← Book details A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 111

Sashe 41

A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ki koma ki kwana a can,da safe saina rakoki,lokacin sun tashi ko?" Ya fada cikin sigar lallami,saboda yadda yakejin kansa yayi week,bacci ma dai a taqaice yaji yana saukar masa.

"Amm....."

"Ba'a musu da babba right?" Ya fadi cikin sigar tambaya yana ritsata da kallonsa,karon farko taji idanunsa sun dan mata nauyi,saita sadda kanta qasa,ya sake sakata a gaba kamar dazu suka koma,jikinta duk a mace, hankalinta a tashe,anty deena ce ta jawo mata,ta yaya zata kwana daki daya dashi?.

Yayi mamaki sanda ya dawo yaga babu hafsat din ba dalilinta,sai ya tsugunna ya tattara komai waje daya ya adana,har a sannan widad na zaune a takure a waje daya,ac din dakin ya kashe gaba daya,ya rage fitilun falon,saiya kalleta

"Muje ciki ki kwanta" fuska ta tattare waje daya,tanason cewa a'ah amma kuma batason yaga kamar ummu bata koya mata cewa ba'a yiwa babba musu ba,tunda gashi dazu ya fada,haka ta miqe tana biye dashi har cikin bedroom din nasa.

Da ido take kallon komai,bedroom din nada wani irin weather mai saukar da nutsuwa,sassanyan qamshinsa ya kama dakin sosai,komai fari ne qal,kuma komai yana kan tsari a killace,saita haye kan sofa bed ta dunqule,shi kuma ya wuce bandaki.

A ciki ya shirya cikin wasu silk pyjama sky blue,yayi brush ya feshe jiki da bakinsa da turarukansu

"Zaki canza kaya ne?" Ya fada yana dan duban gefanta,cikinta ne ya bada qululu saboda tsoro,yana nufin ta cire kayan jikinta ta sauya wasu?,a dakinsa?,saita damqe jikinta waje guda kamar wadda ya taho zai rabata da suturarta,ta jijjiga kai da qarfi

"A'ah,wadan nan nakeso na jikina" dariya taso qwace masa amma ya danne,a yadda take acting yasan lallai batasan meye cikakken ma'anar aure ba,to amma me yasa take tsoro haka,sai ya rabu da ita,ya jawo wayarsa da nufin kiran hafsat din yayi mata sai da safe,duk da baisan me ya fiddata daga dakin ba,ya tsammaci zatace zata kwana kamar jiya.

Sau uku yana kiranta tana katse kiran,abun yadan daure masa kai,amma saiya tattara ya watsar,dare yayi,hutu yake buqata

"Ki koma gado ki kwanta" ya sake fadi,kamar dazun dai a firgice tace masa a'ah,sai da yayi da gaske sannan ta kuma taga ya yibi filo da bargo yana shirin bar mata dakin sannan taji ranta ya sake.

K'ofar tabi da kallo sanda ya fita,sai kuma ta fara baza idanu,dan banzan tsoron nan nata ya dawo,ji tayi kamar ta bishi,amma ba zata iya ba,curewa tayi waje daya ta lulluba har kanta,saita saki kuka,anty deena ce.....duk ita tace sai tazo,gashi nan sun rufe mata qofa,bayan sunsan ta fita,kewar ummu ta taso mata,ta dinga hawaye ita daya cikin filo,har bacci barawo ya saceta.

A hankali ya bude qofar dakin,duk da akwai qarancin haske amma yana iya hangenta a cure waje daya,sai ya kada kansa ya wuce bandaki.

Alwala ya daura ya dawo dakin,ya feshe jikinsa da turare ya sauya jallabiyyar jikinsa,ya taka a hankali zuwa gefan gadon,hannu yasa ya bubbuga saman filon a tausashe,ta motsa kadan kamar zata tashi,sai kuma ta sake qudundunewa,cikin muryar barci tace

"Don Allah ummu,ba'a idar ba,yanzu aka tayar" shuru ya danyi yana nazarinta,ta kwabe fuska gaba daya tana tura baki gaba a shagwabe,har kuma a hankali ta saki bakin nata,da alama ta koma bacci sosai.

