← Book details A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 111

Sashe 26

A Rubuce Take Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Yauwa alhmdlh,ga mai gidanta nan ma ya fito,mun dauka ai baka nan shi yasa tun dazu bamu yimaka magana ba" dukka idanu suka waiwayo suka zuba masa,take yaji ya muzanta,ya aro jarumta da juriya ya qaraso wajen yana riqe da hannun mimi,wadda tunda ta ganshi ta sheqo da gudu ta maqale ubanta.

Qarawa yayi ya miqa hafsa din ita yana cewa

"Wuce gida" saboda ganinta cikin mazan ba qaramin quntata masa rai yayi ba,ga kuma baqincikin tahowar da tayi babu izini ko shawara dashi.

"Alhaji kayi haquri,amma babu inda zata saita cikamin kudina,zata gane ni din matsiyaci ne na ainihi" fuska a daure abbas ya juya yana dubansa

"Kaga,barta ta tafi,za'a biyaka koma nawa ne"

"To shikenan alhaji" sai daya tabbatar ta shiga gida ita da kayanta sannan ya juyo ga mutumin

"Me ya faru?" Gyara tsaiwarsa yayi yana sake riqe qugunsa

"Tun daga tashar kawo na daukota alhaji ita kadai qwallin qwal da sunan shata tayi,mukayi ciniki ita akan dubu sha biyar,sai da mukazo nann sannann zata hadani da dubu goma,wai nayi haquri bata da kudi,kudinta basu kai ba" cikin matuqar bacin rai ya fara laluba aljihunsa

"nawa ne cikon kudin naka?"

"Dubu biyar ne ranka ya dade" mai motar ya fada cikin matuqar jin dadi ganin hakkinsa zai fiti,sai ya irga ya miqa masa,yasa hannu ya amshe yana godiya,ya juya yana komawa motarsa

"Lamarin mata sai haquri,tun dazu muketa qoqarin raba rigimar mu bashi kudin amma taqi saurararmu,Allah dai ya kyauta" maqotan nashi suka fada,gaba daga kunya ta gama baibayeshi,kamar shi matarsa tana fada dame mota akan cikon dubu biyar,bayason tsaiwa bare suja wata doguwar magana,duk da sunyi qoqari kuma alkhairi sukayi masa,sai ya basu hannu sukayi musabaha yana musu godiya,ya juya ya shige cikin gidan,xuciyarsa da rayuwarsa na wani irin quntata,wannan wanne irin kwance zani ne a kasuwa tayi masa?,me ma takeyi a bauchi?,wa ya bata ikon tahowa?,da wadan nan tambayoyin ya saka kai cikin gidan,kai tsaye ya zarce sassanta.

Yana sallama cikin falon su mimi suka taho da gudu suka rungume qafafunsa,ya duqa ya daukesu gaba dayansu yana musu oyoyo,ba tare da ya zauna ba yake qarewa falon kallo,bata a ciki,saidai kayansu da suka taho dasu watse a falon,yawan kayan ya tabbatar masa gaba daya kayansu ta debo daga can,ya jinjina kai ya sauke yaran yana kunna musu tv

"Ku kalli cartoon ina zuwa" ya fadi yana shafa kansu,mimi dake da wayo ta gyada kai ya wuce ciki.

Daya shiga tana toilet,don yaji motsin ruwa,sai ya harde hannayensa a qirji ya jingina da jikin madubinta yana qarewa dakin kallo,a hargitse dakin yake,babu kintsi kwata kwata,da alama tun sanda zasu tafi kadunan haka ta barshi.

Tana motsa qofar ya mayar da dubansa kai,sai gata ta fito da alama alwala ta daura,ko sallar la'asar dinma bata samu yi ba kenan,suna hada idanu ta daure fuskarta da kyau,batason ta karaya ko yayi mata kwarjinin da zata kasa fadin maganganun dake cikinta,ta dauke kai kamar bata ganshi ba tana nufar inda abun sallarta yake a watse a qasa zata dauka

"Yaushe kika nemi izinina da har kika baro kaduna kika taho bauchi?" Dagowa tayi,tanason dubansa kai tsaye amma tasan tayi qarya,a kaikaice take duban gefansa

"Saina nema izininka?,tunda bani da amfani ai ya kamata na shaida hakan,na baka waje,mutumin da bashi da kimar da za'a bashi sabuwar mota kaga wacce daraja gareshi?" Idanunsa ya lumshe yana ambatar sunan Allah,wani abu ya tsaye masa a wuya,tabbas inda shi madokin mata ne yau din nan sai ya tsitsinkawa hafsa mari,banda tsabar hauka a yanayin da ake ciki na matsalar tsaro da aka fara fuskanta tana matar ASP zata debo yara har guda biyu su kamo hanya ita kadai?,sannan duka ba tare da wata hujja mai qarfi ba illa dai kawai yaqi canza mata mota?.

