← Book details A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 37

Sashe 7

A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read

"Kawai dai me? Ki tashi ki je kawai." Miƙewa tayi ba tare da ta kalli kowa ba ta fice daga ajin kyakkyawar fuskar nan ta ta a haɗe. A filin makarantar ta hange shi zaune da wani a gefensa, da alama magana suke yi. Gefen fuskarsa kaɗai ake iya hanga wanda hakan ya matuƙar bayyana kyawunsa musamman da fuskarsa take a juye. Sosai wata zuciyar take zugata akan kada ta je, kawai ta koma, se kuma wata ta zugata akan kawai ta je, ai ba wani abun taje nema wajensa ba. A nutse ta cigaba da takawa zuwa inda yake ɗin, se da taje inda take da tabbacin ze ganta sannan ta tsaya kanta na kallan gefe tayi shiru, dan ta san ya ganta, kuma shi ne ya nemi ta zo ba ita ce ta zo wajensa neman wani abun ba. A nutse Gwani ya cigaba da tattaunawa da mutumin nan, sam be nuna ya san akwai wanzuwar wata halittar a wajen ba. Hakan ba ƙaramin baƙantawa Lulu yayi ba, ga shi yana wani magana a hankali daga shi har wanda suke maganar, se dai shi ta shi ko sautinta ba a ji saɓanin ɗayan da ake iya jiyo sautin tasa muryar. A hankali ta ɗan saki tsaki tana runtse idanunta, wannan faɗin ran nasa da nuna shi wani ne bayan shi ɗin ba kowa bane yana ɗaya daga cikin abin da ke sanyawa bata yinsa ko kaɗan. Uwa uba kuma yadda kowa ke son shi, kowa ke nan nan da shi, se take ɗauka duk suna yi saboda kyawunsa ne da ke yaudararsu, shi yasa ita sam be taɓa birgeta ba se ma haushinsa da take ji daga shi har mutanen da ke son shi, dan gani take yadda suke son na shi ne yake sanyawa baya ganin girman kowa, baya tsayawa inda Allah ya ajiye shi. Tafi ƙarfin minti 5 tsaye a wajen, zuwa lokacin ta gama fusata, duk da Malaminta ne amma se take ganin kamar idan ta buɗe baki ta masa magana, ko da ba a tausashe ba ne ba ze ɗauka itama ta yaba da shi ɗin ne, kamar yadda kusan kowa yake yi. Ji take kamar ta tafi ba tare da tace komai ba, yayin da wata zuciyar ke faɗa mata ta masa magana ba ze ɗauki komai ba, haka dai ta daure, ta cije ta haɗa rai ta juya ta kalli inda suke tace murya a cunkushe

"Malam, ga ni!" Se a lokacin ya ɗaga kyawawan idanunsa ya kalli inda take tsaye, cikin er basarwa yace

"Assalamu alaik." Daga haka ya maida kansa wajen mutumin suka cigaba da magana. Runtse idanunta tayi tana jin wani irin takaici da kunya da haushi duk sun taru sun rufeta. Me yake nufi da ita? Kafira ce ita ko me yake nufi? Ƙirjinta har wani bugawa yake saboda tsabar takaici da haushi. Yanzu duk da irin wannan dizgin da rashin kirkin da yake a haka ɗalibai da yawa ke son shi, a haka suke cigaba da mu'amalantarsa kamar wani mutumin arzik'i. Yadda zuciyarta ke tafasa ta san ko ta buɗe baki ma ba abin da zata iya faɗa, dan haka se da ta ƙara wajen minti 2 tsaye a wajen. Se da ta ji ta ɗan soma dawowa daidai sannan ta sake juyawa cikin rashin mafita tace

"Ga ni!" Sarai ya jita, ba ya kuma san yayi shiru dan ya san hakan be kamata ba, se dai kuma yanda take magana kamar da sa'anta ko ma ƙaninta ya ga lallai ya kamata ya koya mata hankali, dama ya daɗe da gane take_takenta tun ba yanzu ba. Toh a yanzu kuma da ya zama malamin ajinsu shi ba ɗaukar kowanne hauka ze yi ba, dan haka ya zama dole ya taka mata birki. A nutse ya sake ɗaga kansa a karo na biyu ya dubi inda take ba tare da ya kalli fuskarta ba yace cikin basarwa

"Ba a koya miki sallama ba? Toh ki je ki koya se ki dawo!" Daga haka ya miƙe a nutse hannunsa ɗauke da wani littafi ya bi bayan wanda suke magana dan ya riga shi tashi. Bin sa tayi da kallo tana jin yadda zuciyarta ke tafasa tana mata zafi, wani irin baƙin ciki da ɓacin rai duka suka haɗu suka tarar mata. Kawai se ta ji ƙwalla a cikin idanunta, gaba ɗaya ta gama muzanta, ya gama yarfata, ya gama wulaƙantata. Se ta buɗe ido ta fara duba gefe da gefenta ko da akwai wani a kusa da ita. Fatan ta guda ɗaya Allah yasa babu wanda ya ga wannan cin mutuncin da yayi mata, ga shi kuma wani ƙarin baƙin cikin ya tafi ya barta a wajen, wato ga mara aikin yi, idan ta gaji da tsayuwar se ta ƙara gaba. Ganin da tayi kowa da abin da yake yi, se kuma waɗanda ke fitowa daga aji saboda an tashi, se dai da alama kowa harkar gabansa yake yi, ya sanyata soma takawa a hankali kamar babu laka a jikinta tana jin yadda gaba ɗaya jikinta yayi sanyi, haushi da takaicin Gwanin na sake cikata. Gaba ɗaya ta ƙi barin zuciyarta ta huta, se tunanin abin da ya faɗa mata ɗin take cikin wannan muryarta sa me kauri da daɗi. Duk da kalaman da ya faɗa ɗin basu da yawa amma ita a wajenta ji tayi kamar an gama muzanta ta muzancin da ba a taɓa yi mata ba, wai yau ita ɗa namiji ke faɗawa magana. Cigaba da takawa ta cigaba da yi har zuwa sanda ta ƙarasa ajinsu, ko lura da masu fitowa ma ba ta yi ba, se da Didi ta kamo hannunta tace

"Kee!" Se a lokacin ta kalli Didin da idanunta da ƙwalla ta gama taruwa se dai taƙi bata damar zubowa saboda kada wani ma ya gane akwai abin da aka mata, bare ma a tambayeta kuma idan ta faɗa ɗin ita ce zata ji kunya.

