Sashe 21
A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read
"Ameen_Ameen." Abeey da Ummeey suka amsa addu'ar, se dai shi Gwani ya kasa cewa komai saboda mamakin Abban na biyan kuɗin bayan a haka dai za a iya cewa ba su da wani haɗi. Se da ya ga da gasken Abban fita ze yi sannan ya soma takawa cikin nutsuwa, kyakkyawar fuskarsa na ƙawatuwa da murmushin da ya matuƙar karɓar fuskarsa yace
"Muna godiya sosai. Allah ya bar zumunci, ya saka da alkhairinsa.." ya faɗa dan tabbas ya ji daɗin yadda Abban ya nuna kulawarsa a kan Abban tun da farko. Ya riga ya san babu kyau maida hannun kyauta baya, ba dan haka ba da se ya faɗawa Abban ya bar kuɗin tunda ga su ya samesu. Se dai ko babu komai idan har ya bar shi Abban ze ji daɗi, ya kuma san yana yin wasu abubuwan ne duk dan ya sake wanke kansa a kan laifin da ba shi ya aikata ba.
"Allah ya ƙara afuwa." Abba ya sake faɗa yana ficewa daga ɗakin. Ɗan sake lumshe idanunsa Gwani ya yi bayan fitar Abban, a nutse ya taka ya nemi waje kusa da Ummeey ya zauna yana sauke ajiyar zuciya.
"Affan a ina ka samo wannan mutumin?" Abeey da har lokacin be koma bacci ba ya faɗa. Se a lokacin ya ɗan buɗe idanunsa. Se ya jefa idanunsa gefe a ransa yana tunanin abin da ya kamata ma yace. Ƙarya ba halinsa ba ce dan haka buɗar bakinsa se cewa ya yi
"Mahaifin ɗalibaina ne!"
"Ɗalibai kuma?" Ummeey ta faɗa cike da mamaki. Se ya jinjina kai dan tabbatar da abin da ya faɗa sannan ya ɗora da
"Ehh Ummeey.."
"Ikon Allah.. Allah ya saka masa da alkhairi.." Abeey ya faɗa yana sake jinjina kirki irin na Abba.
.. Tafiya ta ke yi cike da sassarfa, fararen idanunta sun cika taff da ƙwalla wadda ƙiris ta ke jira ta zubo. Jefa ƙafarta kawai ta ke yi ba tare da sanin inda za ta saka ƙafarta ta ba. Babu abin da ta ke hangowa ta ke kuma sake tunawa se maganganun Ladi da Abida masu muni marasa kuma daɗin ji.
"Ba za su biyomu ba koh?" Little da ya gama firgecewa tun ɗazun ya faɗa a tsorace. Ba ta iya amsa masa ba, se cigaba da tafiya da ta yi har lokacin jikinta be dena rawa ba. Daidai sanda suka kusa isa gida ta sake jiyo muryar Little na faɗin
"Lulu ba za su biyomu ba koh?" Se a lokacin ta tuna daga ina suke, ina suke shirin zuwa yanzu, waye kuma a hannunta. Take ƙirjinta ya wani irin buga. Se ta sanya hannu ta sauke shi daga kafaɗarta zuwa kan wani dandamalin ƙofar wani gida. Da sauri ya sake riƙota yana faɗin
"A'ah kar ki tafi ki barni kin ji?" Ya faɗa yana kallan gefe da gefensa. A take ta ji duk wani tunanin gidan nan ya soma yin nasa wajen. Tsoro da fargabar tunkarar gida ya mamayeta. Ta manta sam ba ita kaɗai ba ce, ballantana idan ta koma gida ta haɗa ƙarya ta faɗa. Ita da Little ne, a yadda kuma ya tsoratan nan babu abin da ze hana shi bayar da labarin abin da ya faru. A tambayeta ina ta je tace mene ne? Wane gida ne? Me ta je yi gidan? Tuna abubuwan nan da ta yi ne ya sanya ta riƙo Little ɗin, daidai lokacin da wata sabuwar ƙwalla ta taru a cikin idanunta. Se kawai ta koma ta zauna a kan dandamalin cikin rashin sanin abin yi...
