← Book details A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 111

Sashe 34

A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Waye ma to a ciki?" Ta tambayi kanta,bata sani ba don haka ta tabe baki,cikin wannan d'arin d'arin nata da rashin sabo da maza ta saka kai ciki tare da yin sallama.

A lokacin kansa yana duqe a qasa,yanata trying number hafsat ce,wadda tunda ya taho basuyi waya ba,duk kiran da zaiyi sai ace masa is switched off.

A hankali ya daga kansa yana motsa labbansa tare da amsa mata sallamar,idanuwansa suka fada a kanta sanda take takowa kamar mai takatsantsan kada ta taka kwalba,baby face dinta dake tsakiyar blue black din hijab dinta ta fito fes,qananun gashinta masu santsi dake kwance gaban goshinta sun sake qawata fuskar,dan qaramin bakinta me red lips ta dan tsukeshi waje guda,fuskarta sam babu fara'a,sai ya lumshe idanuwansa kana ya maidasu qasa ga hannunsa inda wayarsa ke riqe,shidai baisan me hajiya ta hango ba data zabi ya auri qaramar yarinya har haka,kyau?....ko kuwa me hajiyan ta kalla?,shi kansa bai sani ba.

Tazarar wasu inches ta bayar a tsakaninsu ta ajjiye kwandon,tana daga tsugunne ta gaidashi da siririyar muryarta

"Ina kwana?"

"Kin tashi lafiya?" Ya amsa mata yana sake daga kanshi gareta a karo na biyu,bata amsa masa ba sai miqewa da tayi tsaye ta soma shirin ficewa a setting room din,saboda gaba daya a tsorace take,already ummu tayi mata horon tsoron maza sosai da shan inuwa daya dasu,a yanzun kuma bata gama sanin muhimmancin abbas din ba

Da kallo yabi bayanta,dariya ta taso masa can qasan ransa,ta yaya cikakkiyar budurwa mai shekaru da wayo ta aikata haka?,sai ya gyara zamansa kadan yana lalubo sunanta

"Widad" ya furta a tausashe,tsayawa tayi cak gabanta yana faduwa,dama yasan sunanta wai?,ta tambayi kanta

"Zo mana" ya sake fadi,abinda yasa ta waiwayo kenan,suna hada idanu duk wani kuzarinta yayi nasa waje,sai ta narke fuska

"Ummu zata yimin fada idan na dade" kai ya girgiza yana lumshe idanunsa kamar yadda yake a al'adarsa

"Ba zaki dade din ba,yanzun nan zaki tafi" kallonsa takeyi,sai ya jinjina mata kai alamun tabbatarwa,don haka ta dawo a hankali,ta samu nesa dashi ta zauna.

Tattara dukka hankalinsa yayi ya zuba mata idanu,yanzun ta ina zai fara mata bayani ma?da wanne harshe zai mata magana ta fahimci abinda yake cewa quruciya duk ta baibayeta?,a qa'ida babbar budurwa ce yanzun zaune a gabansa,sai yafi sanin yadda zai dinga handling abubuwa har su saba da juna.

Motsawa tayi kadan tana hade rai saboda yadda yake kallon nata ya sake takurata,ya fahimci haka sai ya aje wayar hannunsa,a bisa tilas ya arawa fuskarsa murmushi sannan ya fara magana

"Ummu ta gaya miki an daura miki aure ko?" Kai ta gyada tana kallonsa

"Good,daga yanzu na zama yayanki,na zama kuma abbanki,zamu tafi dake can zan kaiki gidana,zamu tafi tare,kema gidanki ne duka,zakiyi duk abinda kikeso a ciki,kina so?" Idanunta masu tsananin haske da ratsin gold color ta fara rarrabawa a tsakanin nasa idanun,sai ya kafeta da idanu sosai yana kallon yadda suke juyawa,yadda ta mele baki ta kuma tabe fuska hadi da lumshe idanunta,eye brows dinta masu tsayi suka hade waje guda sannan ta sake bude idanun warrrr a kansa yasa tsigar jikinsa ta zuba

"Bazan dade ba zaka dawo dani wajen ummu?" Ajiyar zuciya mai nauyi ya sake yana dan murmushi kadan

"In sha Allah,nima daga yau na zama yayanki ko?"

