Sashe 15
A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read
"Barta ta je, ina son na yi miki faɗa ne sosai. Idan tana nan zata dinga rarrashinki, idan kuwa bata nan fa? Didi je ki abinki.." tun kafin Mamin ma ta gama maganar Didi ta fice daga ɗakin. Lulu ta bita da kallo har ta fice ɗin. Sannan ta dawo da dubanta kan Mami da itama ta bi Didi da kallo har ta fice. Ajiyar zuciya ta sauke sannan ta saka hannunta a cikin jakarta ta ɗauko waya, kana ta ɗago tana kallan Lulu ta soma faɗin
"Kina ji na?" Tayi maganar tana juya wayar hannunta..
*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*
By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_
*CHAPTER ONE*
Page_10
__"Ehh Mami." Ta faɗa tana kallan wayar. Se da Mamin ta gyara zama sannan tace
"Riƙeta ki ji." Tayi maganar tana miƙa mata wayar. Babu musu ta saka hannu ta karɓa tana kallan Mamin, dan ta ƙagu ta ji abin da zata faɗa matan.
"Ki ajjeta a wajenki, za a kiraki zuwa anjima. Kada kice ba zaki ɗaga ba dan na san halinki, kin ji koh?" Baki ta tura gaba tana ajje wayar kamar wadda ta ga wani abun tsoro, ta kuma soma yamutsa fuska. Harara Mami ta jefa mata sannan tace
"Bana son iya shege Lulu.."
"Ni wallahi a'ah Mami, bana so. Ni nace miki ina son waya?" Iska Mami ta furzar tana tunanin yanda zata yi ta shawo kan Lulun.
"Tsaya ki ji, ki ajje wayar nace a wajenki koh? Na ji ba za a kiraki yau ba, se gobe uhmm?"
"Wai ke ce zaki kira?" Ta tambaya cike da sakarcinta.
"Wayyo Allahna Lulu.." Mami ta faɗa tana dafe kanta gami da sauke ajiyar zuciya.
"Bani wayar" tayi maganar tana ɗaukarta daga inda Lulun ta ajjeta. Kasheta tayi gaba ɗayanta sannan ta miƙe ta ƙarasa zuwa wajen wardrobe ɗinsu, ta buɗe ta Lulu ta sakata a ƙasan kayanta sannan ta dawo ta zauna tace
"Na san Yaya da kuma Amminku ba za su barki yanzun ki fara kula samari ba. Toh wata gagarumar dama ce ta samemu Lulu, saboda haka wannan wayar ki kunnata zuwa gobe zan kiraki. Sannan kuma ko da an kiraki ki ɗaga, wani ne ya ganki yace yana so. Ki ba shi haɗin kai kinji? Idan komai ya daidaita ni da kaina zan sami Yayan da maganar. Me ye dan kin fara soyayya a S.S 1?" Ita tun ɗazu da ta fara magana sam bata fahimci abin da take so ta faɗa ba, se yanzu da ta ambaci soyayya. Dan haka cikin sauri ta soma ƙoƙarin miƙewa tana faɗin
"Kaii!!" Tayi maganar tana fiddo da idanunta waje. Hannunta Mami ta janyo, tana tunanin yanda zata ɓillowa Lulun kada ta ɓarar musu da wannan gwagwgwaɓar damar. Se dai ta riga ta san halin Lulun wani lokacin a botsare take. Dan haka cikin rarrashi tace tana murmushi
"Dawo ki zauna daughter."
"Ni wallahi ki sakar min hannu Mami. Hmm uhmm jam!" Ta faɗa ainahin ƙuruciyarta na bayyana, wanda hakan har se da ya sa Mamin ta sake murmusawa.
"Ke da wasa fa nake. Dawo ki yi zamanki, ni ce na siyo miki wayar saboda na ga kina sonta.." Se a lokacin sannan Lulu ta tsaya tana kallan Mamin.
"Don Allah?"
"Ehh mana, ko ba kya so?" Se tayi murmushi tana komawa ta zauna cike da jin daɗi. Se kuma ta ɓata fuska tace
"Toh ta yaya zan yi amfani da ita? Idan kuma Abba ko Ammi suka gani fa?"
