← Book details A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 111

Sashe 65

A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kaine fa ka bani tsoro" dariya taso bashi amma ya dake,saiya langabe kai kamar yadda yaga tayi

"Banda ke banga wadda take tsoron mijinta ba" kamar ya tunzurata,don batason kalmar miji,sai ta fara qoqarin zame hannnunta daga cikin nashi

"Ni ba mijina bane kai"

"To waye ni?" Ya tambayeta yana dage girarsa sama

"Uncle" kai ya girgiza kawai yana sake sakin boyayyen murmushi

"Riqe uncle dinki,banaso,let me treat your wound first" ya fada yana sake kamo hannunta.

Kujera ya saka mata ta zauna akai,sannan shima ya jawo wata ya zauna,har gwiwoyinsu suna haduwa da juna,ya bude first aid kit din ya fada wanke jinin,yana yi tana rintse idanu,ya daga idanunsa ya kalleta,idanuwansu suka hadu waje daya,sai taji hakan ya mata nauyi sosai,ta kauda nata idanun numfashin su yana gauraya da juna.

Har ya gama mata babu wanda ya sake cewa komai,ya sakar mata hannun yana hade kayan waje daya

"Jibi idan Allah ya kaimu zanje bauchi" kallonsa tayi da sauri,hakanan kwanakin nan sai ta dinga jin batason zuwa garin

"Zanje nayi one week,zamu taho da hajiya,the next day zamu wuce umara ni da ita in sha Allah" zuwan da yace hajiyan zatayi taji yayi mata dadi,har zumudinta ya bayyana a fili

"Amma wata daya ya kamata tayi,ko ka dawo da ita nan kawai" ta fada tana langabar da kanta,cak ya tsaya yana kallonta,yaji mamakin jin furucin daga bakinta,abinda bai taba ji daga bakin hafsat ba tsahon zamansu da ita

"Hajiya ba zata zauna ba" ya amsa mata yana miqewa riqe da kit din.

Koda ya dawo sai ya fara rolling hannun rigarsa zuwa sama,tana daga zaune tana kallonsa har ya gama,idanuwanta suka sauka kan lallausar gargasar dake lullube da hannunsa,abar da take yawan burgeta ba tare da tasan dalilin ko kuma amfaninta

"tell me what you are cooking sai na qarasa" idanu ta narke

"Zan iya qarasawa uncle,don't spoil it" girarsa ya daga ya watsa hannayensa

"I will finished it anyway idan ma baki gayamin ba" ya fada yana qarasawa,ya bubbada tukwanen

"Kin kusa gamawa ai" ya fada ba tare daya juyo ba,yana mamakin qoqarin da tayi,kai ta gyada masa.

A nutse yake ci gaba da aikin,har ya kammala,duk inda ya motsa idanunta suna biye dashi,yana ankare da ita amma bai nuna ya ganta ba,har ya kammala,zata karba gyara kitchen din shima ya hada ya gyara komai,mamakinsa sake cikata yakeyi kullum,shi kam baya jin aiki ne?.

************Tana nade saman kujerar falon,tayi lamo kamar 'yar magen data samu waje mai laushi,sanye take da atamfa dinkin riga da skert na atamfa,ta yane saman kanta da dankwalin atamfar,jikinta na fitar da tattausan qamshin turarenta,daga gaba kadan kujerar ta uku daga gefanta,abbas ne a tsaye yana qarasa zuge jakarsa ta tafiya,yanayi yana amsa waya daga office,har ya kammala,ya kashe wayar ya sanyata a aljihu,ya dauki jakar ya rataya a kafadarsa.

Sai a sannan ya waiwayo inda take zaunen,yadan zuba mata idanu yana karantar yanayin fuskarta,duk sanda zayaje bauchi indai bada ita bane sai yaga wannan damuwar a tare da ita,saidai a wannan karon damuwar kamar tafi ta kowanne lokaci.

Yadda tayin kamar wata marainiya ya bashi tausayi da kuma dariya,ya taka a hankali ya tsaya a gabanta,ya miqa mata dogayen lausasan hannunsa.

