Sashe 18
A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read
"So abin da nake so da kai.. ka zauna a gida ka yi hutunka. Ban son fice_ficen nan.."
"Ohk.." Sallamar Mom cikin ɗakin ita ce ta sanya Daddy kallanta, ya amsa sallamar sanda take cigaba da takowa cikin ɗakin. Kai tsaye kusa da ɗanta ta je ta zauna tana murmushi. Se da ta saka hannu ta kamo hannunsa sannan ta kalli Daddy tace
"Barka da wannan lokaci Yallaɓai.." ta kira shi da sunan da Mommah ke kiransa da shi a lokuta da dama. Hakan ne ya sanya shi murmushi, kafin shi ma ya amsa mata da sunan da ya saba kiran Mommahn da shi a duk lokacin da ta kira shi da 'Yallaɓae'
"Barkanki dai Ranki ya daɗe.."
"My boy.."
"Mom.." ya faɗa tana kallanta can ƙasa. Maida dubansa Bad Man ya yi kan Abba yace
"Abba ka faɗa wa Mom, ta de na kirana da Boy, look at me fa.." ya yi maganar yana kallan kansa. Murmushi Abba ya yi shi ma se ya kalli Bad Man ɗin, duk da ba wasu shekaru na azo a gani ke gare shi ba amma da ke ƙaƙarfa ne shi, me murɗaɗɗen jiki da kallo ɗaya za ka masa ka gane ya horu da ɗaga ƙarfe ya sa ba za ka iya ƙiyasta shekarunsa a yanayin jikinsa ba.
"Gaskiya dai.. ki dena kiransa da Boy.."
"Oh my gosh.." Mom ta faɗa tana girgiza kai, fitinar Areef ɗin yawa gareta. Amma dai ta san idan har ba denawar ta yi ba ba ze dena mata mita a kan hakan ba. Dan haka tace
"Noted Sir.." ta faɗa tana kallan Daddy da murmushi kan fuskarta. Shi ma murmushin ya yi. Daga haka se suka ɗan cigaba da hira, Bad Man na gefensu yana danna waya, dan shi sam be saba da wata hira ba, yanzun nan za ta ginshesa. Dan ma ya ga suna buƙatarsa cikin ɗakin ne, hakan ne ya sanya shi zama ɗin se dai gaba ɗaya hankalinsa na kan wayarsa ne.
... A karo na barkatai ta sake kiran layin da ta ɗora shi a kan wayar da ta bawa Lulun, se dai kamar ko yaushe yanzun ma faɗa mata suke yi a kashe layin yake. Ta yi tsaki babu adadi, ta shiga zagaye ɗakin tana jin ɓacin rai na taso mata. Jadwa da tun ɗazu take ankare da ita tace
"Mami wai har yanzun?" Kamar jira take dama, se kuwa ta soma faɗin
"Ki bar min ja'irar yarin mana. Ina ganin jiki zan saɓa na sake zuwa can gidan ko zan samu Kaseem ya ƙyaleni na huta." Mami ta faɗa tana komawa ta zauna a kan kujera. Tana zama kuwa se ga kiran Kaseem ya sake shigowa wayarta. Kamar ba za ta ɗaga ba, se kuma ta ɗaga ɗin ta kara a kunnenta. Daga can ɓangaren yace
"Amm Madam dama cewa na yi, why not ba za ki ba ni address na gidansu ba? Idan ya so kai tsaye se na je wajenta. Ko ma na fara zuwa wajen mahaifinta saboda wallahi da gaske na ke aurenta zan yi." Ajiyar zuciya Mami ta sauke kafin ta soma faɗin
"Kaseem ka yi haƙuri, ka san fa yarinyar nan dududu a S.S 1 ta ke.. Abbanta kuma na so ta yi karatu. Ko ma ba haka ba bana jin ze aurar da ita ba ta gama secondary ba, shi ya sa na ke nema maka wata hanyar da zaku samu dai kuna gaisawa." Kamar yana gabanta ya shiga girgiza kai sannan yace
"Ki yi haƙuri, don Allah ki ba ni address ɗin. Idan na je wajen mahaifin nata ina so ne kawai a san da zamana ko da ba yanzu ze aurar da ita ba. Amma na fi so ko me zan yi na yi shi ne da sanin mahaifin nata." Shiru Mami ta yi se kawai ta amsa da
"Toh shi kenan.." Daga haka ta katse kiran. Duk abin da dama suke cewa Jadwa na ji, se da Mamin ta katse kiran sannan ta soma faɗin
"Mtswww, wai shi a lallai dole mutumin kirki.. duk ƙoƙarin da kike yi be gani ba shi uban iya. Aikin banza" ta ƙare maganar tana maida kanta kan wayar da take dannawa. Ita dai Mami ba tace komai ba duk da dai ta yadda da abin da Jadwan ta faɗa.