"Ba ma zasu gani ba, se dai idan ke ce kika yi niyya." Mami tayi saurin bata amsa. Ta buɗe baki za tayi magana Ammi tayi sallama cikin ɗakin. Se ta fasa cewa komai. Ammi ta ɗan kallesu sannan ta ƙaraso ta nemi waje ta zauna.
"Uhmm bari ki ga na zo na tafi.. dama unguwa fa zan wuce daga nan ɗin." Mami ta faɗa tana miƙewa. Kallanta Ammi tayi da ɗan mamaki, se dai kawai ta basar tace
"Haba dai, har kuma zaki tafi?" Yaƙe tayi tana faɗin
"Wallahi kuwa, gwara na tafi.." ta faɗa tana yafa mayafinta. Lulu da Ammi suka miƙe, suka fito parlourn tare. Da sauri Didi da ke zaune a ɗakin ta kulle idanunta kamar me bacci, dan ita dai haka kawai yau ɗin take jin haushin Mamin.
"A'ah Afrah bacci take kenan?" Mami tayi tambayar ba dan tana buƙatar amsa ba. Har compound suka rakata, suka yi sallama. Har kuma suka koma Ammi bata basu damar keɓewa sun yi magana ba, wanda hakan ba ƙaramin sosa zuciyar Mami yayi ba, dan dai kada a fahimci wani abun ne ya sanyata mazewa.
.. Sanye cikin ƙananan kaya kamar yanda kuka san Bad Man ɗin ma'abocinsu ne yake, kansa ya ɗora masa wata haɗaɗɗiyar facing cap da ya juyar da ita ta baya. Hannunsa ɗaya na cikin aljihun wandonsa yayin da shegiyar hamshaƙiyar wayarsa ke ɗayan hannun nasa kafe a kunnensa yana amsa waya. A haka ya cigaba da takawa har zuwa wajen motarsa. Kai tsaye ya shige, bayan ya katse kiran ya tasheta. A bakin tanƙamemen gate ɗin gidan nasu ya tsaya yayi horn, da yake yana idar da Sallahr isha'i ya fito, se ya kasance yawanci duk suna cikin masallaci, se ɗaiɗaiku saboda ba a barin wajen haka babu kowa. Be haƙura ba ya sake danna horn fuskarsa a matuƙar haɗe yana kallan wanda ke tsaye a wajen. Daga gefe yaji an yi knocking glass ɗin gefensa. Kamar ba ze juya ba, se kuma ya juya a hankali ya watsawa wanda ke tsaye a wajen idanun nan nasa bayan ya sauke glass ɗin kaɗan. Cikin lokaci ƙanƙani ya ɗan daburce, da ƙyar ya iya soma faɗin
"Yallaɓae sun ce kada a buɗe gate ɗin. Wai kada kowa ya fita. Kayi haƙuri yallaɓae." Ya ƙarasa maganar cike da girmamawa.
"Kai! Ni sa'anka ne?" Ya ƙare ransa a ɓace, yana jin yanda zuciyarsa ke tafasa.
"Will u just open the gate for me ko kuma.." Tun kafin ya ƙarasa Idi yayi gaba da sauri ya ƙarasa jikinsa na rawa ya buɗe gate ɗin. Me gadin da ke zaune a wajen yana kallansa. Se dai bece komai ba har Bad ɗin ya fice daga gidan. Se a lokacin ya kalle shi yace
"Shi ne ka buɗe masa kofar koh? Idan suka fito me zaka ce musu?" Cikin fushi Idi yace
"Me yasa da na buɗe a gabansa ba ka zo ka rufe ka ce ba ze fita ba? Se yanzu zaka wani zo kana faɗa min magana."
"Ni dai wallahi idan suka zo babu ruwana, ban ma san kayi hakan ba." Tsaki Idi ya ja duk da yadda shi ma yake a tsorace, amma tsoron Bad Man ɗin yafi tsoron mutanen. Dan kuwa ya san idan da be buɗe masa ƙofar ba ko me nene ya biyo baya shi ya jawa kansa.
