← Book details A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 111

Sashe 54

A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hannu yasa zai karba,yadda tayin yana burgeshi,duk da abub mamaki bane,duba da gidan data fito,muhsin kadai ya ishi a shaidesu,don ko cikin abokansu daban yake,wani abune da zai iya cewa baisan lokaci na qarshe da hafsat tayi masa ba wai don zata bashi abu.

Sakin ruwan tayi da sauri sanda hannunsa ya sauka akan nata,jikinta ya dauki rawa,taja da baya tana yarfe hannu jikinta yana rawa,hawaye na shirin tarar mata a ido,shi bai kula bama,don ya duqa zai dauke ruwan bayan ya furta

"Subhanallah" sanda ya dago harta samu waje ta rakube,ya bita da kallo yana mamakin yadda take matuqar tsoron tarayya dashi,kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa,ya bude gorar ruwan ya fara sha,sannan ya miqe yana cewa

"Zanje sallah,idan na dawo zaki shiga ciki ku gaisa da mutanen gidan,ga abinci nan a leda ki dauki naki" kai ta gyada masa gabanta na faduwa,bata samu nutsuwa ba har sai da yayi alwalar ya fice,ta bishi da kallo tana hararar hanya qwalla na gangaro mata,yanzu idan ummu ko mommy suka ga wannan abun da yakeyi fa?.

A falo ya tsaya jiranta,ta fito yafe da mayafin abayar bayan ta cire hijabin da tayi sallar dashi

"Koma ki samo babban mayafi,akwai mutane a waje" yayi maganar sanda yake dage labulen falon yana sake duba farfajiyar gidan,jikinta ta kalla,itadai bataga wani aibu a haka ba,amma sai batace komai ba ta koma ta lalubo mayafi cikin kayanta ta fito,suka jera zuwa cikin gidan.

Babban gini ne,don yadan fi nasu girma da kayan alatu,sanda ta shiga ta samu matar gidan a falo,ta karbeta da fara'a,saidai tunda ta gaidata ta rasa me zata cemata.

"Ban gane fuskar taki ba,ko kanwar amaryar abbas ce?" Qas tayi da kanta tana jin nauyi yana kamata,saita girgiza kai alamun a'ah

"Ko amaryar ce da kanta?" Saita daga kai alamun eh,matar ta maida kanta sosai tana kallon widad din sosai,abbas data sani,abbas dake da.babbar mace kamar hafsat yaje ya auro wannan qwailar?,lallai Allah mai iko,sau tari mazan da suka fiya izza da kuma jin kansu daga qarshe haka suke qarewa,har gwara wannan din,kyakkyawa ce data amsa sunanta,komai nata mai ban sha'awa da daukan hankali,nan gaba kadan idan ta ida zama cikakkiyar mace lallai ba shakka sai an kalleta an qara,dole hankalin hafsat din ya tashi,amma a fili sai tace da ita

"Ma sha Allah,Allah ya bada zama lafiya kinji amarya" bata iya amsa mata ba,sai shuru data sakeyi kawai kanta a qasa,gaba daya bata jinta a sake,tun asali dama ita din bamai saurin sabo bace,tana da wuyar sakewa da baqin fuska,don haka bata wani jima ba ta miqe tace zata tafi

"To ina zuwa" ta fadi tana miqewa ta shige ciki,ranta da zuciyarta fal mamaki,ba jimawa ta fito da wasu kayan barci set uku ta bata,hannu biyu widad ta saka ta karba sannan ta fito.

A inda ta barshi ta sameshi,ya sake mata jagora suka koma ciki,tana ta kallon gate,ji take kaman ta fita ta miqe qafarta,suna shiga falon ta miqa masa kayan kamar yadda takewa ummu a gida idan an mata kyautar abu

"Gashi" ta fada tana ajjiye masa kusa dashi,dai dai lokacin da ledar ta zame,matan dake jikin takardar sanye da irin kayan baccin dake cikin ledar suka fito.

Kusan tare suka dauke idanunsu shi da ita,taja baya da sauri qafafunta na sarqewa zata wuce ciki

"Zonan" yayi kiranta yana karantarta,da baya da baya ta dawo,ita a lallai ba zata iya kallonsa ba,har abun yaso bashi dariya,ya dake da yanayin dakiyarsa da kuma miskilancinsa

"Dauke abinki ki tafi dasu"

"Banaso" ta fada kai tsaye tana maqale kafada,a mamakance yake kallonta

"Bake ta bawa ba?"

