← Book details Al'farma Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 44

Sashe 23

Al'farma Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Malam Muhammad "da malam abdullahi" asalinsu yan garin bokos ne dake jahar plateau "tunsuna kanana sukatashi cikin sodakaunar juna,idan kagansu zakayi zaton ciki daya sukafita,alhalinkuwa zallar abokantakace hadeda aminantaka,harsukazamo kamar ciki daya sukafita"haryakaiga daya yana zuwa gidan daya yakwana "batareda wata damuwaba dankuwa tasanadiyyarsu iyayensu suma suka kulla zumunci"ahaka rayuwa tacigaba da gudana har izuwa samartakansu" watara, watarana suna zaune sunahira kamar yadda sukasaba,malam abdullahi yadubi aminin sa wato malam Muhammad,yace idan Allah yakaimu mukayi aure ya azirtamu da haihuwa ,muhada yayanmu aure dansu surike zumuncinmu dakyau kada suyi wasa,cikin fara a malam Muhammad yace kamar kasan abinda kecikin zuciyata"shikenan kaga hatta jikokinmu zasu tashi kamar yadda mukedinna,insha Allah zamu kulla wanna alakar kuma alkawari,suka rike hannun junansu kamar haka馃馃徎 sukakuma hadabaki wajencewa mundau alkawarin hada yayanmu aure dan daurewar zumuncinmu nahar Abadan....... hatta mahaifansu sunsan dawannan zancen.....
Haka rayuwa tacigaba datafiya..bayan wasu yan shekaru cikin yardan ubangiji Allah "saikuwa dukansu sukayi auren....watanni kadan matan sukasami ciki,murna wajensu ba a magana,bayan wata tara kowannensu tahaihu.koda akasanrmusu damurna kowannensu ya isa gida,nan akeshaida musu duka matan maza suka haifa "saisuka danji badadi dan sunsha alwashin yayansu nafari sukeson hadasu auren,daga karshedai sukayiwa sarkin halittu godiya.ranar suna,Dan malam Muhammad yacisuna adam,Dan malam abdullahi kuma' bashir"tundaga kansu ubangiji baisake basu haihuwaba.......rayuwa yaja shekaru sunshude..Bashir da Adam sunginrma" iyayen nasu sunsanyasu makarantar islamiyya dana boko dukdakuwa alokacin sai wane da wane sukezuwa makarantar boko.... Malam Muhammad da malam abdullahi"zaunesuke agindin bishiya gurinda sukasaba zama kodayaushe"Malam Muhammad yy gyaran murya yace aminina kuma dan uwana"munso hada zumunci maidaurewa amma hakan batasamuba"kumani har ayanzu ina kanbakana,inasha Allah wanna zumuncin bazata taba sayuwa iyakanmu kadaiba,hatta jikoki da tattaba kunne saiya yalwata sakaninsu"wayanna yaya maza da Allah yabamu Allah yasanyamusu albarka"malam abdullahi yace ameen"yacigaba.idan Allah ubangiji yarayasu yakumaja kwananmu.sukayi aure sukahaihu"in Allah yayarda alkawarinda mukadauka akansu zaidawo kan yayansu wato jikokinmu kenan"malam abdullahi yace alhmdllh Allah abingodiya"insha Allahu kuwa hakan za ayi.....batareda bata lokaciba sukatara yayansu wato bashir da Adam" sukasanarmusu da wanna babban alkawari wacce sukaso cikasa akansu,sai ubangiji yy ikonsa akahaifesu dukansu maza....Adam da bashir sunyi farinciki dajin hakan dankuwa suma sunshaku sosai. sunkuma dau alkawarin cikawa mahaifan nasu burinsu....... watarana