"Kinsan abinda kikeyi kuwa?" Ya fada bayan ya bude idanunsa yana dubanta

"Na sani mana" ta amsa shi kanta tsaye,sannan ta dora

"Ai babu dole,yadda ban maka dole ba nima bazakamin ba,kowa yayi abinda ransa yakeso,Kaduna ne bazan zauna ba,ka nemo wadda zata zauna da kai cikin wadanda kake baiwa kyautar" sosai maganar ta dakeshi,wani bacin rai ya lullubeshi,ya bude bakinsa a zafafe mimi ta turo qofar riqe da.hannun nawwara,dole ya hadiye abinda ke taso masan,sannan yabar jikin madubin yana dosar qofa

"Hakane,kiyi abinda ranki yakeso,nima zanyi abinda raina yakeso,zan baki mamaki tabbas wannan karon hafsa kamar yadda nasha fada,zan kuma nemo mai zama dani din" daga haka ya fice ba tare da yaja mata qofar ba.

Da kallo ta bishi,haka kawai cikin jikinta taji jikinta yayi sanyi,yadda yayi maganar kamar he's serious,amma kuma data tuna ya saba fada dama sai ta tabe baki kawai,tasan ya fada ne kawai saboda yayi mata barazana,don haka ta karkade abun sallarta ta shimfida tana cewa

"Mu bawa juna mamaki dai" ta sanya hijabinta ta tayar da sallar.

Sanda ta idar yaran nata mata rigimar yunwa

"Ba uban da zai sakani wani shiga kitchen na kwaso gajiya" saita laluba jakarta ta fito da biscuit da lemon roba guda daya ta miqa musu,maimakin ta tashi ta gyara koda dakin nata ne daya cika da shara da qura,sai ta koma saman gadonta ta miqe abinta,ta dauki wayarta ta fara chart.

Hankalinta kwance take chart dinta,yaran nata basu qoshi bama babu wanda ta kula,ba jimawa kira ya shigo wayarta,data duba sai taga yayarta ce,ta gyara kwanciyarta tana saka wayar a kunnenta.

Bayan sun gaisa take ce mata

"Ana hada gudunmawar bikin nafisatu ne,nace bari nayi miki magana,don an kusa gama hadawa" take ranta ya baci fara'arta ta janye,bata qaunar abinda zai sanyata fidda kudi,itafa abu indai ba abbas bane zaiyi mata shi to ta gwammace ta haqura da yinsa koda ita zata amfana,a yanzun kuwa da suketa uwaka ubaka dashi ba zata ma dosheshi da wata buqata ba,da sai ta lallaba ta karba wajensa,ta zabge rabi ta basu rabi

"Nifa gaskiya anty shamsiyya bani da kudi" takaici da haushi ya kamata,suna ganin yanzun mijin hafsatun ya fara danshi danshi amma ko daya yarinyar bata banbaruwa

"Ke dama kullum cikin babu kike,to ba kyauta nace ki bani ba,contribution ne na biki,idan zaki bayar ki bayar,idan baki bayarwa ki fada ki daina batan lokaci" murya a cunkushe tace

"Nawa ne kudin?"

"Dubu goma goma ce ba wani kayan gabas ba,kuma ko atika da bata da wani qarfi tuni ta bada nata"

"Shikenan zanyi shawara,zan kiraki idan sun samu" bata amsa mata ba ta kashe kiran,hafsa taja tsaki tana gyara kwanciyarta,gaba daya sunbi sun dameta ba gaira ba dalili.
*H U G U M A*

*_A RUBUCE TAKE_*
(K'addarata)
*Arewabooks:Huguma*

Page 24

Kai kawo ya dinga yi cikin dakin,ransa na masa suya,me zaiyi ya huce takaicin hafsa?,yasan dai tabbas bazai qyaleta ba,anzo gabar da dole ya koya mata lesson kamar yadda yasha fada.

