← Book details A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 111

Sashe 32

A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tana daga kwancen tana kallon yadda ummu ita da warisha qanwar abbanta suketa hada kaya cikin manyan buhunhuna da kwalaye,wanda gaba daya kayan ummu tace nata ne,gidanta za'a kai mata ayi mata jeranta,itama ta samu nata gidan na qashin kanta,duk sanda ummu ta fadi hakan dadi takeji,amma yau gaba daya jikinta ya sanyaya,gwiwarta ta fara sagewa.

Ana tsaka da wannan latifa tayi sallama ta shigo dakin ummun,ta tsaya daga bakin qofa yana gayawa ummu game gyaran jiki tazo,tunda widad din taji haka ta runtse idanunta tahau baccin qarya,ita kwata kwata batason wannan kwabe kwaben da aketa shafa mata yau wajen sati guda kenan,tana jin sanda ummun ta waiwaya tana qwala mata kira,amma sai ta sake lafewa cikin bargo tayi kamar bacci take,har ta gaji da kira ta juya ga latifa

"Inaga kawai abar aikin nan haka,dama yau da gobe ne kawai ya rage"

"To shikenan,bari na sallameta,yauwa......anty madina tace na gaya miki,kayan miyar ya za'a yi dasu,a markada gaba daya azubasu a freezer baya?"

"Eh hakan yayi,don kada su lalace kafin jibin"

"To shikenan" sai latifan ta juya ya fita,su kuma sukaci gaba da hada kayan,tana labe cikin bargo tana satar kallonsu,tana jin anty warisha na cewa

"Banda abun ummu nawa ma jikin widad din yake,me ya sameshi ma da za'a mata gyara,ita da dama fatarta me kyau ce,a haka ma a karon banza daukan ido takeyi"

"Wallahi madina ta matsa sai anyi mata,to ya na iya,itakam dama ta iya biyewa shirmensu,yanzu haka ta gama tsara musu komai,har kudi tasa muhsin ya karba musu wajen ango wai zasuyi walima" dariya warisha ta sanya

"Kai,Allah mai iko,widad amarya" sai ummun ta murmusa kawai,don dauriya kawai takeyi batason aga rauninta.

Tun tana labe tana kallonsu har baccin gaske ya dauketa,bata farka ba sai dab da la'asar,sanda ta tashi dakin babu kowa,sun gama aikinsu sun fice,bandakin ummun ta shiga ta daura alwala,ta shimfida abun sallar tayi sallarta,saita dan zauna tana jin hayaniyar su nabiha da sauran jikokin gidan,daga bisani ta gaza daurewa ta fito.

Ido kuwa yayi mata caaa,mutane anata kiranta da amarya,saidai ta tura baki tayi gaba abinta,itafa shi yasa tunda aka fara baqin ma batason fitowa,a haka dai ta samu ta wuce sassan anty madina,a canne ta sake sosai abinta,harta manta da komai ma,har sai da anty madina tace lallai gobe za'a tsefe kai ayi kitso,a nan fa suka raba gaari da ita,saboda ta ambato maqiyinta wato kitso.

*RANAR DAURIN AURE*

Cikin jerin gwanon motoci na alfarma suka taso,tun daga garin bauchi zuwa cikin garin kano,qarqashin jagorancin jami'an tsaro da matakai masu tsauri,a ranar tamkar dai wani shugaban qasa,duk yadda ya dauki daurin auren sai ya wuce masa haka,tamkar dai dama ya dade da shiryama hakan,shi kansa cikin sabuwa dal din motarsa yake,yana seat din baya shi da suraj,sanye da wata danyar shadda wadda koda gari aka baka ka canki kudinta ba zaka ajeta nan kusa ba.

Tunda suka taso fuskar hafsat ke masa yawo,tunda zancan ya tsiro bai taba jin tausayinta irin na yau ba,yana hangen yadda fuskarta ta sauya a sanda yake shiga motarsa cikin shigar dake jikinsa a yanzu,saidai zuciyarsa cike take fal da mamakin mene ya sauya hafsat?,me kuma ya kawo wannan sauyin?,yasan halinta ciki da bai,meye ya sanyata zub da makaman yaqinta?,wannan amsar ce har yanzu ya kasa lalubota,sai tarin wasi wasi da yake fama dashi kullum kwanan duniya.