Hannun tabi da kallo kafin ta mayar saman fuskarsa dake dauke da wani irin haiba da wani sirritaccen kyau da ba kasafai kake iya hangensa farat daya a fuskarsa ba,har cikin zuciyarta takejin wani iri babu dadi,saboda wannan ne karon farko da zaije yayi sati daya,kwana biyu rak yake ya dawo duk sanda ya tafin,idan da itane ma suke kwana uku.

Sake miqa mata hannun yayi,saita noqe hannun nata tana lumshe idanunta hadi da kwantar da kanta tsakanin cinyoyinta.

Murmushi ne mai sauti ya kubce masa,cikin taushin murya yace

"Get up,tashi muyi sallama" curewa tayi waje daya,saita saki kuka kawai

"Ya rabb"ya furta yana sauke jakarsa daga kafadarsa ya ajjiyeta a qasa,sannan ya duqa saman gwiwarsa a gabansa

"Na gayawa hajiyane baki barni inje na daukota ba?,ko na gayawa maman mimi baki amince naje muyi sallama ba?" Furta sunan mommy hafsat da yayi ya sakata zabura,ta kuma daga kanta da sauri,sunanta kawai na sanya gabanta faduwa,hajiya kuwa tana jin nauyi da kuma kunyarta fiye da yadda baki zai furta,dukkansu babu wanda zataso ya gayawa abinda yace zai gaya musun.

Kai ta girgiza masa da sauri,ya lumshe idanunsa ya kuma budesu duka a tare

"Wipe your tears" hannu biyu tasa ta goge hawayen yana kallonta, cikin ransa yana jin wani irin yanayi daya gaza tantance wanne iri ne,a yau apart from hajiyansa,yau ga wata halitta dake amsa sunan matarsa tana jin babu dadi wai don zaiyi nesa da ita,a wajen mutum guda yake ganin hakan..... hajiyan sa,babu na biyun sai a yanxun da yake gani daga wajenta.

Sai daya hilaceta ta dan saki jiki,sannan ya miqe ya dauki luggage dinsa yayi mata sallama ya fice,tana tsaye a jikin window har motarsu ta tashi suka fice daga gidan.

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K'AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Page 59

Ranar gaba daya wunin falo tayi,tayi kwance cikin kujera ta kasa hasala komai,,haka kawai take jinta wani sukuku,jikinta duka babu dadi,sai bayan sallar la'asar tana kwance kiran anty deena ya shigo

"Lafiya kike?" Ta tambayeta jin muryarta tayi qasa da yawa,sai ta kama mata hawaye kafin daga qarshe ta gaya mata ya tafi bauchi ya barta ne,abun ya baiwa anty deena dariya,wohoho...... widad har yanzu quruciyar dai tana nan,sai data bata baki sannan tayi mata zancan da yasa ta kirata

"Akwai watsapp groups da za'a saki,inason kowanne idan an sakaki ki tsaya kibi duk hirarrakinsu kinji ko?,akwai qaruwa sosai qanwata"

"To anty" ta fada tana gyada kai,sun jima da anty deena din suna hira,sai data debe mata kewa sosai sannan sukayi sallama.

Washegari haka ta tashi jikinta babu qwari har ta gama shirin makaranta,bayan kowanne minti daya saita kallin dukka wajen da yafi zama ko tsaiwa,sai taji hawaye sun cika mata idanu,tasa hannu ta share da sauri,sannan ta dauki school bag dinta zata fice a dakin,qarar wayarta ya dakatar da ita,ta waiwaya ga inda ta ajjiye wayar saman madubinta,ta koma ta zuba mata ido tana kallon number wayar,sai kuma ta miqa hannu ta dauka.

Lallausar muryarsa ta bayyana cikin wayar,gaba daya kamar wadda aka bigewa gwiwoyinta haka taji,ta koma da baya ta zauna tana qoqarin amsa sallamar tasa,yana jin sautin muryarta ya saki boyayyen murmushi

"Ina kwana?" Ta gaisheshi muryarta na rawa

"Kin tashi lafiya?"

