Sashe 22
A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read
"Shi kenan. Zan sake zuwa na lallaɓata. Ki saka a ranki kin gama samun Afaaf." Abida ta faɗa tana murmushi dan ta kwantar da hankalin Ladin. Aikuwa se ta yi murmushi tana faɗin
"Allah ko Abida?"
"Ƙwarai kuwa.." Abida ta faɗa tana sake yin wani murmushin kai ka ce ta ma kawo mata Lulun ne.
.. Baƙuwar motar da ya gani ce a ƙofar gidan ya sanya shi dakatawa. Cike da mamaki ya ke kallan motar ganin da gasken a ƙofar gidan ta tsaya.
"Ɗan uwa zan kiraka zuwa anjima.. pls ka da ka ƙi amsawa.." Kaseem ya faɗa sanda ya hangi Abba. Daga can ɓangaren shiru ne ya ɗan wanzu kamar ba waya ya ke ba, se kuma a hankali na ji an ce
"Oh..k.." daga haka tun kafin Kaseem ɗin ya katse wayar aka datse kiran. Girgiza kai Kaseem ya yi a hankali yana furta
"Wannan baudaɗɗen Areef ɗin halinsa se shi.." Da sauri ya sauka daga motar ya ƙarasa inda Abba yake bayan ya jefa wayarsa a aljihu. Cike da girmamawa ya tsuguna yana faɗin
"Barka da wannan lokaci.."
"Barka dai.." Abba ya faɗa yana riƙe hannun Kaseem suka gaisa sannan ya ɗora da
"Tashi mana" murmushi Kaseem ya yi kana ya miƙe ɗin. Se kuma ya ɗan yi shiru har se da Abba yace
"Se dai kuma ban shaida fuskar ba.."
"Ehh wato dama dai ba ka sanni ba.. amma dai na zo ne a kan Afaaf" ya faɗi sunan kamar yanda Mami ta faɗa masa.
"Toh.. Allah ya sa dai ba laifi ta yi ba" Abba ya faɗa dan har ya fara tunanin ko malaminsu ne ya kawo ƙararta kuma. Da sauri Kaseem ya shiga girgiza kai har lokacin kansa na ƙasa
"A'ah a'ah wallahi, babu abin da ta yi. Kawai dai wata maganar ce daban." Se a lokacin Abba ya ji daɗi dan har se da ya sauke ajiyar zuciya sannan yace
"Toh mu je daga ciki mana.." Cikin jin daɗi Kaseem ɗin ya bi bayan Abba zuwa cikin gidan. A compound ɗin gidan suka zauna kan wasu kujeru masu kyau.
Shiru Abba ya yi sanda ya gama saurarar maganar Kaseem ɗin. Se ya sauke ajiyar zuciya sannan yace
"Gaskiya ka zo da magana me kyau. Kuma zuwa wajena da ka fara yi ya sake tabbatar min da ingancinka. Se dai kuma wani hanzari ba gudu ba.." da sauri Kaseem ya ɗaga kai ya kalli Abba, cike da tsoron abin da ze fito daga bakin nasa.
"Ita dai yarinyar nan yanzu haka a S.S 1 take, yanzu ne suke ƙoƙarin shiga S.S. 2. Saboda haka ko da zan aurar da ita na fi ƙaunar ta gama secondary school, idan ya so se ta cigaba a gidan mijinta. Idan hakan ya yi maka toh babu damuwa se na soma ba ka dama wajen ita yarinyar. Idan har kun daidaita toh se mu san abin yi kuma." Ajiyar zuciya Kaseem ya sauke yana murmushi kamar wanda aka ce an ɗauki Lulun ne ma an ba shi gaba ɗaya.
"Na gode sosai Yallaɓae, Allah ya saka da alkhairi ya ƙara girma. Hakan da ka yi ya yi daidai, kuma nima ya min. Bani da damuwa da gama secondary ɗinta idan dai har ta amince da ni.." ya ƙare maganar ƙasa_ƙasa cikin er jin kunya. Murmushi Abba ya yi dan hankalin yaron ya burge shi yace
"Toh babu damuwa. Allah ya ba da sa'a." A zuciyarsa ya amsa da Ameen ɗin daidai sanda Abba ya miƙe. Ba dan ya so ba shima ɗin ya miƙe yana ta kokawa da zuciyarsa a kan kada ta rinjaye shi ya furta yana son ganin Lulu.