Wani ƙaramin joint se dai haɗaɗɗe Bad Man ya wuce. Ya sauka ya soma takawa zuwa ciki, gefen swimming pool inda mutanen da ke zaune a wajen basu da yawa, se dai kowa da abin da yake yi.
"Heyy Bad!" Na ji an faɗa cikin er ɗaga murya. A nutse ya ɗaga lumsassun idanunsa ya kalli Hero da ya kira sunansa. Ya ɗan yi murmushin da ke ƙawata kyakkyawar fuskarsa. Cikin sauri Hero ya ƙaraso ya rungume shi yana faɗin
"Wai dama da gaske kake?" Be ce komai ba se
"Uhmm" kawai da yace.
"Let's go Friend.." Hero ya faɗa yana jan hannunsa suka ƙarasa suka nemi waje suka zauna. Ɗan kishingiɗa Bad Man yayi yana sauke ajiyar zuciya ganin tarin drinks a wajen kala_kala se wanda ya zaɓa.
"Kana nan kana sharholiyarka koh?" Yayi maganar a hankali kamar wanda aka ma dole. Ɗan shafa kansa Hero yayi yace
"Ba zaka gane ba ne Friend.. dole se ana yi ana ɗan ehh yaaa..nee." Hannu Bad Man ya saka ya janyo wata hamshaƙiyar kwalba wadda da alama ma ko taɓata ba a yi ba. Ya ja ƙaramin tambulan ya tsiyaya a ciki sannan ya janyo ruwa shi ma ya ɗan tsiyaya a kai kana ya ɗauka. Duk abin da yake Hero kallansa kawai yake yi. Se da ya ga yana shirin kaiwa baki sannan yace
"Wait Friend.. Me nake gani? Kana nufin.."
"Yeap!" Bad ya katse shi da faɗin haka. Wani ihu Hero ya saki hadda miƙewa tsaye. Se kuma ya koma ya zauna yana dariya yace
"Shege Bad Man.." shi dai be bi ta kansa ba ya soma kai cup ɗin bakinsa ya shanye abin da ke ciki tass. Be jira ba ya sake ƙara wata cikin cup ya sake kaiwa bakinsa, shi kuma Hero se zuga shi yake yi cike da farin ciki. Ana cikin haka, zuwa lokacin ya ɗan soma jin kansa na ɗaure masa, dan be tsaya tunanin komai ba ya fara afata a cikinsa. Se dai sam tsadarta ba ta kai wadda yake amfani da ita ba, shi yasa ma ya ji ta kamar wani sabon abu. Wayarsa da ke ajje ta soma ringing. Da idanunsa da ke a lumshe ya ɗan buɗe ya kalli wayar, shi sam be saba jin irin yanayin nan dan ya sha wani abun ba, ya dai buɗe idanun nasa yana gyara zamansa. Ɗaukar wayar Hero yayi yana faɗin
"Noo Bad. Ba zaka iya answering call ba a wannan yanayin.." Ɗan tsuke face yayi yana watsa masa idanunsa duk da har lokacin kansa sake yi masa nauyi yake. Yace bayan ya ɗan janyo iska daga huhunsa
"Give..me.." yayi maganar a ɗan rarrabe yana miƙa masa hannu. Babu musu ya miƙa masa wayar, ba tare da ya kalli me kiran ba ya ɗaga. Daga can ɓangaren Aunty (ƙanwar Mom) tace
"My son.." sarai ya gane muryar wace duk kuwa da yanda yake jinsa kamar ba shi ba. Cikin ƙarfin hali yace
"Yes Aunt.."
"Ya na ji muryarka haka? Ko har yanzu baccin gajiya ka ke?" Auntyn ta tambaya
"Uhmm" kawai ya faɗa har lokacin idanunsa a lumshe. Fahimtar bacci yake yi ne ya sanyata faɗin
"Olright i will call u later.. Sleep well.." Daga haka ta yanke kiran ba dan ta so ba, dan ta so ne su ɗan gaisa sosai saboda yadda wata muhimmiyar tafiya ta kamata a ranar da ya dawo daga California.