← Book details A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 37

Sashe 3

A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read

"Ranki ya daɗe cikin satin nan Yallaɓae Areef ze dawo." Kafin Hajiya Sa'adah ta bada amsa, Atine suka yi 4 eyes da Hajiya Salma, duk se ta duburburce, ta miƙe a sukwane, a hankali ta zo ta gifta ta gefen Hajiya Salman ta fice daga ɗakin. Wata banzar harara Hajiya Salman ta bita da shi kafin ta ja ƙwafa ta ƙarasa shigowa ɗakin. Kyakkyawar farar bafulatanar da ke zaune kan kujera sanye cikin wata haɗaɗɗiyar atamfa me mugun kyau ɗinkin doguwar riga, ta juya ta kalli inda Hajiya Salma ke tsaye dan ganin abin da ya saka Atine fita haka babu faɗar dalili, se taga Hajiya Salma na cigaba da takowa zuwa cikin ɗakin. Murmushi ta saki duk da na ƙarfin hali ne kasancewar ta ɗan kwana biyu bata ji daɗi ba.

"Ki ƙaraso mana" Ƙarasawar tayi ciki se dai bata nemi waje ta zauna ba, ta ɗan ajje numfashi kafin tace.

"Har an kawo miki gulmar yarona ze dawo kenan?" Ta tambaya tana kallanta. Ɗan murmushi Hajiya Sa'adah tayi kana tace

"Ba gulma ba ce, kawai dai ta faɗa min ne ko da ban sani ba" Jinjina kai Hajiya Salma tayi tana ɗan taɓe baki

"Eyyah, don Allah Sa'adah ki fita a harkar ɗana, ban san wannan ɗin wane irin abu ne ba. Ka da kice zaki shirya masa wani abu, dan yana da uwar da zata shirya masa, baya buƙatar na shishshigi. Don Allah ki kama kanki ki bari idan kika haifa se kiyi rawar kan akansa." Tun da ta soma magana Hajiya Sa'adah ke kallanta, ba tayi mamakin soma maganar da tayi ba dan dama ba yau ne karon farko da ta ke faɗa mata makamancin waɗannan maganganun ba, se dai yau ɗin mamakin yafi kamata sosai musamman da har se da ta shigo ɗakinta sannan take jifanta da waɗannan kalaman. A nutse ta buɗe baki duk da yadda take jin wani irin ɗaci a cikin bakinta, maganganun Hajiya Salman tabbas sun daketa sun kuma taɓata sosai

"In Sha Allah." Shi ne abin da ta iya furta wa sannan ta ɗauki wayarta tayi stairs ɗin da ke cikin ɗakin nata. Tsaki Hajiya Salma ta ja tana bin ta da kallo, a ranta tana fata da addu'ar Allah yasa ta bar mata ɗanta, ta dena wannan shishshigin ta bari idan ta haifi na ta se ta yi duk abin da za ta yi.

... A ɓangaren Twins kuwa ko da suka isa makaranta kai tsaye aji suka nufa, lokacin babu wanda ya shigo ajin, da yake ajin ba baya ba wajen sanin ya kamata se kowaccensu ta ɗauki Qur'an ta soma bitar haddar da za a karɓa yau ɗin. Kallan Lulu Didi tayi tace a hankali saboda karatun da ake yi

"Ki maimaita karatun mana" ta faɗa ganin ta ɗauki wani hadith tana dubawa.

"Didi na iya fa, ba se na maimaita ba." Sanin Lulun na da kaifin hadda ne ya sanyata yadda da hakan, ta rabu da ita, ita kuma ta cigaba da karatunta. Duk da yadda idanun Lulu ke kan hadith ɗin da take karantawa amma gaba ɗaya hankalinta ba ya kai, duk taurin kanta se take ji kamar ta ɗauki Qur'an ta yi haddar, amma se ta ji zuciyarta ta ƙeƙashe, hakan ne ya sanyata jan tsaki da siririyar muryarta ta cigaba da karatunta. Dukan da aka ɗaka mata a kafaɗarta ne ya sanyata saurin juyawa bayan ta ɗan saki ƙara saboda yadda dukan ya shigeta.

"Masoyiya!" Ta faɗa tana buɗa baki. Galla mata harara wadda ta kira da Masoyiyar tayi kana tace

"Ni zaki wa rashin mutunci koh? Ya miki kyau" ta faɗa tana neman waje ta zauna kusa da ita ta haɗe rai.

"Ke dallah makara fa muka yi, na ɗauka kin tafi" Lulu ta faɗa tana kallan Fateema Kabeer wadda ta kasance babbar ƙawarta a Islamiyyar ta su.