lokacin suna aji 5 wata kungiya dakecikin birnin BAUCHIN yakubu.sukaziyarci makarantarsu,kungiyar yawosuke,garigari dan diban dalibai, wadanda sukafarayin karatun boko Dan cigaban karatunsu. saisu kawosu cikin birnin BAUCHI ,sudauki nauyin karatunsu harsu kammala,koda kungiyar ta iso makarantarsu" sukayizama da malaman makarantar sanna sukabukaci dalibai guda 10"dakuma ganawa da iyayensu ,cikin dalebanda aka diba kuwa harda bashir aciki"abokinsa Adam" yy kuka rabuwa da amininsa wanda amintakarsu tasamo asali tundaga iyayensu"bayan ganawar kungiyar da mahaifan daliban "akwashesu , akatafi dasu....Adam saidayayi zazzabi narashin abokinnasa.daga kan aji 6 karatun Adam tasaya...shiko bashir yanacan yanatakan cigaba dakaratunsa,dukkuma sanda sukasami Hutu yanazuwa gidane yysa....bayan shekara 20____________rayuwa tajuya iyajuyi,bashir zuwa wanna lokacin yasami cigaba.cikikuwa harda kammala karatunsa dasamun aiki maisoka"banankadai yasayaba harda harkan kasuwanci daban daban,Allah kuma yadafa masa,kankace me yazamo hamshakin maikudi" yakumayi aure acandin,da matarsa maisuna aminatu...harkokinsa kuwa ba iya Nigeria kadai yasaba hatta kasashe da dama yana zuwa dangudanar da kasuwancinsa....
Adam ma yy aure ammashi Allah bainufesa da arzikiba"kuma abotansu tundaga kan yarinta tasaya" yanzu bashir yakandau lokaci mosawo kafin yazo garin"saidai kodayaushe yakan aiko da alkhairai masuyawa. wa mahaifinsa da aminin mahaifin nasa harda abokinsa nayarinta wato Adam, bayan wani lokaci aka aikadacewa aminatu matar Alhaji bashir tahaihu da namiji"zokaga murna wajen malam Muhammad da malam abdullahi, dansuna saran kamsu komaga mahaliccinsu burinsu zaicika"ranar suna yaro yacisuna Ibrahim"har alokacin kuwa matar Adam batasami cikiba,bayan shekara biyar ,nanma matar Alhaji bashir takuma haihuwa diya mace,akasanyamata suna Khadija..
Zuwa lokacin Adam yafara cirerai gasamun haihuwa.sukansu iyayen nasu harsunfa kariya da lamarin ...nanan shekaru sunataja,kwasam Allah yabaiwa matar Adam ciki,sunyi muna dafarinciki sosai,bayan wata tara tahaifi diyarta mace"kyakyawar gaske kamar diyar larabawa,akasanyamata suna" UMMU RUMAINA, wacce tacisunan kakanta wato mahaifiyar Adam" bayan lokacin badawani jimawa sosai ba matar Alhaji bashir tasake haifar yarta na uku maisuna Basma.. Duksawon wanna lokacin kuma Adam baitaba sa iyalen Alhaji bashir a idonsa ba "hasalima labari sukasamu yamabar kasar gaba daya.yarinya UMMU RUMAINA nata kara wayo" lokacinda UMMU RUMAINA tacika shekara 8,lokacin cutar ajali yakama kakanta malam abdullahi,yanacikin zafin ciwo yarike hannun amininsa malam Muhammad "yatunasar masada da alkawarinsu,yakuma daura dafadin koda bayan ransa yatabbata yacikamusu alkawarinsu" nan Allah yakarbi kayansa,sunyi kuka sosai narashin dattijo nagari,bayan kaisa makwancinsa"anadawowa gida,Malam Muhammad, yatara jama a yasaya goro,atake agun akadaura auren IBRAHIM da UMMU RUMAINA.................