"Lafiya qalau" shuru yadan ratsa sai yace

"Baki kirani kinji yadda na sauka ba,tsakani da Allah ba amana,ni ina nan ina tunaninki" wata irin kunya ce ta saukar mata,har taji kamar gata a gabansa,saita saki murmushi tana qunshe fuska

"Kayi haquri" ta samu kanta da fada,don ko kadan ta kirashin baizo kanta ba,hasalima ita batace ga number dinsa ba

"Yayi kyau,yanzu me kikeyi?"

"Makaranta" ta bashi amsa a taqaice,daga nan inda yake ya kalli agogon dake gefansa

"To a dawo lafiya"

"Allah yasa" ta fada cikin dan karsashin data samu

"Babu komai ko?" Shuru ta danyi,da kamar tace masa gidan babu dadi,kamar tace masa jiya da qyar tayi bacci,kamar tace masa ya dawo don Allah,amma kuma saita kasa ta amsa masa da babu,sukayi sallama ta kashe wayar ta barta saman gado sannan ta fito ta cimma driver suka bar gidan,tana jin ta samu wani karsashi Cikin jiki da zuciyarta.

Wayar yabi da kallo bayan sunyi sallama ya kashe wayar,hafsat data fito daga wanka tayi zaune gaban madubi tana shafa jambakin dole ta sake binsa da kallo ta cikin mudubin,tunda ya fara wayar gaba daya ta tattara hankalinsa a kansa,kusan wannan dabi'arta ce,tanaso ta cinye amma ta kasa,tadan gyara zamanta tana matso jambakin ba tare data shafa ba tace

"Dawa kake waya ne?" Kansa ya daga yana kallon fuskarta ta cikin mudubin,maimakon ya maida kai ga amsa tambayarta,sai duka tunaninsa suka koma daren jiya tsakanin shi da ita

"Hasbunallah" ya furta qasan ransa,bacin ranta ya motsa masa amma sai ya kori shaidan

"Wanka kikayi?" Ya mata tambayar data bata mamaki,a mamakance ta amsa masa

"Eh,baka gani ba?" Kai ya jinjina

"I see,but.....zo muje in nuna miki wani abu" ya fada yana yaye lallausan duvet dinsa sabo fil da dole ta sanyashi daukoshi,saboda yazo ya tarar da nashi anci ubansa,tun kafin yayi magana ma tace masa nawwara ce,haka ya tattarashi a daren ya bawa mai gadinsu yace ya yar,shi kuwa ya kaishi baya cikin murna ya jiqashi zai wanke,saidai shi dinma yana wankewar yana tsinewa qazantar hafsatun a ranshi,saboda wani irin gamayyar hadakar dauda ne a jiki harma da guntun kashi dana fitsari.

Kai tsaye ya shige bandakin,ta ajjiye jambakin ta bishi da kallo,itafa ba wannan takeso ba,bai amsa mata tambayar ta ba,abun yayi mata tsaye a rai tunda taji suna waya da yarinyar,abinda bata taba ji yayi da ita ba,to amma kuma dole ta lallaba a yanzun,bataso suyi tashin hankali,kada ta barar da umrarta,don tunda taji labarin tafiya umarar ranta ya raya mata harda ita a ciki,qilan bai fada mata bane,saboda ya saba,yana da wani irin miskilanci da shan qamshi ta wannan bangaren,ba kasafai idan zai maka abu yake gaya maka ba,har sai dab da faruwar abun,dole ta miqe ta bishi bandakin,zuciyarta nq raya mata dole ta kira yarinyar tabi ba'asi,ta kuma sake kada mata warning,dama ranta a bace yake tunda taga yazo babu ita,don ta hada himilin qazantarta,mai wankinsu ya gudu amma yace mata yana qauyensu,tana ta jira fa taji wayam,dole ta tattara duk wasu tarkacen kayayyakinta takaisu store din bayan gidan ta kulle saboda abbas din,ta tabbatar idan ya gani sai yayi fada,ita batasan uwar daya sanya yanzun sai yayi zuwa biyu baizo da ita ba,ko a yanzun wannan kusan zuwasa na biyun kenan,idan ta bigi cikinsa sai yace mata makarantar ya sanya haka.
Chapter 65 · 0% Book details