← Book details A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 89 OF 111

Sashe 89

A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bai musa mata ba,don a yadda takeyin din yasan zancan gizo baya wuce na qoqi,bataso ya shiga yaga ba dai dai ba ya gyara mata ko yayi mata fada,ko shi din yasan idan ya shiga babu lallai ya samu sashen a yanayin da zai iya zama,so no need ya matsa sai ya shiga din,don haka ya juya da yaran suka wuce sashen nasa.

Tun daga qofa yaga abinda aka saba,a yau dinma sashen nasa babu gyara,yadda ya barshi kusan wata guda haka yake a yanzun,sai ya basar,ya ajjiye yaran ya zauna shima saman kujerun falon,ta yiwa jakarsa mazauni sannan ta juya tana kallonsa

"Bari na fara dora maka wani abun sai nazo na gyara nan din" manyan fararen idanunsa ya daga ya kalleta

"No,a bani abinda kuka dafa kawai da rana".

Da sauri tadan kalleshi,sannan cikin yanayi na rashin gaskiya tace

"Ba zaka iya ci ba,infact ma inajin sun cinye....."

"Eh daddy,indomie ce mommy ta dafa mana,kuma saida nawwara ma tace tana jin yunwa s......" Yarinyar bata qarasa ba saiji kake fafff ta doke mata baki,take kuwa bakinta ya fashe

"Shegiyar maganar tsiya,muna magana uban waye ya sako bakinki a ciki?" cikin bacin rai abbas ya kama leban yarinyar yana dubawa,sai da ya gama ganin iya wajen da ya fashe din,ya goge mata wajen ya dorata kan cinyarsa yana lallashi sannan ya dubeta cikin bacin rai

"A gabana zaki fasawa yarinyata baki?,kece me abun duka ba ita ba,amma waye ga dakeki?,na rantse da Allah kinyi na farko kinyi na qarshe,bance kada ki hukuntasu ba,amma ba ta irin wannan hanyar ba".

Ranta ya baci sosai,ta dinga jefawa yarinyar harara,tanason bata mata budget gaba daya,amma tasan maganinsu,tattarasu zatayi kaf kwanakin wajen widad.

Saboda tana da plan sai bata tanka masa ba,illa bata fuska sosai data yi,ta juya tana ficewa daga sassan ranta a bace.

Kai tsaye ta nufi sassan widad,gwara ta fito da ita tun yanzun ta kama mata ayyukan,saboda yau aikin nata suna da yawa,ko gyaran sassansa zuwa abuncinsa aiki ne babba a wajenta,ga nata sashen da tasan zaici tsintsiya ruwa da klien,saidai tun kafin ta qarasa taga kaman babu mutum a sassan,kasa gasgata idanunta tayi,ta dinga ganin kamar gizo,har dai data taba qofar,takuma yi knocking taji shuru.

Sak tayi,ta tsaya yana jinjina kanta,baizo da ita bane?,ko kuma ta wuce gidan hajiyarsa yadda ta tsiri wannan iskancin wani lokacin?,bata da amsa,don haka sai ta wuce sassanta,ta dauki wayarta ta kira muneera.

Tambayar farko tace mata gatacan ita da hajiya a falo suna hira,ta zuqi iska ta fesar,lallai kan yarinyar ya fara wayewa,ita za'a mayar 'yar iska?,aqalla wata guda da wani abu kenan bata saka yarinyar a idonta ba,ko zuwanta na qarshe kwana guda kwata kwata tayi a gidan suka koma.

Sake fitar da iska me zafi tayi daga bakinta,maganganun anty ummee suka dawo mata,ai kuwa ba zata bari hakan ta faru ba,tare ta karantawa yarinyar karatun manya,dole tabi da ita,dole tabi hanyarta,dole ne kuma ta fara gane banbancinta da ita,sai ta fara dora abinci sannan ta kwashi kayan shara ta wuce sashen nasa tana sake saqa abubuwa da yawa da take da shirin aiwatarwa.

