← Book details A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 37

Sashe 35

A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read

"Tambayata ki ke? Ina iyayenki suke? So nake na mareki a gabansu na ga abin da za su iya yi.. Ba so kike ki zubar min da mutunci ba? A banza.." ya ƙare yana murmushin takaici. Ita ba ma saurararsa take ba, kawai ta yi shiru ne kamar tana jinsa amma tana kallan gefensa ne tana tsara yanda za ta yi tsalle ta fice daga ɗakin. Se dai har kuma lokacin "Waye shi?" ta ƙi barin ƙwaƙwalwarta. Jin da ya yi ta yi shiru ne ya sanya shi sake kufula, se kawai ya cigaba da takawa, daidai lokacin da ta yi iya ƙoƙarinta wajen yowa gaba dan ficewa daga ɗakin. A fusace ya kai hannunsa kan lallausar fuskarta ya shimfiɗa mata wani gigitaccen mari. Se dai aka samu akasi be sameta ba, saboda yanda ta kauce, hakan ne kuma ya yi sanadiyar faɗuwarta gefe, tsausayi ya sanyata buguwa da gefen drawer. Nan take ta zube a wajen. Ɗan runtse idanunsa ya yi da ƙarfin gaske bayan hannunsa ya taɓa fuskarta. Cikin sakannin da basu wuce 10 ba ya ji gaba ɗaya kansa ya wani irin juyawa, gangar jikinsa ta soma rawa, jiri ya kwashe shi. Kansa ya yi masa wani dumm kamar an ɗora masa wani ƙaton gini a kan nasa. Gaba ɗaya gidan ya shiga juya masa, ya soma ganin sama na komawa ƙasa, se ya riƙo kan nasa da sauri. Se dai duk da haka da wani jiri ya kwashe shi se gashi zube a tsakar ɗakin har kuma lokacin jikinsa be dena wata muguwar karkarwa ba. Daidai lokacin da Habu Driver ya shigo cikin ɗakin. Da sauri ya yi watsi da ledar hannunsa, ya ƙarasa yana kallan Didi da kuma saurayin dake kwance shi ma a tsakar ɗakin. Tsoro duka suka cika shi a lokaci ƙanƙani. Se dai ya riga ya san daga lokacin da ya ga motar ta shigo layin be ci ace har ya aikatawa Didin wani abu ba. Ta yiwu dai wani abun suka shaƙa ya sumar dasu dukansu. Gaba ɗaya saboda tsabar rikicewa se ya rasa ma abin da ze yi. Ya dinga musu fifita zuciyarsa na bugawa. Se daga baya da ya ga Bad bayan en sakanni ya kan ɗan jijjiga da jikinsa sannan ya miƙe ya fita daga ɗakin a guje. Se kuma ya tsaya, tunawa da ya yi idan har ya kira wani daga cikin en unguwar za su iya zargar wani abu. Hakan ne ya sanya shi komawa ciki. Da taimakon Allah ya yi ƙoƙari ya fito dasu ya sakasu cikin mota sannan ya hau ya tasheta ya fice daga gidan. Kai tsaye asibiti ya wuce da gudu, yana addu'ar Allah ya sa basu mutu ba. Yana kuwa zuwa aka karɓesu hannu bibbiyu. Da yake akwai mutane da dama da suka san Bad har sun fara ƙus ƙus cikin asibitin suna faɗawa junansu suma suna munafunci. Shi dai Habu Driver yana tabbatar da an shigar dasu babu ɓata lokaci ya ɗauki waya ya kira Abba.

.. Babu daɗewa se ga Abba cikin asibitin hankali tashe. A lokacin ne kuma likita ya nemi ganin wanda ya kawo Bad Man ɗin da kuma Didi. Abba da kansa ya je, dan lokacin ma be fahimci abin da Habu Drivern ke faɗa masa ba. Dan haka ya nemi waje yana jiran cewar doctor.

