← Book details A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 111

Sashe 42

A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga bakin gadonta take zaune riqe da waya a hannunta,lokaci lokaci tana saka hannu ta share hawayen fuskarta,duk furuci daya da zatayi da anty ummee tana jin kamar zuciyarta zata tsinke saboda baqinciki bacin rai da zallar kishi kai daci

"Har kusan qonewa nayi garin saurin na hada masa tea nakai masa,amma wallahi acan na sameta,namiji dan babansa......alamun dana gani ma sunsha dambene,saboda ko dankwalin kanta gashi nan watse a qasa,don Allah anty ummee mai zaiyi da wannan mitsitsiyar yarinyar,banda tsabar cin fuska?" Tayi maganar tana jin kamar zuciyarta zata fito ta bakinta.

"Kinga ki ajjiye wannan a gefe,matuqar zakici gaba daga inda kika tsaya,zaki nuna komai ba komai bane.....hatta kusantar tata ma saikin hanashi gaba daya,meye a cikin ido ne banda ruwa?,ai nasara tana tare da jajircewa"

"Wannan nasarar anya kuwa tana tare dani?"

"Kin saare a dare daya kenan?" Anty ummeen ta tambayeta tana jinjina zallar gajen haquri irin na hafsa din

"Shin ba'a gabanki komai ya dinga gudana tsakanina da amaryar abban sayyid ba?,yanzu tana ina?"

"Banqi ta taki ba.....amma akwai nisan tazarar banbanci mai yawa tsakanin abbas dashi.....abbas anty.....yana da ra'ayin riqau kafiya da kuma magana daya,yana da wuyar sha'ani,yana da wuyar canza ra'ayi,idan yace eh.....tofa a haka zata yita tabbata"

"Uhmmm,mace fa tafi gaban tunanin dukkan wani mai tunani,saidai idan ba zaki iya ba"

"Zan iya" ta fada tana son sake bawa kanta qarfin gwiwa,ji take kamar ta rufe idanu ta kuma bude taga komai ya tarwatse,komai yazo qarshe,ta rufe idanunta kana ta budesu duk kusan lokaci daya sannan tace

"Na rasa ta yadda abbas yaga yarinyar nan anty ummee......abbas fa?,mara damuwa da abubuwa masu yawa,wanda wani abun ma sai kinta cewa kalli....ko ka gani" ta jefawa anty ummeen tambayar da taketa damunta tare da yi mata yawo a kai,har yanxu kums bata samu amsarta ba

"Namiji yafi gaban haka,kedai ki maida kai ga mission dinki....."

"Ina zuwa" ta fada da sauri tana sauke wayar daga kunnenta sanda fa jiyo alamun taku ana nufowa dakin,ta kuma san babu wanda zai shigo din sai shi.

Da hanzari ta ajiye wayar,sannan ta fada bandaki ta maida qofar,da tattausar muryarsa yayi sallama ya tura qofar ya shigo,sai ya tsaya daga bakin qofa yana qarewa hargitsatsen dakin kallo,komai baya kan tsarinsa,baisan kuma sai yaushe zata gyara ba.

Ajiyar zuciya ta sauke,ta matsa gaban babban madubin dake bandakin wanda ya cika da jirwayen ruwan wankan da ba'a wankewa,ta debi ruwa ta wanke fuskarta,saboda batason ya gane ruwan hawaye ya fita a idanunta,taja zaninta da tayi daurin qirji dashi saman t.shirt dinta ta gyara daurin,sannan ta goge fuskarta da towel ta fito.

Suna hada idanu ta cika fuskarta da fara'a,sai ya dan lumshe idanunsa ya kuma budesu lokaci daya yana kallonta,qasan zuciyarsa kuma yana masa sanyi na yanayin da ya ganta a ciki,ba wata damuwa

"Yanzu nake shirin fita mu gaisa da baqi,gashi ka tarar dani" ta sake fada tana murmushin da ita kadai tasan ciwon da yake mata.

Agogo ya kalla kafin ya amsa mata

"Kaman yayi wuri,gwara ki kwanta ki sake hutawaYou are very tired, you need a rest maman nawwara" ya fada yana sauke mata murmushi.