Comments and Share

MAMYN TWINS CE
12/30/19, 14:53 - 拼ar Gatan 茦ainuwa: 馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲

*ALFARMA*

馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲

*By*鉁嶐煆�

*Rasheeda S' Director*

*亘爻賲 丕賱賱賴 丕賱乇丨賲賳 丕賱乇丨賷賲*
___________________________________

*馃寛KAINUWA WRITERS鉁嶐煆� ASSOCIATION*馃馃徎
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________

馃吙57馃憠馃徎58

""""""""Adam yaji dadi sosai da malam Muhammad yacikawa mahaifinsa burinsu" malam Muhammad yakiyarawo dansa,Alhaji bashir,yasanarmasa,dayau alkawari yacika"dakuma rasuwan amininsa"Alhaji bashir saida yadiga hawaye danjin rasuwar aminin mahaifinsa,yakumayi farinciki dayau mahaifansu suncika burunsu na shekara da shekaru"baiyi kasa agoiwaba,yakirawo dansa IBRAHIM"wanda yanzun yazamo general na soja"yanakuma zama a kasar Switzerland, yanzu,saidai yakanzo Nigeria duksanda bukatar hakan tataso,kasancewarsa babban sojar kasar,Alhaji bashir yashaidawa dannasa yananimansa cikin gaggawa,batareda batalokaci ba,IBRAHIM"yahayo jirgi yazo kasarda mahaifinsa kedazama,wato America,dankiran mahaifin nasa,bayan isarsa America,sukasami ganawa da mahaifinsa"nan yakeshaida masa duk abinda yafaru,dukdadai dama tuncan yasan alkawarinda kesakanin kakansa da amininsa"batareda nunawata damuwaba yace to babu komai,yayiwa daddy insa ta aziyar mutuwar aminin babansa,sanna yadaura dafadin, nakuma taya tsoho murnar cika alkawarinda ya kakabawa kansa,,to idanda bananan watakila saidai shi ya auri yarinyar" inbanda wani iyayensa anfadamasa zamaninmu irin nasune"Alhaji bashir yy masa dakuwa ,yace kaci gidanku baban nawa kakewa shedananci"ai zamanin nasu sunsan mahimmancin alkawari"amma kuzamanin naku ina alkawarin take"saiwane dawane ne kadai ke Iya cikashi"shidai kafada yadaga alamun ko ajikinsa" danshi alokacin aikinsa kadai yasa agabansa"aranar yy sallama da daddy insa yakoma Switzerland.....
Haka rayuwa tacigaba da tafiya,UMMU RUMAINA natagirma,lokacinda tacika shekara sha uku.tun alokacin samaruka suka farayin layi akofar gidansu,tunsawon wanna lokacin kuma IBRAHIM baitaba tako kafansa yazo dan duba matarda aka aura masaba"hakama iyayensa, iyayen UMMU RUMAINA "sunsami labarin dowowar iyalen Alhaji bashir Nigeria" sunkuma taxuba ido kozasuzo amma shiru"malam Muhammad, kullum amaibaiwa"adamu hakuri akan rashin kyautawar dannasa da jikarsa yake"watarana malam Muhammad "yasa akakirawo masa adamu,koda adamu yaje kiran.bayan sungaisa,malam Muhammad yace,nakirawo kane domin nadada baka hakuri akan rashin kyautawar da bashir da dansa IBARAHIM sukayi,kadada hakuri,jiya shi IBRAHIM din yakirawo waya,dangidan tanimu yakawomin" munyi magana dashi,yacemin ayi hakuri zaizo karshen satinna"yanzu abinda nakeso dakai shine,kaje kasa wanna.yarinya UMMU RUMAINA tayi kwalliya taje gun idi mai photo yymata photo, sai akawomin"idan dai yazo xanbasa dan yafara ganinta kafin yaje can gidan naku"adamu yace to babu damuwa,barinaje ,,hakakuwa akayi bayan komawarsa gida yasa UMMU RUMAINA tayi wanka tayi kwalliya tajegun idi mai photo yymata photo guda hudu"tadawo gida"saita cire gudabiyu daga cikin photo ta aje,sanna tabaiwa baban nata guda biyu"adamu yakaiwa malam Muhammad photo....lokacinda karshen satin yacika sai samun labarin zuwan IBRAHIM sukayi,malam Muhammad yakada yarawa akan yaje yaduba matarsa"tunda dai dama bayanzu za abasa itaba saitadada girma"ammadai yaje yadubata yakuma gaida iyayenta,amma firyaki"sai cewa yy waisauri yake idan yakuma zuwa zaijeshi gidan,labarin zuwansa kadai iyayen UMMU RUMAINA sukasamu.saida sukadanji badadi......,hakasukacigaba dakula datarbiyyar yarsu"duk saurayinda yazo gurinta,saidai sucemasa haryanzu ba'abata damar sayuwa da saurayiba" bayan wani lokaci....kwasam watarana mummunar labarin yariski dangi da yangari cewa "Alhaji bashir yarasu tasanadiyar hadarin mota". anyi kuka sosai,narashinsa" dankuwa dukda bayazuwa garin sosai ,amma alkhairinsa na isowa garin"......yau kimanin shakara 8 kenan da auren UMMU RUMAINA da IBRAHIM,tuntsawon wanna lokacin bawanda yatabazuwa adangin IBRAHIM akan maganar auren su bayan malam Muhammad........
Baba yasauke numfashi yakalli gefen danake"alokacin kukana yatsanan.tashin hankalin danakeciki yaninku"saijuya kaina nake INA tunanin anya bamafarki nakeba kuwa"baba yadaura dafadin mamana yazama dale musanarmiki da wanna rubutaccen'al'amarin.kobayauba,bareyau dabukatar hakan tataso"yakalli mama yace da ita.waneni wanna IBRAHIM din maidanganta kansa da yarmu "haryanafadin shi mijintane" mama tasauke numfashi sanna tace bawani IBRAHIM din bane nadaban ayanzu nafi zargin shidindai shine IBRAHIM mijintan kamar yadda yafada to amma aina yasanta?shiru baba yy nadanwani lokaci,sanna dagabisani yace to lallai idan hakankuwa yakasance to lallai yacika mara adalci" dukdakuwa abinda ya aikata ba haramun bace amma baiyiwa yarinya da mukanmu iyayenta adalciba...zamu Iya kiran abinda ya aikata darashin adalci kodakuwa tanamasayin matar tashi"maganar baba nayanzu yadada firgitani, matarshi namaimaita afili"namike tsaye kamar maitashin aljanu "dasauri mama tarikoni, tamaidani nazauna.baba baikuma cewa komaiba yamike yafita...

