← Book details A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 111

Sashe 51

A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Zan dan fita....." Tun kafin yakai qarshe ta daga manyan idanunta ta watsa a kansa,haka kawai yaji nashi idanun suna lanqwashewa zuwa lumshewa,kafin ya budesu ya azasu a kanta,har zuwa sannan manyan fararen idanunta suna kanshi,ta yaya zai fita ya barta a wannan gidan ita kadai?,duk da bata da tabbacin ita daya ce cikin gidan gaba daya,amma itakam ko dakin ummu bata yarda ta zauna ita kadai,inaga gidan gaba daya

"Bazan dade ba zan dawo,za'a knocking za'a kawo abinci,saiki bude ki karba,idan kuma wani abu ya taso ki kirani a waya" wani mugun tsoro ne ya shigeta sanda ya juya yana ficewa,kuka sosai yazo mata,ta cure waje guda tana cusa kanta tsakanin qafafunta

"Wayyo ummu"ta fada muryarta can qasa wadda ke cike da kuka,sun kawota inda bata da kowa,kamar basa sonta,itakam meye tayi musu?,sai taci gaba da rera kukanta a hankali,har zuwa sanda taji kiran sallar isha'i ta miqe ta bada farali,ta sake komawa yadda take.

Tana jin anata knocking kamar yadda yace amma ko yunwa zata kasheta bata jin zata iya miqewa zuwa falon har ta bude,tana jinsu har suka gama bugunsu suka tafi,saita sake sakin kuka tana takurewa waje daya.

Lokaci lokaci tana duban agogo tare da fadin

"Allah kasa ya kusa dawowa" saita sake maida kanta tana sharar hawaye,har kusan awanni uku babu shi babu dalilinsa.

A karo na barkatai ta sake daga kanta don kallon agogo,saidai hasken farfajiyar gidan ya hasko mata mage dake tsaye jikin window din dakin nata tana kada jela,wani mugun tsoro da razani ya shigeta,take jikinta gaba daya ya fara rawa,hawayen idanunta suka ninku,ta fara karanta ayatul kursiyyu a rarrabe saboda yadda bakinta yake rawa,a duniya babu abinda ta tsana take mugun tsoro irin magen,don saboda ita kowa na gidan ya haqura da ita,sabod koda ka kawota sai ummu ta sanyaka ka maidata inda ka daukota.

A hankali magen ta soma kankarar glass din jikin window din kamar me neman hanya tana kuka mieeeuuuu mieeeuu,ba abinda yaxo kwanyar widad illa ga magen har ta shigo ta fada mata a ciki,take ta saki wata qara hade da kuka.

Sautin muryarta yakai kunnuwansa sanda yake tsaye yana knocking qofar falon,kusan sau biyar kenan amma baiji motsinta ba,har ya fara tunanin ko tayi barci ne?,sai kuma saqon muryarta ya riskeshi.

Sosai yaji hankalinsa ya tashi,to meye ya sameta?,cikin hanzari da kuma gaggawa ya fara laluben keys din dake aljihunsa,ya fiddosu ya fara gwadaw jikin qofar cikin hanzari da zafin nama,har sannan ihunta na tashi saidai da yake harabar gidan tana da yalwa,babu lallai wanda ke can nesa kamar malam bala ya jiyota.

Cikin sa'a ya samu key din,ya bude ya tura sannan ya shige da sassarfa zuwa dakin nata.

Motsin bude qofar dakin ya zake dagula kissafinta,ya kuma sakata ta sake gigicewa gaba daya,a nata zaton magen ce ta bude window din

"Calm down mana,ki nutsu,menene?" Ya jefa mata tambayar yana riqe da dukka kafadunta,idanunta da suka jirkice ta daga ta kalleshi,batayi wata wata ba ta shige jikinsa ta qanqamesa kamar yadda ta saba yiwa ummu,sannan ta daga yatsanta tana nuna masa window.