"Wato ita yarinyar buguwa ta yi da wani abu a gefen kanta. Wanda hakan ya janyo mata suma saboda yanda ta bugu ɗin. Shi kuma Yaron bisa rashin sani, ko kuma da saninsa ya sha wasu ƙwayoyi ne da suka yi wa ƙwaƙwalwarsa girma sakamakon rashin saninsu da ta yi. Se ta kasa karɓarsu saboda ba ta saba da su ba. Hakan ne ya janyo masa fita daga hayyacinsa. Se dai cikin ikon Allah ita yarinyar ta riga da ta farfaɗo. Shi kuma yaron gaskiya dai har yanzu be farfaɗo ba, se dai muna saka ran nan da dare ya farka ɗin In Sha Allah.." Ajiyar zuciya Abba ya sauke kafin yace

"Na gode.."

"Amma yana da kyau ku kira mahaifin yaron.."

"Mahaifin yaron kuma? Ka san shi ne?" Abba ya faɗa yana kallan Doctor ɗin.

"Yeap. Ɗan gidan Alhaji Matawalle namu ne fa.."

"Alhaji Matawalle?" Abba ya faɗa cike da mamaki.

"Ƙwarai kuwa.." Likitan ya faɗa cike da tabbarwa. Miƙewa Abba ya yi ya miƙawa Doctorn hannu suka yi musabaha sannan yace

"Thank u.." daga haka ya fice daga Office ɗin.

... Har ya isa ƙofar gidan mamaki be bar kansa ba. Ya rasa gane me ya kawo ɗan gidan Alhaji Matawalle gidansa? Me Didi ta masa da yazo wajenta? Mene ne ya sumar dasu gaba ɗayansu kuma lokaci ɗaya? Duk da likitan ya yi masa bayanin dalili amma yana buƙatar wani gamsheshshen bayanin, musamman a kan zuwan Bad ɗin cikin gidansa. Dan kuwa Habu Driver ya faɗa masa yanda komai ya faru, kamar yadda kuma ya zo ya gansu a sume hakan ya faɗawa Abba. Yanzu kuma shi ne ya ba shi shawarar zuwa ya sanarwa da Alhaji Matawallen abin da ya faru, sannan ya masa magana a kan ya jawa ɗansa kunne a kan zuwan da ya masa cikin gida.

"Yace ka jira shi a ɗakin can.." Wani ya faɗa yana kallan Abban. Kallansa Abba ya yi da ɗan mamaki, dan be taɓa tunanin a zuwan farko Alhaji Matawallen ze yadda ya gan shi ba, bayan yadda wasu ke faɗar shi yana da jin kai. Se dai tun a karon farko maganganun mutanen na ƙoƙarin tashi a matsayin ƙarya da baƙar hassada. Har ɗakin aka raka shi. Ya nemi waje ya zauna har kuma lokacin hankalinsa gaba ɗaya na kan Didi da aka tabbatar masa da babu abin da ya sameta. Cikin nutsuwa ya yi sallama cikin ɗakin. Abba ya amsa yana kallansa.

"Tabbas da gaske shi ɗin ne" Abba ya faɗa a ransa yana sake kallan Alhaji Matawallen. Se dai shi yau ɗin da ya gan shi a fili ma se ya ga kamar yafi kyau a kan yadda yake ganinsa a hoto.

"Barka da wannan lokacin.."

"Barka dai.." Daddy ya faɗa. Se da suka gaisa dai sannan Abba ya gyara zama yace

"Na san za ka yi tunanin ko me ya kawo ni gidanka? Toh dama dai magana ce a kan ɗanka.." Da sauri Daddy ya ɗaga kai ya kalli Abba cike da mamaki yace

"Ɗana kuma? Me ya faru da shi?" Ya faɗa hankali a tashe. Babu ɓata lokaci Abba ya shiga zayyana masa abin da ya faru daga farko har ƙarshe. Yana shirin zayyane masa dalilin zuwansa se ya ga ya miƙe yana faɗin

"Ya Subhanallahi.. Ya Salam.. Babu dai abin da ya sami ɗiyar taka koh?" Daddy ya tambaya cike da kulawa.