Idanunsa suka sauka akan wayarsa,sai ya jawota da hanzari ya fara kiran layin hajiya,bugu biyu ta daga

"Abbas ya akayi?" Ta tambayeshi da mamaki,ganin bai wani jima da barin gidan ba,qoqarin dai daita muryarsa yayi,don bayason ta fuskanci akwai wata matsala ne ta tashi hankalinta

"Lafiya lau hajiya,cewa nayi zai yiwu a gabatar da neman auren cikin satin nan?" Kai ta jinjina cike da mamaki,anya babu walakin goro a miya?

"Eh to,saidai na nema kawunnanka naji"

"Idan zaiyuwu hajiya kawai ayi,na shirya" tana saurin gano damuwa da kuma fushinsa,yadda yayi maganar a jikinta taji akwai damuwa,amma zata tambayeshi a hankali

"Shikenan,zanyi magana dasu,duk yadda ake ciki zaka ji"

"To hajiya na gode,gobe da yamma zan wuce,zan shigo ta nan kafin na wuce din in sha Allah"

"To ba damuwa,Allah yakai mana rai" daga haka sukayi sallama.

Cikin mamaki take sauke wayar,saidai kuma ta samu kanta da sakin murmushi tare da fadin

"Alhamdulillah" zuciyarta na gaya mata wataqila akwai alkhairi mai tarin yawa a abun,shi yasa Allah ya kawo komai a kurkusa haka ya sauqaqe matsala da damuwa.

"Tofa,ta samu kenan hajiya?" Faccalarta da suke tare a falon,ita da yayar abbas din mai suna mabruka suna hira ta fadi,wayar ta ajjiye gefe tana cewa

"Aure ne ya tasowa danki" da mamaki ta kalleta

"D'ana,wa kenan?"

"Abbas mana" kallonta sukayi gaba daya cike da mamaki,abbas din da kowa yasan dabi'arsa,mutumin da ko auren hafsa dinma kamar bazaiyi ba saboda tsabar I don't care manner irin nashi da rashin baiwa lamarin soyayya muhimmanci?

"Abbas din yaushe har yaga wata yanaso?" Faccalar tata da yara ke kira da gwaggwo fanteka ta fada

"Tayani tambaya gwaggwo,na dauka ma bashir ko yaya sa'id zata ce,ko kuma Sunusi" kai ta girgiza tana murmushi

"Abbas ne" kai suka jinjina su duka,mabruka tace

"Ya cancanci ya qara aure dama tuni,wannan rayuwar da akeyi a gidansa bata da ma'ana sam,naga qoqarinsa ma,ganin baida wannan ra'ayin yasa ban taba tuntubarshi da maganar ba,ga 'yammata nan cike a dangi,ya zabi wata ya qara ko zai samu sassauci,haba abun na hafsa yayi yawa" kai gwaggwo ta gyada itama

"Gaskiya dai,yammata kyawawa fa gasunan masu hankali,ita wannan din a ina ya samota?,cikin yan uwansa ne?,amma banji batun ba sai yanzu?" Gwaggwo ta fada cike da son jin wace?,tana fata ya zamana cikin yaranta ne,duk da tasan zaiyi wuya,don inda cikin nasu ne da tuni ta fahimta,amma rabonta da abbas a gidan tun sanda tayi wata rashin lafiya ya shiga ya dubata

"Ba cikin dangi bane,wata yarinya ce diya take a wajen muhsin abokinsa,dukkanku ai nasan kunsan muhsin?" Ta fada tana kallon fuskokinsu, gwaggwo da tuni fuskarta ta sauya tace

"Qwarai kuwa" sai hajiya ta dora

"Yarinya ce ma,amma nutsuwarta da hankalinta ya bani abbas din xai samu nutsuwa a gidansa,zai kuma ce ayi ayi,a bari a bari"

"Turqashi" gwaggo fanteka ta fada ba tare da tasan kalmar ta fita a bakinta ba,wani bacin rau na motsa mata,yaron da dukkan alamu suke nuna zaiyi arziqi cikin dangin nasu,taketa qulafucin ganin ta samu ta jogana diyarta,lokaci daya hajiyan ta wargaza fatanta da burinta ta dauko wata bare ta maqala masa?.

"Banda abun hajiya ruqayya,gida bata qoshi ba za'a baiwa dawa?,gamu da yaran yammata duka sun tasa saiki dauko bare ki bashi?,duk da itama hafsan akwai alaqa amma ai baiyi alaqar sa da yaran kawunnansa ba ko?" Gwaggo fanteka ta fada tana dora murmushin yaqe kan fuskarta

"Gaskiya nima wannan tunanin yazo min" mabruka ta fada tana gyada kai, murmushi hajiya tayi
Chapter 26 · 0% Book details