.. Sanye cikin wata lallausar brown ɗin jallabiya, sumar kansa saye cikin irin wannan naɗin da larabawa ke yi a wajen goshi zuwa bayan kansu. Kyakkyawa ajin farko, fari me ɗauke da wasu idanu masu mugun kyau, manya masu ɗauke da baƙar ƙwayar ido me shegen kyau, wata irin gira ce da shi wadda take a jere kamar wadda aka saita ta ta zauna akan fuskarsa ta matuƙar ƙawata ta, hakan ya sa har haɗewa da junansu se da suka yi, saboda se da suka bada wani irin shahararren kyau a tsakiyar goshinsa. Bakinsa ɗan ƙarami ne kamar na mace, kuma ja kamar wanda yake shafawa jan baki ko wani abun makamancinsa, se dai sam ba haka bane. Hannunsa ɗauke da wasu littattafai na Addini kasancewarsa ɗaya daga cikin manyan Malaman Addini a makarantar, ba ma a makarantar kaɗai ba hatta a yankin yana ɗaya daga cikin manyan Malamai, duk da ƙarancin shekarunsa da ba zasu wuce 25 ba amma da yake gada yayi daga wajen mahaifinsa da ya kasance Babban Malamin Addini a garin. Se hakan ya sake siyo masa soyayya daga wajen mutane da dama, ba ga mata ba ba ga maza ba, kowa ƙaunarsa yake. Se dai kuma shi ɗin mutum ne me matuƙar bauɗaɗɗen hali, idan dai har ka fahimce shi a bai_bai ba zaku taɓa zauna wa lafiya ba, zamanku baze taɓa daɗi ba, se dai kuma idan har ka fahimce shi shi ɗin mutum ne me matuƙar kirki da sanin darajar ɗan adam. Abu ɗaya ne yake sakawa a kasa fahimtar inda ya dosa kasancewarsa miskili na ƙin ƙarawa, hatta da magana bata dame shi ba, za a iya masa wani abun ko kuma ayi abu a gabansa amma ba ze ta tanka ba. Sam baya ɗaukar raini, ba ya ma bada fuskar da za a raina shin shi yasa ba a taɓa jinsa da wata ɗaliba ko ɗalibi ba, dan idan dai har ze shiga aji abin da ya kai shi ne kaɗai yake yi, daga nan ba lallai ma wata magana ta shiga tsakaninsa da wani ba. Sallamarsa da muryarsa me amo da daɗin sauraro yayi cikin ajin, se dai kasancewarsa mutum mara fara'a a halitta ya sa fuskarsa a cunkushe take, dan kuwa za a iya kiran Gwani Affan da "Sad Man" Gaba ɗaya ajin suka haɗa baki wajen amsawa, se ya sako kansa cikin ajin cikin nutsuwarsa da tayi matuƙar haɗuwa da tsarin halittarsa. Ɗan lumshe manyan idanunta Lulu tayi tana jin yanda ƙirjinta ya buga sanda ya shigo cikin ajin, tsoron da ya lafa mata tun ɗazun yanzu ya dawo sabo, amma saboda ƙeƙashashshiyar zuciya irinta ta se ta sauke ajiyar zuciyar tana tsara abin da zata faɗa idan ya zo kanta a karɓar haddar.

Tsayawa nayi ina kallan ikon Allah sanda na ji bakinsa ya furta

"Ina Hafsa Abba?" Dan ban taɓa tunanin za a iya yi masa Hausa ya ji ba ballantana ya furta da bakinsa saboda daga yanayin halittarsa har shigarsa da larabawa yayi kama, se dai maganar da yayi ce ta sanyani fahimtar tabbas bahaushe ne, se dai a cikin hausawan irin na daban ɗin nan ne, wanda za a iya cewa sun samu komai, musamman ma dai a wajen Gwani Affan da aka ba shi kyau, da kuma ilimin Addini, se dai kamar kowanne ɗan adam ba za a rasa wani abun da ya rasa ba, ban san a wajen Gwani Affan ko akwai abin da ya rasa ba dan ni dai a fili ban gan shi ba. Zumbur Hafsa Abba ta tashi bayan maganar da Gwani yayi, tace a hankali

"Malam ga ni!" Ba tare da ya kalleta ba ya jinjina kai sannan ya fita daga ajin, bin bayansa tayi zuwa wajen tana ɗan gyara tsayuwarta.

"Se gobe idan Allah ya kai mu zan kar6i hadda! Ki sanar da en ajin"

"Toh Malam" Daga haka ya juya ya soma takawa dan barin wajen cike da nutsuwa, se da ya ɓacewa ganinta sannan ta juya ta koma ajin ta sanar da su saƙon shi. Lulu kaɗai tayi farin ciki da hakan, dan kuwa gaba ɗaya en ajin farin ciki suke da dawowar Gwanin ajinsu. Haka dai ba dan sun so ba suka haƙura. Yau ɗin sosai take cikin farin cikin tun da suka fito daga makarantar murmushi yaƙi barin baby face ɗinta. Didi na lura da ita kuma ta san dalili amma bata kulata ba. Maganar da Fatima Kabeer ta yi ne ya sanyata kallanta

"Masoyiya baƙuwa na miki magana tun ɗazu." Juyawa Lulu tayi ta kalli wadda Masoyiyar ke magana a kanta, itama ita take kalla tana murmushi, yaƙe tayi kana tace

"Sannu!" Daga haka bata sake cewa komai ba. Daidai lokacin da suka zo zasu rabu, se suka yi sallama da yake ita baƙuwar zuwan makociyarsu Fatima Kabeer ne ya sa suka yi hanyarsu.

"Wallahi ƙawar nan ta ki ta min Fatima, kyakkyawa da ita kamar ita tayi kanta" Murmushi Fatima tayi tace

"Allah koh?" Ba tare da tunanin komai ba Abida tace

"Wallahi kuwa dama zaki haɗani da ita!" Kallanta Fatima tayi cikin er rashin fahimta da maganar ta ta sannan tace

"Ban gane ba?" Dariya Abida tayi kana tace

"Mu yi ƙawance mana"

"Uhmm ai ga ki ga ta, dan in dai Masoyiya ce wallahi dizgaki za ta yi" Se da Abida ta tsaya ta kalli Fatima har se da Fatiman ta tsargu sannan tace

"Shi kenan!" Daga haka babu wadda ta sake cewa komai suka cigaba da tafiya.

_Claremont California U.S
Tunnel Rd Berkeley
East Bay Hotel_
Chapter 3 · 0% Book details