Duk da cewa bata kalleshi ba amma tana jin saukar murmushin nasa har tsakiyar zuciyarta,murmushi ne da ita kadai tasan tsadarsa

"To ya za'a yi,kamawa takeyi ai,gashi na kasa hada musu breakfast" ta sakeyin maganar tana zaqulo hijabinta cikin hargitsatsun kayan wardrobe dinta wadanda yana daga tsaye yake tayata kallon yadda suke a hautsine,haka suke koda yaushe,idan kayi magana tace su nawwara ne tana bacci suka aikata,ko kuma suna neman teddy dinsu ne

"Ba matsala,kinyi qoqari sosai,zan saka a kawo musu breakfast"

"Da dai yafi,na gaji da jegon jaka" ta fada qasan ranta tana zura hijabin a jikinta,sannan ta matso tana cewa

"Bari naje mu gaisa kada suga rashin kyautawa ta,mun tashi gida daya ban leqasu ba" da kallo ya bita,duk da qoqarin sakewarta amma yana hangen wani.abu can qasan qwayar idanunta,zuciyarsa na alaqanta hakan da kishin da takeji a kansa.

Hannayensa ya bude mata,cikin taushin nan nasa

"Zaki wuce bamu gaisa ba madam" kallonsa tayi saita kauda kai tana qoqarin kawo murmushi kan fuskarta,tabbas idan tace zata shiga jikinsa a wannan yanayin kuka zata barke dashi,kukan kuma zai zame mata tonon silili ne.

"Ina kwana oga?" Ta fada tana ci gaba da tafiya,sai ya maida hannayensa yayi folding nasu a qirjinsa yana kallonta,qaramin murmushi na sauka saman labbansa,irin gaisuwar da yafi qauna daga wajenta kenan,amma dama yasan zaiyi wahala ya samu yadda yakeso din

"Alhmdlh madam,a dawo min da yarana mana?"

"Zasu dawo dole yau" ta bashi amsa ba tare data juyo ba

"Alright" ya amsa mata yana kallota ta cikin madubinta

"Bari naje na dawo" ta fada tana jan masa qofar,tana so taje ta saje tantance widad din,yadda ta ganta a jiyan haka take ko idanuwanta ne da kuma sharrin dare?.

Idanuwanta nakan dukka wani kayan qawa na falon,da qyar ta iya riqe kanta saboda yadda zuciyarta ke wani irin tsalle,ko ba'a gaya mata ba auren 'yar gata ne daga dukkan alamu,saboda yadda aka shirya gami da qawata sassan nata gaba daya,babu ce kadai babu,jere mai aji da nutsuwa.

Ta basu fuska sosai ta gaidasu inna laila dasu momma,har tadan zauna suna dan taba hira,tana ta baza ido taga ta inda widad din zata fito,saiga nujood,kamar inna laila tasan buqatar ta tace da ita

"Kira widad,kice tazo ta gaida yayarta"

"To" ta amsa tana okomawa ciki da mopper din hannunta data goge inda ruwa ya zuba.

"Yaaa latifa" widad din ta fito tana fada,hannunta riqe da dankwalin lace din nata da yaqi dauruwa,anty deena dake wanka kuma tace lallai saita daura.

Hankalin hafsa ya fara kaiwa wajen,tana tafe da dankwalin fuskarta a kwabe tamkar shagwababbun 'ya'yan fari,gashinta dake wani irin sheqi da walqiya a daure cikin ribbon jelarsa na reto a bayanta, yanayin qirar jikinta kadai abar kallo ce,sai kace wata babbar budurwa,tun a yanzun coca-cola shape dinta ya fita sosai,kallo dayan data mata ya kusa tafiya da numfashin ta,ta dinga qoqarin riqe kanta da kyau,kada ballinta ya watse a wajen.

*Arewabooks:Huguma*

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K'AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)

Page 38

"Don Allah ki dauramin,na kasa wallahi" tayi maganar tana miqawa latifa dankwalin ba tare data lura da hafsa dake zaune a gefe ba,tana jin kamar ta mutu,abbas ya gama cutarta,yaje ya auro yarinyar data kusa haifa?, sannan kumata fita komai da komai na siffa?,duk da tana qoqarin qaryata kanta da kanta,tana qoqarin gayawa kanta idonta ne yake ganin hakan

"Kawo,Allah ya gyara min ke,bansan sanda zaki koyi daura kallabi ba" dariya tadan saki

"Ni nauyi Allah,banda anty deena ta takura"

"Ga antynki nan baku gaisa ba" latifa ta fada bayan ta karba dankwalin tana lanqwasashi.