Kai ya girgiza kawai,bai hango komai ba banda zallar quruciya a tattare da ita,shikam baisan ya al'amuran zasuci gaba da tafiya ba,bai hango sauqi ba,sai nauyi daya sake hawa kansa,sai ya juya a nutse ya nufi qofa,yana kama handle din zai.bude ta bude idanunta a hankali, saboda yadda taji cikin jikinta ba'a gida take ba,saboda duk sanda tayi irin haka ummu saita takurata akan sai ta tashi koda ba'a tayar da sallar ba.

Tana qyallara ido ta hangoshi,saita zabura ta miqe tana rarraba idanu,a nutse ya waiwayo ya kalleta,sai baice komai ba ya sanya kai ya fice.

Sai data daina jin motsinsa sannan ta miqe a hankali cike da tsoro ta tura bandakin ta shige tayo alwalar itama ta dawo ta gabatar da sallar,har Allah Allah take ta idar ta fice zuwa wajensu anty madeena,tana idarwa bata ko tsaya addu'a ba tayo waje.

Cak ta tsaya a qofar falon kamar zata saki kuka,ganin garin da duhu har yanzu,gashi dukka fitilun harabar gidan an kashesu,dan banzan tsoronta kuwa bazai barta ta wuce sashenta ba,saita koma.bakin qofa ta rabe tana maida qananun hawayen dakeson sauko mata,ba zata koma cikin dakin ba kuwa,a nan zata yita zama har sai gari yayi haske.

Baiyi zaton zai sameta zaune a bakin qofa ba,don haka cike da kuzari da kuma hanzarinsa ya buda qofar falon

"Subhanallah" ya fada da sauri yana kama murfin qofar ya riqe a hannunsa,sai kuma yadan dai daita yanayin fuskarsa yana kallonta

"Me kikeyi a nan?" Mele baki tayi fuskarta a yamutse,da alama qiris take jira ta fashe

"Ina kwana?,can zan koma,kuma wajen da duhu bazan iya fita ba" sai daya juya ya sake kallon harabar gidan,shi yasa aka kashe fitilun saboda yaron gidan yace sunata wasa da wutar kada su lalata qwayayen,qwayaye ne masu tsada da daraja

"Basu bude ba suma,ki koma ciki sai rana ta fito" kai ta maqale a kafada,sannan ta miqe kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,ta koma saman kujera ta takure waje daya,bai sani bama ko hawaye take sharewa.

Dakin ya wuce,bai jima ba ya dawo,ya haye saman doguwar kujerar daya kwana a kai,yaja bargonsa zuwa qugu ya rufe, lokaci lokaci yana dan daga idanu ya dubeta,yadda take curewa waje daya ta kwanta shine ke bashi mamaki,amma baice da ita komai ba.

Wantsalowa tayi daga saman kujerar sanda agogo ya gama buga qarfe bakwai dai dai,suna hada idanu sai kuma ta koma dai dai ta zauna,fuska a narke take dubansa,cikin salo na roqo da magiya tace

"Don Allah.....ka rakani,gari yayi haske fa?" Ido ya tsura mata na wasu sakanni yana kallonta,sai ya janye idanun nasa yana zame bargon jikinsa,daki ya sake shiga,bai jima ba ya fito yana gyara button na rigarsa

"Muje" da saurinta ta sauko muryarta tabi bayansa,don kafin yakai qofa har ta kusa cimmasa,yadan sake binta da kallo sannan ya buda qofar suke fice.