A yi manage da wannan pls. Gobe idan Allah ya kai mu za mu haɗe.
https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8
*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*
By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_
*CHAPTER ONE*
Page_14
___Ta shafe fiye da minti 10 zaune a wajen ba tare da ta sake niyyar ko da miƙewa ba ne. Se da ta jiyo muryar Little na taɓata yana faɗin
"Wai anan za mu zauna?" Se a lokacin ta sauke ajiyar zuciya lokaci ɗaya tana ɗan lumshe idanunta sannan ta miƙe a hankali ta kamo hannun Little ɗin. Karon farko tun fitowarsu daga gidan nan ta buɗe baki tace
"Gida za mu tafi.. ka da ka faɗawa kowa inda muka je ka ji?" Ta faɗa tana kallansa.
"Kaiii!!" Ya yi maganar kamar wani babba yana jinjina kai gami da waro idanunsa masu kama da na Twins sakk. Se da ta ja doguwar ajiyar zuciya sannan cikin rarrashi ta soma faɗin
"Zan siya maka sweet idan ba ka faɗawa kowa ba. Ai babu inda muka je daga makaranta koh.?"
"Ehh" ya faɗa yana ɓata fuska, se kuma ya ɗora da
"Amma babba.." murmushin da ya tsaya a iya bakinta ta yi, saboda har lokacin ba ta gama komawa daidai ba.
"Yeap.. babba sosai ma."
"Yes!" Ya faɗa kamar wani babba yana murmushi. Se ta saka hannunta ta sauko da shi ta kama shi suka soma tafiya zuwa gida, har lokacin tafiyarta ta dai babu wani kuzari. Suna zuwa ƙofar gida ta kalli Little tace
"Ina ma muka je?"
"Makaranta." Ya amsa mata da sauri yana murmushi. Kamar wata mara laka haka ta cigaba da takawa zuwa cikin gidan. A hankali ta yi sallama a ƙofar parlourn cike da fatan babu kowa a ciki. Aikuwa babu kowa ɗin a ciki se ta yi saurin shigewa cikin ɗakinsu. Anan ta samu Didi da Ammi suna sallah. Se kawai ta saki hannun Little da sauri ta shige toilet. Se a lokacin ta sauke ajiyar zuciya gami da jingina kanta jikin bangon toilet ɗin tana lumshe idanunta. Wasu irin hawaye masu ɗumi suka zubo a kan kuncinta. Sam ba ta da saurin kuka, ko kuma zuciyarta ta karye da wuri, se ga shi yau ɗin cikin ƙanƙanin lokaci zuciyarta ta karye, ta ka sa mantawa da abin da ya faru a yau ɗin. Daidai lokacin da ta ji ƙarar buɗe ƙofar ɗakin alamar an fita ta fashe da kuka kawai, kukan da ba ta san dalilinsa ba tunda dai Allah ya kuɓutar da ita. Se da ta gama kukan sannan ta ɗauro alwala ta fito bayan ta wanke fuskarta sosai. A ɗakin ta tarar da Little zaune kan gadonsu yana cin abinci, yayin da Didi ke kwance a kan gadon saboda zazzaɓin da har lokacin be gama sauka a jikinta ba. A hankali ta ƙaraso ta ɗauki dadduma ta shimfiɗa, tana gyara zaman hijab ɗin jikinta ta jiyo muryar Didi na faɗin
"Har kin gama kukan?" Se ta dakata da sauri tana kallan Didin da ke lulluɓe da blanket. Kallan Little ta yi da ke cin abincinsa hankali kwance. Ta san idan ya ji maganar Didin ze iya tuna abin da ya faru, hakan ne ya sanyata kallansa tace
"Little.. je ka ci abincin a parlour ka ji?" Babu musu ya miƙe riƙe da ƙaramin plate ɗin da abincin ke ciki ya fice da sauri. Se a lokacin ta kalli Didi a hankali tace bayan ta ɗan yamutse fuska
"Ni fa ba kuka nake yi ba.."
