Sashe 20
A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read
"Duk yanda ki ke kwatanta min ita ai ta ninka hakan sau 10 Abida. Wannan aba haka kamar ita ta yi kanta? Kalleta fa don Allah? Ke na ninka miki kuɗinki sau 3, dan na tabbatar yau ɗin nan akwai ƙurewa daɗi maleji.." Ladi ta faɗa tana sakin wani shu'umin murmushi har lokacin idanunta na kan Lulu tana binta da wani irin kallo kamar tsohuwar mayya..
https://chat.whatsapp.com/BClMNPwWybg2n3oRvtemv8
*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*
By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_
*CHAPTER ONE*
Page_13
___Cikin er rashin fahimta Lulu ta ɗaga kai ta kalli matar da a lokacin ta miƙe daga inda ta ke zaune ta soma takowa zuwa wajen Lulu, lokaci ɗaya tana furta
"Karɓi yaron ki ajje mata shi.. Me ya sa ma ku ka taho da shi?" Ta yi maganar sanda ta ƙaraso dab da Little. Ta saka hannu ta riƙo hannunsa. Da sauri ya fuzge hannunsa yana ɓata fuska gami da shigewa jikin Lulu. Tashi ta yi daga kan kujerar tana sake riƙe hannun Little da ke kuma ƙanƙame hannunta. Se dai ga mamakinta se ta ji matar na faɗin bayan ta kalli Abida
"Ɗauke shi ki fita da shi, ze hanamu rawar gaban hantsi.." Ba ta ƙarasa maganar ba se kuwa Abida ta ƙaraso ta kai hannunta wajen Little dan ɗaukarsa. Iya ƙarfinsa ya saka ya fashe da kuka daidai lokacin da Lulu ta gama fusata da su gaba ɗayansu. Cikin fushi tace
"Wai meye haka ne? Ina za ki kai Little ɗin? Ina ruwanki da shi? Idan za ki gama abin da ya kawoki gidan nan ki zo mu tafi toh. Idan kuma ba za ki tafi ba ki faɗa min na kama hanya.." Da mamaki Ladi ta kalli Abida cikin ƙasa da murya tace
"Ki na nufin ba ta san abin da ya kawota gidan nan ba?" Se da ta ɗan yamutse fuska sannan tace
"Da ta sani da ba ki ganta cikin gidan nan ba.."
"Ohhh.. na gane.." Ladi ta faɗa tana jinjina kai daidai lokacin da ta maida dubanta kan Lulu. Ɗan lumshe idanunta Lulu ta yi saboda yadda ta ga Abidar da matar na neman maidata er iska, ta yi magana ma sun juya suna wasu maganganun. Hakan ne ya sanya ta saɓi Little da ke matse ƙwalla a kafaɗarta sannan ta yi hanyar fita. Da sauri Ladi ta yi maza ta tare hanyar tana faɗin
"Na shiga ukuna, ina kuma za ki je?" Cikin rashin fahimtar dai Lulu tace
"Ban gane ba? Nan ɗin gidanmu ne da in zan fita za a tambayeni inda zan je?" Ta tambaya tana watsa mata wani kallo. Ajiyar zuciya Ladi ta sauke tana tunanin ta yadda za ta ɓullowa Lulun, dan daga yadda ta ke magana kaɗai ta fahimci ita ɗin ba irin matan da ake kawo mata ba ne. Dole se ta yi da gaske, idan ba haka ba tana ganin wannan ganimar haka za ta tafi ba tare da ta ƙaru da komai ba. Cikin rarrashi ta soma faɗin
"Kin ga ki kwantar da hankalinki, ba wani abun tashin hankali ba ne. Kawai fa harka ce ta jin daɗi da za ki samu kuɗi bayan jin daɗin.. Ke Abida zo ki buɗa mata bayani yanda za ta fi fahimta.." ta ƙare maganar tana kallan Abida. Kamar wata doluwa Lulu ta bi Abidan da kallo tana jin yadda jikinta ya yi wani mahaukacin sanyi, har wani rawa ya soma yi, dan kuwa hatta hannunta da ke ɗauke da Little se da ya ka sa riƙe shi, ta ɗan sassauta riƙon sanda shi kuma ya ke sake riƙeta kamar ze shige cikinta.