"Zauna.. bari na turo maka ita." Wani irin sanyi ne ya ji ya ratsa shi, har se da ya lumshe idanunsa yana komawa ya zauna kan kujerar. Se kuma ya tuna be cewa Abban komai ba, hakan ne ya sanya shi ɗaga murya wajen faɗin
"Toh Allah ya saka da alkhairi"
A parlour Abba ya sami Ammi, Didi da kuma Lulu zaune suna kallo. Ya kalli Didi da ke kwance yace
"Afrah ya jikin?"
"Da sauƙi Abba"
"Toh Masha Allah, Allah ya ƙara afuwa."
"Ameen Ameen" suka haɗa baki wajen faɗar hakan.
"Sannu da zuwa Abbansu." Ammi ta faɗa.
"Yawwah.. Ke Afaaf.." Abba ya yi maganar lokaci ɗaya.
"Na'am Abba.."
"Tashi ki je waje, kin yi baƙo.." gaba ɗayansu suka ɗaga ido suka kalli Abban cike da mamakin furucinsa.
"Baƙo kuma?" Ammi ta tambaya tana kallan Abban. Se da ya nemi waje ya zauna sannan yace
"Yanzu dai ta fara zuwa ka da a bar ɗan mutane da jira. Ke kuma zauna na faɗa miki yanda a ka yi.." Kallan Abba kawai Lulu har ma da Didi suke yi, jikin kowaccensu a sanyaye, musamman ma Lulu da har jikinta ya soma rawa, idanunta sun tara ruwan hawaye, jin wai ita ce ke da baƙo kamar a film. Toh me aka zo yi wajenta kenan? Me aka zo a ce mata? Ko dai ɗan makarantarsu ne? Kai ta ma fi tunanin hakan, tunda da dai ita a shekarunta yanzun dai ba soyayya take yi ba.
"Daɗina da ke Afaaf shininniƙi. Afrah maza shirya ki rakata. Ba wani abun ba ne ba.." jin abin da Abban ya faɗa ne ya sanya duka suka ji ɗan sauƙi. Duk da har lokacin jikin Didi be gama komawa normal ba, haka ta miƙe dan ba za ta iya barin Lulun ta fita ita kaɗai ba, duk da Abban yace musu babu komai, shi ya sa itama ta gama kawowa ranta ɗan ajinsu ne. Babban hijab kowaccensu ta saka, a haka suka fito daga ɗakinsu, kowaccensu dai har lokacin jikinta a sanyaye kamar waɗanda aka yiwa mutuwa. Bin su da kallo Ammi ta yi se dai ta gaza furta komai. So take kawai su fita ta ji bayani daga bakin Abban. A hankali suke takawa cikin compound ɗin, se baza idanu suke yi, ko da za su ga wani wanda suka sani zaune. Se dai har suka kusa ƙarasowa ba su ga alama ba. Hakan ne ya sanya Didi dakatawa tace
"Kin ga dai wajenki a ka zo, ni dai wallahi komawa zan yi." Kamar za ta yi kuka Lulu tace
"Don Allah Didi ka da ki tafi. Don Allah ka da ki koma kin ji? Wallahi a tsorace na ke, matuƙa tsoro nake ji. Ban san ko ɗan ajinsu waye ba. Ko kuma yayan wata ne a cikin en ajinmu."
"Ehh kuma haka ne" Didi ta faɗa, se kuma ta ɗora da
"Kin ga bari na zauna anan ina hango ku. Zan ƙaraso daga baya."
