← Book details A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 37

Sashe 13

A Jini Take Izzata Part 1 Compleete Hausa Novel · about 8 min read

"Ke dai fita ki tabbatar." Se ta fice daga ɗakin da sauri cike da zumuɗin son ganin Abban nata.

"Abba sannu da zuwa." Ta faɗa sanda ta zauna a kusa da shi tana murmushi. Se ya kasa ƙin amsa mata saboda fushin da ya taho da shi yace

"Yawwah.."

"Abba na yi kewarku sosai." Ta faɗa tana kwaɓe fuska da iya gaskiyarta.

"Je ki ɗakko kayanki ki wuce mu tafi." Abba ya faɗa, ita sam bata kawo komai game da maganar Abban ba, hakan ne ya sanyata miƙewa dan zuwan Abban ya sa ta tuna yanda tayi kewar gida.

"A'ah Yaya lafiya kuwa?" Mami ta faɗa tana riƙo hannun Lulu. Abin da ya dakatar da ita kenan, se kuma itama ta juya tana kallan Abban

"Ba lafiya ba. Daga yau ta gama zuwa ko ina, gwara ta zauna a gabana na dinga ganin duk wani abu da take yi." Da sauri dukansu suka buɗe ido suna kallan Abban. Anya kuwa da gaske Abban yake? Me Lulun tayi? Me aka ce masa tayi? Jan hannunta Mami tayi dan zama a kan kujera, se ta zame ta zauna a ƙasa, yayin da Mamin ta zauna a kan kujera tana kallan Abba tace

"Me aka ce maka tayi Yaya? Me ya faru?" Shiru Lulu tayi tana jin yanda jikinta ke rawa, musamman yanda ta ga lokaci ɗaya yanayin Abban ya chanja kamar ba shi ba, har idanunta se da suka kawo ƙwalla, dan kuwa kafin Abban yayi fushi da su ana daɗewa.

"Ashe abin da take yi kenan a makaranta? Ni zata zubarwa da mutunci? Afaaf ni zaki zubarwa da mutunci?" Abba ya ƙare maganar yana kallan Lulu. Zuwa lokacin oily eyes ɗinta sun gama cika taff da ƙwalla ƙiris ya rage ta zuba. Sosai ƙirjinta ke bugawa, tana tsoron fushin Abban, dan a lokacin da yayi fushi se ka ji ka tsani kanka. Kafin ya sake cewa komai Mami tace

"Wani abu aka ce maka tayi Yaya? Hala basu faɗa maka abin da suke yi mata ba? Wallahi nan yarinyar nan ta dawo gida tana kuka kamar wadda akama mutuwa. Ni maganar ma da nake cewa nayi zan maka magana a cireta daga makarantar, ko anan unguwar ne in sama mata wata ta shiga, tunda dai ba iya makarantar ce kawai a duniya ba. Wallahi cin kashin da suke wa Lulu yayi yawa, nan ta zauna tana faɗa min abubuwan da ake mata kamar nayi mata kuka. Haka kawai sun tsaneta babu gaira babu dalili." Ta dakata anan. Kusan second 10 sannan Abba yace

"Kin gama?" Shiru Mami tayi tana yin ƙasa da kanta, dan ta san ma'anar wannan tambayar tasa.

"Nace kin gama?" Ya sake tambaya.

"Ka yi haƙuri Yaya.." shi ne abin da ta faɗa. Se a lokacin ya sauke ajiyar zuciya sannan yace

"Ke! Tashi ki je ki shirya ki fito mu tafi."

"Amma da baka tafi da ita ba don Allah. Idan ma wani abun tayi ni me iya yi mata faɗa ce." Ta faɗa sanda Abban ya miƙe. Ya san idan yace ba zata dawo ba be kyauta wa Mamin ba, dan haka yace

"Zata dawo tukunna. Amma yanzu kam se na ga kamun ludayinta." Shi ne abin da Abban ya faɗa yana yin gaba.

