Sashe 23
A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read
"Ni kuma?" Didi ta faɗa tana buɗe ido.
"Ehh fa.."
"Toh waye shi?" Didi ta katseta da faɗin hakan.
"Nima ban sani ba. Amma ki je se ki ji koh?"
"Ni ba inda zan je." Didi ta faɗa tana juyawa dan komawa cikin gida. Da sauri Lulu ta yi maza ta koma gabanta tana faɗin
"A'ah Didi ka da ki yi haka. Kin ga har wajen Abba ya je plss.."
"Toh me zan masa?" Ta yi maganar tana tura ɗan ƙaramin bakinta gaba.
"Toh ki je ki jiyo mana." Ba dan taso ba haka ta soma takawa cike da takun nan nata na nutsuwa zuwa wajen bayan Lulu ta ɗan rakota. Cikin siririyar muryarta ta yi sallama tana neman waje ta zauna. Tunda ta tunkaro shi ya zuba mata idanu. So yake ya gano shin akwai banbanci tsakaninta da wadda ta tafi yanzun ko kuwa da gasken tsananin kamarsu ce ta ruɗa shi har ya kasa tantance wadda ta ruɗa masa tunani, ta hana shi nutsatstsen bacci, kullum se tunaninta, da hango kyakkyawar fuskarta.
"Lallai Allah me halitta." Ya faɗa sanda Didi ta ƙaraso wajen, lokacin kuma da ya gama fahimtar lallai da gasken dole ne ya ruɗe, ya kasa bambance wadda ya fara gani har ta tafi da shi. Wani irin sabon sonta ya tsirga masa tun daga kansa har ƙafa. Ya ɗan lumshe idanunsa kafin ya buɗe yana amsa sallamarta ta kana ya ɗora da
"Amincin Allah ya tabbata a gareki ya ke wannan kyakkyawar ma'abociyar kwarjini."
"Ameen kaima haka." Didi ta faɗa tana ji kamar ta tashi daga wajen ta ruga zuwa cikin gida, musamman saboda yadda kanta ke ciwo, da kuma yanda take jin wani banbarakwai, tana kuma ji kamar saɓo take aikatawa zaman nata da wani namiji a irin shekarunsu.
"Kin wahalar min da zuciya Kyakkyawatah." Ya faɗa a narke kamar wani ƙaramin yaro, har se da hakan ya sanyata saurin ɗaga ido ta kalle shi. Ya sakar mata wani murmushi yana sake langaɓar da kai gefe kamar yaron goye lokaci ɗaya yana furta
"Da gaske na ke fa. Na san da yau ta wuce ban yi ido huɗu da fuskarki ba za a iya ganina a gadon asibiti, saboda yanda ko da yaushe zuciyata ke harbawa saboda ƙaunarki.." yanzun ma dai ƙare maganar ya yi a shagwaɓe. Daidai lokacin da wayarsa ta soma ringing kenan. Se ya kalleta a nutse yace bayan ya sakar mata murmushi
"1mint pls.." ya yi maganar yana miƙewa. Itama miƙewar ta yi ta soma takawa zuwa inda Lulu take. Haushi da takaici kamar su karta.
"Didi me ya faru?" Lulu ta tambaya tana kallan yanda Didin ta haɗe rai kamar wadda aka daka.
"Ɗan iska ne!.." Da sauri Lulu ta buɗe ido sosai tace cikin rashin fahimta
"Ɗan iska kuma?" Ta yi maganar manyan kyawawan idanunta a waje.
"Ehh mana.. Ni ze yi wa shagwaɓa." Didi ta faɗa tana harara kamar Kaseem ɗin na gabanta..
https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8
*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*
By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_
*CHAPTER ONE*
Page_15
___Dariya Lulu ta sheƙe da ita har da sunkuyawa. Se da ta yi me isarta sannan ta ɗago tana kallan Didi tace
"Shagwaɓa kuma Didi? Ƙato da shi?" Taɓe baki Didi ta yi sannan tace
"Ehh fa, ba kyan gani.." ta ɗan dakata daga nan se kuma ta ɗora da
"Ke mu tafi gida, ni jikina ma rawa yake yi tun ɗazu.."