"Me ya faru?" Didi ta tambaya tana kafeta da idanunta. Duk da basa ɓoyewa junansu komai amma yau ɗin so take kawai ta kwanta tayi bacci ta manta da abin da ya faru ba tare da kowa ya sani ba, dan haka tayi ƙarfin halin faɗin

"Kaina ke ciwo!" Duk da bata wani yadda ba, amma ta san koma mene idan ta matsota zata faɗa mata ne, hakan ne ne ya sanyata faɗin

"Ki wuce gida, kina zuwa kuma ki sha magani kin ji koh?" Didin ta faɗa cikin kulawa. Jinjina kai Lulu tayi kawai se ta cigaba da bin Didin da ke riƙe da hannunta suka fito. Suka yi sallama cike da kewar junansu sannan Lulu ta shige cikin motar da ta zo ɗaukarta, yayin da Didi ta kama hannun Little suka tafi gida.

Tun da ta shigo Jadwa ke binta da kallo, ganin ba a irin yanayin da ta saba ganinta ba yau ɗin ta ganta a ciki. Hakan ne ya sanya lokacin da ta nemi waje ta zauna kan gadon, se itama ta zauna tana kallanta tace

"Sistor wai me ya faru?" Murmushin yaƙe Lulu tayi kafin tace

"Babu komai fa. Me kika gani?" Yamutsa fuska Jadwa tayi tace

"Kin ga yanzu dai babu Didi a gidan nan, idan zaki faɗa min damuwarki mu haɗu mu yi maganinta toh. Idan kuma ba zaki faɗa min ba se in san inda kika ajjeni." Kallan Jadwan Lulu tayi kamar ba za tace komai ba se kuma tace

"Babu komai fa nace miki" ta faɗa fuskarta a haɗe saboda tuna abin da ya faru ɗazun.

"Akwai ɗin kenan. Just tell me, mu haɗu mu yi finding solution." Jadwa ta faɗa bayan ta tauna chewing gum ɗin bakinta ya bada sautin 'ƙaƙas'. Ji tayi kamar yanzun ne Gwanin ya faɗa mata maganar, ji take kuma kamar yanzun ne ya shayata a tsaye kusan mintina nawa. Kamar za ta fasa ihu tace

"Jadwa ki ƙyaleni don Allah. Malaminmu ne ya ɓata min rai." Cikin rashin fahimta Jadwa tace

"Ban gane ba? Kin je wata makaranta ne hajjaju? Yaushe kika fara zuwa University bani da labari?" Kallan rainin hankali Lulu ta bi Jadwa da shi jin maganar da tayi ɗin irinta rainin hankali, se kawai tayi mata shiru fuskarta a haɗe cikin zuciyarta na cigaba da tafasa.

"Common Babe, Allah kuwa ban gane me kike nufi ba" Jadwan ta faɗa tana riƙo hannun Lulu.

"Idan nace miki Ya Sayyadi zaki gane? Toh shi ne ya gama yarfani da girmana da mutuncina." Kallanta Jadwa ta cigaba da yi tamkar wata sabuwar halitta, se kuma daga baya kawai ta sheƙe da dariya hadda riƙe ciki. Haushi gami da tuƙuƙi suka sake cika Lulu, se ta miƙe a fusace zata bar ɗakin, Jadwa tayi saurin riƙo hannunta. Fuzge hannun tayi kamar zata rufe Jadwan da duka. Ganin hakan ne ya sanya Jadwa miƙewa tana maida dariyarta ta soma faɗin

"Sorry my love. Tun farko ce min zaki yi Malamin Islamiyya. Ni da kika ce min Malami na ɗauka wani shahararren Malamin University ne, shi yasa nake dariya. Kin ga mu je mu zauna." Ta faɗa tana jan hannun Lulun. Yanzu dai se ta bita ɗin suka zauna. Da rarrashi ta haƙura ta bata labarin abin da ya faru ɗin. Se da suka ɗauki wajen minti 1 bayan gama bada labarin sannan Jadwa tace

"Wai kina nufin Malami, Malamin ma Malamin Addini shi ne kika zauna yana ƙoƙarin manna miki hauka?" Jadwa ta faɗa cike da mamaki wanda ya gaza ɓoyuwa har akan fuskarta..

Me son karanta A JINI TAKE (IZZATA) har ƙarshe ze tura ₦300 ta 8124818273 Zahra'u Yusuf Ishaq Opay. Shedar biya ta 08124818273.

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*

By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_

*CHAPTER ONE*

Page_05

___Shiru Lulu tayi, dan ita maganar ma da Jadwan ke yi sake tunzurata take yi, tana sanyawa tana tuna abin da ya faru ɗazun, tana kuma sake sakawa tana jin Gwanin yayi mata ƙarshen cin mutunci. Kamar ba za tace komai ba se kuma can tace muryarta a cushe
Chapter 7 · 0% Book details