"Ni ta bawa,amma banaso,bana saka irinsu" dariyar da yaketa riqewa ta subuce masa,amma saita fita ta sigar murmushi

"Zauna" yace da ita yanata kokawa da dariyar tasa,ta baya ta zauna har yanzu taqi yarda su hada ido dashi.

"kinsan amfanin wadan nan kayan?" Fuska ta qara daurewa,tana sake tabbatarwa basu hada ido ba,kai ta girgixa masa ba tare da tayi magana ba

"Oya....open your mouth,ban jiki ba"

"Ban sani ba,kayan 'yan iska ne fa" tayi maganar tana narke fuska,kamar zata saki kuka.

Wannan karon duk yadda yaso boye dariyarsa sai data fidda sauti,yayi qoqarin daidaita kansa,da gaske ta jahilci aure,da alama aiki je jajur a gabansa a kanta,bai tsawwala sai ya samu komai daga gareta ba,amma aqalla ta gama sanin meye auren kansa,don da alama batasan meye shi ba.

"Kwashesu ki tafi" ya bata umarni a taqaice,ta baya ta zuro hannunta ta jawo ledar zuwa gabanta,sannan ta miqe da sauri sauri tayi dakinta.

Tana shiga ta jefa ledar saman sofa bed tana zumbura baki kamar zata fashe,ledar ta qarasa yayewa kayan suka fito sosai,bata gama kula da hotunan jiki bama sai yanzu,ta qarasa tana daga kayan saita jefar zuciyarta a a cushe

"Lallai matar nan ma 'yar iska ce ashe itama,don me zata bata wadan nan kayan?" Hadasu tayi ta cukuikuye ta jefa cikin sif,ta koma saman gado ta lafe a cikin bargo abinta,idanunta ta rufe,tana fata bacci ya dauketa tun tana iya jin motsinsa,basai waje yayi shuru ba.

°°°°°°°°°Washegari ma haka ya fita,bai tsaya yin breakfast ba,yauma ita dinma kamar jiya,bayan ta gama 'yan gyare gyarenta da zata iya,saita dawo bakin window din falon ta zauna,lokaci lokaci tana yaye labulen tana leqa farfajiyar gidan,abinda ya tayata zama kenan,duk da yace mata tana iya shiga cikin gidan ta zauna a can,kota debe kewa,amma kasancewarta mara saurin sabo taji gwara tayi zamanta a nan har zuwa sanda ya dawo gida.

To tsahon kwanaki biyar kusan haka rayuwar ta dinga gara musu,da safe idan zaya fita aiki zai sameta ne a falo,sabida yafi dakinta haske,zatayi masa a dawo lafiya bayan ta gaidashi,ya ajiye mata kudi ya kuma tambayeta bata da matsala,sannan ya mata sallama,takan bishi da idanu tana jin kamar ta bishi,wani lokacin yana ankare da ita,wani zubin hankalinsa yayi gaba,zata gyara dakinta data fara sabawa dashi,ta gyara falo ta goge shi tasa,duk da cewa tana daukan lokaci kafin ta gama,amma yana kintsuwa,kyan sharar nata da gyaran nata yake gani,saboda tafi hafsat nesa ba kusa ba, at least ita bata barin qura ko datti,sabanin hafsat din da ko ina a birkice yake,duk da suna da komai a store,to amma bata taba dora girki ba,yana sawa a kawo mata abinci,idan ya dawo tana cikin falon,amma wata qurya ta daban,a can zata zauna ba um ba um um,tana kallonsa kawai,duk da tana buqatar hira da wanda zatayi hira dashi,sai idan yaga tana gyangyadi kota gaji zai rakata ta kwanta ya dawo falo yaci gaba da sabgoginsa kafin ya tattara shima ya wuce nasa dakin.

Duk sanda tsautsayi yasa ta farka cikin dare kuwa da qyar da sudin goshi take komawa baccin,saboda dan banzan tsoro,a rayuwarta bata taba kwana daki ita daya ba sai a wannan karon.

