Sashe 16
A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read
.. A nutse ya saka kansa cikin ɗakin bakinsa ɗauke da sallama. Ummeey ta amsa sallamar tana kallansa. Se ya ƙaraso ya nemi waje ya zauna kusa da Ummeeyn. Sanye yake cikin wani tattausan yadi me kyau wanda ya matuƙar yi masa kyau, kansa babu hula, se kwantacciyar baƙa ƙirin ɗin sumar kansa kamar ta larabawa. Yau ne karon farko da na soma ganin kansa a buɗe, ni se na ga ma kamar yafi kyau a hakan. A nutse ya kalli kan gadon da Abeey ke kai a kwance yace
"Ummeey bana son fita. Ki bari na soma kai shi asibiti tukunna." Kallansa Ummeey tayi yanda ta ga damuwa ƙarara a kan kyakkyawar fuskarsa. Se ta maida dubanta kan Abeey tace
"Ka bari ya kai ka a dubaka mana." Girgiza kai Abeey yayi yana ɗan murmushin ƙarfin hali kafin ya buɗe baki yace
"Haba.. haba.. ciwo ne fa kamar na ko da yaushe. Duk kun bi kun damu kanku kamar yau na fara irin wannan ciwon? Kai Affan.." ya dakata yana kallan Gwani
"Na'am Abeey."
"Tashi ka tafi makaranta. Ka bar ɗalibai na jiranka."
"Abeey!" Gwani ya faɗa yana kallan Abeeyn da kana kallansa ka san baya jin daɗi.
"Affan! Ni nace maka ka je koh?" Abeey ya faɗa yana kallansa. Se ya jinjina kai a nutse kafin ya miƙe jikinsa a sanyaye. Duk da be so hakan ba, amma tunda Abeeyn yace ya tafi gwara ya tafi ɗin. Dan haka ya juya ya kalli Ummeey yace
"Ummee bari na je.. Abeey Allah ya ƙara maka lafiya."
"Ameen_Ameen ɗan albarka. Allah ya tsare." Abeey da Ummeey suka kusan haɗa baki wajen faɗar hakan.
"Ameen." Ya amsa a nutse, kafin ya fice daga ɗakin. Kai tsaye ɗakinsa ya koma ya sake shiryawa kamar yanda ya saba fita, ya naɗe kansa sannan ya fice zuwa makarantar.
.... "Wato Afaaf baki da kirki koh? Ni zaki zubarwa da mutunci a idon duniya?" Da sauri ta ɗaga kanta cike da mamakin jin furucin Abban. Se dai ta riga ta san halin Abban, idan yana faɗa baya so a ce komai. Hakan ne ya sanyata yin shiru, ta maida kanta ƙasa, kamar mutuniyar kirki ta gaske.
"Tunda har suka kirani suka faɗa min laifinki, hakan ya nuna ba tun yau kika soma ba. Wato kin daɗe kina nuna musu rashin daraja, se da kika kaisu bango sannan suka faɗa min. Ni ba ma su burgeni ba da basu zane min ke ba, sannan kuma ki dawo ni nan na ƙara miki da wani sabon, shashashar yarinya." Sosai Abba ya cigaba da mata faɗa, wanda a yadda na ga yanayinta kamar ya shigeta. Se daga ƙarshe Abba ya ƙare da faɗin
"Ina so ki buɗe kunnenki da kyau ki ji, ka da ki bari, ka da ki sake a sake kawo min ƙararki daga makarantarku, ko bokon ko islamiyyar. Idan ba haka ba wallahi zan saɓa miki Afaaf, zan saɓa miki kin ji na faɗa miki." A hankali ta ɗaga kai alamar "Ehh" sannan ta buɗe baki a hankali tace
"Ka yi haƙuri Abba."
"Ka da ki sake." Ya faɗa kawai yana soma takawa dan ficewa daga ɗakin.
"Cewa en uwanki su fito mu tafi, yau da kaina zan kai ku." Bata kawo komai a ranta ba, ta miƙe ta koma cikin ɗakinsu, inda Didi ke zaune duk da ba jin faɗan take ba, amma duk a dame take kamar ita aka yiwa faɗan. Da sauri ta kalli Lulun, se dai yanda ta ga fuskarta ne babu yabo ba fallasa ya sanyata ɗan jin sanyi tace
"Lulu!"