*_W A S H E G A R I_*

Karfe goma na safiya ya fito tsaf dashi,cikin lallausan yadin filtex na maza mai asalin kyau da tsada,komai yana yinsa ne a wani kasalance da rashin kuzari,duk kuwa da cewa a jiyan ya samu yadda yakeso daga hafsat din,to amma sai yakejin wani irin mugun banbanci mai tazarar yawa,banbancin da zai iya kiransa kwatankwacin nisan dake tsakanin sama da qasa,gaba daya ma zai iya cewa wani irin bacci yayi mara dadi cije da kewar widad din,duk juyin da zaiyi sai ya dinga ganin kamar itace a gefansa,amma dole ya tattara dukka wadan nan ya danne can qasan zuciyarsa da qarfin gaske gudun shiga hakkin me hakki.

Yana daura links a hannunsa tayi sallama ta shigo dakin,hannunta dauke da plate din data soya plantain wadda ta qone tayi baqi abinta,yadan bita da kallo kadan,tana nan gayanta,bayan wankan ibada da tayi kafin sallar asuba babu wani abu data qara,koda da turare kuwa,wanda zuwa yanzu zamansa da widad hancinsa ya saba da shaqarsa.

Yana yiwa turare wani mugu mugun so,amma ita nata ra'ayin sunyi hannun riga da ta'ammali dashi,sai randa ranta yaso,ko kuma aka taki sa'a ranar tana da ra'ayinsa.

"Fita zakayi kenan" ta fada tana zama gefan gadon da har yanzu ta kasa gyarashi,don tuni dama yayi sallama da kwana a sashenta

"Eh,akwai wani abu?" Ya fada yana takawa gaban mudubi,ya dauki cup din coffe din da yace ta hado masa dashi yakai bakinsa.

"Aah,inason zuwa gidan hajiya ne" dire mug din coffe din yayi saman madubin bayan daci ya ziyarci bakinsa,sannan ya zarce da dubanta yana nazarinta.

A ka'idarta zaiyi wahala taje gidan hajiyan haka siddan,shi yasa maganar ta bashi mamaki ko a yanzun ma,amma taqi yarda ta kalleshi bare ya karanto gaskiyar abinda ke cikin zuciyarta,har ya gama kallonta,ya jawo qonanniyar plaitain din ya fara kokawa da ita

"Saikin dawo" ya amsa mata daga baya,yana tsame hannnunsa daga plate din,yaja tissue yana goge maiqon daya bata masa hannu.

Sarai taga yadda ya cakali abincin,abu na farko da ya kamata tayi taji dalilin da yasa bai maida kai yaci ba,tunda fita zaiyi,amma inaaaa,ba wannan bane a gabanta,sai kawai ta kwashe kwanukan bayan fitarsa,ta hada da kudin cefanen daya ajiye mata,duk da babu abinda zasu siya,ta soke a lalitarta,sannan ta shiga bandaki tahau shiryawa a gurguje,don tana da tabbacin zaiyi wuya idan ba gidan hajiyan ya nufa ba,tanason kuma ta cimmasa a can ayita ta qare.

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Page 82

Qwafa taja sanda ta gama parking motarta kusa da tashi,ranta ya quntata sosai,duk sauri da taga yana yi dama nan ya nufa,tafison hakan dama,gwara ayi komai a gabansa,ta kashe motar, saidai kafin ma ta zare key din daga jiki tuni mimi ta bude murfin motar ta fice abunta.

Da harara tabi bayan yarinyar,ta tsani yadda take rawar qafa akan wannan tsohuwar,amma tana qara wayo zataci ubanta ne,ba zata dauka wannan ba.

Da gudunta yarinyar ta fada falon tana kiran sunan anty widad da hajiya,abbas ya bita da kallo yana hade ransa

"Koma kiyi sallama" da sauri ta koma tayo sallamar ta sake shigowa,saidai hakan bai rage mata karsashinta ba,tana shigowar ta fada saman cinyar hajiyan,kafin su sake cewa komai hafsat tayi sallama ta shigo

"Ikon Allah,ashe tare kuke" hajiya ta fada tana ma hafsat din sannu da zuwa.

Idanunta akan kwanukan daya gama cin abinci, qamshin abincin yana nan daram a falon,kana shigowa kuma zai buwayi hancinka,haushi da kishi suka cikata,abind aya sassauta ma abinda takeji a ranta rashin ganin gilmawar widad din kwata kwata.