"Allah nima haka" Lulu ta faɗa tana riƙe hannun Didin dan komawa gida. Se kuma Didi ta dakata a hankali tace
"Amma kamar ba mu kyauta ba koh?" Cikin mamaki Lulu tace
"Me muka yi?"
"Da zamu tafi mana ba sallama" Shiru Lulu ta ɗan yi na sakanni, se kuma can tace
"Toh mu je mu ce masa se da safe." Duk se suka juya suka soma komawa zuwa inda Kaseem ɗin yake, aikuwa daidai lokacin da shima ya gama wayar da yake yi. Se da ya sakar musu murmushi sannan yace yana kallansu su duka
"Tabarakallah Masha Allah.." ya faɗa sanda ya sake tabbatar da lallai kamannin nasu sakk da sakk ne wanda shi dai be ga wani banbanci ba. Ba dan hijab ɗin jikinsu kala daban daban ba ne da babu yanda za a yi ya gane Didin tasa.
"Lafiya dai koh Gimbiyata?" Ya yi maganar yana kallan Didi. Sosai dariya ta ciyo Lulu se dai ta maza ta yi ta a cikin ranta, a kan laɓɓanta ta furta
"Wai gimbiya.." yayin da Didi kuwa waɗannan sunayen da yake ta kiranta da su ita haushi ma suke bata. Daga ganin mutum kawai se ya dinga ce mata Gimbiya. Gashi kuma dama tun ɗazu a tsorace take saboda wannan sabon al'amarin na keɓewa da namiji su yi magana.
"Tafiya zamu yi." Ta faɗa cikin sanyin nan nata. Lumshe idanunsa Kaseem ya yi yana jin muryarta ta har cikin zuciyarsa, sannan ya yi murmushi yace
"Kin gaji ne?" Da sauri ta jinjina kai. Se ya sake yin murmushin kafin yace
"Tohm shi kenan. Bari na tafi amma fa zan dawo. Ki kula min da kanki. Allah kuma ya tsare min ke a ko ina.." Wata irin kunya ce ta lulluɓe Didin, ita har ga Allah kunya yake ta bata, babba da shi ya dinga irin waɗannan maganganun. Se dai kuma haka kawai ta tsinci kanta da yin murmushi da kuma dena jin haushinsa da ta ji a farko. Ita kam Lulu se ta juya kamar ta fashe da dariya a wajen.
"Toh" shi ne kaɗai abin da Didi ta iya furtawa.
"Good nyt Twinnynmu" ya yi maganar yana kallan Lulu.
"Uhmm" Lulu ta faɗa bayan ta juyo tana ƙaƙalo murmushin yaƙe. Daga haka suka juya a tare zuwa cikin gidan. Se ya yi murmushi yana jin yanda zuciyarsa ta yi wani irin sanyi, yau ɗin se yake jinsa kamar yafi kowa dace tunda ya yi tozali da kyakkyawarsa. Kai tsaye ficewa ya yi daga gidan ya hau motarsa ya soma driving cike da farin ciki. Ba ya jin ze iya sake yin ko da kwana 1 ne be sanyata a idanunsa ko ya ji muryarta ba.
"Oh my god.." ya faɗa sanda ya tuna be karɓi contact ɗinta ba.
"Ya aka yi haka ne? Me ya mantar dani?" Ya yi tambayar kamar akwai wani a gefensa da ze ba shi amsar. Jin shiru ne ya sanya shi lalubo amsar da kansa, ya san tabbas ganinta da ya yi ne ya mantar da shi ma wata number. Aikuwa ya yi babbar mantuwa wanda dole ne ya koma ko dan nemo abin da ze sanya shi dinga jin muryarta ko da yaushe.
