← Book details A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 111

Sashe 48

A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallo daya ya mata ya maida kansa ga takardunsa,kallon da ya bata mata rai sosai taji kamar ta koma ita da abincinta,amma ta hadiye ta danne,tana da burika da yawa da takeso ta cimma,kuma anty ummee ta tabbatar mata sai ta iya mallakar kanta da kuma fushinta.

Wani table qarami na glass ta jawo ta aza kayan a kai,tana shirin zama tace masa

"Ga abincinka nan"

"Am okay,ki kwashesu" ranta tadan bata,ta zumbura baki,kamar zatayi magana sai kuma tayi shuru,taci gaba da kallonsa,yayin da shi kuma ya aza dukka hankalinsa akan takardar dake dauke da wani zane mai kama da map,ya sani ba zata iya bashi haquri ba,abune mai wahala kaji kalmar haquri daga bakinta.

Sai da ya gama abinda yakeyi ya ninke takardar sannan ya miqe

"Jibi zamu wuce kaduna in sha Allah" ya fadi mata don ya fita hakkinta,gabanta yadan fadi

"naji kace zaku wuce,kai da wa?"

"Widad" ranar farko da ya fara ambatar sunanta,idanu ta qanqance cikin mamaki da ba zata tace

"Na dauka a nan zaka barta ko"

"Saboda ke ba zakije ba,kowa ma haka ne?" Wani tashin hankali ne taji ya ziyarceta,me abbas yake nufi?,ita zai barta a nan,ya tasa qanqanuwar yarinya a gaba su tafi garin da yake aiki?,ita tana nan tana me?.

Sai da tayi yaqi da zuciyarta sannan ta hadiye maganganun da su taji sunfi dacewa ta gaya masa

"Amma idan kun tafin me zata tsinana maka?,ka barta kawai a nan ta saba da dangi mu tafi tare" kai ya girgiza yana nufar wardrobe dinsa ya budeta sannan ya amsa mata

"Ai bana magana biyu,kinfi kowa sanin hakan,zancan tafiya kaduna mun rufe wannan babin dake har abada,abinda yasa na gaya miki yanzun ma don na fita hakkinki,duk weekends zan dinga shigowa in sha Allah" wani abu ya taso ya tsaye mata a wuya,wannan karon taji ba zata iya shuru ba,ta yaya zai sanya yarinya qarama a gaba su tafi har wani gari,ita din tana jingine a gefe,sai qarshen sati sannan yazo mata?,me ma tayi kenan?,abinda take gudun afkuwarsa tabbas zai afku

"Gaskiya ni ban yarda ba,saboda nice babba ni ya kamata ace na bika,ko ka bani zabi....."

"Wanne zabi zan baki?,ki manta tun kafin wanzuwarta kika yiwa kanki zabi?,hafsat kinga..... please bana son ciwon kai,zancan ya isheni haka.....ina underwears dina?" Ya jefa mata tambayar yana ritsata da ido

"Ban wanke ba" ta amsa masa tana miqewa cikin hucin bacin rai

"Good" yace da ita yana maida murfin wardrobe din ya rufe zuciyarsa na masa zafi,duk sanda yake da buqatar neat underwears saidai ya zauna ya wanke abinsa da kansa,ko kuma ya diba yakai mata,ya kuma jaddada mata amfani zaiyi dasu,wataran ta diba wasu daga ciki ta wanke masa,wataran kuma ta wanke duka idan taso.

"Abban mimi...." Ta kirayi sunansa da kaushi, ganin bai qara bi ta kanta ba,ya nufi ma qofar toilet dinsa

"Duk haquri da kuma kawaicin da nake maka hakan bai hanaka gaza yimin adalci ba ko?,to wallahi bazan yarda ina zaune a tauyemin hakkina ba" zuba mata idanu yayi sosai fiye da dazu yana kallon zallar ainihin rashin kunya daga wajen hafsat din,eh rashin kunya mana,banda haka ta manta abinda tayi masa

"Tunda kika zabi zama a bauchi baki isa ki bini ko ina ba,kince na nema mai zama dani a kaduna kuma na samu fine....na dauka hankali kikayi kika fara gyaro kura kurenki,ashe ba haka bane,to a wannan karon ina mai gaya miki da kakkausar murya,kibi a hankali,don bazanci gaba da lamuntar halayenki ba,if not kuma.....mu zuba dani dake" daga haka yayi gaba ya bude qofar toilet din ya shige abinsa.