"Don Allah da gaske?" Lulu ta faɗa
"Ehh wallahi.." Se a lokacin sannan Lulu ta sauke ajiyar zuciya kana ta soma takawa zuwa inda Kaseem ke zaune. Se ta nemi kan kujerar ta zauna tana faɗin
"Ga ni!" Wani murmushi ne ya suɓuce masa sanda ya ɗora idanunsa a kan Lulu. Wani farin ciki na mamaye ilahirin jikinsa. So daga ƙarshe dai ya yi tozali da wannan kyakkyawar fuskar bayan tsawon lokacin da ya ɗauka yana begenta. Ya ɗan lumshe idanunsa kaɗan sannan ya buɗe yace
"Barkanki da fitowa gimbiya." Cikin rashin fahimta ta juya tana kallansa, ba ta san sanda tace
"Gimbiya kuma?" Murmushi ya sake yi kamin yace
"Ƙwarai kuwa.. Na san za ki yi mamakin zuwana, se dai wannan ɗin sam ba abin mamaki ba ne idan muka yi duba da kwanakin da na shafe ina nemanki." Ita duk wannan maganganun nasa ba ganesu take yi ba, ta fi so ta ji ya fito kawai ya faɗa mata shi yayan wance ne ta aiko shi wajenta.
"Wato tun ranar da na soma ganinki za ki shiga islamiyya ke da ɗan uwanki. Allah ya ɗora min ƙaunarki. Na kasa haƙuri har se da na bi ki gidan da ki ka je, ashe gidan Aunt ɗinki ne. In taƙaice miki labari dai ta hanyarta na bi na sameki yau ɗin nan.." ya ƙare yana murmushi, yana sake kallan fuskarta cike da so da ƙauna.
"Da yaro ka ganni a hannuna?" Ta tambaya bayan ta juyo gaba ɗayanta.
"Ehh" ya faɗa da murmushin dai.
"Kuma a dawowa se ka ga na shiga gidan Aunty Sadiya.."
"Exactly.." ya faɗa yana nunata, irin kin gano ɗin nan. Se kawai ta saki murmushi a karo na farko tun bayan fitowarta wajen. Se ya shagala da kallanta yanda ta yi wani shahararren kyau da ta yi murmushin
"Kenan idan haka ne Didina ka gani?"
"Ban.. gane.. ba!" Ya faɗa a ɗan rarrabe yana kallan Lulu. Murmushin dai Lulu ta sake yi ko kunya ba ta ji, bayan da farko ko murmushi ta ƙi yi.
"Twin sister ɗina ce.." Waro idanu Kaseem ya yi cike da mamaki da kuma al'ajabin abin da ke fitowa daga bakin Lulun.
"Twin sister na ki kuma?" Ya tambaya a mamakance, wanda tsananin mamakin se da ya bayyana a kan fuskarsa.
"Ƙwarai kuwa.." Cikin matuƙar mamakin dai ya shiga jinjina kai kafin ya sauke ajiyar zuciya yace
"So ki na nufin ki ce min duk wannan neman da na ke ba ke na ke nema ba? Twin sister ɗinki ce?"
"Ehh.." in ji Lulu.
"Ikon Allah.. ya sunanta?"
"Afrah.." jinjina kai Kaseem ya yi, se kuma ya saki murmushi kafin ya soma faɗin
"Ko daga sunan ma namu ya fi daɗi.." dariyar da ba ta shirya yi ba Lulu ta yi na jin maganar Kaseem ɗin. Mutumin da ko wadda ya ke ƙauna ɗin ya kasa ganewa, wai shi ne me faɗin suna ya fi daɗi.
"Ko ba ka faɗa ba, sunan Didina ya fi daɗi dama ai."
"Uhm humm. Pls kira min ita, wallahi na ƙagu na yi tozali da kyakkyawar fuskar da ta hanani bacci kwana da kwanaki. Tsananin kamannin da kuke yi ne ya sanya na kasa banbance ku." Se ta miƙe kawai lokaci ɗaya tana jinjina kai, kenan me Abbansu ya ke nufi? Aurar da su ze yi a waɗannan shekarun nasu ko kuwa dai me?
"Zo ki ji Didi.." Lulu ta faɗa sanda ta ƙarasa inda take zaune. Miƙewa Didi ta yi dan dama ta gaji da zaman
"Alhamdulillah, mu tafi. Wallahi dama kaina se sara min yake yi."
"Toh Didi wajenki fa ya zo, ya ɗauka ni ce ke.."