"Uhmm! Abba yace ku fito ze kaimu." Tun kafin ta ƙarasa faɗa Little har ya miƙe ya fice daga ɗakin a guje. Didi ta miƙe cikin sanyin nan nata ta riƙo hannun Lulu tace
"Sorry." Ta faɗa fuskarta a ɗan narke. Ɗauke kai Lulu tayi sannan tace
"A'ah. Ai dama haka kike so." Waro manyan idanunta Didi tayi sannan tace
"Nii! A'ah fa.. Ni kawai so nake ki chanja daga wannan Lulun kin ji?"
"Tohm" Lulu ta faɗa.
"Dat's my baby gurl." Didi ta faɗa a ranta tana fatan Allah ya sa daga yanzun Lulun ta chanja gaba ɗaya. Kai tsaye compound ɗin gidan suka nufa. Abba na cikin motar har ya tayar da ita ma. Babu ɓata lokaci suka shige bayan motar dan Little ya shekara a gaba. Se da suka shiga sannan Abba ya tayar da motar suka bar gidan. Kai ba zaka ce Abban ne yanzu ya gama faɗa ba, yanda ya saki jiki yana jan 'ya'yan nasa da hira. Hakan ba ƙaramin kwantar da hankalin Lulu yayi ba, ko babu komai ta san ya sakko. A ƙofar makarantar Abba yayi parking motarsa. Se dai ga mamakinsu su duka, se ya sauka daga motar shi ma. Kallan juna Didi da Lulu suka yi, Lulu ta ɗan karkatar da kanta alamar tana tambayar Didin ko ta san dalilin Abban na yin haka? Girgiza kai Didi tayi. Ganin babu wanda ze amsa musu tambayar ya sanya su saukowa daga cikin motar.
"Abba a dawo lafiya." Suka haɗa baki wajen faɗa.
"Allah ya sa. Mu je ciki, ina son ganin malaminku." Haka kawai dukkansu suka ji jikinsu yayi sanyi, amma se suka basar suka bi bayan Abban dake riƙe da hannun Little zuwa cikin makarantar.
"Afrah kama hannun Little ku shige. Zamu ga Malam Affan." Abba ya faɗa yana miƙawa Didi hannun Little. Karɓar hannun nasa tayi tana faɗin
"Toh Abba." Se ta kalli Lulu da ke tsaye kamar wadda aka dasa. Dan tunda Abba yayi maganar ta kasa cewa komai. Ɗan lumshe mata idanu Didi tayi tana jinjina mata kai dan ta bata ƙwarin gwuiwa. Se itama ta lumshe idanun tana ɗan sauke ajiyar zuciya. Haka nan kawai se ta ji a ranta ba se ta tambayi Abban dalilin tsayawarsu ba, dan ta san zuwa yayi kawai ya gaisa da Gwanin. Malam Ahmad ne ya ƙaraso wajen Abban, ya miƙa masa hannu suka gaisa sannan Abba yace
"Malam Affan be shigo ba ne?" Jinjina kai Malam Ahmad yayi kana yace
"Wallahi kuwa. Amma na tabbatar wani babban uzuri ne ya riƙe shi. Zaka iya jiransa idan ba sauri kake ba."
"Ehh toh.. da yake dai akwai inda zan je ne, ina ga zan tafi, se na dawo." Wani irin sanyi Lulu taji yana ratsata jin furucin Abban. Sosai hakan ya mata daɗi dan dama bata so a ce Abban da kansa su gaisa da Gwanin. Se dai tun kafin Malam Ahmad ya kai ga cewa komai Gwani ya shigo cikin makarantar cike da takun nan nasa na nutsuwa.