"Shi kenan. Na gode." Mami ta faɗa. Se ta juya ta kalli Lulu bayan fitar Abba ta kama hannunta zuwa cikin ɗaki. Janta tayi cikin jikinta ta rungume kana ta soma faɗin

"Ka da ki damu kanki, halin Abban naku ne baki sani ba? Shi faɗansa kin san dai na lokaci ɗaya ne koh? Daga zarar ya wuce shikenan. Saboda haka ki samu ki bashi haƙuri, zan zo gidan da kaina na ɗaukeki mu dawo." Ita dai Lulu saurararta kawai take yi ba dan tana fahimtar abin da take faɗa ba. Da kanta Mamin ta haɗa mata kaya, har lokacin Jadwa na baccin takaicin da ya ɗauketa. Har compound Mami ta rakosu cike da kewar Lulun. Haka dai suka shiga mota, ta ɗaga musu hannu suka bar gidan. Ita dai Lulu ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne dan har lokacin jikinta a sanyaye yake da Abban.

... A ɓangaren Bad Man kuwa, tun lokacin nan da ya kwanta bacci, se da ya ɗauki fiye da awa 3 sannan ya tashi. A nutse ya shiga buɗe sexy eyes ɗinsa da suka sake lumshewa saboda baccin da yayi, su a maimakon su yi rashin kyau, se ƙara kyau da suka yi na musamman. Ya kalli cikin ɗakin da yake kamar ne neman wani abu. Se kuma a hankali ya zura ƙafarsa ƙasan gado, ya saka takalmi sannan ya sauko yana ɗan lumshe ido, tun yanzu har ya soma missing na kayan maye, dan haka ya zama dole ya samarwa kansa mafita. Kai tsaye toilet ya faɗa, ya ɗauki fiye da 30min yana wanka kamar me shirin chanja fata, sannan ya fito yana ta zuba wannan ƙamshin nasa kamar na ko yaushe da ke ratsa zuciyar me shaƙarsa. Kamar ko da yaushe yanzun ma cikin riga da wando ya shirya, se dai wannan karon ma cikin crazy jeans ya shirya. Ya riga ya saba duk sanda ya fito daga wanka ya kan tsaya ya chanja ɗan kunnen da yake sakawa, yana shirin juyawa wajen da ya saba ajje su, se ya tuna nan ɗin fa ba California ba ne. Ɗan ƙaramin tsaki ya saki yana sake jin rayuwar Nigeria na sake fice masa a rai. Kawai se ya ɗauki face cap ya ɗora a kan kyakkyawar sumar kansa da ke kwance kamar wadda aka shafawa mai. Tsaff ya gama shiryawa, ya fito sak a Bad Man ɗinsa, se dai abubuwan da ba'a rasa ba waɗanda be yi amfani da su ba dan kasancewarsa a Nigeria. Ɗakin Mom ya wuce kai tsaye, dan ya san ta daɗe tana jiransa. Idan yaso in ya fito se ya je wajen Mommah su gaisa. Shi ya riga ya saba, ko ina ze shiga kai tsaye yake shiga babu sallama, hakan ne yasa yanzun ma a haka ya shiga, hannunsa ɗaya cikin aljihun wandonsa. Wannan ɗin sam ba damuwar Mom bace, tunda dai ya shigo shi kenan. Dan haka tasowa tayi cikin jin daɗin ganinsa tace

"Oyoyo my Boy, yanzun nan nake so na zo na tasoka, baccin haka ba ka ci abinci ba ya isa." Ɗan murmushin gefen baki yayi wanda ya mugun ƙawata fuskarsa sannan yace

"So gani dai.." ya faɗa yana soma takawa. Sallamar da aka yi daga bakin ƙofar ne ya sanya Mom kallan ƙofar, yayin da shi kuma ya cigaba da takawa cikin tafiyarsa me cike da kuzari. Cike da mamaki take kallan Hajiya Sa'adah da er aikinta Atine da ke shigowa cikin ɗakin. Wani irin takaici da baƙin ciki ne suka kamata lokacin da ta hangi warmers a hannun Atinen. Daidai lokacin da yake ƙoƙarin zama idanunsa suka sauka a kan Hajiya Sa'adah, se ya miƙe da murmushi kan fuskarsa ya ƙarasa inda Mommahn ke tsaye, yana zuwa ya bata side hug yana faɗin

"I missed you Mommah." Daskarewa Mom tayi ta kasa ko da ƙwaƙwƙwaran motsi ne. Murmushi Mommah tayi tace

"Missed you more Areef. Ka dawo lafiya?"