"Kin ga Afaaf, ki kwantar da hankalinki, ka da ki tashe shi. Ba fa wani abu ne me wahala ba, kawai dai za ku ɗan shafe mintuna ne fa da Jakadiya ku ɗan jiyarwa kanku daɗin jikinku.." Runtse idanunta Lulu ta yi sanda bugun zuciyarta ya ƙaru, yanayin yanda jikinta ke rawa ma ya ƙaru. Ta kai wajen second 20 idanun na ta a lumshe, wanda farin ciki har ya soma cika zuciyar Ladi da ke ganin Lulun za ta amince da buƙatarsu. Se dai me? Cikin sakannin da basu wuce 3 ba Lulu ta buɗe idanunta a kan Ladi da kuma Abida da ke kusa da juna, muryarta har rawa take yi sanda ta soma faɗin
"Ashe Abida ke ɗin mutuniyar banza ce? Ashe mutuniyar wofi ce ke mara tsoron Allah? Ashe shi ya sa tun kallan farko da na miki na ji ba ki min ba? Na kasa sakin jiki da ke duk saboda yanda zuciyata taƙi aminta da ke? Amma ki ka yi yadda za ki yi, ki ka yi amfani da muguwar zuciyarki da muguwar manufarki ki ka sakani na soma kulaki, har na iya ɗakko jiki na rakoki wani wajen? Tirr da irin wannan rayuwar taku. Tirr da wannan ƙazamar rayuwar taku da ba kwa jin kunyar idanun mutane ballantana ku ji tsoron Allah. Wa'iyazubillahi, Allah ya kiyasheni da aikata aikin danasani da nadama.. Matsamin na wuce.." Ta yi maganar sanda ta sake rungume Little.
"Babu inda za ki je. Ai kin shigo kenan.. ta yaya ma zan bari ki shigo gidan nan sannan na barki ki fita ba tare da na ji kalarki ba? Tun da Abida ta ke kwatanta min ke na ji na ƙawatu da son ganinki. Daga kuma lokacin da na yi ido biyu da ke na ji duk wani burina na son ganinki ya ruguje, abin da kawai na ke buƙata shi ne kasancewa da ke.." Ladi ta faɗa tana matsowa kusa da Lulu. Wani irin hawaye me zafi ne ya zubo daga idanun Lulu na dama na tsantsar takaici da kuma sake yin tirr da halin Abidar da Ladin. Ganin yanda ta ke matsowa kusa da ita ne ya sanyata saurin matsawa gefe tana faɗin
"Ka da ƙazamin jikinki ya soma gangancin taɓani.. ki matsamin na fita idan ba haka ba wallahi zan miki abin da ba za ki taɓa mantawa da Afaaf a rayuwarki ba.." Lulu ta faɗa duk da yanda take jin ƙirjinta na wani irin bugawa cike da tsoro.