Wasu qwalla masu zafi ne suka biyo kuncinta

"Wallahi zankai inda za'a qwatar min hakkina,nima na gaji" ta fadi tana juyawa da gudu gudu ta fice daga dakin.

Sanda ta gifta sassan widad dake kulle sai taji kamar ta koma ta shiga ta shaqeta ko zata rage zugi da radadin da zuciyarta ke mata,amma wata zuciyar ta hanata,ta wuce da sauri sauri zuwa sashenta tana kuka sosai.

*Arewabooks:Huguma*

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K'AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)

Page 43

Gefan gadonta ta zauna hannuwanta rufe da fuskarta tana kuka sosai,me yasa abbas bazai fuskanceta su zauna lafiya ba?,yasha gaya mata zai bata mamaki,bata taba zaton irin wannan mamakin zai bata ba,ba ruwansa da harkar mata,kamar ma baida damuwa dasu,wannan yasa ta saki jikin cewa duk wani mataki da zai dauka a kanta bazai wuce ya qaurace mata ba,ita kuma bata da wannan damuwar,bata da yawan buqata,tasa buqatar ma damunta takeyi.

Wayarta ta jawo dake gefan gadon ta soma laluba number kyawunta zatayi abinda ta saba wato kai qara,saidai tana kallon agogo taga dare yayi,wata zuciyar na ingizata ta kirashi,wata zuciyar na cewa tayi haquri ta barwa safiya,saita aje wayar,amma kuma yadda zuciyarta ta cika ta tumbatsa da bacin rai da kuma fushi,sai taji ba zata iya kwana ita daya da wannan baqincikin a cikin ranta ba,don haka ta sake daukar wayar ta kira number anty ummee.

Cikin sa'a ta shiga,tana shiga din kuma ta daga

"Ke lafiyarki a wannan tsohon daren?" Ta jefa mata tambayar jin ta fashe mata da kuka

"Anty kaduna zai dauketa jibi su tafi"

"Ita wa?,au amaryar taki?" Kalmar tayi mata ciwo,amma saita gyada kai kamar tana wajen

"To sai kuma me ya faru?"

"Na gaya masa ni.ban yarda ba,shine yake wani gayamin wai aini na zabi haka, mukayi fada dai dashi na baro masa dakin" wani tsaki anty ummee taja

"Dadina dake wallahi baki da qwaqwalwa kwata kwata wani zubun hafsatu,ke da zaki nuna murna,kice hakan da yayi shine dai dai,zasufi sabawa da juna?" Ido hafsat ta zaro,kukanta ya tsaya cak

"Anty?,suje su kebe su biyu wani abun ya faru kenan fa?,kaduna fa nake gaya miki,gidan da daga shi sai ita"

"To ubanme ma zakije kiyi a garin da baki da ko kashi?,kibar kowa naki asalinki da tushenki a nan,suje sai sun dawo,sannan ma kuma sai akace miki haka zaki barta idan sun tashi tafiyar?,tsaya kiji,bude kunnenki da kyau" tarawa anty ummee nutsuwarta tayi,duk da tanajin babu wata mafita data wuce tayi masa bore,ko ya tafi da ita ko ya aje yarinyar a gida,saidai cikin minti biyar da fara sauraran anty ummee fuskarta ta washe da farinciki.

**********Tun daren jiya bai kwanta ba sai daya tabbatar ya hada duk kayan da zaiyi tafiyar dasu ranar asabar din,idan da sabo kusan ya zame masa jiki,a shekarun da sukayi da hafsat zai iya irga sau nawa ta taba hada masa kaya wai don zaiyi tafiya ko zai koma bakin aiki.