.. "Abeey wallahi ba ka da lafiya.. ka bari na kira mota mu kaika asibiti.." Murmushin ƙarfin hali Abeey ya yi yana kallan Gwani kafin yace cikin ƙarfin hali
"Na sani.." ya ƙare maganar yana ɗan sauke numfashi kamin ya ɗora da
"Idan ma asibitin kuka kaini wani abun za su ƙaƙalo su ce a yi aiki kamar wancan karon.. toh ina kuɗin su ke? Ina za a nemo kuɗin?" Ɗan lumshe manyan fararen idanunsa Gwani ya yi sannan ya buɗe yace
"Allah ze kawo Abeey. In Sha Allah ma ba wata babbar damuwa ba ce.."
"In Allah ya yadda.." Ummeey ta faɗa cike da tausayin Abeeyn da ke sauke taggwan ajiyar zuciya kamar wanda ya yi aikin wahala..
https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8
*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*
By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_
*CHAPTER ONE*
Page_12
___Cikin mamaki Didi ke kallan Abida da ke cigaba da shigowa cikin parlourn. Abida ta saki murmushi sanda ta ida shigowa cikin ɗakin. Har ta ƙaraso ɗin Didi ba ta dena binta da kallan mamaki ba. "Me ya kawota gidan?" Ita ce tambayar da ke ta lugude cikin zuciyarta.
"Wannan daga gani Didinmu ce.." Abida ta faɗa tana murmushi. Ɗan lumshe idanu Didi ta yi tana ɗauke kai sannan ta dawo da shi kan Abidar tace
"Lafiya dai koh?"
"Eh fa. Kawai dai na zo ne mu gaisa da Umma. Ina Afaaf?" Ta yi maganar duka a haɗe. Sauke ajiyar zuciya Didi ta yi, se ta shiga lalube cikin zuciyarta ko da za ta iya hasaso dalilin Abidar na zuwa gidansu, bayan ba su da wani haɗi da ita, daga ita har Lulu?. Kawai dai se ta fice daga ɗakin zuwa na su ɗakin inda Ammi da Lulu ke zaune.
"Ammi kin yi baƙuwa." Didi ta faɗa tana neman waje ta zauna. Da mamaki Ammi tace
"Baƙuwa kuma?"
"Ehh ƙawar Lulu ce." Da sauri Lulu ta kalli Didi jin ta ambaci sunanta.
"Ƙawa kuma? Ni ɗin?" Ta tambaya cike da mamaki
"Fatima?" In ji Ammi. Girgiza kai Didi ta yi sannan tace
"A'ah wannan wata sabuwa ce.." ta faɗa tana ɗaukar littafinta da ta ke karantawa. Babu shiri Lulu ta sakko daga kan gadon tana faɗin
"Am eager na ga wace friend ɗin ta wa.." ta faɗa da iya gaskiyarta. Dan da gasken ta ƙagu ta ga wacce me ƙarfin halin ce har da biyota gidansu? Dan ita dai ta san ba ta da wata ƙawa bayan Masoyiya.