Tun daga titin farko zuwa abinda yakai layin da zao sadaka da ainihin gidan alhj salim mai fata cike yake tanqam da jama'a,idan akace maka jama'a ina nufin jama'a na gaske da zakayi tsammanin daurin auren wata hamshaqiyar budurwar data ci ta qoshi da karatu da wayewa akeyi,gaba daya unguwar a hargitse take sakamakon halartar daurin auren da manyan 'yan siyasa gwamnoni da kuma qusoshin gwamnati da abbas yake hulda dasu sukayi,jama'a dake tsaye a gefe guda suna ci gaba da lissafa gwamnonin da sukaga suna shiga unguwar tasu,sai da suka lissafa shida casss!.

"Bisa dukkan alamu wannan karon babban kamu akayi a gidan nan,lallai yau sun jawo babban kai,kai kaga motocin dake ta gilmawa kamar daurin auren 'yar shugaban qasa?" Ire iren maganganun da matasa 'yan zaman banza a bakin layi keyi kenan,sunayi suna ci gaba da dorawa a lissafin su.

Daga can cikin gidan kuwa a shaqe yake da jama'a,ko ina idan ka kalla hada hada akeyi,zaka tsammaci an dauki shekaru ne ana yiwa bikin tanadi,saidai hausawa suna cewa,kowanne aure da arziqinsa yake zuwa,wanna haka yake,domin kuwa a lokacinne aka baje lefen widad wanda ya iso ne tare da 'yan daurin aure,akwati mai sunan akwati,akwati na alfarma guda goma sha biyar,kowanne maqare da sutturu masu daukan hankali,duk wanda ya daga idanu ya kalla koda baiso magana ba sai bakinsa ya subuce ya furta

"Ma sha Allah"mafi yawan mutane cikin family da wadanda ke cikin gidan dake zuba idon suga wani abun kaico ya bulla sai jikkunansu suka fara yin sanyi,musamman da labarin irin manyan mutanen da suka halarci bikin yajewa kunnuwansu..........

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K'AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)

Page 29

Qarfe biyu na rana bayan sallar azahar aka daura auren asp abbas da amaryarsa widad mahmud salim akan sadaki naira dubu dari,dubban jama'ar da suka halarci wajen suka haida,labarin kuma ya kai har cikin gida ya fara yawo a tsakanin mata.

Dai dai lokacin widad na zaune tsakiyar anty deena da anty warisha,sai sharban kuka takeyi,duk yadda sukayi da ita tayi shuru bare a samu ayi mata kwalliyar daurin aure taqi,sai suka sakata a gaba kawai suna kallonta.

Anty madina ce tayi sallama ta tana turo qofar dakin,dakin da babu kowa sai su ukun kawai,warisha ta amsa sallamar anty dina dake danna wayarta kai kawai ta daga ta kalli anty madina

"A'ah,na zata zanzo na tarar kun gama,an gama daurin aure fa,angwayen ma yanzun zasu shigo za'ayi hotuna"

"Inafa akayi kwalliya,kin ganta nan ko kayan taqi ta saka ma,ni bansan me yake damunta ba" anty deena ta fada tana ajjiye wayarta a saman madubin dakin.

"Ashsha,haba widad,mene hakan?" Hawayenta taketa qoqarin tsayarwa ta hanyar shareshi da hannuwanta amma hakan ya gagara,wani irin bacin rai tsoro da kuma takura takejin kanta a ciki,wanda ita kanta batasan dalili ba,kawai batason barin gida ne,hakanan shi uncle abbas din ta yaya za'a wani ce shine mijinta tana zaman zamanta?.

Anty madina ce ta cewa su deena din su basu waje minti biyar kacal,nasu musa ba suka miqe,anty deena ta dauki mayafinta mahadin lace din jikinta ta fara yin gaba,don dama ta fara gajiya da zaman lallashin widad din,wadda bata da alamun daina kukan.

