← Book details A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 37

Sashe 10

A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read

"Sorry Mom, ka da ki ji ni shiru, zan ɗan yi bacci kaɗan.." daga haka ya ajje wayar a gefensa, ya haye lallausan gadonsa kana ya ja blanket yana rufe jiƙaƙƙun eyes ɗinsa da har yanzun akwai ruwa a lashes ɗinsa.

.. Da mamaki ta kalli Jadwa tace

"Baƙuwa kuma? Anya ni?"

"Aikam dai wajenki ta zo, may be daga gida aka mata kwatance."

"Ohk" ta faɗa tana saukowa daga gado ta ɗauki wani ƙaramin mayafi ta ɗaure sassalkan gashin kanta da ke a buɗe kuma a tsefe. Ƙarasawa tayi da sauri tana faɗin

"Oyoyo Masoyiya!" Ta faɗa tana rungumeta. Rungume juna suka yi cikin farin cikin ganin junansu kafin suka saki juna kowaccensu ta nemi waje ta zauna.

"Sannu da zuwa." Lulu ta faɗa tana murmushi. Murmushin itama Fatima Kabeer ɗin ta maida mata da shi sannan tace

"Yawwah Masoyiya, se kika ganni a gidan nan kawai."

"Wallahi kuwa, amma fa na ji daɗin zuwan nan naki." Kafin Lulun tace komai Jadwa ta fito daga ɗaki sanye cikin riga da wando kamar koda yaushe, ta ƙarasa ta rungume wata budurwa da ta shigo ɗakin. Itama budurwar rungumeta tayi, Jadwa na faɗin

"Oyoyo Ƙawata." Kallansu Fatima tayi dan yadda suka bata mamaki, yanayin yadda suke rungumar ma kaɗai ba irin tamu ce, irin ta turawan nan ce da ake sumbatar gefen kumatu. Juyawa tayi ta kalli su Lulu tace

"Hey sannunku."

"Yawwah" suka amsa kusan a tare, sannan suka wuce ɗakin Jadwa.

"Kee!" Lulu ta faɗa tana kallan Fatiman. Se da ta sauke ajiyar zuciya bayan ta juyo sannan tace

"Masoyiya!"

"Na'am" Lulu ta faɗa.

"Life style ɗinku ba iri ɗaya da ta en gidan nan ba ce, kalli yanda suke abu kamar wasu turawa, kalli shigar er gidan, ina baki shawara da don Allah kar ki biyewa wannan yarinyar, ki din ga kaffa kaffa a komai. Amma kiyi haƙuri idan ba ki ji daɗi ba." Ta faɗa da ita gaskiyarta.

"Toh na ji." Harara Fatima ta jefa mata sannan tace

"Ai na san halinki ne, ni dai na faɗa miki." Ba dan bata so ta ja maganar da nisa ba da ta tambayi Masoyiyar meye aibun shigar Jadwa? Su suna rayuwa ne babu ruwansu da kowa, rayuwar 'yanci suke gabatarwa a gidan nan, kowa yayi abin da ya ga dama, babu me takura masa. Ba sa saka ido akan kowa, kamar yanda ba sa so a saka musu ido. Ba ta wani daɗe ba Fatiman ta yiwa Lulu sallama ta tafi, cikin jin daɗin zuwan nata Lulu ta rakata har gate sannan suka yi sallama ta koma cikin gida.

.. Kamar za tayi kuka tace

"Little don Allah ina ka jefa min shi?" Ta faɗa tana cigaba da duba cikin ɗakin.

"Yana can fa." Little da ke shirye cikin Uniform ya faɗa yana nuna mata gefen gado. Sake dubawa tayi, kamar ɗazun dai yanzun ma babu komai a wajen, hakan ne ya sanyata kallan Little ɗin ta galla masa harara daidai lokacin da Ammi ta shigo cikin ɗakin.

"Afrah wai me kuke yi ne har yanzun ba ku fito ba?" Ammin ta faɗa tana ƙarasowa cikin ɗakin.