"Ke ce?" Ta faɗa cike da maɗaukakin mamaki a kan fuskarta. Gyara zama Abida ta yi tana ji kamar ta tashi ta rungume Lulun, se dai ta basar tace tana murmushi
"Wallahi kuwa.." taɓe baki Lulu ta yi lokaci ɗaya tana jinjina kai.
"Ikon Allah.." ta faɗa tana ƙarasowa ta zauna kan kujerar da ke kusa da wadda Abidar ke kai. Tana zama se ga Ammi ta fito. Cikin sauri Abida ta sauko daga kan kujerar da take kai ta tsuguna har ƙasa, tun kafin Ammin ta gama ƙarasowa cikin ɗakin tace
"Ina wuni Umma? An yini lafiya?" Ta tambaya lokaci ɗaya.
"Lafiya ƙalau Alhamdulillah.." Ammi ta faɗa tana neman waje ta zauna. Se Abidar ta cigaba da zama a ƙasan tana ɗan murmushi jefi_jefi, wai ita a lallai dole me hankali.
"Ki koma kan kujerar mana." Ammi ta faɗa tana murmushi. Da sauri ta girgiza kai tace
"A'ah Umma nan ɗin ma ya yi.." miƙewa Ammi ta yi tace tana kallan Lulu da tun shigowar Ammin ba ta sake cewa komai ba
"Ki kawo mata ruwa mana?"
"Toh" ta amsa da hakan, yayin da Ammi ta shige ɗaki. Tashi tsaye Abida ta yi tana faɗin
"Ki bar shi ma kawai wallahi, gida zan tafi. Ai mun gaisa da Umman. Bari na wuce.."
"Toh ki gaida gida.." Lulu ta faɗa.
"Gida ze ji.." Abida ta faɗa tana ficewa daga ɗakin. Lulu ta bi ta da kallo har ta fice, kafin ta ɗaga kafaɗa tana taɓe baki ta wuce ɗaki.
... Jikinsa a matuƙar sanyaye ya fito daga cikin office ɗin. Se ya ɗan dakata a gefe, ya jingina jikinsa da jikin bango idanunsa a ɗan lumshe. Gaba ɗaya tunaninsa ya tafi ne wajen yadda ze dinga samun kuɗin da za a dinga yi wa Abeeyn wankin ƙoda duk bayan sati 2. Bugun zuciyarsa har wani ƙaruwa ya yi, sanda ya ke wannan tunanin. Sam be lura da tsayuwar wani a kusa da shi ba, se lokacin da ya ji magana kamar daga sama
"A'ah Malam Affan.. Lafiya dai koh?" Abba da tun ɗazu ya hango shi ya faɗa bayan ya ƙaraso dab da shi. Se a lokacin ya buɗe idanunsa da sauri ya sauke su a kan Abban. Shaida fuskar da ya yi ne ya sanya shi ƙaƙalo murmushin yaƙe yace
"Lafiya ƙalau.." ya yi maganar yana miƙa masa hannu suka gaisa. Girgiza kai Abba ya yi yace
"Anya kuwa?" Ƙarya ba halinsa ba ce, hakan ne ya sanya shi gyara tsayuwarsa sannan yace
"Ehh toh.. Abeey ne babu lafiya..Amma In Sha Allah babu wata damuwa, dan yanzu haka ma fita zan yi, daga zarar na dawo za mu koma gida ne.."
"Ikon Allah.. Toh Allah ya ba da lafiya me ɗorewa."
"Ameen Ameen.."
"Mu je na gaishe shi koh?" Abba ya tambaya yana kallan Gwanin.
"Eyyah da yake ya samu bacci yanzun.." jinjina kai Abba ya yi cike da gamsuwa da maganar Gwanin, tun kafin ya ƙarasa yace
"Toh shi kenan, Allah ya ƙara afuwa."