Mutuwar zaune yayi,a yadda ta shige masa jiki gaba cikin ba zata,wani irin sanyi ya sauka a gabbansa, tashin farko kamar an zare masa laka,don matasan tudun qirjinta gaba daya sun hade da nashi qirjinsa,yana iya jinsu sosai,ya daga kansa kamar mai ciwon wuya ya waiwaya ga window din,dai dai sanda magen tayi tsalle ta sauka daga window din,take ya fahimci ainihin dalilin rudewarta,sai ya dawo da dubansa kanta yana qoqarin zareta daga jikinsa,tare da fadin

"Am beside you,calm down, mage ce fa,look there,she's already gone" ya kuma fada yana qoqarin tsaida fuskarta tsakiyar tafin hannunsa tare da qoqarin lalubo qwayar idanunta don bata qwarin gwiwa.

Sam taqi ganewa abinda yake fadi din,sai ya tuna abinda ya faru washegarin randa tazo gidan,don haka ya buda hannayensa ya sanyata cikin qirjinsa ya rufe,wata qatuwar ajiyar zuciya tana subuce masa.

Dukka idanunta ta fidda waje kamar zasu zazzago,gabanta yayi mummunar faduwa,zai kuma?,irin ta ranar nan?,me yasa shi din dan iska ne?,take wata huduba data baro bauchi da ita ya fado mata,cikin dan qaramin qarfinta da bai taka kara ya karya ba ta saka hannayenta duka biyun tana qoqarin tureshi,ko kusa ko alama baiyi gezau ba,amma yaji abinda take shirin yi din,haka kuma yake buqata,sai yaja da baya yana kallonta.

Kuka sosai ta fashe dashi,kukan takaici da baqincikin rungumeta da yayi,wannan wanne irin iskanci ne,haka kawai sai ya dinga taba ta?

"Ya isa,ta tafi nace" ya fada calmly yana kallon yadda sumar kanta ta biyo ta gefan fuskarta,kamanninta suka fita sosai,fuskarta tayi jazur saboda kuka.

*Arewabooks:Huguma*

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K'AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)

Page 46

Space ya bata,ya zauna daga nesa yana kallonta har sai data gamsu don kanta ta tsagaita kukan,don ya fuskanci kukan da take harda na sakalci ma,sanann ya miqe yana duba dakin ko zaiga abincin da yace a kawo mata amma baiga alamunsa ba,waiwayawa yayi yana dubanta

"Ina abincin da nace a kawo miki?" Baki ta tabe sosai irin na yaran da suka gwanance wajen shagwaba

"Naji ana knocking,inajin tsoro ne bazan iya fita ba" dan qaramin bakinta me dauke da jajayen lips yabi da kallo,wannan da alama ba abinda ta sani sai sangarta da sakalci,ya janye idanuwansa yana laluba aljihunsa ya fidda wayarsa,a nan ya samu tarin miscall na wanda ya aika din,yana kiransa kafin yace komai ya gaya masa yayita bugu ba'a bude ba

"Ba matsala,am back,zaka iya kawowa" ya fada yana nufar qofar dakin da zummar ficewa,saidai tun bai sanya qafarsa a falo ba ta miqe ta rufa masa baya.

Tsayawa yayi bayan ya zame wayar daga kunnensa sannan ya waiwayo yana kallonta,saita dauke kanta gefe tana turo baki gaba gami da tabeshi

"Ina zaki?"

"Ni binka zanyi,Allah ba zan zauna a nan ba" saiga hawaye yana biyo bayan maganarta

"Saqo zan karbo"

"Zan bika" ta sake fada wasu hawayen na sake zubowa

"Yanzu zan dawo,just a compound din gidan nan ne" wannan karon maqale kafada tayi saboda kuka ya riga da ya subuce mata

"Oh god" ya fada yana dan lumshe idanunsa hadi da budesu duka lokaci guda,kafin ya sake cewa wani abu anyi knocking,sai kawai yayi gaba,ta kuwa take masa baya yana dauke qafarsa tana saka tata.