"Uncle dina dai ko?,naji nujood na cewa sunanka uncle abb...." Kasa qarasa sunan nashi tayi,tana jin kada tayi abinda bata kyauta ba,murmushi ya subuce masa ba tare da ya shirya ba,har fararen haqoransa suna bayyana,ya fuskanci nauyin kiran sunan nasa take

"Uhnnnn,uncle abbas" sai ta gyada kanta tana hade hannayenta waje guda,yakai duba ga hannun nata,tsararren jan lallen nan nata yana nan tas saman hannunta,ya zuba masa idanu kamar mai karnatar taswirar zane,lallai akwai hikima mai yawa ga masu yin lalle,har da suke iya tsara zane haka ya bada wani kala da nau'i mai kyau.

Rai ta hada sosai ganin yana ta kallon hannun nata, saita zare hannuwan nata zuwa cikin hijabin tana sake qudundunewa waje guda,ya dauke kansa yana maidawa ga dan qaramin leda yar mitsitsiya daya shigo da ita,sai ya dauka ya tura mata

"Wannan waya ce,ki cewa ummu a kunna miki,akwai komai a ciki,zan dinga kiranki,sauran kuma kudi ne,duk abinda kikeson siya ko kike son amfani dashi ki dauka a ciki,kada ki sake tambayar kowa yayi miki wani abu" murna farinciki da kuma mamakin bata waya da akayi ya lullubeta,to amma kuma tana tsoron kaiwa umnu kayan tace wani ne ya bata,duk yadda take zumudin wayar saita noqe

"Wallahi ummu zata dakeni,zatace waye ya bani" murmushin dole ya sake subuce masa

"Kice uncle abbas ne,idan ma bata yarda ba kice a kirani,bazata miki fada ba" sai ta matso kadan,ta dauki ledar tana cewa

"An gode,Allah ya saka da alheri" girma yaji addu'ar tayi masa,sai ya bita sa kallo kawai harta fice,ya maido dubansa cikin falon yana sauke gauron numfashi,tsahon zamansa da hafsa bata taba fadin haka ba,duk girman kyauta idan yayi mata

'An gode' shine iya abinda ta iya fade kenan,bata buqatar cin komai,so yake kawai yaga sun dauki hanyar bauchi,to amma babu dadi su kawo suga baici komai ba,gashi ya baro baqi a masauki,don haka ya fidda qaramin flask din tea dake cikin kayan,ya hada tea.

A gaggauce yake sipping,yana tsaka da kurba uncle muhsin yayi sallama

"Aah ya haka bakaci komai ba?" Ya fada bayan sun gama gaisawa yaga abbas na ajjiye cup din

"Sauri nake ne,ya kamata mu dauki hanya da wuri,saboda kamar gobe nakeson komawa kaduna,akwai gyare gyare da za'a yi acan,a office ma kuma ina da ayyuka da ban gama settling nasu ba bare na dora da nawa,ban taba aiki a kaduna ba sai wannan karon,kaga ina buqatar maida hankali na sauke nauyin al'umma dake kaina" kai muhsin ya jinjina

"Gaskiya ne,to shikenan,muje kayi sallama dasu saimu fita tare,zaka saukeni a al-hamsad tower zan shiga wani shago akwai abinda nakeson dubawa,zuwa azahar an kammala walima in sha Allah saiku wuce kafin la'asar"

Sai data gama nuqu nuqu da fargabar nunawa ummu kayan daya bata,da taga ba zata iya ba saita wuce sassan anty madina,ta sameta ta fito a wanka,don haka ta zauna cikinsu walid dake falo suna kallo harta gama shiryawa ta fito ta sameta

"Widad,har ya tafi baqon?" Kai ta gyada tana miqa mata ledar

"Wannan ya bani,sai da nace bazan karba ba ummu zatamin fada,yace wai ba zata min komai ba" dariya ta subucewa anty madina

"Taso nan" tace da ita bayan ta karba ledar,suka matsa gefe can inda yaran ba zasu jiyosu ba,zama tayi ta zaunar da ita a gefanta