A sakarce ta waiwaya ta dubi hafsa din da irin kallon da takewa kowa,ba tare da ta bawa matsayinta muhimmanci ko matsar dashi gaba daga matsayin da take bawa kowa data fara saninsa ba

"Ina kwana?" Ta furta cikin girmamawa kamar yadda ta saba gaida dukkan wanda ya girmeta

"Lafiya lau qanwata,ya kwanan baqunta?" Hafsat ta fadi da wani murmushi da takejin kamar na sossoka qayoyi ne cikin bakinta.

Murmushi ta danyi tana maida dubanta ga latifa,saboda batasan amsar da zata bayar ba,don batasan amsar da ake bayarwa din ba,ta dan ranqwafa kadan latifa ta soma daura mata dankwalin.

Cas ya zauna a kanta,ta daga kai latifan tana kallonta

"Ehen.....yauwa,yanzu kikai dauri" latifa ta fada cikin tsokana.

Idanunta hafsa takai kai,cikin sakanni taji ba zata iya ci gaba da zama tana kallon yarinyar ba,wani irin mugun kyau da kwarjini daurin yayi mata,saita miqe cak tana cewa

"Bari na koma,yau jiki yayi nauyi ban samu dafa muku komai ba,kuyi haquri" murmushi inna laila tayi

"Lah,babu komai fa,yaran ma suna gab da kammala dafa abun karyawan,ai ansha hidima wallahi,mun gode,Allah dai ya qara hade kanku,ya kade fitina,gata nan sai ayita haquri da ita,har yanzu akwai quruciya sosai a tare da ita,sai ana yi mata nuni,ana kuma gyara mata inda tayi kuskure,ayi haquri da ita don Allah" ta fada zuciyarta na danson naqaltar mata fuskar hafsatun

"Aiba komai wallahi" ta fada a taqaice,can wani sashe na zuciyarta yana jin kamar ya zundumawa inna laila ashar,babu zancan quruciya uzuri ko daga qafa ga duk wadda ta aurar mata miji,koda kuwa widad din qyanqyasar yau ce,tunda har ta iya sanin meye so?,ta banbance tana sonshi,ta kuma iya sanin meye aure ai magana ta qare,babu daga qafa babu ragi babu kuma rangwame,haka ta dinga jefa qafarta zuwa sassanta idanunta basa gani sosai,fatanta Allah yasa abbas ya wuce sashensa,ya kamata ta rage kukan dake damunta a qirji.

Cikin awannin da suka biyo baya suka sake shiga qalqale sassan nata da kyau,duk sauran abubuwan da ba'a gama kintsawa ba suka kammalasu,sun gama kuwa da wuri,saboda wadanda ke presidential lodge din da aka kaisu motoci sun kwasosu sun dawo dasu gidan,nan da nan sashen ya dan qara cika,anata hira da barkwanci,kusan kowa gidan widad djn ya tafi dashi,saboda babu ce kawai babu.

Duk da wannan jikinta ya mata wani mugun sanyi,babu wannan hayaniya ko kazar kazar din,tana lafe a waje daya kusa da inna laila,itace ta zame mata kamar ummun nata,mugun kewar ummun take,gaba daya zuciya da jikinta babu dadi,duk da yadda suketa qoqarin janta da hira da kuma wasanni.

Qarfe sha biyu har sun fidda jakankunansu harabar gidan,sun kuma fito waje,zuwa sannan idanun widad fararen nan sun fara kadawa suna tara ruwan hawaye,hakanan ta riqe hannun inna laila gam.

Sanda suka fara shiga motocinsu dai dai lokacin ya iso,shi ya fara qarasowa wajen sannan hafsat wadda keta yashe baki tana sake binsu da murmushin yaqe.

Cikin nutsuwar nan tasa yake tsaye gaban motocin,yana sanye da wani soft yard na maza gray color da yayi matuqar kwantawa a lafiyayyar fatarsa,jikinsa na fidda soft scent mai kwantar da hankali.
Chapter 42 · 0% Book details