"Ehh.." Abba ya faɗa. Komawa Daddy ya yi ya zauna yana mamakin abin da Abban ya faɗa, kenan me ya kai Areef gidansa? Me ya sanya shi ya sha wani abu bayan be taɓa sha ba? Ko dai wasu ne suka ba shi ya sha ba tare da ya sani ba? Yana da tabbaci a kan ɗan nasa, dan kodayaushe cikin masa addu'a yake. Ya kuma san ba ya neman mata, ballantana yace kai tsaye ya je wajen yarinyar ne dan ya haiƙe mata. Toh amma me ya faru kenan?

"Mu je asibitin.." Daddy ya faɗa yana sake miƙewa. Miƙewa Abba ya yi yana kallan Daddyn cike da tausayawa. Haka kawai ya ji ya ba shi tausayi a kan yanda mutane ke kallansa. Ashe haka yake da sauƙin kai?. Duk yanda masu kula da Daddyn suka taho dan yin aikinsu, haka Daddyn ya dakatar dasu. Ya hau motar da kansa, sannan Abba ya hau ɓangaren me zaman banza, Daddy ya tashi motar.

Tunda suka shiga asibitin se idanu suka koma kan Alhaji Matawalle. Magulmata suka ƙaru, aka cigaba daga inda aka tsaya. Ko bi ta kansu Daddy be yi ba ya sauka daga motar zuwa cikin asibitin. Kai tsaye ɗakin da aka kwantar da Didi ya fara zuwa ya dubata. Tana kwance tana baccinta hankalinta kwance. Daddy ya sauke ajiyar zuciya sannan ya nufi ɗakin da aka kwantar da Bad Man. A hankali ya ƙarasa yana kallan kyakykyawar fuskarsa da ta yi fayau kamar mara lafiya. Cikin tausayawa ya kai hannunsa ya ɗan shafa goshinsa. Wayar Bad ɗin da ya gani ajje ya ɗauka ya ɗan soma dannawa. Kai tsaye message ya fara dubawa, ganin babu wani abun da ze gani ya sanya shi shiga call logs. Number Hero ce ƙarshen wadda aka kira. Hakan ne ya sanya shi kiran layin ya sakata a hands free yana kallan Abba da ya shigo cikin ɗakin. Kira 1 Hero ya ɗaga wayar cike da mamaki.

"Bad ba dai har ka dawo gida ba? Ina yarinyar take? Marin nata kawai ka yi kamar yadda kace ko kuwa dai wani abun ya faru? Ka na nufin kace min babu wani abu da ka mata? Ka bani labari don Allah.." Hero ya faɗa hankali a ɗan tashe. Dan ya san in dai har ƙwayar nan ta yi aiki a jikin Bad Man, toh ba ze samu damar da har ze iya kiransa a waya ba, dan ya san yanzu haka ma yana can a wata duniyar in dai ta yi masa aiki.

"Ƙitt!!" Daddy ya katse wayar. Se ya nemi waje ya zauna a cikin ɗakin ya kifa kansa a kan hannunsa. Ɗa ne Allah ya ba shi mara jin magana, ba dan haka ba ya daɗe da raba shi da irin waɗannan abokan. Yanzu ga shi suna neman tura shi ga halaka be sani ba, da tsausayi ya faru se dai su janyo masa azabar Allah da kuma kunyar duniya, da ɓacin suna. Yayin da suke gefe babu abin da ya damesu. Ko me ye ribarsu idan sun tunkuɗa wanda ba shi da ra'ayin aikata abu? Ko me za su ji a kan hakan?

"Ya ilahy.." Daddy ya faɗa. Neman waje Abba ma ya yi ya zauna. A hankali yace

"Lafiya kuwa?" Se a lokacin Daddy ya ɗago idanunsa ya kalli Abba. Ya gyara zamansa sannan ya soma faɗin
Chapter 35 · 0% Book details