"Uhmm, ya miki kyau.. ban san lokacin da muka fara ɓoyewa juna wani abun ba. Amma ki cigaba." Didi ta faɗa tana gyara kwanciyarta. Shiru ta yi dan ita kanta ta san abin da ta ke ƙoƙarin yi ɗin ba daidai ba ne, kasancewar ba sa taɓa ɓoyewa junansu wani abun. Dan haka gudun ka da ta ja lokaci ya sanyata tayar da Sallah. Se da ta idar sannan ta miƙe ta koma kan gadon, a hankali tace
"Didi.." juyawa Didi ta yi daga ɓangaren da ta ke, ciki ciki tace
"Ka da ki ce min komai malama.."
"Am sorry.." ta yi maganar a narke.
"Ke yanzu fa ba zan ji ba. Duk sanda kika yi niyyar faɗa min kya faɗa min, ae dama na ga take_takenki kwana biyun nan" girgiza kai Lulu ta yi tana faɗin
"Haba mana Didina.."
"Kya ji da shi dai.." Didin ta faɗa tana ture hannunta. Murmushi kawai Lulu ta yi, dama yanzun kwata kwata ba ta son yin zancen nan, dan haka gwara ta bari idan Didin ta sakko se ta ba ta labarin, zuwa lokacin itama ta nutsu.
.. "Ba za ki gane ba ne Jakadiyarmu.. Tsorona Allah tsorona ka da yarinyar nan ta ɗauka maganar nan ta je ta yaɗani a wajen mutane." Tsaki Ladi ta yi tana girgiza kai cike da fusata da zancen Abidar da ya ƙi ci ya ƙi cinyewa.
"Ke ki dakata da min maganar nan na faɗa miki. Ita ɗin banza ta faɗawa wani? Ni nan ni ce fa na faɗa miki ba za ta sanarwa da kowa ba. Ko ba ki yadda da ni ba ne? Idan ba ki yadda ba ki cigaba da damun kanki. Kuma ma dan an sani se mene ne? Kina tunanin duk zuwan da ki ke gidan nan dama babu wanda ya taɓa ganinki? Kin ga kawai ki yi sha'aninki hajjajuna.." Ladi ta faɗa tana gyara zamanta.
"Toh." Abida ta faɗa tana karkatar da kanta lokaci ɗaya tana ɗan taɓe baki kawai.
"Maganar Afaaf?" Kamar wadda Lulun ke gabanta ta saki murmushi hadda lumshe idanunta kafin ta soma faɗin
"Zan ba ta dama ɗaya ne a yanzu haka.. ki sake gwada sa'arki wajen janyo min hankalinta zuwa wajena. Idan kuma taƙi se na chanja wani salon, kin san ance idan dama taƙi se a koma hagu. Naga kan yarinyar na rawa saboda haka zan taka mata birki. Zan saka a wulaƙanta min abin da take taƙama da shi sannan daga ƙarshe dole ta dawo ƙarƙashina a lokacin da rayuwarta za ta koma mara amfani a wajen kowa. Ni kuma a sannan ne zan ci karena babu babbaka. Kin ga ta yi biyu babu kenan.." ta ƙare tana murmushi tana kuma hasaso yanda komai ze tafi. Jinjina kai Abida ta shiga yi bayan gama sauraron maganar Ladin. Tabbas Ladin ta fusata, kuma ba komai ne ya sake ingizata ba se ganin Lulun da ta yi, kuma ba ta sameta ba. Ta riga ta san abin da take faɗa ɗin da gasken za ta aikata, za ma ta iya aikata abin da yafi haka. Dan haka za ta yi ƙoƙari wajen sake janyo ra'ayin Lulun ko dan ka da Ladi ta saka a ɓata mata rayuwa.