"Yeap!" Ya faɗa a gajarce bayan ya koma gefe ya tsaya yana kallan wayarsa da kira ya shigo cikinta. A hankali Mommah ta ɗaga ido ta kalli Mom da har lokacin take tsaye, ta riga ta san halin Hajiya Sa'adahn, duk yadda aka yi wani abun take shirin yi. Ita bata san me tayi mata ba, bata san me yasa bata san alaƙarta da ɗanta ba. Ita har ga Allah, Allah ma ya ga zuciyarta tana ƙaunar Areef ɗin ne da zuciya ɗaya, amma Mom ɗin ta kasa fahimta, dan ba tun yau ba take raba duk wata alaƙa da zata shiga tsakaninsu, se kuma aka samu sauƙi ya tafi ƙasar waje karatu, shi ne abin yayi sauƙi. Tana so ko yaya ne ta yiwa Areef ɗin wani abun na burgewa a matsayinsa na wanda ya dawo gida daga can wata ƙasa, se dai ta san ba lallai mahaifiyarsa ta bar shi ya shiga ɗakinta ba. Hakan ne ya sanyata ɗakko abin da tayi masa ɗin zuwa ɗakin nata, ta ba shi a gabanta. Atine da ta gaji da tsayuwa ne ya sanyata faɗin

"Hajiya na ajje kayan ne?" Jinjina kai Mommah tayi tana kallan Mom tace

"Barka da wannan lokaci." Se ta maida dubanta kan Atine tace

"Ki ajiye ki fita." Cike da girmamawa Atine tace

"Toh Hajiya." Ta faɗa tana yin gaba. Cikin hanzari Mom ta saka hannu ta janyo hannun Atine da ƙarfin gaske tace cikin ɗaga murya

"Gidan uwarki zaki je?" Taga_taga Atine tayi kamar zata faɗi, tana ƙoƙarin ganin ta tsaya a kan ƙafafunta amma hakan ya citira, se kuwa ta yi baya, hakan ne ya bawa warmers ɗin da ke hannunta damar faɗuwa a ƙasa da ƙarfi. Cikin lokaci ƙanƙani faɗuwar da suka yi ya bawa abin da ke cikinsu damar tsarwatsewa cikin parlourn..

*♡☆A JINI TAKE☆♡*
*(IZZATA)*

By
_*ZARAH MAITAMA (Mhiz Innocent)*_

*CHAPTER ONE*

Page_09

___Kusan a tare dukkansu suka kai dubansu inda abincin ya zube. Ɗan runtse idanunta Mommah tayi har cikin ranta tana jin ɗacin abin da Mom ɗin tayi. A hankali ta mayar da kanta kan Atine da ke zaune a wajen kamar wadda aka koro, tayi zuru_zuru, cike da mamakin abin da Mom ɗin tayi, da kuma tausayin Mommah da ta tabbatar ta shafe awanni da dama tana yin girkunan nan duk dan Areef ɗin.

"Mu je." Mommah ta faɗa cikin sanyayyiyar muryarta me cike da nutsuwa. Bata jira Atinen tace komai ba tayi sauri ta fice daga ɗakin. Se a lokacin sannan Atine ta ɗaga ƙafafunta itama ta fice daga ɗakin ba tare da ta bi ta kan warmers ɗin ba. Ɗan lumshe ido Bad Man yayi yana cije lips ɗinsa na ƙasa, se kuma ya ɗan furzar da iska daga bakinsa sannan ya sauke ajiyar zuciya ya soma takawa dan ficewa daga ɗakin. Sam Mom bata lura da shi ba, se da ya wuce ta gabanta har ya kusa fita daga ɗakin sannan ta gan shi. Cikin sauri ta bi bayansa tana faɗin

"A'ah, Areefullah ina zaka je?" Ta ƙarasa maganar sanda tazo dab da shi.
Chapter 13 · 0% Book details