Takeaway na abincin ya karba ya maida qofar ya kulle,daya juyo sai kuma tayi tsaye tana jin banbarakwai,ya tako taja baya hadi da yin gefe ta bashi hanya,ya isa tsakiyar falon

"Dauko plate a kitchen da spoon" ya fada yana ajjiye ledar,hadi da zama saman kujerar sannan ya fara qoqarin cire agogon hannunsa.

Jin shuru bata amsa ba,bata kuma motsa ba ya sanyashi dago kansa,tana tsaye ta marairaice fuska kawai tana kallonsa

"Bakiji bane?" Ya tambayeta da kaurin murya

"Tsoro...."

"Subhanallah" ya furta a hankali,sai kawai ya miqe ba tare da yace komai ba,nan ma batayi qasa a gwiwa ba ta rufa masa baya,tana tsaye ya dauko plate din,ya hado da spoons da bottle water da drink na kwali guda daya sannan suka rankayo suka fito.

Wannan karon a qas ya zauna sosai,ya bude ledojin ya hada komai da komai kowanne plates d'ai d'ai ya tura mata hade da ruwan da kuma lemon,ya sanyawa nashi palate din spoon ya fara diban abincin yana ci bayan yayi bismillah,hannunsa daya riqe da wayarsa yana dannawa.

Shuru tayi tana kallon plate din nata,tun asali ita din bata saba cin abinci ita kadai ba,tun tasowarta,saboda ta taso mutum ce mara son cin abinci,wannan yasa kowanne lokaci da ummu sukeci,suna ci tana hilatarta har sai taci me yawa,idan kuwa tana azumine ko kuma tana makaranta taci kafin ta dawo wanda zaiyi wuya ma ta rigata ci din,saita hada mata da wani cikinsu Aafiya,ko ta tafi sassan anty madina taci cikin jama'a,shine fa take ci da dan dama,ko zuwanta bauchi kullum da latifa sukeci,to a yanzun saita kasa tabuka komai,har yayi nisa da cin nasa abincin.

Bai kula ba sai da yayi nisa sosai,ya daga idanunsa ya kalleta,itama shi take kallo,ta narke fuska kamar wadda kukan da tayi bai isheta ba tana neman qari ne

"Dauki kici" ya fadi yana mata nuni da abincin da ido,saita girgiza kai

"Na qoshi" mamaki ya kamashi,baici ace bata jin yunwa ba,yasan tun sanda suka fito rabonta da abinci,saiya rasa yadda zai mata taci.abincin,don daga qarshe ma baya taja ta rungume qafafunta kamar wata marainiya.

Ajiyar zuciya ya sauke yana ajjiye nasa plate din,shikam ya gamu da gamonsa,da alama rainon zaiyi da gaske,suraj da suke chart dashi a lokacin ya turawa gajeran saqon tambaya

_"If you want a child to eat and he refuses, what will you do for him?,ina buqatar taimakon,its urgent please"_. Sai daya tura masa sticker din dariya sannan ya amsa masa

_"yar rainon taka hala?,ka lallabata,malam ka kuma koyi magana,wannan ba hafsat bace,ita din ba zata gane shuru ba,be a child like her for a while,sannan ne komai zai daidaita"_

_"thanks,i will tray_" ya amsa masa sannan ya kashe data dinsa ya ajjiye wayar

"Oh God, give me courage" ya fada can qasan ransa yana kallonta

"Let's share the food,come closer" ya fada yans miqa hannu yaja plate din,makarantar da tayi mai tsada ce sosai,don haka ko a iya js data tsaya tana jin turanci fes tana kuma iya mayarwa,don haka taji sarai abinda ya fada,to amma fa ita tsironsa takeji,ta sani tun a gida cin abinci da maza ba abu bane me kyau,uwa uba hudubarta tana nan a kanta fes bata bace ba,ya zataci abinci da wani?,to amma kuma yunwa takeji,idan kuma bai tayata ci din ba tabbas tana iya kwana da yunwa
Chapter 51 · 0% Book details