Bangaren hafsat kuwa kullum a rana saita kirata,ta tambayeta me ya faru a jiya,me yake faruwa a yanxu,amsa kawai take buqata,tana ji zata katse wayarta,saidai idan weedad dince tabi bayan kiran tace a bata su mimi.

Zuwa sannan fa fara jin dadin wayarta,da kanta da kanta ta koyi yadda ake sarrafa abubuwa da dama a cikinta,ta dauko games kala kala da suke debe mata kewa sosai,wannan yasa dogon wunin kadaicin da takeyi ya ragu sosai.

_wannan kenan_

*Arewabooks:Huguma*

KI KULANI miss xoxo

DAUDAR GORA Billynabdul

RUMBUN K'AYA hafsat rano

IDON NERA Mamuhghee

A RUBUCE TAKE huguma

_sinkin labaran dake dauke da dukkan wasu nau'ikan salo da kuke so_

_masoya ku biya kudinku ta wannan hanyoyin_

0022419171
Maryam sani
Access bank

Saiku tura shaidar biya ga
+234 903 318 1070

*Masu katin waya ko VTU zaku tura ta nan*
09166221261

*Al'ummar nijer🇳🇪🇳🇪🇳🇪 zaku tuntubi wannan number*
+227 96 09 67 63

*Thanks for choosing us*🔥🔥🔥🔥🔥🔥

*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)

Page 49

Awanni kusan hudu kenan tana abu guda,baya ga kitchen din data yiwa kaca kaca kota ina,kamar wadda ke girkin mutum ashirin,sannan daga bisani ta samu ta kammala tuwon shinkafa miyar kubewa iya yadda taga latifa tana yi,ta zuba cikin sabbin warmer masu kyau da aka hado cikin siyayyar cefanen da aka kawosu jiya.

Dafe bayanta tayi bayan ta kammala gyare kitchen din

"Shi tuwo dama haka yake da wahala?"ta fada tana yatsina fuska,duk da can qasan ranta farinciki ne fal,wai yau itace da yin girki cikin kitchen dinta,ba kwaba ba hantara babu bakiyi dai dai ba,ta juya ta soma diban warmers din takai saman dining,ta jeresu da kyau,tana kallonsu tana murmushi,har cikin ranta dadi take ji idan ta tuna wai yau ance tayi girki.

Dakinta ta koma tayi wanka,ta shafa powder a kyakkyawan fuskarta mai santsi da sheqi dauke da tambari na quruciya,dubai abaya wine color da tasha adon duwatsu masu walwali ta fidda ta sanya,ta daura dankwalin saman kanta,ta kuma shafa turarukanta kamar yadda ya taba gwada mata yadda ake sanyasu,tun daga ranar kuwa ta dauke tsaf,yadda ya kwatanta matan haka take sakawa,ita kanta sai taji tafi jin dadinsu.

Sosai abayan ta haska jar fatarta,kamanninta suka fito sak na ainihin tushen yankin data fito,ta koma gefan gadonta bayan ta dauko wayarta dake saman madubi,ta bude ta shiga wata game da taketa daukan hankalinta ta fara bugawa cikin qwarewa.

Hankalinta yayi nisa sosai a game din,har bataji qarar motarsa zuwa shigowarsa cikin gidan ya kuma tura qofar dakinta ba,sai ya tsaya riqe da handle din qofar dakin,zai iya lissafa adadin shigowarsa dakin,idanunsa saman fuskarta,tattausan siraran labbanta sunata qyallin lips balm,tana ta juyi saman gadon,duk sanda taci game din sai tayi dan tsalle kadan na murna sannan taci gaba.

Idanunsa ya dauke sannan yayi gyaran murya kadan ya hada da sallama,daga idonta tayi daga kan wayar zuwa kansa,saita aje wayar gefanta tana masa sannu da zuwa,sannan a dabarance tana laluba maballan gaban rigarta taji sun rufu da kyau?,ta kuma tsareshi sosai da ido taga ko.yana kallonta?.

Sarai yaga abinda takeyi,amma sai ya kauda kai ba tare da yakai idanuwansa kan qirjin nata da yake ganin basu da maraba da qirgar dangi a wajensa ba

"Tare da baqo nake,ki kawo abincin" kai ta gyada masa,ya saki handle din qofar ya juya zuwa falon,yana duba wayarsa daketa ringing.
Chapter 54 · 0% Book details