BAUCHI
tunbayan fitar ***I'B baikuma lekowa gidaba,sojojin gidan kuwa gabadaya sukabazama niman RUMAINA" zaune mommy take abakin gado tarafka uban tagumi"tarasa ta inazatafara"afili tace"lallai natafka babban kuskure.nantake hawaye yafara gangarowa afuskarta,tanafadin Alhaji kayafemin"wlhy kaima kasan bahalina bane,natabbata wanna sharrin shaidanne yamantardani alkawari mafi girma a rayuwa"takifa kanta saman pillow,saiga mommy nakuka kamar karamar yarinya...Basma dayanzu shigowarta tariske mommy cikin wani hali dasauri tahaye saman gadon,tarungume mommy itama tafashe dakuka cikin kukan takefadin "mommy menene?meyasameki?mommy kifadamin"mommy tashare hawayenta tamike zaune ganin yartata nason shiga wani hali,tadubi Basma tace" hakika natafka babban kuskure arayuwa"Basma nagaza cikawa mahaifinku alkawari,cikin kuka Basma tace mommy kidaina fadan haka.mommy menene bakiyiba akan duk wani abinda daddy yadaura miki nauyin akanki"mommy tayi murmushi takaici tace "akwai Basma akwai babban abunda nakasa cikashi,lokacinda ran Alhaji yakedaf dabarin jikinsa yabarmin yabarmin watsiyya mafigirma wadda yajima yana nanatamin ita kafin ubangiji yy ikonsa.................

馃槣馃弮鈥嶁檧馃弮鈥嶁檧馃弮鈥嶁檧馃弮鈥嶁檧

Comments and share

MOMMYN TWINS CE
12/30/19, 14:53 - 拼ar Gatan 茦ainuwa: 馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲

*ALFARMA*

馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲馃尲

*By*鉁嶐煆�

*Rasheeda S' Director*

*亘爻賲 丕賱賱賴 丕賱乇丨賲賳 丕賱乇丨賷賲*
___________________________________

*馃寛KAINUWA WRITERS鉁嶐煆� ASSOCIATION*馃馃徎
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
___________________________________

馃吙59馃憠馃徎60
Chapter 23 · 0% Book details