina narawa nakifa fuskata jikin damtsen hannunsa,cikin hanzari yadagoni tareda juyodani gabansa yace menene meyasameki??zillewa nayi nashige cikin kirjinsa sainasaki kuka cikin muryar kuka nace banason ganinsu tsoro sukebani,dada rungumeni yy yanafadin sojan susuke baki tsoro?" cikin sauri narika nagyada masa kai"murmushi yy maisauti saiyace kedayau zakisa kayan soja kokinmance kematar soja ce to amma kike tsoron soja,saiyashiga bubbuga bayana alamun lallashi,nidai dada cusa fuskata nayi cikin kirjinsa...
Suna isa dafdamu sukatsaramasa tareda kamewa guri guda,wani dagajikin sojan narikedawata riga Wanda tun durowarsu daga saman motocin rigar dakuma hula rigar irin nasune,cikin girmamawa irin nasoja yakima tsaramasa sanna yamikamasa rigar"shikuma yamika hannu yakarba nan sojan yakuma kamewa,asannu yacironi daga cikin kirjinsa yanayimin magana cikin kasa damuya yace idan kikabari sukagane tsoronsu kikeji tofa harbeki zasuyi dan haka yanzu kiboye tsoron nasu kinuna kamar bakijin tsoronsu zakiga su yanzu sundawa jin tsoronki kinji?cikin dardar nagyada masakai yace good girl, rigarda kerike ahannusa yasanyamin gabanrigar abudeyake ana iya hango kayana wanda dama yake jikina sanna yakuma daura hular akaina saman gyalena" saiya juyar dani kamar yanda yake tsaye muna fuskantarsu,jinayi kamar nakwalla ihu dana kalli jikina nakuma kalli gungun sojojin dasuke tsaye agabana,danatuna cewa idanfa naji tsoronsu tofa harbeni zasuyi saina tattaro duk wata jarumtata nahadeta guri guda nakankame hannunsa dakecikin hannuna,yana juyo dani gabadayansu suka kuma tsarawa hadeda kamewa"hannusa yasaka daidai saitin kunnensa alamun tsarawa saiyacemin kema kiyi yanda nayi dakyar na iya daga hannuna nayi kamar yanda naga yayin"saisuka daga bakin bindigoginsu sama suka saki harbi tas..tas.."cikin rudu da dimaucewa nacakumeshi tareda kwalla kara,dasauri yarirrikeni taredayima sojojin nuni dahanu sutafi,nanma saida sukadada tsaramasa kafin sukajuya sukaje jikin motocinsu,
Mannani yadadayi akirjinsa nace wayyo ALLAH zasu harbeni nidai kamaidani gida bazan zauna ananba,yarankwafo dakansa yakawo bakinsa saitin kunnena yace gaisuwafa sukeyimiki ba harbinki zasuyiba,nidai kin sauraransa nayi Dan gabadaya nagama firgicewa, saiyajanyo hannuna muka isa jikin wata mota kan mukaraso aka bude marfin kulle idanuna nayi harmukashiga motar wani soja dakecikin motar yaja muka haura titi...........

Comments and Share

MOMMYN TWINS CE

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

ALFARMA

🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼🌼

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*____________________________________*

🅿89👉🏻90
Chapter 38 · 0% Book details