A compound ɗin gidan ya ajje motarsa kasancewar babu wanda be san shi cikin gidan ba, shi yasa be samu tsaiko ba a lokacin da ze shigo. Dan haka yana gama parking se ya sakko daga motar har lokacin murmushi yaƙi barin fuskarsa ya wuce parlourn Daddy bayan sun yi waya da shi. Da sallama ya shiga cikin parlourn, Daddy na zaune a kan wasu haɗaɗɗun kujeru da ke zaune a can wani gefe cikin ɗakin, waɗanɗa da alama an yi su ne dan hutawa ko kuma karatu. Daddyn na zaune kan kujera yana karanta jarida idanunsa sanye cikin wani glass da ya matuƙar amsar kyakkyawar fuskarsa me kama da ta Bad Man.
"Barka da wannan lokaci Daddy" Kaseem ya faɗa sanda ya nemi waje a ƙasan kujerar Daddy ya zauna. Murmushi Daddy ya yi yana ajje jaridar hannunsa sannan ya saka hannu ya sauke glass ɗin fuskarsa kana yace
"Barka dai Kaseem. Ka shigo?"
"Ehh Daddy.."
"Toh barka da zuwa.. Ina ɗan uwan naka?"
"Na ɗauka ma zan same shi a nan ɗin ai Daddy. Buh let me call him." Ya yi maganar yana fito da wayarsa dake cikin aljihu.
"Nop! let me call him my self." Daddy ya faɗa yana ɗaukar rantststsiyar wayarsa dake a gefensa ya ɗakko number Bad Man ɗin ya kira. Ringing 1_2 ya ɗaga.
"Kana ina?" Daddy ya tambaya. Daga can ɓangaren ya ɗora wata hula me kyau a kansa sannan yace
"Ina ɗakina."
"Amma ka manta maganar da muka yi?"
"Ohhh sorry Dad.. Bari na zo." Ya faɗa yana takawa zuwa kan gado ya zauna ya shiga gyara zaman takalminsa. Be daɗe cikin parlourn ba ya fito zuwa sashen Daddyn se zuba ƙamshin daɗɗaɗan turarensa yake yi, tafiyarsa kaɗai abin kallo ce, haka zalika kayan dake jikinsa ma na tashin kai ne. A haka har ya ƙarasa parlourn Daddyn.
"Sannu da hutawa.." Bad Man ya faɗa bayan ya zauna a kan kujerar gefen Daddy ya ɗauki ƙafa ɗaya ya ɗorata a kan ɗaya. Wani kallo Daddyn ya watsa masa ba tare da yace komai ba. Se ya ɗan buɗe baki sannan ya saka hannunsa ya sauke hular dake kansa kana yace
"Sorry Sir.." ya faɗa yana saukar da ƙafar da ya ɗora a kan ɗayar. Se a lokacin sannan Daddy ya kalli Kaseem yace
"Koma kan kujerar." Ya san halin Daddyn ba ƙaunar musu yake yi ba musamman kasancewarsa mutum me zafi dan haka kawai se ya hau kan kujerar kusa da Bad Man ya zauna. Se a lokacin suka gaisa, duk da basu daɗe da yin magana a waya ba. Bayan wajen minti 2 Daddy yace
"Amm kai Areef.. ga ɗan uwanka nan In Sha Allah zuwa nan da sati 2 nake so ku soma kasuwancinku na ƙashin kanku. Ba na so kowa ya zauna ƙarƙashina, hakan ba abin tutiya bane. Na fi so dukanku ku ci gashin kanku." Jinjina kai Kaseem ya yi sannan yace
"Muna godiya sosai Daddy. Allah ya ƙara girma da arziƙi me amfani."
"Ameen ya rabb" Daddy ya yi maganar yana maida dubansa kan Bad da ke danna wayarsa. Duk da ya ji abin da Daddyn ya faɗa se dai shi gaba ɗaya hankalinsa ma na kan Hero da suke magana, yanzu kuma ya ji Daddyn na maganar kasuwanci, hakan na nufin ko da yaushe ze iya fita daga gida ba tare da wani takunkumi ba.
"Heyy!" Daddy ya faɗa yana kallan nasa. Kamar kuwa ya san da shi ake, daidai lokacin da ya ajje wayar ya ɗaga kai ya kalli Daddyn kana yace