Bai kwanta ba sai kusan biyu na dare,a nan ma tunani ya hanashi sakat,yayita juyi from side to side,yanata bitar halayen hafsat,ya yarda matar aure ta qwarai dace ne,bai taba kawowa hafsat din zata sauya haka ba,bai taba kawowa cewa haka halaye da dabi'unta suke a zahiri ba,bai samu bacci ba sai wajen uku da rabi na dare,asuba nayi yayi alwala ya wuce masallaci.

Bai shigo gidan ba sai wajen qarfe tara na safe,ya tsaya taron magidanta da akeyi a unguwar duk qarshen wata,kafin sannan hafsat takai ta kawo a sassansa ya kusa sau uku,so take ta aiwatar da shirinta tun da wurwuri,plan din anty ummee yafi kwanta mata fiye da nata plan din,saboda idan tanason barin garinta to tana qaunar mutuwarta.

Sunyi sabani,tana komawa sassanta yana shigowa gidan,kamar ko yaushe a matsayin widad na baquwa sai ya fara da sashenta.

Dai dai lokacin suna bedroom din widad din,latifa ta gama musu breakfast,harma sunci,don basa iya cin abincin hafsa,wanna yasa ma basa jiranta,itama kuma ana kwanaki biyar ta daina kawowa,saidai ta aiko a kirata tazo suyi dinner,sai akaci sa'a widad din mai wahalar sabo ce bata zuwa.

Sabbin kaya latifa ke ware mata,saboda ta soma shirin komawa kano,amma dai bata bari widad din ta sani ba,don kada ta birkice mata

"Wadan nan kayan dasu zakici gaba da kwalliyar,kinji dai abinda anty deena ta gaya miki?" Kai ta gyada

"Bakiga kullum sai nayi abinda tace din ba"

"Eh amma har yanzu baki qara zuwa wajen uncle din naki ba,kuma na gaya miki a can ake kwana" ido ta fiddo,waisu basa jin kunya suke mata zancan ta kwana da namiji?,bayan ummu ta gaya mata ko hannunta aka riqe ciki zatayi kuma mutuwa zatayi?,kafin tace komai anyi knocking qofar,latifan tasan ba wanda zai.shigo kansa tsaye saimai gidan,don haka ta zube kayan hannunta tana yiwa widad nuni da.hannu akan ta bude qofar.

Itakam bata gane komai ba,ta sauko daga saman gadon,ta isa bakin qofar ya buda a hankali manyan idanuwansa suka fada cikin manyan fararen nata idanun,ta saki qofar cikin rashin sabo da d'ari d'ari taja baya tana cewa

"Ina kwana?"
"Lafiya qalau" ya amsa mata yana duban kayan jikinta,kayan bacci ne riga da wando masu taushi da kauri,wandon iyakarsa qauri,rigar ce ma mai dogon hannu,ya kauda ganinsa yana sanyo kansa cikin dakin,sai tahau raba idanu tana duban latifa dake jiran ya gama shigowa su gaisa ta basu waje,gabanta tana dan faduwa.

Gaidashi tayi ya amsa,sai ta juya ta nufi qofa,widad din batayi qasa a gwiwa ba tabi bayanta zata fice itama cikin jin tsoro

"Zo nan" ya kirata a hankali,saita waiwayo fuskarta a narke kamar zata saki kuka,ya kalli siraran labbanta jajaye data tabesu

"Bari na dauko hijabi na" ta sake fada tana sanya jelar dankwalinta tana faman boyon na shanunta da suka fara bayyana kansu ta cikin rigar jikinta.

Dariya taso bashi acan qasan zuciyarsa,ya fuskanci me take boyewa,ko me zasu sakashi ji wadannan qananun abubuwan oho,ya fada a ransa,saiya sanya hannu ya jawo hijabin da ya gani a gefansa ya miqa mata,kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki,tana ta faman cukuikuye gaban rigarta ta qaraso ta sanya hannu ta karba hijabin ta zura,sannan ya nuna mata waje ta zauna.
Chapter 48 · 0% Book details