Saman kujerar dake daura da hajiyan ta zauna,a maimakon zama a qasa kamar yadda ta samu abbas din

"Hajiya ina kwana?" Ta gaidata tana sake qarewa falon da kwanukan abincin kallo,a mutunce ta amsa mata cikin nuna kulawa gami da tambayarta yara da kuma gida,duka ta amsa mata da lafiya lau,sai kuma shuru ya biyo baya,dai dai lokacin da baba usaina tayi sallama ta sako kai

"A'ah yau kece a gidan?" Baba usaina ta fada tana zama itama,fuska hafsat din tadan saki,saboda saboda alaqar dake tsakaninsu ta amsa mata tana gaidata,suna tsaka da gaisawan mimi ta dami hajiya da batun anty widad

"Tana daki,leqa kice idan ta gama tazo su gaisa da umminki,a kwashe kayana abincin nan ma a wajen" ta kuwa falla da gudu tayi dakin,abbas yabi yarinyar da kallo,yana jin shima kamar yabi bayanta.

Sauke idanunsa yayi yana miqewa tsaye hadi da daukar wayarsa dake aje gefe

"Kada ka fita fa,inason zamuyi magana ne ai" aninda ya dauke wutar magana cak a falon,kowa yayi shuru sai sautinta daya fita dake yawo,da mamaki ya kalleta,wacce magana ce da basuyita ba kafin ya fito sai a nan?

"Hajiya wajenki nazo akan abbansu mimi"

"Tooo.... ikon Allah,koma to ka zauna" hannuwansa ya sauke,ya koma hannun kujerar daya tashi a kai ya zauna,can qasan zuciyarsa nason darsuwa da bacin rai amma yana kaudarwa,tunda har yanzu baisan dalilin zuwan nata ba,saidai kwanyarsa nata son hakaito masa abinda ya faru da zai sanya tayi tattaki qafa da qafa har gaban mahaifiyarsa ta kawo qararsa,duk da bawai yau aka fara ba.

Kafin takai ga cewa komai widad ta fito,riqe da hannun mimi sunata dariya abinsu,cikin wani lace sky blue da ratsin farin zare da aka yiwa dinkin tea bubu,bata daura dankwali ba sai siririn mayafi data dora a kanta mara nauyi kalar sky blue din.

Idonsa ya lumshe ya kuma budesu yana sake zubesu a kanta,yaji wata nutsuwa na maye gurbin abinda keson motsawa daga zuciyarsa.

Tare da qamshin nan nata ta iso,ya buwayi falon kuwa gaba daya,cikin ransa yake raya tabbas itama da qaunar turare cikin jininta,ta duqa cikin girmamawa ta gaida baba hassana.

Kadaram kadaham ta amsa mata,tana qare mata kallo a fakaice

"Tirqashi" ta fada qasan ranta ganin yadda yarinyar take sake juyewa,kyakkyawar siffarta da kuma kamanninta suna sake ninkuwa da bayyana kansu,idan akace za'a hadata da hafsat ko a yanzun ratar me yawa ce,balle kuma ace nan gaba?,ai sai abinda idanu suka gani,ita kuwa lami(mahaifiyar hafsa) tana aikin me?.

Sanda widad din take gaida hafsan sai data tattaro dukkan qarfin halinta sannan ta iya amsa mata,gaba daya yarinyar tayi mata ba zata,tsahon wata dayan da bata ganta ba sai taga ta cika sosai,ta kuma fara zama cikakkiyar mace,gabanta yayi.mugun bugawa sanda zuciyarta ta laqana mata tambayar shin me zai kawo wannan sauyin?,ita kadai ta girgiza kai,bata yarda komai zai faru ba,a yadda abbas din yazo mata a zafafe jiyan ta tabbatar bai samu komai daga gareta ba,inda ya samu din ta tabbatar bazai zo mata a birkice haka ba,bataga wani sauyi daga wajensa ba duk sanda yayi mata zuwa irin wannan,saima qaruwa da abun yayi,duk da cewa taga wasu qananun sauye sauye,kamar mitar rashin shaving da turare a jikinta,saidai basukai mizanin da zata dorasu a komai ba,tunda batasan da zuwansa ba ai,ganinsa tayi katsam,bai kuma gaya mata yana da buqata ba ballantana ta shirya,kai koda ya gaya matan ma iya abinda zata iya shi tayi shi kuma zata ci gaba da yi.

Motsawa baba usaina tayi

"Bari na baku waje,naga kamar magana zakuyi"
Chapter 89 · 0% Book details