"Ammi Little ne fa ya ɗaukar min niƙab, kuma be san inda ya jefa ba!" Kallan Little Ammi tayi tace

"Ina ka jefa mata?" Se da ya tura baki sannan yace

"Na manta" Maida dubanta kan Didi Ammi tayi tace

"Kin ga wuce ku tafi, kada ku makara, zan duba miki In Sha Allah kafin ku dawo." Kamar za tayi kuka tace

"Tohm." Tana jin duk babu daɗi, saboda ta saba fita da niƙab ɗin zuwa ko ina, idan har dai ba boko ba.

Hannunta riƙe da na Little suke tafiya, se hira yake mata yana tsalle_tsallensa, ita dai amsarta duka bata wuce "Ehh ko A'ah" gaba ɗaya hankalinta ya tafi kan makarantar da take Allah Allah su isa saboda rashin niƙab.

"Fatabarakallahu Ahsanal Khaliqin." Ya faɗa yana sake buɗe idanu dan cigaba da kallan wannan kyakkyawar halitta da a ganin farko ta tafi da shi. A karon farko ya ayyana wa kansa tabbas ya samu matar aure, dan a yadda ya ji zuciyarsa ta harba daga lokacin da yayi arba da Didi. Saurayi ne da aƙalla ze kai shekara 29 baƙi se dai ba can ba, babu laifi kyakkyawa ne, yana cikin manyan kaya masu haɗe da babbar riga, hakan ce ta kara masa kwarjini, yana kame cikin motarsa me kyau, shi yake driving da kansa, se dai ganin Didi da yayi ya sanya shi dakatawa. Ganin alamar tana neman kuɓuce masa ne ya sanya shi saurin cigaba da driving ɗin cikin takatsantsan ya soma binta. Sam bata lura da wata mota da ke binsu ba har suka isa makaranta.

Ko da taje makarantar ma duk se take jinta a takure, dan ta gama sabawa da niƙab ɗin musamman a Islamiyya. Lulu da ke kusa da ita tace

"Didi wai duk kin kasa sukuni akan wannan abun."

"Ina ruwanki?" Didi ta faɗa tana murguɗa baki. Murmushi kawai Lulu tayi tana maida dubanta kan Abida da ta juyo daga bench ɗin gabansu tace

"Hajiya Afaaf, kin dai ƙi zama ƙawata. Amma na fi tunanin Masoyiyarki ce ke hanaki kulani." Kallan juna Lulu da Masoyiyar suka yi se suka saka dariya. Ɗan cizar leɓenta na ƙasa Abida tayi kafin ta rufe idanunta sannan ta buɗesu a lokaci guda, Allah ma ya gani ba tun yau ba Lulun ke matuƙar birgeta, tana birgeta yadda ya kamata, se dai ta ga ita ɗin ba ta wasa bace, amma za tayi iya ƙoƙarinta wajen ganin tayi wani abun da ze sa su soma samun kusanci har ta saki jikinta da ita, kafin ta fito mata a mutum, se dai za ta bi komai a nutse ba za tayi gaggawa ba. Babu daɗewa Gwani ya shigo ajin kamar ko da yaushe cikin irin shigar nan da ya saba yi wadda ke matuƙar yi masa kyau da sake fito da ainahin kyawunsa da kwarjininsa. Daga shigowarsa kowa ya nutsu. Babu ɓata lokaci ya nemi waje ya zauna. Kamar ko da yaushe se ya soma karɓar hadda kafin yayi littafi, hakan ne yasa ya fara karɓa babu ɓata lokaci. Da yake a jere kawai yake karɓar haddar, yana gama karɓar ta Didi, se Lulu da ke kusa da ita ta gyara zama ta cigaba da zamanta tana ɗaɗɗaure fuska irin dan kada ma ya ga fuska bare yayi mata magana. Se dai ga mamakinta se jinsa tayi yace, bayan wajen rabin minti

"Kee!!" Bata juyo ba duk da tayi tunanin da itan yake, se dai ta nuna kamar ta ɗauka da wata yake. Da sauri Masoyiya tace ƙasa_ƙasa

"Lulu da ke fa yake.." Se a lokacin ta juya, bata kalle shi ba tace cikin dakewa

"Ban iya ba!" Shiru ne ya biyo bayan maganar da tayi, dan babu wanda ya taɓa tunanin abin da za tace kenan. Jin alamar kamar be ji bane ya sanyata sake buɗe baki za ta yi magana daidai lokacin da yace

"Tashi ki fita!"