"Shi wannan ai ba baqo bane yanzu,mijinki ne kin gane?,kamar ni da abban walid,kamar ummu da alhaji,kin gane?" Tadai jita,amma bata gane mai take nufi ba,ita kallon abban walid da anty madina takeyi a mazaunin yayanta ne,ummu kuma alhaji babanta ne

"Bari muga me miji ya baiwa matarsa kyautar farko?" Ta fada tana dariya,ta zazzage ledar,kwalin kyakkyawar waya qirar samsung ta fado hade da sabbin kudi a miqe fil dasu

"Lalalala,ah lallai wannan diya tamu da goshi take,tun yanzu?" Dariya ta kubcewa widad,haka kawia taji kunya ta kamata,saita sanya tafin hannunta ta rufe fuskarta anty madina na tayata dariyar

"Zankadi,bude idonki ki gani" saita bude idon da sauri,ba qarya wayar ta hadu,take taji murnarta ta qaru,qaunar wayar kuma ta shigeta,suna shirin kunnawa momma tayi sallama falon

"Wa'alaikumus salam,qaraso momma,duk sun cika falon" anty madina ta amsa tana qoqarin tattare kudaden waje guda

"Wannan sabbin kudi fa,ko na liqi ne da kikayi canji?,aisai ki adana abunki,bikin da babu ko kidan qwarya bare DJ,kamar wata amaryar buzuzu"

"Uhmmm,momma kenan" anty madina ta fada tana dariyar yaqe

"Albarkar aure ai ake nema,bare widad ma nawa take?,ina qawayen ma bare ace za'a zauna yi mata irin wannan bidi'ar?,ni ban canzo kudin komai bama,angonta ne ya bata hade da wayar?" Sai a sannan idanunta yakai kan wayar

"Kai!" Ta fada cikin ranta,tasan wayar fes,irin wayar da deena tace yallabai(mijinta) ya kawo mata tsarabarta ne daga india a wannan satin daya dawo daga course daga can

"Tofa,da gamo da kasawa,kada fa muna nan mun shanya baki muna kallonta yarinya qarama amma ace har tasan komai,kodai ta bada wani abune aka bata wannan tukuicin haka?" Momma din ta fada tana kama baki, zuciyarta cike fal da qyashi da baqinciki,don ko yanzu data baro sassanta maganar da suka gama kenan da batulu matar babanta da 'yan uwanta da basu tafi ba,duka dai akan widad din,suna ganin komai anyi mata fiye dana 'yan uwanta,ana kuma wuce makadi da rawa a kanta saboda tana da daurin gindin ummu,sun manta kowanne aure da irin nasa nasabin yake zuwa,labarin lefe data samu,manyan mutanen da suka halarci daurin auren da kuma kayan da aketa hadawa za'a tafi jere dasu kawai sukeyi,banbamcin da ake nuna mata akan nasu 'ya'yan yayi yawa.

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K'AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 90 16 59 91

*Zafafa biyar kadai keda sinqin nau'ikan kalar labarun da kukafiso jimilla a lokaci guda*🤝😄

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks: Huguma*

Page 31

Maganar ta qonawa anty madina rai sosai ta kuma bata haushi,sannan sai taji.maganar kamar tayi girma a kunnen widad,tana girmama dukka faccalolin nata saboda dukkansu sun girmeta,ita kadaice qarama a cikinsu,shi yasa take musu kallon yayunta,don haka ta tattara wayar da kudin ba tare data gama saita wayar ba ta miqawa widad

"Kaiwa ummu ta gani ta adana miki,anjima zan shigo saina qarasa gyara miki" karban kayanta tayi ba tare data ma fahimci maganar me momma takeyi ba,ko baqincikin dake manne a ranta ba ta qara gaba cikin doki da zumudi.

Da kallo momma ta bita sannan ta tabe baki

"Kinga yarinya sai rawar kai take,Allah yasa bai lasa mata zuma a baki ba ya barmu da....."

"Kai.....kai momma" anty madina ta fada tana kama kai fuskarta na nuna zallar rashin jin dadi

"Wannan maganganun sunyi girma da yawa fa"
Chapter 34 · 0% Book details