"Bana son taurin kai Malama Afaaf.. kawai ki yi biyayya, salin alin za ki fice daga gidan nan da kuma damin kuɗi a hannunki.." In ji Ladi tana sake matsawa kusa da Lulu
"Ke ce matsiyaciya ba ni ba, ke kuɗi suka dama.." Kafin Lulu ta ƙarasa faɗa ta yi gefe saboda yadda Ladi itama ta yi gefe dan so take kawai ta ƙwace Little daga hannun Lulu sannan ta san yanda kuma za ta yi da Lulun. Hakan ne ya janyo Lulu ta taka ƙafarta se ta yi baya kamar za ta faɗi, ta yi saurin dafe Little tana ƙoƙarin miƙewa a kan ƙafarta Ladi ta riƙota. Kuka Little ya sake fashewa da shi saboda yanda ya tsorata, ga wannan matar da ta gama tsorata shi. Se kuwa ya shiga rera kukan shi. Abin da ya sake ƙular da Lulu kenan, ta saka hannunta bayan tattaro duk wani ƙarfinta ta tunkuɗa Ladi gefe. Se kuwa ta yi baya ta zube a wajen. Da sauri Lulu ta yi amfani da wannan damar ta tura ƙofar ɗakin ta fice da wani irin saurin da ba ta san tana da shi ba, a ranta tana karanto duk addu'ar da ta zo bakinta. Yunƙuri Abida ta yi dan bin bayan Lulu, Ladi da ke zaune a ƙasa zaman daɓaro ta yi saurin dakatar da ita ta hanyar faɗin
"Ka da ki bi ta. Batta na san yanda zan yi da ita.. Na ganta koh? Kuma ta min. An kawo min ita ta gudu.. Za ki ga abinda zan mata.." Ta ƙare maganar tana sakin wani murmushin takaici, musamman idan ta tuna wannan samu da rashin. Ga Lulun har gida amma ta tafi ba tare da ta aiwatar da abin da ta ke da niyyar aikatawa ba. Sosai ƙirjin Abida ke bugawa, ita ba rashin samun damar da Ladi ba ta yi bane yafi tsaya mata a rai ba. Gaba ɗaya tunanin ta ya tafi ne ka da Lulu ta je ta faɗi abin da ya faru, ta kuma tona mata asiri a cikin unguwa bayan babu wanda ya santa da wannan hali. Lura da yadda Abidar ta shiga damuwa ne ya sanya Ladi faɗin
"Ka da fa ki sakawa kanki damuwa. Ni ce fa Jakadiya Ladi.." ta ƙare tana tuna surar Lulu da ta iya gani daga cikin hijab, uwa uba kyau da kuma yarintar da ke tattare da ita, suna cikin abubuwan da suka ɗauki hankalinta na son kasancewa da ita.
... A hankali ya saka hannunsa ya tura ƙofar ɗakin da Abeeyn ke kwance da sallama a bakinsa. Duka suka amsa masa sallamar. Ya ƙaraso ciki, se dai da mamaki kan fuskarsa ya ke kallan Abba. Cike da mamakin dai ya furta
"A'ah Yallaɓae...!"
"Uhmm Malam Affan sannu da dawowa." Ɗan lumshe kyawawan idanunsa ya yi kaɗan kamin ya nemi waje ya zauna saboda gajiyar da ya yi kana yace a nutse
"Yawwah.. Ashe ba ka tafi ba. An gode Allah ya bar zumunci.."
"Aou ka san abin da ya yi kenan?" Ummeey da shigowarta kenan ta faɗa tana murmushi. Se ya kalli Ummeeyn da ɗan mamaki a kan fuskarsa, dan be fahimci a kan abin da take magana ba, ya girgiza kai yana faɗin
"Ummeey.." Daga inda Abeey ke kwance yace shi ma yana murmushin
"Ka godewa Allah ka godewa wannan bawan Allahn Affan. Ya hutasheka wahala dan kuwa ya biya kuɗin wankin ƙodar.." Da sauri Gwani ya kalli Abba cikin mamakin jin abin da ke fitowa daga bakin Abeeyn. "Ya biya kuɗin?" Ya tambayi kansa. Ya riga ya san Abban ba ze masa wasa a irin wannan abin ba. Hakan ne ya sanya shi sake kallan Abban yace
"Yallaɓae..?" Murmushi Abba ya saki kafin ya miƙe yana faɗin
"Dama jiranka na ke yi Malam Affan.. tunda ka dawo bari na tashi na tafi.. Allah ya ƙara afuwa ya sa kaffara.."