Cikin mintuna goma sai ga hawayen ta tsaya tas,anty madina kuma ta shiryata da kanta,hatta da undies ita ta bata ta saka,tana jin kunya tana nonnoqewa,ta shiryata cikin wani lafiyayyen lace fari da ummu ta kashe maqudan kudade wajen siyansa,aka kuma shirya masa nutsatsen dinkin doguwar riga,gashinta da yasha gyara ta tufke mata,sannan ta qawata mata kanta da sarqa ruwan gold da aka sanyawa saman ka,wanda kusan al'adace ta asalin yarensu,hannayenta sun sha warware masu kalolin gold masu asalin tsada,haka yatsun hannunta kowanne zobe ne bibbiyu daga tsakiya.

Fes widad din ta fito,asalin quruciya da qaranci shekarunta na sake bayyana kansu,wanda ya cakuda da qyallin amarcin da akewa kowacce mace feshinsa,komai kyau ko muninta,indai sunan nan na amarya ya hau kanta.

Kiransu anty deena tayi sanda taji hayaniya ta fara cika gidan,muryoyin maza na tashi,alamu dake nuna tawagar angwaye ne suka shigo gaisawa da surukansu,daga inda take sai ta dinga jin kamar an daureta,gabanta ya tsananta faduwa,wani tsoro yana shigarta,kanta a qasa,nutsuwa ta musamman irin wadda duk wanda yasan widad din bai santa da ita ba ta saukar mata.

Shi daya ne cikin motar kwance a seat din gaba,ya dage dukka baqaqen gilasanta,da hular da kuma babbar rigar duka ya ciresu ya jefa seat din baya,ta cikin motar yana iya hagen kai da kawon jama'a,ciki harda gungun abokansa da suka masa karar da ko auren farko bai sameta ba.

Amatsayinsa na jimi'in tsaro,duba daya yayi musu yana daga kwancen ya fahimci shi suke nema,yasan zancan bai wuce ace su shiga cikin gidan,abinda sam bashi a tsarinsa kenan,saboda yana kallon haka a mazaunin keta haddin shari'a,tu dazu ya shigo ya kwanta,ya kuma gargadi Samuel kada ya gayawa kowa yana ciki.

Idanunsa ya janye a hankali daga inda yake kallo sanda yaji ana knocking qofar motar,fuskar suraj yake hangowa wanda yayi wujiga wujiga saboda yawan al'ummar dake wajen,sai yasa hannu a nutse yana daga kwancen ya buda murfin motar,suraj ya sunkuyo yana sako kansa.

Ajiyar zuciya ya sauke

"Gaskiya baka kyauta mana ba,kaifa ake nema tun dazun,zaa shiga gaida iyaye da kakannin amarya,ga masu hotuna suna jira suma zasu wuce" kamar wanda baya son yin magana ya buda bakinsa

"Duk da wannan uban jama'ar zamu kama mu shige musu gida suraj?"

"To ya za'ayi,al'adace" kai ya girgiza

"Ba dani za'ayi wannan aikin ba,idan ya zama dole ka sallamesu su tsaya iya waje,mu shiga koda mu uku ne muhsin yayi mana jagora iya sashen ummu kakarsa mu gaisa mu fito" dan hade rai suraj yayi,sai kuma ya saki dariya

"Kai mutumina,anya ba kishin matarka ka fara ba?" Wani kallo ya watsawa suraj din

"Waikai me yasa baka da girma saina jikinka,yarinyar da idan auren qauye ne na haifi kamarta?"

"Allah yasa motsin gado ce,bar ganin allura,duk qanqantarta qarfe ce,any way.....banga laifinka ba,bari ina zuwa" ya fadi yana maida murfin motar ya rufe.

Sai da yayi settling komai yadda abbas din yakeso sannan ya sanar dashi,hularsa ya dauka ya mayar saman kansa,ya riqe babbar rigar a hannunsa,yana jin ta masa nauyi,saboda rashin sabo da sanyata,tunda gaba daya aikinsa yafi alaqa da qananun kaya.
Chapter 32 · 0% Book details