"Ni?" Ta faɗa tana nuna kanta kamar da gasken bata san da ita yake ba. A karo na biyu bayan ɗaukar wasu sakanni ya sake furta

"Fita!!" Ya faɗa idanunsan nan cike da fushi, haka zalika muryarsa na fita da wani amo na ɓacin rai, yana jin a wannan lokacin idan dai har tace zata nuna masa rashin tarbiyya a gaban kowa ze hukuntata, hukunci me tsanani ma kuwa. Gaba ɗaya en ajin kallansa suke yi cike da mamakin yanda ya chanja ɗin lokaci guda, kowannensu ya san shi ɗin tsayayyen namiji ne wanda baya ɗaukar raini, baya bayar da fuskar da za a raina shi, se dai yau ɗin ya sake nuna musu real Affan ɗin ne. Kanta ta ɗauke duk da yanda ƙirjinta ke bugawa amma ta riga ta ɗaukar wa kanta alƙawarin babu wanda ya isa ya wulaƙantata musamman ma kuma Malamin makarantar islamiyya. Hakan ne ya sanyata yin shiru tana ɗan lumshe idanunta. Gaba ɗaya en ajin kallanta suke yi, wasu na mamakin taurin kai irin nata, yayin da wasu da suka santa suke jinjina yadda ta iya yiwa Gwanin taurin kai. A hankali Didi ta runtse idanunta tana ji kamar tayi kuka saboda takaicin abin da Lulun ta aikata. Cikin dabara ta kai ƙafarta kan ta Lulun ta taka sosai, har se da Lulun ta juya ta kalleta, suna haɗa ido Didi ta girgiza kai, kyawawan idanunta cike da ƙwalla. Da sauri Lulu ta ɗauke kai, dan sarai ta gane abin da Didin ke nufi. Sam bata son ɓacin ran Didin se dai ita bata bin bayan dizgi ko waye kuwa ze yi mata ba zata ɗauka ba. Se dai cikin dakewa da basarwa ta miƙe a hankali ta soma takawa hannunta harɗe a ƙirji, fuskarta a haɗe ta fice daga ajin. Duk da abin nan da ya faru har ta fita ɗin ba ka jin motsin kowa, ko na surutunsa, kowa ya bar maganar ne a ransa, imma dai idan Gwani ya fita su tattauna ko kuma idan aka tashi. Kwantar da kanta Didi tayi akan bench ɗin gabanta tana sauke ajiyar zuciya.

"Why Lulu?" Ta faɗa akan laɓɓanta har zuciyarta tana jin babu daɗi sam. Se dai a wannan karon tana ganin dole ne ta faɗa wa Ammi abin da Lulun take yi dan ayi wa tufkar hanci tun yanzun.

Da sallama ya shiga Office ɗin me makarantar, ya nemi waje ya zauna fuskarsa a cunkushe babu fara'a, da yake dai dama can ba wata fara'a gare shi ba so yanzu ma idan ka ganshi ba zaka gane a wane yanayi yake ciki ba, se dai shi kaɗai ya san yadda yake jin ɓacin rai a yau ɗin.

"A'ah Malam Affan, Barka da zuwa." Malam Ahmad ya faɗa yana murmushi.

"Yawwah." Ya faɗa a nutse. Baya san ɓata wani lokaci hakan ne ya sanya shi faɗin

"Amm, wata magana ce.."

"Toh Ikon Allah, ina jinka." Malam Ahmad ya faɗa yana kallansa cike da mamaki, dan kuwa ba kasafai Gwanin ke zuwa da wata maganar ba. A nutse ya soma faɗin
Chapter 10 · 0% Book details