*Arewabooks:Huguma*

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K'AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)

Page 37

Cak ta tsaya sanda suka isa bakin part din nata,ta juya tana fuskantar sa,fuskarta a narke,tana wasanda yatsunta,da alama magana takeson masa,amma ta kasa sai motsa yatsunta da takeyi,shi kuma ya kafeta da idanu,ganin ta kasa magana sai yayi gyaran murya,ta daga idanu ta dubeshi,kafin yace wani abu ta magantu

"Don Allah kada ka shigo" mamaki maganar tata ta bashi,sai ya kafeta da idanu yana neman ba'asi,bata gane ba,murya a narke tace

"Kaji?" Saiga qwalla ta biyo bayan maganar,bai shirya ba amma dole ta sanya qaramin murmushi ya qwace masa,sai ya kauda kansa gefe na sakanni yana danne murmushin kafin ya dawo da dubansa gareta,ya gama gano abinda take nufi,don haka yace

"Is okay" sai ya juya a hankali yabar wajen yana nufar sashen hafsat.

Ajiyar Zuciya ta sauke tana binsa da ido,sai taji dadi a ranta da ya tafin,don idan da ya tsaya ba shiga zatayi ba,da wanne ido zata kallesu?,me zatace musu?,ta samu relief don haka ta juya tana dosar qofar falon nata.

Kamar wata munafuka haka ta dinga rarraba ido tana rabewa a bango,jikin labulen bakin qofa ta tsaya tana leqen falon,inna laila ce saman dining ita da batulu,sai nujood zaune saman kujerar falon,Momma na zaune daga qasa,dukkansu kowa sanye da hijab,da alama tun tashin asuba ne basu koma ba.

Tana daga tsayen ta hangi anty deena ta fito dauke da wata jaka ta ajjiye saman kujera,ta kalli nujood tana cewa ta tashi su sake gyara falon,latifa ta riga ta gyaro ciki,saita matso ta wajen bakin qofa zata dauka mopper dake ajiye a wajen.

Motsin mutum ya sanyata waiwayawa ta dubi wajen,cikin mamaki take kallon widad

"Ke kuma me kike yi a nan a tsaye ke daya?" Rau rau tayi da idanu,a yadda anty deena ta kafeta da idanu saita fara hawaye kawai

"Meye haka widad?" Tambayar da ta sanya jikinta rawa,saboda tana ganin kamar anty deena din ta hangi abinda ya faru jiya,hankalin anty deena yadan dauko kadan,ta zaci ko wani abun ya gudana tsakaninsu,sai kuma taji hankalinta yadan kwanta kadan da taga yanayin tafiyarta bai canza ba,tana tausayinta,koda wani abun zai faru ma ta gwammace basa nan.

Sai data mata da gaske tabar kukan ta shigo,momma dake zaune ta bita da harara

"Ja'ira,zakiyi bayani ne" kasa hada idanu tayi da kowa,sai ta wuce ciki sum sum sum.

Dakinta ta murda ta fada tana sauke ajiyar zuciya mai qarfi,sai a sannan ta nutsu,ta soma bin dakin da kallo. Sosai ya qayatar da ita,an gama shirya mata komai sai qamshin sabinta yakeyi,ta waiwaya ta dubi bandaki inda anty deena tace akwai ruwan zafi,ta shiga tayi wanka,ta kuma zabi kaya masu kyau ta sanya,ta juya zata shige sai aka turo qofar,anty basma da anty ramziyya da anty marwa suka shigo,kowanne riqe da yaronsa,marwa dince kawai mai ciki bata samu rabo da wuri ba.

Nan bakin gadon suka zauna sunata tsokanar widad tare da da son jin me ya faru jiyan,kuka ta saki sosai

"Ni wallahi ku daina banaso,bayan ummu ta hana,babu kyau,wallahi ba ruwana" haka ta dinga fada tana sharar qwalla,su kuwa ganin abun suke kamar almara,wai yau widad din ummu ce aka aurar?,a wata uwa duniya?,ta tafi tabar ummu duk qaunar dake tsakaninsu?,Allah ne ya kawo anty madina ta korasu,sannan ta kada kan widad zuwa wanka,bayan ta fito kuma ta shiryata da kyau cikin wani lace da yayi masifar karbarta,ya fidda kyau da hasken fatarta,ita kanta ta dade tsaye gaban mdubi yana kallon kanta,tana ta zuba shirmenta na kyan da tayi,anty madina na binta da murmushi gami da goge qwalla a fakaice.
Chapter 41 · 0% Book details