"Aff, ka gan shi ma ya zo." Malam Ahmad ya faɗa yana murmushi. Cikin jin daɗin ganinsa Abba yace
"Toh madallah." Suka sake gaisawa sannan Malam Ahmad ya bar wajen. Se da suka gaisa da Gwani ya faɗa masa Abba wajensa ya zo sannan ya wuce. Wani irin takaici ya zo ya cika Lulu, ta ji kamar tayi kuka dan haushi, ta faki idanun Abba ta watsa masa harara sannan tayi saurin ɗauke idanunta kada ko shi ko Abban wani ya ganta. Sallama yayi sanda ya ƙaraso wajen Abban. Abba ya amsa sallamar yana miƙa masa hannu suka gaisa cike da girmama juna.
"Amm Malam Affan, idan babu damuwa ga Afaaf nan na dawo da ita. Ina kuma sake baka haƙuri don Allah kayi haƙuri, In Sha Allah hakan ba zata sake faruwa ba." Nauyin maganar da ke fitowa daga bakin Abban ya sanya Gwani ɗago kai yana girgiza kai sanda wani ɗan murmushi ya suɓuce a kan fuskarsa yace
"Ka dena bani haƙuri don Allah.." Shi ma murmushin Abba yayi kafin yace
"Toh shi kenan. Amma ga ta nan na kawota ta baka haƙuri!" Da wani irin sauri ta ɗaga kai ta kalli Abba tana so ta tabbatar da gasken abin da taji a kunnenta, hakan Abba ya furta? Kallan gargaɗin da taga Abba ya jefeta da shi ne ya sanyata shan jinin jikinta. Shi kuwa Gwani se a lokacin ma ya san da wanzuwarta a wajen.
"Babu komai, kaje kawai, zuwanka ma ya wadatar." Gwani ya faɗa. Girgiza kai Abba yayi be ce komai ba se sake kallan Lulu da yayi kafin yace komai ta fahimci abin da yake nufi. Dan haka ta ɗan lumshe idanunta tana jin yadda bugun zuciyarta ke cigaba da ƙaruwa. Narkakkun idanunta sun cika taff da ƙwallar baƙin ciki ta soma takowa zuwa inda suke. Da ƙyar ta iya tausar zuciyarta ta tattaro kalmar haƙuri, se dai bata kai ga furtata ba ta jiyo muryar Abba na faɗin
"Tsuguna ki ba shi haƙuri." Yayi maganar fuskarsa a haɗe, dan kuwa shi kansa ya soma fuskantar take_taken Lulun, shi kuma ba ze yi sake ba wajen kula da tarbiyyarta. Dan haka idan ma tana tunanin tafi ƙarfin kowa ciki kuwa hadda malaminsu, toh yau ɗin zata gane malamin nasu ya fita matsayi. Sosai taji kanta ya wani irin juya mata, idanunta a rufe na tsawon sakanni, ƙafarta na wani irin rawa, tana jin maganar da Abba ya faɗa ɗin kamar wata wuƙa aka saka aka yanketa. Ita a wajenta ma har gwara a yanketa ɗin da a ce ta tsugunawa Gwani wai ta bashi haƙuri. Kallanta Abba yayi a ransa yana fata kada a ce Lulun ta sake nuna halinta tun ba a je ko ina ba, dan idan hakan ta faru toh babu shakka yau me raba shi da ita se Allah. Cikin rashin sanin mafita ta zube a kan gwuiwoyinta, zuwa lokacin tuni hawayen da suka cika mata idanu sun gama zuba a kan fuskarta. Wani irin sanyi na kaɗa ilahirin jikinta. Ba dan taso ba, ba dan kada ta wulaƙanta Abbanta a gaban mutane ba, da babu abin da ze sanyata tsugunawa ta bawa Gwanin haƙuri, ko da kuwa korarta za a yi daga makarantar. Duk yadda zuciyarta ke mata ƙuna, tana hanata aikata abin da mahaifin nata ya umarceta da yi, haka ta take, ta cije, ta buɗe baki da ƙyar tace
"Ka yi haƙuri.." ta faɗa wasu sabbin hawaye masu ɗumi na kwaranyowa a kan fuskarta, lokaci ɗaya tana ji har abada mutuncinta da kuma ajinta ya gama tsiyayewa a bainar nasi..
*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*
By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_
*CHAPTER ONE*
Page_11